Showing 6001 words to 9000 words out of 438336 words
ke ɗaukata mai shiru-shiru. Har wasu kan dangantani da hakan da iya yardarsu. Basu sani ba idan aka taɓoni banda ragi banda ragowa sam. Na isa office ɗin MD, bayan nayi knocking sai da nai tsaiwar kusan minti ɗaya kafin ya bani izinin shiga ciki. Kallo ɗaya na masa na ɗauke kaina, dan mutum ne shi mai shegen son kallon mutane kamar zai cinyesu. Cikin son kawar da idanunsa dake yawo a kaina ya ce, “Zauna”.
Zaman nayi a ɗarare nace da shi, “Good morning sir”.
A taƙaice ya amsani da, “How are you?”. Batare da ya jira amsawata ba ya cigaba da maganarsa yana turomin wata ƙyaƙyƙyawar mujalla da wani envelope mai kama da invetion card. Bana ganin fuskar mutumin daya mamaye bangon farko na mujallar gaba ɗaya. Sai jikinsa dake sanye cikin wasu shegun suit sky blue zuwa ƙafarsa dake cikin cover shoes dake wani shining duk da kuwa a hoto ne. Zaune yake a kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya, hakan ya bani ɗan damar ganin hannunsa mai ɗauke da dogayen fararen farata dake riƙe da glass cup da guntun drink ke ciki. Sai zobe guda ɗaya mai ƙyau sosai a yatsarsa...
Duk da baifi a sakanni goma na ƙarema hoton irin wannan kallon ba a ɗan kamar fusace naji gyaran muryar MD a kaina. Saurin gyara yanayina nayi na maida hankalina gareshi, fuskarsa a ɗan ɗaure yana famar yamutsa fuska ya ce, “Ɗauka ki duba”. Ɗaukar nayi, sai dai ban kallaba yanzu na maida hankali garesa da nuna alamar shi nake saurare. Shima sai naga ya ɗan sassauta yanayinsa. Ya nuna ni da faɗin, “Samraah na zaɓoki ne saboda nasan zaki iya. Wannan mujalla ce ta TAURARINMU A YAU data fita jiya. A gaba ɗaya abinda ke cikinta ya ta'allaka ne akan matashin ɗan kasuwar nan da sunansa ke amsa kuwa a ƙasashenmu na Africa dama duniya a ɗan tsakanin nan. Wato *_AWWAB EL-MU'AZZ._* sai dai kowa yafi saninsa da *_MAASH_* ne. Maash ɗan arewa ne haifaffen garin Kano sai dai mazaunin jihar Lagos. Yana da tarin cibiyoyin kasuwanci a kudancin ƙasar nan dama wasu ƙasashen Africa. Hakama a ƙasashen turawan da larabawa yana da rassan kasuwanci. Amma abin mamaki bai taɓa kafa wani abunsa a arewacin nan namu ba. Hakan yasa mutanenmu sukai masa ca, suke kuma sukarsa akan hakan, har takai suna ƙalubalantar dukiyar tasa musamman idan akai dubi da ƙarancin shekarunsa. Duk da kuwa an san mahaifinsa nada kuɗi, hakama Kakansa sanannen mutum ne, sai dai ko kwatar abinda shi MAASH ɗin ke da a yanzu mahaifinsa bai mallaka ba. Kace nace ya sake yawaita a kansa ne a watanni uku da suka gabata, dalilin bayyanar Companyn sa na jirage dake jigilar mutane daga Nigeria zuwa ƙasashen ƙetare. Domin a farko jirage goma ne ciff suka fara aiki. Sosai manyan gidajen jaridu sun so tattaunawa da shi amma Maash yaƙi bada kowacce irin dama. A duk lokacin da hakan ta taso sai dai a tattauna da P.A ɗinsa. To nadai taƙaice miki zance a yanzu haka bayan ka-ce-na-ce da aka sha yimasa akan gudun arewa da ƙaruwa Mujallar nan ta fitar da bayanan buɗe ɓoyayyen katafaren company da kusan wata uku kenan ana aikinsa batare da mutane sun san na wanene ba a cikin Kanon nan. Company ne na ƙera motoci da babura da abubuwa masu yawa da suka shafi ababen hawa. Irinsa shine na farko a Africa, a duniya kuma na uku. Kuma Maash da kansa zai zo Kano bikin buɗesa. Hakan yasa tunda naga mujallar nan na shiga na fita sai da na samo mana invetion card ɗin shiga wajen, dan hatta ƴan jaridar da zasu halarci wajen a ƙa'ide suke. Dan haka na kwana nazari a daren jiya, na kuma hanga na hango a kaf gidan nan kece nake ganin zaki iya mana wannan aikin, fatanmu kiyi duk yanda zakiyi kisa Maash ya magantu a gaban ƴan jarida karo na farko dan ALLAH. Hakan zai zama ba ƙaramar nasara ba a garemu da ma wannan gidan namu baki ɗaya. Sannan ke a karan kamki ma wata sabuwar ɗaukakace da nike da tabbacin zata zamewa rayuwarki alkairi in ALLAH ya yarda.”
