Showing 339001 words to 342000 words out of 438336 words

Chapter 114 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2152

ɗin ranar fa?”.
Murmushi kawai ya saki da ɗan jinjina min kansa batare da yace komai ba. Gaba ɗaya sai ma na gagara cewa komai dan mamakinsa. Harga ALLAH mutumin nan ya fara bani tsoro, sai kuma can da nai tunanin camara ya saka a ɗakin nashi yasa na ɗan ji nutsuwa. Abinda ya kunna a laptop ɗin ne ya ɗauka hankalina. Sai na nutsu ina kallo. Gaba ɗaya abinda ya faru jiya ne lokacin da suke shigowa gidan da Ummie. Kasa daurewa nayi sai da nayi dariya, tare da jan hancinsa ina faɗin, “Oh My Lion ashe kaima bakinka ya iya magana haka. ALLAH ya shirya Yaya Fahad wlhy, harda wani faɗin a dafasu a tukunya a baku kunci kuna kora ruwan companyn Maashh.”
Murmushi kawai yayi baice komai ba. Nima sai na cigaba da faɗin, “Amma Ya Awwab ka kalla yanayin Baba kuwa? Da Hajiya ƙarama? Sannan video ɗin waccan ranar ka kallesa?”.
Kansa ya jinjina min. Sai kuma a hankali ya furta, “Mi kika fahimta ke?”.
Ɗan jimmm nayi alamar tunani, dan bazan iya katoɓarar fitowa fili na sanar masa ainahin abinda ke'a raina ba gaskiya. Kakansa ne fa, tab ɗin ba ruwana.
“talk”.
Ya faɗa yana matsa hannuna.
Murmushi na ɗan masa da faɗin, “Uhmm inaga mubi a hankali kawai watarana zaka fahimta. Dan zata iya yiwuwa abinda ni nake tunani daban wanda yake gaskiya daban. Amma dan ALLAH ka amsa min abin nan ɗaya kuma yana cimun zuciya. Shin mutumin nan da naga ka zare wuƙa a jikinsa lokacin bikin buɗe Companyn ka kai ne ka kashe shi? Ko miya faru?”.
Ɗan murmushi ya saki a karo na farko, tare da kai hannuna dake cikin nasa kan mitsitsin bakinsa ya sumbata.
“Yau kuma aikin jaridar ne ya tashi?”.
Cike da shagwaɓa na ce, “Oh ALLAH daga tambaya”.
“Nima ai bance bazan amsa ba”.
Ya faɗa yana ɗago ido ya kallan. Sai kuma ya gyara kwanciya da maida su ya lumshe. Numfashi ya ɗan furzar da fara magana a hankali. “Mama ta baki tarihin gidan nan dan haka zan faɗa miki daga dalilin buɗe Company.”
Kaina na jinjina masa cike da zumuɗi. Cigaba yay da faɗin, “A tsakanin da Ummie ta samu lafiya aka ƙirƙiri samar da companyn Kano. Kusan ma itace ta zo da shawarar hakan dan mace ce mai matuƙar experience akan Bussines. Sai dai koda najema Baba da batun sam bai bada goyon baya ba shi. Sai ma illolin yin hakan daya nuna min game da ƴan arewa. Abin ya tsayan a rai na sake samun Ummie da batun amma sai ta balbaleni da faɗa tare da cewar umarni ai ita ta bani ba shawara ba. Dan haka nabi Umarnin aka fara samar da Company. Ban sani ba ko hakan ne ya ɓatawa baba rai sai ya fita daga batun gaba ɗaya. Ana gab da gamawa jikin Ummie ya ɗan fara motsawa. Hankalinmu ya tashi matuƙa muka shiga neman mai maganin nan na Togo amma babu shi babu alamarsa. Tun muna ɗaukar komai zai dai-daita har abu ta ɓaci sosai, abubuwa suka ƙara rikicewa. Haka dai cikin dauriya na ƙarasa gina wannan gidan na muka tare. Sannan na shirya batun buɗe Companyn Kano. Tun bayan sakowa da ga batun auren Paah