Showing 99001 words to 102000 words out of 438336 words

Chapter 34 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2215

nan akai knocking ƙofar ɗakin jiyyar tawa. Kai tsaye ya bada izinin shigowa. Cikin gurɓatacciyar hausa hamshaƙiyar mace fara tas ƴar duma-duma tayi sallama ta shigo. Kallon cikin ido mukaima juna. Sai kuma matar ta janye nata tana maidawa kan doctor tare da rissinawa tana gaisheshi irin dai girmamawar ƙabilu. Ya amsa mata da kulawa. Sai kuma ya nuna mata ni. Hankalinta ta sake maidowa gareni tana murmushi. Sai kuma cike da kulawa ta gaidani da jiki. Amsa mata nayi a ɗarare, dan haka kawai naji matar batai min ba. Sai dai me bayani naji doctor na mata akan ya gama komai daya dace sai ta wuce dani. Kallonsa nayi a firgice zanyi magana sai kuma zuciyata ta ƙwaɓeni dan na tuna aljananci da hatsabibancin mai asibitin. A take na canja yanayi kawai na fara masa godiya.
Nurse ɗin da suka kula da ni ne sukai min rakkiya har inda motar matar take. Babu abinda zuciyata take face luguden daka da saƙawa da kwancewa. Dole fa a wannan karon na kuɓutar da kaina dan wannan ce kawai dama ta ta ƙarshe ta ƙuɓuta a hannun mutumin nan. Saboda zuciyata ta gama tabbatar min shine ya turo matar nan, idan kuma bashi bane to tabbas zai iya min wani tarkon da ita kamar yanda akai min a Kano sanda na baro gidansa.
“Ya rabba aiko nayi mantuwa”. Na faɗa dai-dai ina ƙoƙarin shiga motar da Semi ta buɗe min. Su duka kallona sukai, amma sai na sake zabura cikin hanasu damar min tambaya ina faɗin su jirani zan ɗakko na dawo yanzun nan. Yanda naga babu wacce tai yunƙurin bina nasan sun fahimceni, daga haka nai gaba cikin ɗan sauri-sauri da sassarfa irin ta mai gaggawa. Ina tabbatar da na ɓacema ganinsu na canja hanya. Duk da a rikice nake hakan bai hanani nemawa kaina dakiya ba na fara tafiyar nutsuwa. Da ƙyar nake iya gane inda nake jefa ƙafa har ALLAH ya fito da ni wajen wasu fanfuna da igiyoyin shanya. Akwai mutane tsiraru a wajen suna wanki, da alama wajen an tanadesa ne domin haka. Caraf idona akan hijjab dake shaye a igiya, tuni na tuɓe na jikina na ja wancan na saka, ɗan kwalin abayar jikina na naɗa a fuska tamkar niƙab. Daga haka na fito a wajen. Tambaya na dingayi har ALLAH yasa na fito a cikin asibitin gaba ɗaya dan babu laifi babbane sosai. Ajiyar zuciya mai haɗe da hawaye ne ya kufce min ganina akan titi, sai dai babban tashin hankalin banda ko sisi a jikina banda kuma abin siyarwa sisi. Ba kuma zan yarda kowa yaban lift ba dan an koyan hankali a baya. Haka na shari titi ina addu'a, ganin nayi nisa sosai da Asibitin zuciyata ta tabbatar min da zafa su iya biyo bayana su ganni duk da na canja hijjab. Ai tuni na kauce a titi na shiga wani street da naga an rubuta a ƙaramin symbol dake farkon shiga. Ganin an rubuta street nasan komai nisa zan fita, dan haka na zage damtse sosai naita tafiya duk da rashin ƙarfin jiki ga kuma rana mai zafi dake dukana ban damuba.....

★★★....

