Showing 408001 words to 411000 words out of 438336 words
naka, kai cin zuciya irin taka Bab.....” kuka mai cin rai ya sarƙe Paah, hakama su Uncle Abdullahi kuka suke sosai a wannan gaɓar. Su dukansu suna maimaita masa inama ace ba shine mahaifinsu ba. Inama zasu iya canja ƙaddararsu. Wani irin ratsa zuciyar Baba prof kalaman yaran nasa sukeyi matuƙa, kodan basu taɓa haɗe kai sun masa hakan ba a tare ne oho. Komai fa yayi ne domin su, domin jin daɗinsu, amma a ƙarshe ma gashi suna kaico da kasancewarsa mahaifinsu. Kokuwa anzo gaɓar da shima zai ɗanɗani ɗacin hakanne oho. Sai kawai ya fara jijjiga kamar ɗazun, dole dai aka sakasu suka fito likitoci suka ƙara rufuwa a kansa. Kafin wani dogon lokaci abin ya rincaɓe matuƙa. Sai aman jini ta hanci ta baki. Haka suka kusa kwana a kansa, sai dai kuma babu tsumi babu dabara. Lokaci yayi. Prof an tafi ba'a nema gafarar kowa ba, zuciyar ma batayi nadama da yarda ta aikata ɓarna ba. Hatta ƴaƴansa kaico suke da kasancewarsa mahaifinsu, babu kokarin da ba'ai ba na ya kama kalmar shahada da suke karanta masa sai ma saɓanin hakan ke fita a bakinsa.
Su kansu likitoci da jami'an tsaron dake tare da shi jikinsu yayi sanyi. Yayinda kowa ke jifansa da ALLAH wada rai. Babu wanda za'a ambatawa mutuwarsa ya faɗi alkairi ko nema masa rahama. Sai dai a ce halinsa ya bisa. Wasu ma cewa suke sai kuma aje a tarar da abinda aka shuka.
Cikin matuƙar kuka Uncle Abdullahi ya ce, “Kaicon mu ƴan uwa, Kaicon mu. ALLAH yasa muyi dawwamammen tuba kafin mu koma garesa. Wlhy ƴan uwa ba'ata yaya rayuwarka ta ƙare ba ko yaya ƙarshenka ya kasance ne abu mai sauƙi. Ka cutar da mutane ka kwanta jiyya ko fuskantar wani iftila'i na rayuwa ne sakamakon ba ko ƙaddarar laifunka. Babban tashin hankali da bawa zai fuskanta a rayuwarsa bayan shuka mugayen ayyuka shine ya bar duniya batare da neman gafarar kowa ba kamar yanda mahaifinmu ya kasance a yau. Ya bar duniya ZUCIYARSA na mai kasancewa a bushe batare da rinisa ga UBANGIJI ba. Ya bar duniya jama'ar dake zagaye da shi a kusa ko nesa suna mai jifansa da ALLAH wadarai da murnar an rage musu mugun iri irin. Yabar duniya kowa naji a ransa shari'ar UBANGIJI tafi wadda za'a kwatanta yimasa anan duniya. Ya bar duniya ana ALLAH wadai da gagara nema masa gafarar UBANGIJINSA😭😭. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, ƴan uwa mun san minene raɗaɗin FITAR RAI kuwa? Mun san MINENE KWANCIYAR KABARI KUWA? Mun san MINENE TASHIN KIYAMA kuwa? Munsan MINENE WUTA DA ALJANNA kuwa? Ƴan UWA ni da ku duk bamu sani ba fa😭. Amma UBANGIJI ya mana nuni da su a cikin littafinsa mai tsarki a ayoyi daban-daban, MANZON ALLAH ya isar mana da saƙon tabbatattu ne kuma zamu kai garesu ko mun shirya, ko bamu shirya ba. Ko mun yarda, ko bamu yarda ba. Mi muke kallo ƴan uwa? Mi muke jira? Mi muke tsammani? Mi muke hange? Ina muke tunanin kaiwa?. Itafa duniya sunanta kawai DUNIYA. Ribarka da ita kawai ka BAUTAMA UBANGIJI, kayi biyayya ga MANZON ALLAH. Sai UBANGIJI ya baka ƙyaƙyƙyawar makoma domin RAHAMARSA da GAFARARSA. Dan ALLAH, dan ALLAH, dan girman ALLAH ƴan uwa mu tuba mana. Mu zubda mugayen ayyukanmu mu koma ga ALLAH. Kin san kina bin Bokaye domin biyan buƙatar duniya mara amfani a gareki, akan KISHIYA, ko Mallakar MIJI, ko Mallakar abokan zama, ko Mallakar ƴan uwanki, mahaifiyarki, oganki a