da Hajiya ƙarama yanda take nuna damuwarta akan Ummie da ni yasa nake ɗan sakewa da ita. Har itama na koma kiranta da Ummy, ko bana gida takan kirani ko na kirata a raina ina jin bayan Mama kamar itama uwa ce. Dan hatta cin abinci takan nuna damuwarta da naci ko ban ci ba a duk sanda ta kirani. Hakama idan ina gida ko asibiti ta dawo a gajiye takan tsaya ta samar min abinda zanci hakan yasa na ƙara bata muhimmanci fiye ma da Paah da nake matuƙar jin zafi. Sai dai me a gaɓar bikin buɗe Company duk sai suka ƙi shirin halarta har Baba dan barin ma ƙasar yay shi. Raina ya sosu nai fushi na fita batunsu da ga ni sai su Hayatu da yarana muka tafi. Kwatsam an fara gudanar da taro lokacin da kike barin wajen akai kiran hayatu a waya. Ta gefen ido nake kallon yanda yake amsa wayar yan zufa, kafin ya sauke a daburce ya matso inda nake. Sai dai yana ta ƙoƙarin ganin ya saita kansa dan kar a fahimta. A kunne ya gwargwaɗa min kiran da Jaga yay masa da abinda ya faɗa masa, dan haka nai excusing kaina na shiga ciki Hayat ya biyo ni. Da taimakon wayar hayatu muka gano ɗakin da Jaga yake. Da farko na ɗauka set up ne akayi, sai da Jaga ya shiga sanar mana wanda ya sokesa da aikin da ya kawosa jikina da abinda aka aikosa yi a yau amma ya canja shawara shine aka kawosa nan ɗakin dan a kasheshi a kuma maida abun kaina. Dan haka cigaba da rayuwarsa nada muhimmanci garemu dan yana da muhimman abubuwa da zai faɗa mana da zasu amfane mu. Wannan daliline yasa nai ƙoƙarin cetonsa duk da Hayatu na nuna min na barsa ƙarya yake yi. Amma ban saurarensa ba. Ina ƙoƙarin zare wuƙar da aka saka masa ke kuma kika iso batare da mun sani ba. Ashe har muka fita da shi kina biye damu. Duk da dai a lokacin da nake fitowa a ɗakin ƙamshin turarenki yasa naso na farga da ke, amma hankalina ba'a wajen yake ba dan haka na fice kawai. Ansha matuƙar wahala kafin samun rayuwar yaron, sai dai da yake ALLAH ya ƙaddara akwai sauran kwananasa gaba yasa ya warke kamar komai bai faru ba.. Ambatar sunan Grandpa ɗina a wannan ranar da shi Muktar Jaga yayi da ita Lawisa yasa na tabbatar da gaskiyarsa dalilin zuwan sa Kano a bazata har hirar da yay da ke. Tun daga lokacin nai doubling question mark ɗin dana sakama kowa a kansu. Nasa ya zama biyu. Na kuma janyema Lawisa sosai . Wannan video kuma ya tabbatar min da inahin fuskar ita Lawusar dai ce ba wata ba..”
A hankali hawayen da naketa riƙewa suka silalo min. Muryata na rawa na ce, “Hajiya ƙarama?”.
Kansa ya jinjina min alamar eh kawai. Wasu hawayen ne suka sake ɓulɓulo min. Cikin sake ƙanƙamesa na ce, “Yaya Awwab kayi haƙuri, amma wlhy zuciyata na bani sune suka kashe Abie da Babana......”
Da wani irin mugun sauri ya ɗago idanunsa da launinsu ya canja gaba ɗaya ya kalleni. Kaina na jinjina masa nima cikin tabbatarwa na ce, “Tabbas Yaya akwai ƙamshin gaskiya a magana ta. Dan na bibiyi videon ɗin nan da ƙyar tare da tankaɗesa da rairaiye sa. Kuma alamu sun nuna Ummie tasan wani abu shiyyasa ya durƙusar da rayuwarta zuwa wannan yanayin”.