Tun su Semi na irga mintuna har suka kusan haɗa ashirin. Mamaki ne ya kamasu, dan haka ɗayar nurse ɗin tace Bara ta duba Samraah ko ta ɓata hanya ne. Mintuna uku da wasu sakanni ta dawo a hargitse tana sanar musu itafa bata ganta ba. Sannan mutanen dake ata wajen sun tabbatar da bata dawo ba. Su dukansu har matar da doctor da aka je aka sanar mawa rikicewa sukayi. A take kuma doctor yay kiran Hayatu a waya...
Tako ina an bincike asibiti babu Samraah. Har cctv footage aka bincika, sai dai ta iya gaba kawai aka ga shigarta wajen inda ake wanki, kasancewar ta wajen babu camaras ɗin sai ba'a fahimci komai ba. Saboda ta canja hijjab sannan ta fita, ta inda ta fitan ma camara na wajen yana da matsala. Matuƙa Hayatu ya tada musu da hankali, gashi yayi kiran Maash ya sanar masa amma sai yaƙi ce masa komai. Ya kuma san minene ma'anar shirun ogan nasa, dan haka ya sake birkicewa ya birkita likita da Nurses har ma da matar nan da tazo ɗaukar Samraah ɗin. Kai dama kowa na asibitin dan har securitys basu tsira ba da sauran ma'aikatan...

💦💞💦💞💦

Ƙuuuuu!! Razanannen taka birkin ya karaɗe illahirin titin tare da sautin ihu mai firgitarwa. Ba hamshaƙiyar matar dake cikin danƙarereiyar motar kawai ba, hatta da mutane dake kai kawo a street ɗin tuni sunyo caa. Sosai Samraah da aka kusa kaɗewar ta matuƙar razana, dan durƙushe tai ta cusa kanta a cikin ƙafafunta nuna alamar sadaƙarwa kawai. Haushi da takaici ya saka mutane yimata caa da faɗa, dan duk wanda al'amarin ya faru akan idanunsu sun tabbatar da laifin ta ne ba mai motar ba. Ganin yanda wasu ke ƙoƙarin kai mata duka ma adalilin yanda har yanzu taƙi motsi daga durkuson razanar da tai yasa matar dakatar da su da sauri ta hanyar riƙota ta miƙar. Rawa jikin Samraah ya cigaba da yi har hakan na rinjayarta tamkar zata faɗi. Duk wanda ya kalleta yasan a gigice take har yanzu, dan haka matar ta shiga bama mutanen daketa faman hargowar zagin Samraahn haƙuri tare da jan hannunta ta buɗe motar a gefen mai zaman banza ta sakata. Sai da ta rufe sannan ta sake fuskantar mutanen da har yanzu sun kasa barin wajen..
“Kowa yayi haƙuri dan ALLAH kuma mu mata uziri. A yanayin halin rayuwar da ake ciki yanzu muma zamu iya tsintar kammu a fiye da yanda yarinyar nan take ciki yanzu. Tun dai ma komai bai sameta ba ai Alhamdullahi ko, sai muyi fatan ALLAH ya kiyaye gaba”.
