Showing 225001 words to 228000 words out of 438336 words

Chapter 76 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2178

Batare da yace komai ba ya shiga ƙoƙarin haɗa tea dan akwai babban basket mai murfi dake cike da kayan shayi kala-kala da su chocolate da kullum Hayatu baya gajiya da sayowa. Yo ni Hayatu ai zance tunda dai shine ke zuwa da su. Banda jiya da bai zo ba ɗayan yaron nan nasa da har yanzu ban san sunansa ba ya kawo snacks. Tea ɗin ya haɗa a zatona shine zai sha, har na fara gulmarsa a zuciyata sai naga ya miƙa min mug ɗin. Tsayawa nayi kawai ina binsa da kallon mamaki, dan haka muka ƙurama juna ido. Kusan minti ɗaya muna a haka kafin ya janye nasa da suke juyewa golden ƙwayar tsakkiya na zama siririya a wani irin salon yuuu ya ɗan lunshe su. Nima nawan na ɗauke da sauri ina haɗiyar wani yawu mai kauri dan gaba ɗaya jinai maƙogwarona ma ya bushe. Kofin ya ƙara miƙamin kansa a gefe, sai kuma ya miƙe.
Haka kawai kallon nima yay matuƙar min tasiri a cikin jiki da ma jinina, dan haka na gagara sake kallon inda yake har ya buɗe ƙofar ya fita. Ajiyar zuciya mai nauyi na sauke tare da rumtse idanuna na cije lips da ƙarfi. Tea ɗin na cigaba da sha da ɗan zafi-zafi batare dana san abinda nake ba. A haka aka sake buɗe ƙofar, a zatona shine dan haka na gagara ɗaga ido na kalli wajen. Sai da mama Balki ta rangaɗa sallama sannan na ɗago da sauri fahimtar itace.
Inda nake ta ƙaraso cike da tsokana take faɗin, “A lallai ɗiyata ta fara samuwa. Yau kece da haɗa shayi da kanki batare dana sha fama ba kina bata fuska da korafin bakinki ba bu ɗanɗano. To UBANGIJI ya ƙara sauƙi.”
A hankali nace Amin, dan a zatona bata haɗu da wannan pepper ɗin mutumin ba, sai naji hakan yamun daɗi. Sai dai me, bayan kamar mintuna biyar da zaman Mama Balki sai gashi ya sake dawowa tare da doctor. Miƙewa Mama Balki tayi fuskarta ɗauke da murmushi tana faɗin, “Har an kammala Alhaji ƙarami?”.
Cikin girmamawa, muryansa can ƙasa ya ce, “Eh mama sai ku shirya”. Jin abinda ya faɗa ɗin ya sani ɗagowa da sauri na kallesa. Sai muka haɗa ido. Da gudu na janye nawa na maida kan doctor dake min magana ɗan ji nake kamar ma kowa zai gane abinda ya faru tsakaninmu yanzu. Tambayoyi tamun tare da bani shawarwarin yanda zan kula da jikina yanda ya kamata har komai ya ƙarasa dai-daita. Duk bayan kwanaki biyu kuma zata zo har gida koni nazo asibitin za'a dinga sake dubani. Dan ba yau suka so sallamata ba. Sake ɗagowa nayi da mamaki sashen da yake. Yana tsayen dai har yanzu sai Mama Balki ce ke fita da kayayyakin mu tana dawowa alamar a iya ƙofa ake amsarsu. Yanda ya maida hankalinsa akan wayar hannunsa sai naji nutsuwa da alama baya jin duk abinda doctor ɗin ke faɗa. Taimaka min doctor tayi na sakko a saman gadon, hannunta riƙe da nawa ta ce, “Muje ki ɗan tattaka ƙyaji daɗin ƙafafunki tunda kwana da kwanaki kina zaune waje ɗaya babu ko babban motsi. Kaina kawai na jinjina mata, ta ɗauki hijjab da Mama Balki ta ajiye sabo ta saka min da kanta. Har ƙasa hijjab ɗin ya kaimin kamar wanda nake amfani da su a gida. Sai naji daɗi sosai dan yaushe rabo. Ta gabansa mukazo muka gitta bai kallemu ba bai kuma motsa ba har sai da muka fice gaba sannan. Kusan ƴammatan Nurses ɗin nan da suka dinga kulawa dani dasu aka ɗunguma min rakkiya har gaban mota. Sosai motar tai min ƙyau, banyi tunanin yana bayanmu ba, sai da muka iso ina sallama da Nurses ɗin da doctor naga an buɗe masa ya shiga, ba'a rufe ƙofar ba alamar ni ake jira. Ji nai kamar na fasa kuka, dan hakan na nufin a kusa da shi zan zauna kenan. Babu yanda zanyi, dan doctor da kanta ta taimaka min na shiga. Sai da aka maida ƙofar aka rufe har Mama Balki itama ta shiga gaba an ma tada motar muna shirin barin asibitin sannan na lura da shegen karen nan nasa dake tacan jikin waccan ƙofar. Wani irin fasa ƙara nayi tare da daka tsalle na faɗa jikinsa a matuƙar firgice, bazaki gane yanda nake masifar tsoron kare ba wlhy Bily.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒆𝒆𝒏_