Wani irin nauyi naji kaina yamun, dan haka da ƙyar na iya fisgo kalma ɗaya akan harshena na furta. “Amma Sir kaifa kace bai taɓa yarda yayi hira da ƴan jarida ba. Taya kake tunanin ni zan iya samo wannan nasarar? Yaushe ma na fara aiki, wane matsayi na taka a cikinsa? Ni wacece da zanyi abinda manyan ƴan jarida gogaggu suka gagara yi cikin sauƙi haka?”.
“Ba cikin sauƙi bane Samraah. Sannan al'amarin ba iyawa bace ko kaiwa wani matsayi. Sa'a ce kawai kuma kowa da irin tasa a rayuwa. Nima ba ina ji bane wai lallai sai hakan ta kasance ba. Fata dai nake yi da jin yaƙinin zaki iya in sha ALLAHU”.
Shiru kamar bazance komai ba, kafin kuma na sauke nannauyar ajiyar zuciya. Na ce, “Shike nan Sir zan gwada na gani, ai da gwaji jirgin sama ya tashi sama daga bisa ƙasa. Amma dai bani kaɗai ce zanje wajen ba?”.
Ƴar dariya yayi a karo na farko, cikin tsokana ya ce, “Kada kice min ke ɗin matsoraciya ce mana. Bayan kuma kallon jaruma nake miki. Kallabi a tsakanin rawuna”.
“Humm Sir bazaka gane ba. Irin waɗan nan mutanen da suke jin tamkar ma duniyar su suke mata alfarma ba itace ke musu na basu fili a cikinta ba suna kallon mutane ne tamkar wasu dodannin tsaffi a rayuwa. Dan a kullu yaumin zaka gansu ne zagaye da masu tsaro a kowacce kusurwa ta rayuwarsu. Ni gaskiya bana son ƙasƙanci koda a wajen wanda ya fini ne”.
“Wannan itace ɗabi'a ta cikakken mutum ai Samraah. Duk wanda yasan darajar kansa haka ake so kuma ya kasance. Kada ki damu bake kaɗai zaki je ba. Hasalima ke aikin ki shine gabatar da shirin kawai. Akwai Davido da Mansoor da Khulsoom a tare dake. Yanzu sai kije ki tsara tambayoyin da zaki masa ki kawo min, ki nutsu sosai wajen tsarasun daga nan har zuwa Monday, kinga kinada kwanaki kusan huɗu kenan tunda yau muna alhamis. Kije da wannan mujallar domin duba abinda suka rubuta a kansa. Za kuma ki iya wani binciken a kansa ɗin dai koda ta hanyar yanar gizo ne ko wasu mutane. Hakan da zakiyi ne zai baki damar tsara abinda ya dace a kansa ɗin, dan ina fatan mu zama mune taurarin mako mai zuwa”. Ya ƙare maganar yana murmushi.
Nima dai murmushin nayi, dan ya ba ni dariya. “In sha ALLAHU zanje nayi nazarin Sir. Maybe ma kafin Monday ɗin kaga na tura maka duk abinda na tsara ɗin koda ta WhatsApp ne”.