Da kalmar (Amin) suka shiga amsa mata cikin nuna gamsuwa da yabama ƙyaƙyƙyawar zuciyarta, dan ba kowa bane zai iya yin abinda tai ɗin. Daga haka kowa ya fara watsewa itama ta shiga motar dan ta tsarema mutane hanya har wajen ya fara tara mutane musamman masu gadi na cikin gidaje nata fitowa. Bayan rufe motar ta ɗan kalli Samraah ta sauke numfashi mai kauri, batare da tace komai ba taima motar key cike da ƙwarewa ta harbawa saman titi da ƙyau. Tafiyar da bata gaza mintuna uku ba ta samu waje ta gangare gefen titin, dan bata son tai nisa da anguwar ta zamto kuma anan yarinyar take duk da ta ganta da niƙaff a fuska. A yanzu ma dai yarinyar kanta ƙudundune yake a cikin ƙafafunta, yayinda sautin shashshekar kukanta ke fita kaɗan-kaɗan.
“Ɗiyata a ganina godema ALLAH ya kamata muyi, dan da abinda yaso faruwa ya faru da ga ni har ke da ba wannan matsayin muke ba ai. Kiyi haƙuri ga ruwan nan kisha ki samu nutsuwa ko”. Shiru kamar bazata motsa ba, kusan cikar minti ɗaya kuma sai ta ɗago, Samraah ƙyaƙyƙyawace sosai ta yanda hawayen da suka ma fuskarta kaca-kaca bai hana bayyanar hakan ba.
Idanu na tsira mata mai haɗe da sauke ajiyar zuciyar dawowa hayyaci, sai kuma na kauda kai na, a hankali na furta, “Ba kukan tsorata nake ba Hajiya, kukan baƙin cikin rashin tabbatuwar abinda nai fata ne ya sakani kukan nan. Inama ace kin kaɗeni na huta da wannan rayuwar da babu komai a cikinta face kayan ƙunci da baƙin ciki da ruɗani. Inama ace kin kaɗeni na mutu banko shuraba na tafi tafiya ta har abada da babu dawowa na iske su Abbana. Hajiya dan ALLAH ki fitar dani a motar nan na sake tarar gabanki ki bi takain.....”
Cikin sauri ta katseni da faɗin, “Haba haba ɗiyata wace magana kenan! Miyay zafi haka da irin waɗannan furuci masu tsauri. Ai duk da mun san zamu mutu bama fatan mutuwar a kayinmu sai dai dan babu makawa sai ta zo ne. Amma muna addu'ar a koda yaushe ALLAH ya jinkirta mana kodan tara ayyukan alkairi da neman gafarar UBANGIJI da ga na sharri da muka aikata. Minene matsalarki? Miyasa kike ma kanki fatan mutuwa a wannan ƙarancin shekarun naki da zamu iya kallo a matsayin yanzu ma kika fara rayuwar, ko kika fara buƙatar ta? Idan ban shiga abinda ba hurumina ba ki daure ki sanar min ko zan iya fahimtarki da taimakonki da wani abu....”
“Ba taimako nake buƙata ba Hajiya, sannan babu wani abin sha'awa ko birgewa da ƙawatarwa a labarina ko bayana. Ganni ki barni a yanda kika ganni yanzu kawai.” na ƙare maganar da yunƙurin ɓalle murfin motar zan fice. Da sauri Hajiyar ta riƙoni tana girgiza kai. “A'a ɗiyata yi haƙuri ki saurareni”. Juyowa nai na ɗan kalleta, sai dai bance komai ba........✍️