wajen aiki, ogarki a wajen aiki ko kasuwa, family ɗinki ko na mijinki. Kin san kina ZINA, kin san kina MAƊIGO, kin san kina amfani da kanki wajen biyama kanki buƙata, kin san kina shaye-shaye, kin san kina gulma, kin san kina annamimanci, kin san kina zunɗe, kin san kina muguwar kissa wa miji dan ya tozarta abokiyar zamanki, kin san kina yaudara, kin san kina zamba cikin aminci, kin san kina cin bashin mutane, kin san kina kawalci, kin san kina cin amanar mijinki, kin san kina sata, kin san kina sakaci da tarbiyyar ƴaƴanki subi maza dan su samo miki kuɗi, kin san kina cutar mutane ta hanyoyi da dama, kin san kina! Kin san kina! Kin san kina😭. Ya kai ɗan uwa aikinka shine ɓata tarbiyan ɗiyan mutane. Kana matashi ko mai aure kasan yanda zaka yaudari yarinya da kuɗi ka aikata ZINA da ita. Ko ka bita ta ƙarfi, ko yara ƙanana da bama su gama sanin kansu ba. Kasan kana bin bokaye domin asiri yara su bika su soka. Kana bin bokaye dan oganka na office ko kasuwa. Kana bin bokaye dan neman mulkin duniya. Kasan kana LIWAƊI, kasan kana gallazama matarka a cikin gidan aurenka. Duk hakkin da ALLAH yace ka sauke nata kana tauyeta, bata isa kuma tace ka tauyeta ba sai kaci zarafinta. Kasan kayi sakaci da tarbiyyar ɗiyan da ALLAH ya baka matsayinka na mahaifi. Kasan kana sata, kasan kana gulma, munafunci, annamimanci, zunɗe, fallasa sirrin gidanka a majalisa, zamba cikin aminci, durƙusar da makwafcinka na kasuwa ko wajen aiki saboda kai ka tashi. Amsar cin hanci da rashawa ka bama wanda bai cancanci aiki ba ka hana wanda ya cancanta. Shaye-shaye, siyar da kayan maye, kawalci, neman matan mutane a social media, kune munafukan anguwa anzo neman auren yarinya ku ɓata saboda son zuciya, aboki ya kawo muku damuwar gidansa dan ku bashi shawarar banza ku ɗora shi bisa mummunar aƙida. Duk wani munafunce-munafunce a harkar siyasa kana gaba-gaba. Kaine! Kaine! Kaine. To kafa shirya, akwai babban aiki a gabanmu wanda baka san ranar da zai zama MAFARI gare ka ba. Akwai ɗan ɗanar raɗaɗin zafin fitar RAI. akwai kwanciyar KABARI da amsa tambayoyin cikinsa. Akwai tashin alƙiyama, akwai HISABI, akwai makoma mafi girman tashin hankali. Sune guda biyu, dole, dole, dolene a cikin biyu sai kin/ka kasance a cikin ɗaya. Wato WUTA ko ALJANNAH😭😭. Zaɓi ya rage tsakanin ni da kai. Dan haka mu kasance masu sassautama zukatanmu. Mu guji duk wasu mugayen ayyuka da ruɗanin duniya fa shaiɗan ke ɗibarmu garesu komai ƙanƙantarsu. Mu zauna da mutane lafiya dan bamu san randa malaki'an mutuwa zai ƙwanƙwasa mana ƙofofinmu ba. Mu sauke hakkin na ƙasa da mu, mu kiyaye cin hakkin koda iyalanmu ne. Mu bama ƴaƴanmu tarbiyya ta ƙwarai, mu nema daga hankalinmu, muyi haƙuri da kaɗan, wataran sai UBANGIJI ya bamu mai yawa ta hanyar da bamuyi zato ko tsammani ba. Ba sai munyi shirka, ko tauye hakkin wasu zamu samu arziƙi ko ɗaukakar duniya ba. Daga ɗaukaka har dukiyar ba masu amfanar damu komai bane idan har bamubi ALLAH da MANZONSA ba. Domin ita DUNIYA ba nan bane gidan GUMURZUN. LAHIRA itace kankat, sai mai RABO kuma ke samun tagomashi da ROMON dake can. Mu yawaita istigfari, mu yawaita istigfari, mu yawaita istigfari. ALLAH ka gafarta mana ka gafartama iyayenmu. Ya rabbi kasa muyi dawwamammen tuba kafin mu koma gareka. Ya rabbi kasa ranar mutuwar mu ta kasance ranar farin cikin mu, ya rabbi