Ai sosai ya tashi zaune gashin jikinsa na wani mimmiƙewa. Muryarsa har rawa take wajen faɗin, “Samrh miyyasa kikayi wannan tunanin?”.
“Yaya hujjoji da yawa. Dan kasan jami'in tsaro, da lauyoyi, da likitoci, da ƴan jarida al'amarinsu na kamanceceniya da juna. Saboda komai nasu yana tafiya ne a bigiren bincike. Shiyyasa zakaga a mafi yawan lokuta indai masu wannan ayyukan sun san abinda suke basu da wahalar fuskantar case irin wannan da saurin kama bakin zaren sa.”
Hannu ya kai saman yay wani kalar shafosa tamkar mai sharce ruwa ya yarfar. Bawai yau ya fara irin wannan tunanin ba shima. Sai dai a kaf bincikensa bai taɓa samun wanda ya ƙarfafa wannan hasashen nashi kamar ita ba a yau. Dan yanda ta fassara abin da confidence abin a duba ne..
Yunƙurawa yay zai tashi na riƙosa da sauri. “Yaya ina zaka je?”......✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don *_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒔𝒊𝒙_


.......“Ina son naga Ummie”. Ya faɗa da alamar ran ƴan maza ya ɓaci. Kaina na girgiza masa da sake damƙe hannun nasa na ce, “No Ya Awwab ba yanzu ba. Ummie da bata bukatar kowane irin matsi daga garemu akan son sanin gaskiyar al'amarin kamar yanda doctor ya faɗa al'amarin ta daki-daki yake buƙata. Dole mu cigaba da haƙurin binta mataki-mataki dan akwai abinda itama take shiryawa, kar kuma ka manta ya sanar mana ba komai ya dawo kanta yanda ya kamata ba a yanzu. Sannan tanama naka takun tankaɗa da rairaya ne shiyyasa taƙi fitowa fili ta gaya maka koda abinda ya rage a zuciyarta ne. Dan haka mizai hana muyi wani abu domin gabato da komai a gaggauce”.
Idanu kawai ya zuba min batare daya amsa ba. Ban damu ba na cigaba da faɗin, “Ban san tsare-tsaren ka ba. Amma a nawa tunanin ya kamata kayi wani abu saboda dalilai biyu. Na farko matsayin Baba prof mahaifin Paah. Bafa abune ƙarami ba fiddo da ainahinsa ta ɓangarenka kai tsaye ko ɓangaren Ummie. Hakan zai kawo rabuwar kan family ɗin nan, dan koba komai sunan mahaifi yake amsawa a garesu. A kai kanka ma bar ganin ba komai bane wlhy sai ka jigata matuƙar jigata dan jini ya wuce wasa. Sannan babu alfanu duniya ta raja'a akan rikicinka da Family ɗinka. Hanya zaka bama abokan gaba na bayan fage suci tuwo a kanka tako wane fanni. Kasan dai masu iya magana sunce, DAUƊAR GORA CIKI KA SHATA. Dan haka kamar yanda ka fara yaƙin ta hanyar sunƙuru, tofa mafitar ɗayace a ƙarasashi ta hanyar TURNUƘU FAƊAN IBILISAI. yaro bai gani ba balle ya raba. Ma'ana mu zuba kamar yanda suka ɗauki shekaru suma suna zubawa. A maimakon baƙin fenti ya shafe ka, ruwan sama ne zai wankeka tatas ya kuma wanke Ummie su da bakinsu su faɗi ainahin abinda suka shuka, idan ma tonama kan nasu asiri sukai wa duniya sune suka zaɓi hakan. Ya kaga wasan zai kasance”.
Na ƙare maganar da kashe masa ido ɗaya. A mamakina sai naga kawai ya saki murmushi da cije lips ɗinsa. Hannunsa ya dunƙule tare da miƙo min🤜🤛 Nima kawai sai nayi yanda yay ɗin muka buga. Da sauri na janye nawa ina yarfarwa da faɗin, “Shiiii azaba wanan hannu kamar rodi”.