_Kuyi haƙuri da wannan Please. Zuwa anjima idan na samu damar yin wani zan ƙaro muku. Wlhy abubuwane suka min yawa amma ina fatan kammalawa na dawo muku da ƙarfina😘😘_


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙_


........A hankali ta ɗan sakar min murmushi da faɗin, “Ko zaki iya mun alfarma”.
Cikin ƙosawa nace, “Tami?”.
“Ta sanin inda zakije yanzu?”.
“Ban san inda na nufa ba, sai dai ina fata da addu'ar koma ina ne ya kasance hanyar cimma ajalina”.
Ɗan jimm Hajiyar tai kamar mai nazari, sai kuma ta saki murmushi mai ban mamaki tana wani juya idanu cike da salo, “Bazan hanaki tafiya ba, amma zan so ki bani dama ta ƙarshe muje gidana, maybe zan iya nuna miki hanyar cimma nasararki ta barin duniyar kamar yanda kike fata”.
Idanu sosai na tsira mata tamkar mai son tankaɗe gaskiya da rairayeta akan fuskarta, kusan minti ɗaya na ɗan kauce zuciyata na ayyana min na bita na samu mafaka koda na wasu kwanaki ne, dan na tabbatar a yanzu na koma Kano makirin nan zai iya bina. Kuma Abba da su Kawu bashi ni zasuyi, amma yanzu idan na laɓe a bayanta zan iya kiran Yaya Musaddiq muyi shawara dan shiga Kano kai tsaye yanzu haɗari ne. Sai dai kuma ita kanta bawai ina jin na yarda da ita bane ba ma ai. Amma bari na gwada sa'ata mugani. fuskata na ɗago na ɗan kalleta da faɗin, “Kina so kiyi wasa da hankalina ne kawai Hajiya”.
Da sauri ta dakatar da in da faɗin, “Ko ɗaya ba haka bane ba. Mizaisa nai wasa da hankalinki ni kuwa, dama kawai nake buƙata daga gareki zaki tabbatar da abinda na faɗa ɗin in sha ALLAHU”.
Nan ma dai shiru nayi ina kallonta kawai, tai saurin faɗin, “Ki yarda dani koda na sati guda ne, idan kinga ba hakaba zaki iya ɗaukar mataki kowane iri”.
Shiru na sake yi na wasu ƴan sakanni kamar mai nazari, sai kuma batare da nace komai ba na dawo da jikinna cikin motar sosai tare da jawo ƙofar na rufe kamar yanda take. Sosai Hajiya ta sauke ajiyar numfashi da har ya bani mamaki, sannan ta ɗan kalleni, sai dai batace komai ba. Nima ban sake cewa komai ba ina dai addu'a a zuciyata ALLAH ya hanata nasarar cutamin, ALLAH kuma yasa ba daga ƙarƙashin makircin makirin nan Maash tazo gareni ba.

★(✷✷✷‿✷✷✷)★

Tunda Hayatu yake bai taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba musanman a yanzu da yake waya da Maash yana mai sanar masa guduwar Samraah daga asibiti. Dan Maash ɗin yayi wata ƴar tafiya ne ta gaggawa, tunda ya fara harkar business duk inda zai je yana tare da Hayatu, amma a wannan gaɓar ya barsa saboda al'amarin Samraah da ya kasance da ga shi sai shi suka sani.
Har tsawon mintuna biyu babu alamar Maash zai amsa. Kuma yana online. Hankalin Hayatu ne ya sake tashi, muryarsa har harɗewa takeyi wajen sake faɗin. “Wlhy nayi duk yanda kace Sir, zaman jiran isowarsu gidan kawai nake ma amma tai kirana wai basuganta ba. Ba laifina bane, ba daga ɓangarena bane aka samu kurkure ka yarda dani. Ka kuma bani izinin sanarma ƴan sanda na tabbatar tana cikin garin Abuja bata isa fita ba”. Shiru nan ma Maash yaƙi ya tanka. Wayar Hayatu ya cire daga kunnensa ya duba, har yanzu yana online ɗin dai tankawar ce bazai yi ba. Yafi kowa sanin halin Maash yanzu, dan ko iyayensa bazasu faɗa masa hakan ba. Ko motsi da idanu ogan nasa yayi yakan fahimci yaren balle. Ya tabbatar shirunsa a yanzu na ɓacin rai ne, kuma bazai tanka masa ɗin ba har sai idan shine yaso hakan. Hakan kuwa akayi, bai tanka masan ba shi kuma ya kasa yanke kiran saboda shakka, haka ya haƙura akaita ɗibar masa kuɗi har tsahon fin awa sai da shi uban gayyar ya gaji dan kansa ya yanke kiran sannan hayatu ya kai zaune cikin kujera jagwab dan tun ɗazun ko zaman ya kasa yi. Kansa kawai ya dafe yay shiru zuciyarsa na gudu. Dole ma duk yanda zai yi yayi dan gano yarinyar nan kafin cikar awanni ashirin da huɗu. Idan ba hakaba yasan akwai matsala.....