kasa kwanciyar kabari ta zama hutu a garemu, ya rabbi kasa mu kasance a cikin tawagar da MANZON ALLAH zai ceta yayi kuma alfahari damu ranar TSAIWA matsayin al'ummarsa. Ya rabbi kasa duniya a tafukan hannayenmu kada ta kasance a cikin zukatanmu. Ya rabbi kasa kar muje da arziƙi gaban UBANGIJI, hakkokin MUTANEN da muka zalunta a duniya ya cinyesu mu koma MATSIYATA. dan arziƙin DUNIYA ɗan uwa, ƴar uwa ba shine arziƙi ba. Arziƙin tashi da ayyuka ƙyawawa a ranar sakamako, amma haƙƙokin mutane ya cinyesu bayan an gama biyansu mu tashi taskarmu babu komai sai zunubansu da namu shine babban talauci😭. To ALLAH ka bamu ikon sauke hakkin mutane da ke a kammu, mu kuma nema gafararsu kafin mu koma garesa. Ya rabbi kasa mu karɓi LITTAFINMU da hannun DAMA😭😭. Ya UBANGIJI, ya RABBI, ya ALLAH kasa ALJANNA ta kasance makomarmu ni da ku da iyayenmu baki ɗaya 😭😭😭🙏”......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒆𝒍𝒆𝒗𝒆𝒏_
.......A safiyar yau kam ko ina da ina labarin mutuwar prof ta karaɗe. Uncle Abdullahi yazo har gida ya sanar mana. Shiru kawai falon yayi babu wanda ya iya cewa komai. Dama tun jiya da muka dawo daga wajensu kowa sukuku yake. Banyi zaton Ummie zatace muje ba. Amma sai tace muje. Yaya Awwab da Hayatu ma sun fita amma tace su dawo gida. Haka ta tasamu gaba mukaje can gidansa da za'ayi jana'izar sa. A yanda ya shahara, yay kuma suna a tsakiyar manyan ƙasar nayi zaton jana'izar sa sai tayi kamar ta fasa garin Lagos da kewaye. Amma sai me sam munje ƙofar gidan babu kowa. Sai tsirarun masu gadin gidajen maƙota dake tsaitsaye daga ƙofar gida. Sai ƴan sandan da suka kawo gawarsa suma dai nasan kunyar Uncle Abdullahi ne ya sakasu tsayawa. Sai mijin Aunty Mama. Sai kuma mu da mukaje, dan ko mu a cikin gidan iyakar mune kawai, Hajiya Mammah, Aunty Mama, Ummie, Mama Balki, Maman Malika, Malika, Ni, Bahijja, Aunty Falaq. Ba wannan bane kawai abin kuka. Ko sanda za'ai masa salla gaba ɗaya nakan sahu mutum tara ne. Paah, Uncle Abdullahi, Baban Hayatu, Mijin Aunty Mama, Hayatu, Awwab, Fahad da sai da Ummie ta masa dole sai wani mai gadin makwaƙwafcinsa. Sai TJ drivern Maash. Amma sauran mutanen wajen duk zare jikinsu sukayi cikin dabara ana fitowa da gawar tasa.
Wannan abu ya matuƙar saka Ƴaƴansa kuka. Mu ma ya tayar mana da hankali. ALLAH dai ka rabamu da mummunan ƙarshe. Ana dawowa daga kaisa makwancinsa Yaya Awwab ya aiko wai mu fito zamu wuce gida. Hakan yay matuƙar saka Paah kuka na tashin hankali. Ya riƙe hannun Ummie yanayi. Yayinda Fahad ke riƙe da ɗayan hannunta yana janta su tafi. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, wannan abu ya sake taɓa zuciyar kowa. Duk yanda Yaya Awwab ke gudun shigowa gidan sai da ya shigo. Kallo ɗaya yayma Paah dake durƙushe riƙe da hannun Ummie yana kuka ya ɗauke kansa. Jimmm yay a tsayen kafin ya tako a hankali zuwa garesu. Fuskarsa a gefe ya kama hannun paah ya cire daga cikin na Ummie. Batare da yace komai ba ya kama ta suka fita da ita. Sai Uncle Abdullahi da Baban Hayatu ne suka zo suka kama Paah aka shiga da shi ciki. Dan wani irin jan numfashi yake da ƙyar tsabar yanda yake kuka da kiran sunan Ummie. Haka muka tafi muna kuka muma. Dole salon tafiyar kam ya canja yanzu. Ummie da Fahad da Yaya Awwab ɗin suka tafi a mota ɗaya, mu kuma mika shiga sauran motocin muka bisu baya...