“Masha ALLAH, ALLAH ya bada ikon hakan. Amma dai baki da matsala kibi komai a sannu tunda nunada kusan kwana goma kafin ranar”.
“To nagode Sir”.
Na faɗa ina miƙewa hannuna ɗauke da Mujallar. Harna fice a office ɗin ina jin idanunsa a kaina. A raina nace (Maye kawai sai dai kaci kanka kasha baƙin ruwa).......✍️
_Tofa masu karatu yaya kuke tunani akan wannan aiki da MD ya damƙama Samraah. Shin zata samu damar haɗuwa da wannan matashi mai wahalar sha'ani mai suna *Maash* ko kuwa?_.
_Idan ma ta haɗu da shi ɗin taya zata iya abinda wanda suka fita faɗa aji da gogewa akan irin aikinta suka kasa?_.
_Shin wai wanene ma *Maash* ɗin nan ne? Minene dalilinsa na gudun yarda ya bayyana asalinsa ga ƴan jarida. Miyyasa yake ɓoye kansa? Minene baya son a sani game da shi ɗin?_
_Duka wannan amsoshin suna a kundin littafin TSUTSAR NAMA... masu iya magana sunce wai ITAMA ƊIN NAMA ce. Kuzo ku mallaki naku domin jin abinda littafin zai zo muku da shi, domin kuwa ƙumshe yake da abubuwa masu ban mamaki, al'ajabi, makirci, soyayya, cakwakiya, zamba cikin aminci, tare da ɗan karan munafunci daga ɓangarori daban-daban._
*_In sha ALLAHU sayen nagari maida kuɗi gida😊😉😉😘😘🫡🫡._*
______________
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒊𝒙_
.......Zaune na kai jagwaf a kujerar zamana ina dangwarar da mujallar da MD ya bani a desk ɗinmu. Mujallar Ruƙayya ta ɗauka tana faɗin, “Woow kaga wani handsome guy anan. Sam G daga ina haka? Waye shi?”.
Baki na ɗan taɓe kaɗan batare dana amsa mata ba na shiga ƙoƙarin kunna computer ɗin gabana. Itama batabi takan jiran amsar tawa ba ta shiga karanta abinda ke jiki. Wata ƴar zaburowa tai da zazzaro idanunta waje tana faɗin, “Kutt Sam-G wannan ai Maash ne.”
Duk ɗagowa sauran abokan aikinmu sukai suma suna kallonta. Sai kuma suka maido kallonsu gareni kamar yanda take kallona. Ganin na ɗauke kai tamkar bamma san mi sukeyi ba yasa suka sake maidawa kanta tare da miƙewa suka nufeta. Rufuwa sukai akan mujallar suna karantawa su duka huɗun, jin yanda duk suka nutsu yasa na ɗago na kallesu, batare da nace dasu komai ba na warce mujallar a hannun Ruƙayya. Ƴar harara na sakar musu ganin duk yanda suka ɗago suna kallona. “Malamai kowa ya koma kan aikinsa. Kun wani zauna karanta abinda bazai amfaneku ba.”
Ƴar dariya Usman da Asiya da Khalid sukai, yayinda Ruƙayya ta balla min harara. Magiya Usman ya shiga min yana faɗin, “Sam-G Please ki bamu mu ƙarasa karantawa, anya kinsan kuwa wanene wannan na jikin hoton?”.
“ALLAH bazan baku ba kuje kuyi aikinku, mi sanin nasa kuma zai amfaneni da shi da zan damu da so.”