Ƙaramin murmushi yayi da ɗan ɗallamin lips kaɗan da yatsarsa. Sai kuma kawai ya jawoni jikinsa ya rungume tsammm. Ajiyar zuciya muka dinga saukewa a tare. Na ɗan motsa zanyi magana a hankali ya ce, “Shiiii bana son surutu”. Sai kuma ya ɗaukeni cak yay bedroom da ni. (Ba sai kunji miya faru ba kuma ehe😉 dan naga fans ɗin bily kun cika sa ido😌🥱😝🏃)

Lallai yau Samraah taci tuwo a kammu bari mu ware🏃🏃🏃🏃, danginta kuma har daku shinnnnnn😂😝?.

💢🌿💢🌿💢

Ƙarfe goma na dare Baba prof da Hajiya ƙarama suka kama hanyar station. Dan dama tana asibiti tun bayan sallar magrib. Ta can ma Baba prof ɗin ya ɗauketa kasancewar da kansa yay driving abinda ya jima baiyi ba. Amsar tuƙin hajiya ƙarama tayi. Kasancewar al'amarin hanya ce daga babban jami'in da yafi Uncle Abdullahi faɗa aji yasa tun a gate aka tarbe su. Baba prof ya yankema zuciyarsa sai ya fara jin tabakin commondo da tabbatar da gaskiyar Hajiya ƙarama sannan ya fitar da shi, dan ba fitar da shi ɗin ne mai wahala ba, amma maganganun Hajiya ƙarama suka canja wancan tunanin nasa. Yana son tabbatarwa, idan gaskiya ta faɗa shi da kansa zai saka a ɓatar da Commondo tun a daren yau. Idan kuma ƙarya take zai saka a fiddashi batare da saninta ba. Daga ƙarshe hukuncin da yay niyyar ma Commondo zai sa Commondo ɗin ya maidashi a kanta.
Kamar yanda yake nasa tsarin a zuciya itama yana yin nata ne. Dan tayi waya da Dr Khunal yanzu haka zuwa gobe abinta data biya maƙudan kuɗi ita da Baba prof ɗin domin Maash zai iso a daren yau. Za kuma tayi aiki da shi akan Maash kamar yanda suka tsara tun farko, da shi Baba prof ɗin da Mu'azz. Ummie kuwa nata tanadin na musamman ne. Shiko Commondo ta riga ta gama bada kwangilarsa. Jannifer ma Baba prof zai ƙarasa mata ita shiyyasa ta azashi a keken ɓera.
Tunaninta ya katse lokacin da aka shigo da Commondo da Jannifer hannayensu duk da Handcuffs. Ga raunuka a jikinsu dake tabbatar da Dukansu akai babu jinawar nan. Dan bayan la'asar Uncle Abdullahi ya bada umarnin fara tuhumarsu amma su duka sunƙi cewa komai saboda damar da duk suka ƙudiri aniyar bama iyayen gidan nasu na yau kawai. Idan basu zo ba zuwa gobe zasu fara buɗe aiki. Shiyyasa suka jure da dukan bawai dan basa jin zafi bane ba ko ciwo...

Cikin tsawa jami'in daya kawosu ya nuna musu ƙasa matsayin wajen zama. Sannan ya koma daga ƙofar ɗaki ya tsaya dan yasan basu da wata hanyar guduwa tako ina office ɗin zagaye yake da jami'an tsaro irinsa. Daga Hajiya ƙarama har baba prof kallon Commondo da Madam Jannifer sukeyi kamar yanda suma suke kallonsu kallo irin na ƙurilla...
Kusan mintuna biyu kafin Baba prof ya janye nasa idon cikin gyara zama da kafe Commondo da ido ya ce, “Commondo ya akai aka faɗi a ragaya?”.
Murmushi Commondo yay da jinjina kansa. Sai da ya kalla gefen Hajiya ƙarama ya furta, “A ɓaɗinance talalace! A zahirance kuma ɗaurin goro ne!”.
“Akasin lissafi kenan fa”.
Baba prof ya faɗa cike da waro idanu.