Sam gidan babu daɗi, dan tunda muka dawo Ummie ta kulle kanta. Hakama Yaya Awwab rufe kansa yay a ɗaki, duk yanda na dinga roƙonsa ya buɗe ina kuka ƙiy yayi. Itama Ummie Mama Balki nata lallashinta ta buɗe amma bata buɗe ba. Ashe shima Fahad nacan ya rufe kansa a Garden. Haka muka kasance da su har dare. Sai wajen ƙarfe ɗaya aka samu da ƙyar Ummie ta buɗe. Da ga ni har Falaq jikinta muka shige muna kuka. Itama sai ta rungumemu tanayi. Tunda abin nan ya faru babu wanda zai ce yaga kukan Ummie irin yau. Idanunta sun matuƙar kumbura luhu-luhu.
Haka muka koma wajen Yaya Awwab amma shi kam bugun duniya yaƙi ya buɗe. Har gabannin asuba ana abu ɗaya. Haka aka ƙyalesa dole dan kowa ya tabbatar bafa zai buɗe ɗin ba. Wannan yanayin ya haifar min da tashi da ciwo nima. Dan har washe gari dai Yaya Awwab yaƙi buɗe kansa. Su Uncle Abdullahi ma sun zo shi da Aunty Mama da Hajiya Mammah suna roƙonsa ya yafe musu ya buɗe amma ina. Haka dole aka taso Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain daga Kano. Dan Hayatu da yasan Maash ɗin zai iya abinda yafi ma haka yana gani sha biyu tayi yaƙi ya buɗe kawai ya tattara ya tafi Kano. Ƴar matsalar ma da suka samu a airport ce ta sakasu kaiwa Magrib kafin su iso. Lokacin da suka iso mai ɓalle ƙofa nata iya ƙoƙarin sa amma abu yaƙi yiwuwa saboda security ya saka ga ƙofar, gashi ba anyhow ƙofa ba. Ta windows ma kuma duk ya rufe babu ta yanda za'a ganshi.
Da wa'azi Malam ya fara, sannan ya koma nasiha, ya koma lallashi da ban baki. Da ga ƙarshe ya rufe da tsoratarwa akan in fa har ya bari zuciyar Ummie dake cikin damuwa. Ko ni dake matarsa da tsohon ciki tawa zuciyar ta buga, ko Paah ɗin da suke ganin sun sallamashi saboda laifin da yayima mahaifiyarsu tashi zuciyar ta buga yabar duniya batare da ya yafe masa ba shi kenan sai ya shirya amsoshin da zai bama UBANGIJI kuma. Daga haka muka bar wajen. Har mukai sallar magrib ana jiran ko zai buɗe, akai isha'i shiru, sai wajen ƙarfe tara sannan ya buɗe. ALLAH sarki uwa. Jikin Ummie har rawa yake taje ta rungumesa a jikinta tana kuka mai ban tausayi. Ya matuƙar galabaita dan haka dole likita ya fara ƙoƙarin duba shi. Ba kuma kamai ya jawo masa hakan ba sai rashin natural iska da abinci, sai rashin isashen barci saboda idanunsa sunyi lufu-lufu shima, dan ruwa kawai yake sha a ciki. Sai dai akwai Alkur'ani a ajiye da sallaya alamar dai abin alkairi yake yi a ciki ba fushin kawai ba. Wlhy nayi zaton idan ya buɗe zamuga ya fasa komai na ɗakin. Amma sai ba haka ba. Yana a cikin nutsuwarsa sai dai ya gama jigata da galabaita. Kowa yaji daɗin hakan, Malam kansa yanata sanya masa albarka da baiyi fushi irin na yahudanci ba. Faffasa abubuwa ko neman kashe kai, ko zama cikin matsanancin bakin ciki babu ambaton ALLAH ko miƙa lamura garesa.....