Magiya suka shiga mun nace bafa zan basu ba, dole suka haƙura suka barni badan sun so ba. Sai dan ayyukan dake gabansu. Nima nawa aikin na cigaba dayi batare dana sake bi takan mujallar ba. Haka muka cigaba da aikin gabanmu har lokacin tashi yayi. Tarkacena na shiga haɗawa domin wucewa gida aɗan gaggauce, dan nasan Mansoor na jirana. A karo na farko idanuna suka sauka akan fuskar mutumin dake jikin mujallar lokacin da nake ɗakkota zan saka a jakka. Duk yanda naso kauda idanuna hakan ya gagara, dole nai tsai ina kallon ƙyaƙyƙyawar fuskarsa. Sam a zahirance baya kamanni da ƴan Nigeria ma bare Kano, duk da kuwa muma munada ƙyawawan fiye ma da kamarsa, sai dai kuma yanda hasken fatarsa yake tsaka tsaki dan bai wani yi haske dau ba zaka iya kiransa ko haif caste. Abu mafi ɗaukar hankali a fuskar tashi siririn baƙin gashin daya zagaye kumatunsa har zuwa haɓarsa ya kuma zagayo ta bakinsa ɗan ƙarami kamar ba namiji ba. Sam babu fara'a akan fuskar, sai hasken idanunsa dake a wani irin salo kamar na mai jin bacci. Abin mamaki tsakkiyar ƙwayarsu blue-blue zaiba-zaiba bansan yazan kirashi ba, ataƙaice kamar dai na mage ko masu jajayen kunne oho duk yanda kuka fassara. Sai cikakkiyar girarsa mai faɗi. Sosai na sake waro idanu lokacin da nakai dubana ga sumar kansa. Kitso ne guda huɗu akan nasa a kusan tsakkiyar kan dan ta gefe-gefe an aske sai saisayayyen sabon gashin daya kwanta luf-luf baƙi siɗik. Daga ta bayan kunnensa kam a dai-dai dokin wuyarsa zanen tattoo ne anyi fuskar zaki. Kunensa ɗaya manne da ɗan kunnen stone daketa wani irin sheƙi da ɗaukar ido kalar sky blue mai garai-garai kamar diamond. Wani wawan tsaki da ban san dalilin yinsa ba naja ina mai tura mujallar a bag ɗin. Dan sam nikam abin bai mun ba. Ɗan musulmi haihuwar arewacin Najeriya cikin Kano ne haka tamkar wani jinin yahudawa. Toni wannan tunda ma ba wani kama yake damu ɗin ba sosai ai gara ma a dinga jinginashi da ƙasashen ƙetaran mu bar musu kawai yafi, dan gaskiya aka bincika kam a cikin iyayensa akwai wanda ba bahaushe ba ko nace ma ɗan Nigeria gaba ɗaya. Da wannan mitar na fita a office ɗin, dan kusan ma nice ƙarshe su Khalid duk sun fice.
Horn da Mansoor yayi min ne ya ankarar dani in da yake, da alama dama ni yake jira, dan ina shiga yayma motar key muka fice. Har muka fita a layin da station ɗinmu yake muka hau titi sosai babu wanda yay magana a cikinmu. Sai zuwa can Mansoor ya katse shirun namu da faɗin, “Madam duk gajiyar ce haka?”.
Cikin ɗan yatsine fuska na ce, “Kawai dai”.
Maimakon yaji haushi sai yay murmushi kawai, dan ya fahimci yau ɗin ƴan shiru-shirun ne a kaina. Dan ko ɗazu da muka haɗu dama bawani hira nayi sosai ba. Baiyi fushi ba ya cigaba da jana da hira, tun dai ina amsawa a sama-sama harna ware, dan akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanina da Mansoor. Muna a gab da isa anguwarmu na takalo masa maganar da Uncle yay min akan aure kamar yanda Yaya Musaddiq ya bani shawarar nayi. Kamar wanda ya ɗan razana ya kallan, sai kuma ya maida hankalinsa ga titi da sauri ganin nima shi nake kallo..
“Lafiya kuwa? Naga kamar ka razana?”.