“Na dukkan lissafi ne ma aka samu a wannan gaɓar oga. Dan shi macijin cikin ciyawa idan har yay kala da ciyawar sai yayi illa batare da ma'abocin taka ƙafa ya farga ba. Rafi da kogi zasu iya haɗa tafiyar wucewar ruwan cikinsu a hanya ɗaya. Amma shi kududdufi da gulbi koda suna maƙwaftaka akai rami a tsakaninsu ba lallai ruwan ɗaya ya ɓulla a cikin ɗaya ba. Dan ramin su baya kogo kamar na rijiya”.
Cikin ɓacin rai Hajiya ƙarama ta tare numfashin Baba prof dake ƙoƙarin yin magana. “Amma kun san magana cikin duhu haramunne a wannan tafiyar tamu. Anan duk ɗaya muke. Dan itama Jannifer abokiyar cin mushe ce. Banga dalilin ɗaure zance ba bayan muna neman hanyar gudu tare mu tsira tare ne a wannan gaɓar. Idan kuma har kukace wasan na nuna zalama ne, to karfa ku manta ku duk biyun nan linzamin dokin Lawisa ne. Musamman ma kai ɗin nan”. Ta ƙare maganar da nuna Commondo.
Wani shegen murmushi Commondo ɗin ya saki. Cikin ɗage gira ya furta, “Lawisa! Ke ƙaramar giwace, ragon layya kawai yay dogon miƙi zai iya yaddaki a dokar jeji. Ashe baki shirya wasan ba da ƙyau amma kikayi tunanin tararsa. Shi zuciyarki bata baki tabbacin ko Giwa ta faɗi tafi ƙarfin wawason ƴaƴan damisa ba. Shike nan, tunda kince muje a buɗe, muje ɗin, kin san dai ni bishiyar dabino ne wlhy bani ƴaƴan banza. Dan ko a ɗanyena nake rububin cina akeyi”.
“Kamar yanda kasan nafi ƙarfin damisar takarda. Sannan ni uwar bakirikice ba yarinya ba. Duk wanda ya sanni a cikinta ya ganni ba raino na akai ba. Miyyasa ka shirya cin amanata?”.
“Saboda kema naki shirin kenan?”.
“Amma kasan komi nayi akwai dalilinsa?”.
“Kamar yanda kika san nima bana komai sai da dalili. Miyyasa na ɗaukeki Hadari zaki maidani hazo?”.
“Ohooooooh!! da ƙyau!”.
Baba prof ya faɗa yana wani kwashewa da dariya da tafa hannaye. Gaba ɗayansu juyawa sukai suka kallesa. Duk kuma sai suka sha jinin jikinsu. Cikin daina tafin da musu nuni da hannu ya ce, “Ku cigaba mana, miyyasa zaku bari kuma?”.
“No oga relax. Kada ka ruɗar da kanka kadai san makircin wannan wawuyar”. Cewar Commondo da sauri. Da saurin itama Hajiya ƙarama ta cafe da faɗin, “Sai dai wawaye. Kai ni fa a wannan gaɓar banƙi a mutu ba har liman wlhy. Dan na gaji da tafiya da maciya amana waɗanda kansu kawai suka sani. Na kuma gaji da barin jakai ina dukan tanki.”
“Oh really?! To ai Lawisa ke ce babbar mai cin amana a cikinmu. Dan kece kika nunama kowa tashi ta fisheshi. Oga shine ya jawoki a wannan tafiyar ya kuma maidaki abinda kike a yau amma har kike tunanin watsar da shi...”
“Hahahaha!!! Commondo! Commondo!! Commondo!!. Lallai kai jaki ne na yarda. Wai shin kana yin duk wannan ne saboda tunanin wannan abun zai iya fiddaka a wannan wajen? To lallai kayi kuskure dan anzo gaɓar jifar gaffiyar ɓaidu. Dan anzo gaɓar da shi ɗin ma takansa yake bazai iya maka komai ba. Idan ma lissafin barin nan ɗin kake to ka bari, dan zama daram

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login