⭐⭐⭐⭐
Har ranar addu'ar uku babu wasu mutane ko ƴan zaman makoki. Hatta masu irin zuwa gaisuwar nan babu sam. Sai ma hotunan prof ɗin dake yawo a media kowa na faɗar albarkatun bakinsa marasa daɗi a kansa. Da wahala kaji wani ya masa addu'ar neman rahama. Sai sake tono mugayen ayyukansa da ALLAH wadarai, ya kuma zama abin yima mutane ishara...
A ɓangaren mu muma dai sai muce Alhmdllh. Dan kowa dai ya dawo cikin hankalinsa. Sai dai babu wani armashi a gidan sai oga Fahad dake cin amarcinsa. Sai kuma Malam dake ƙoƙarin haɗamu yay mana nasiha kullum da tunatar da mu muhimmancin iyaye da haƙuri da su. A hankali nasihar ta dinga ratsa kowannenmu har washe garin da akai addu'ar uku na prof dai Malam yazo da Paah gidan da duka ahalin prof ɗin. Ummie da yaya Awwab har sun miƙe Malam ɗin ya dakatar da su. Haka dole suka koma suka zauna badan sun so ba. Sai dai sun ƙi sake kallon ko sashen da Paah yake sam. Ni dai cikin ƙarfin hali na gaishesa, hakan da nayi sai Aunty Falaq ma da Bahijja suka gaishesa. Miƙewa mama Balki tai tana mana nunin mu tashi mu basu waje, amma sai Malam ya dakatar da ita yace duk mu koma mu zauna ai zaman namu nada amfani. Komawar mukai muka zauna jikinmu duk a sanyaye...
Shiru na kusan minti ɗaya kafin malam yay gyaran murya yayo addu'a. Sannan ya fara karanto hakkin mata akan mijinta, hakkin miji akan matarsa. Hakkin uba akan ƴaƴansa, hakkin ƴaƴa akan mahaifansu. Daga ƙarshe ya rufe da faɗin, “Kun san miyyasa na fara muku da wannan foundation ɗin?”.
Amsawa mukai mu duka da a'a. Ya jinjina kansa da cigaba da faɗin, “Saboda tun farko idan aka gagara kiyaye wannan haƙƙokin suke ruguza gida dama al'umma gaba ɗaya. Shiyyasa a mafi yawan lokuta zaka samu gidajen mu babu wani ginshiƙi dake riƙe da su. Maganar gaskiya ce ta taramu anan, mu kuma gyara abinda muka ɓata saboda munada sauran dama tunda muna a raye, bamu sani ba kuma ko sakan ne ya rage mana, minti ko awa ko kwana, sati, wata, shekara ko shekaru duk bamu da wannan ilimin. Shiyyasa a duk sanda ka aikata kuskure ka fahimci kuskure kayi yimaza kai Istigfari ko neman gafarar wanda ka zalunta ka kuma yi tuba na gaskiya da cikakken alƙawarin dainawa dan baka sani ba ko iya wannan damar ce kake da ita. Dan ko yana raye kaima kana raye sai ma ka dace da ya yafe maka ne fa. Ga shi kuma UBANGIJI shi baya yafe laifin wani akan wani. Alhaji Mu'azz zan fara da kai. Tun farko kaine baka gina gidanka a yanda ya dace ba, ba kuma ka sauke hakkokin da ya kamata ace ka sauke ba. Tabbas a dukkan abinda ka faɗa min kayi kuskure, kuskure kuma mai girma. Babu wanda baya kuskure a rayuwa, mu kuma maza mukan aikata fiye ga haka ga abokan rayuwarmu mata. Sai dai wasunmu kan ɓoye suje can suyi a gefe matan basu sani ba, ai ko laifi kake aikatawa ana ganin kayi alkunya ka kuma mutunta kanka idan ka ɓoyesa. Amma bayyana shi tamkar izgilanci ne ma UBANGIJI. Na tabbata ga Ummu-Hidaya ta riƙe ka a raine saboda girman kuskurenka na ƙarshe, abinda tayi kuma shine dai-dai, suma kuma yaranta basuyi laifi ba a dalilin juya maka baya da sukayi, hakan shi ya nuna suna kishinta, da mutunta ta dan koni nan abinda zanyi kenan akan