Murmushi ya saki tare da ɗan dubana, sai kuma ya gangara gefen titi ganin yanda duk na wani tsaresa da kallo. Sai da ya kashe motar da ƙyau ya juyo yana fuskantata. Ɗauke nawa idanun nayi daga kansa. Murmushi naji ya saki mai ɗan sauti, sai kuma ya fara magana a hankali. “Dole ne na razana ai Baby, dan farin ciki ne da yazo min a matuƙar bazata. Kema kin san tsahon lokacin dana ɓata ina fatan jin wannan furucin daga bakin ki. Taya yau na jisa ba zanji kaɗuwar farin ciki ba. Ki godema ALLAH ma da ban saki kan motar mun daki fitila ba. ALLAH na gode maka da ganin wannan rana a gareni, ni Mansoor zan mallaki TAURARUWAR MATAN DUNIYA”.
(🤥Ni dai banda ni eh🥱).
Murmushi ne ya suɓuce min, na kauda kaina gefe inayi duk da kuwa akwai facemask a fuskata, harma da eyeglasses dakan ƙara fiddo tsarin ƙyawuna a duk sanda na saka shi. Ganin murnar tashi bazata ƙare ba ga shi lokaci na tafiya murya can ƙasa-ƙasa na ce, “Please ka tada motar nan magrib fa zai yi”.
“A'a Madam, barni na gama murnata dan ALLAH. Mansoor ne fa zai mallaki Samraah Gwarzo. Wani shagalin ma ai sai naje gida hajjaju”.
“To nidai kaini gidan, idan kaje sai ka cigaba dayi”.
Da ƙyar na samu ya tada motar muka tafi, bakinsa baiyi shiru ba har muka ƙarasa. Nidai na sungumi bag ɗina na fice ina cemasa sai da safe.
A falo na iske duk mutanen gidan. Amma babu Hafizzullah da Abbas, da Nabel, hakama Abba da alama bai dawo ba shi da Yaya Musaddiq. Koda yake shi dama Yaya Musaddiq sai kai ma wata baka gansa zaune a falon nan ba. Iyaka ya shigo ya gaida Abba da dare, daga haka ya koma ɗakinsa, abincin gidan ma yakan daɗe yanzu bai cisa ba duk da nauyin kawowa ta dawo kansa badan kuma Abban ya rasa ba sai dan haka Mum ta tsara ayi. Mum ta watso min wata muguwar harara da ta sakani tura baki ta cikin mask ɗina. Batare dana sake kallonta ba nace “Mum good evening”.
“Ko kuma good uwarki ba”. Ta amsa a fusace. Dariya sosai Baby da Bibaa suka kwashe da shi. Sai autansu dake ta aikin homework ɗinsa kamar ma bai san abinda ake a falon ba. Tsawa ta daka min kan nazo. A hankali na nufi gabanta na durƙusa, bamma gama kaiwa ƙasa ba naji saukar lafiyayyen mari daya nema gigitani, dan har eyeglasses ɗina sai da ya faɗi. Idanun kawai na rumtse da ƙarfi, sai dai naƙi yarda hawayen da suka ciko min ido su zubo. A fusace ta ce, “K dan uban uwarki har ni zan sakaki aiki ki tafi sabgar gabanki ki bar min?”.
Karo na farko na ɗan kalleta. Cikin danne kukan dake neman kufce min na ce, “Mum wlhy duk abinda kikace nayi ban tafi ba sai da nayi sa”.
“Oh ƙarya nake miki ke nan ko? Miyar da kika bari akan wuta uwarki ce tai fatalwa ta ƙarasa min?”.
Wani irin rumtse ido na sake yi ina cije lips. Babu abinda kemin ciwo a duniya sama da zagin iyayenmu da Mum kanyi. Kuma in har tayi hakan bana iya daurewa sai na mayar mata da murtani. Yanzun ma hakance ta kasance. Dan cikin kaushin murya da tsiwa na ce, “Mum ai kunsha tubarraki kenan, dan nasan duk abinda zai fito daga Ummie na mai albarka ne, to balle kuma ace fatalwarta, ai nasan albarkar sai ta ninka ma. Bara naje nai salla na sake mata addu'a dan gobe idan zatazo a fatalwar ta dafa mana har abincin ba ƙarasa miya kawai ba”.
Ba Mum ɗin ba hatta su Baby sagade sukai suna kallona. Nikam ko'a kwalar rigata na miƙe tsam. Batare dana yarda na kalla kowa a cikinsu