💞💞💞💞

Wata shegiyar dariya Alhaji Sadisu mai agogo babban aminin Abba ya saki harda ƙyaƙyƙyewa. Cikin ƙuluwa da nuna jin haushi kuwa Abban ya zuba masa idanu. Sai kuma ya yunƙura zai tashi amma Alhaji Sadisun ya riƙosa yana faɗin. “Afuwan afuwan Imamu. Wlhy abin naka ne zabban dariya. In kana abu sai naga kamar wani ɗan yaro bai mai garjejen saurayin ɗa kamar Abbas ba. Yo banda abinka Gwaggo ai gata tamaka wlhy. Ka buɗe bakin aljihu kawai malam musha biki ai ba wuce auren kai ba. Dama dai kaine kaso maida kanka pastor zama da mace ɗaya shekara fin ashirin bayan ALLAH ya baka dukan rufin asiri. Yo ALLAH na tuba da ana yin fin huɗu da ba tuni nayi ba”.
“Amma dai ai na sanar maka matsalata ko Alhaji Sadisu. Kuma kaina shaida ne akan halin Jalilah tunda na gwada son ƙara auren a shekarun baya har sau biyu amma aka nema nakasa yaran mutane.”
“Yo dan ta samu nasara a baya sai akace yanzu ma ka karaya zata samu. Alhaji Imam zama namiji kaji, tun farko kai ne kake ɓata shirin dama da kake sanar mata da wuri. Kayi shirunka yanzu har sai ɗinyar makaho ta nuna a hannunsa sannan ka bada filin fara wasan jifa tunda tsoronta kake ji”.
“Humm bazaka gane ba kawai, amma zan iya yarda da shawararka akan ɓoye matan. In kuma hakan zata faru fa sai dai na nema auren a wajen kano.”
“Wannan duk mai sauƙine, kabar komai a hannuna kawai. Kai dai jeka ka fara shirin gyara inda amarya zata zauna nan da sati ɗaya zan maka jagora kai da kaina sai ka gode min saboda inda zan kaika wlhy”.
Murmushi Abba yay a karo na farko, dan haka kawai yake jin kuma batun ƙara auren na sake masa tasiri a zuciya....

🥱Hummm Abba cin amana ko.

_________★

Gida ne mai ƙyawun gaske madaidaici muka isa a anguwar mai tama kamar yanda na gani a symbol, dan komai najin daɗin rayuwar gani da ido a kwaishi. Ƙamshi da tsarin gidan yafi komai ɗaukar hankalina, dan haka nake ta ɗan kalle-kalle a kaikaice. A karo na babu adadi Hajiya da tuni takai zaune cikin ɗaya daga kujerun falon ta dubeni ganin yanda nai tsaye a farkon shigowa. Cike da kulawa ta ce, “Ƙaraso ciki mana ɗiyata. Kar kiji wani shakku ko tsoro, wannan shine gidana anan Abuja, sai dai bana zaman daya wuce sati biyu a cikinsa a duk ƙarshen shekara. Sai kuwa idan wani uziri ne ya kawoni nakanzo nai kwana ɗaya biyu har ma zuwa uku wasu lokutan na koma. A yanzu haka ma kwana biyu ya rage na wuce”. A hankali na haɗiye yawu alamar son cewa wani abu, sai dai kafin nace ɗin Hajiya ta katseni ta hanyar ƙwala kiran sunan “Janny!”.
“Yes Ma'am”.
Wata murya ta amsa daga can gefen wata ƙofa da hanyarta aka shirya kujeru da tebiri. Kafin na gama nazarin tsarin da kujerun dining ɗin sukayi da zamansu a wajen wadda Hajiya ta kira da Janny ta fito. Budurwa ce itama sai dai zata girmeni sosai, da gani shigarta da uban gashin attachment dake saman kanta ya isa baka amsar ba musulma bace. Cike da girmamawa Janny ta sake gaida Hajiya tana ɗan satar kallonna. Nuna ni Hajiya tai da faɗin, “Kije da ita ciki, tai wanka a bata abinci”.
Murmushi Janny tayi a karo na farko, cike da girmamawa ta amsawa Hajiya tana nufoni. “Sannunka”.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login