......Da uban sauri TJ ya taka birki dan shima firgita yayi, hakama Mama Balki, ya juyo zaiyi magana da sauri ya kauda kansa dan gaba ɗaya Samraah ta koma saman jikin ogan nasa ne. Mama Balki ma kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kanta tana Murmushi. Shiko gogan tun faɗa masa jiki da tayi idanunsa kawai ya lumshe saboda ƙarar da tai har cikin tsakkiyar brain ɗinsa ya jita. Shi mutum ne da sam baya son hayaniya. Taɓasan da Laalah ya ɗan yi yana gurnani ya sa ya fahimci abinda take ma tsoro. Lumsassun idanunsa ya buɗe, ya ɗan kalli Laalah ɗin sai kuma ya kalleta. Tayi masifar cikuykuye sa daga ita har ƙatoton hujjab ɗinta. Shi sai abinma ya so bashi dariya. Amma sai ya danne baiyi ba.
Cikin silent voice ɗin nan tasa yay kiran sunan TJ. Amsa masa yay da girmamawa, sai kuma ya buɗe motar ya fita. Kasancewar glass ɗin ta inda Laalah yake an saukesa ya sa ya ɗan duƙo ta wajen sai dai kansa a ƙasa ba kallonsu yake ba. Maimakon amsa masa sai ya ɗan shafa kan Laalah ɗin tare da furta, “Maidashi wajen su Shu'aibu”. Kaɗa bindi Laalah yay alamar dai yaji ubangidan nasa. Tj na buɗewa ya dira da kansa.
Duk abinda suke ina jinsu. Ina jin ya fita na sauke ajiyar zuciya mai nauyi tare da zame jikina daga kan nasa. Ban yarda na kallesa ba na koma can jikin ƙofa na lafe. Ban kuma sake yarda na ɗago ba har muka iso gida. Sosai naji wani irin farin ciki da zaƙuwar ganin naje ga Ummie, dan bazan ɓoye miki ba har cikin tsakkiyar rai nake jin ƙaunar baiwar ALLAHr nan wlhy bily. Ƙagara nayi motar ta tsaya, amma sai bata tsayan ba sai da akaje har ƙofar sashensa. Muna fitowa ina zumuɗin tafiya na koma waccan ƙofar Mama Balki ta dakatar da ni, magana na ɗago zanyi ta dakatar dani, tare da jan hannuna muka shige sashen nasa dan shi tuni yama shige abinsa. Mamaki ne ya kamani, yanzu kam kasa haƙuri nayi sai da nai magana kamar zanyi kuka.
“Mama mi kuma zamuyi anan? Dan ALLAH mu tafi sashenmu ko wajen Ummie”.
Kanta tsaye ta ce, “Banda ikon yanke wannan hukuncin Samraah. Sai dai mu jira daga bakin Alhaji ƙarami”.
Sosai mamaki ya ƙara kamani, zan sake magana ta kama hannuna tai ciki dani. Zaune muka samesa a falo TJ na ajiye masa kofin coffee daketa tururi alamar yanzu nan ya haɗo masa shi. Tj ne ya amsa sallamar tamu, amma shi ko kallon ta inda muke ma baiyi ba. Wajen zama Mama Bilki ta nuna min, ban musa mata ba na zauna fuskata a kumbure. Kobi takaina batayi ba ta juya ta fita. A zatona wani abu zata ɗakko ta dawo, sai naji shiru har tsawon wasu mintuna. Ga TJ shima ya fice da ga ni sai shi. Karo na farko cike da ƙosawa na ɗaga kai na kallesa. Coffee ɗin sa yake sha hankali kwance tamkar ma bai san da zamana a wajen ba. Jinai raina ya sake ɓaci, amma sai na danne murya a sanyaye na ce, “Dan ALLAH zanje wajen Ummie na ganta”.
Kamar bai jini ba, sai da ya mula dan kansa sannan ya ɗan ɗago idanunsa ya kalla ta inda nake. Dai-dai na ɗan hararesa ni kuma batare da tunanin zai ɗago ɗin ba.
“Oh hararata ma kike?”.
Ya faɗa fuska a dake. Da sauri na marairaice fuskata kamar bani ba, cikin kalar tausayi na ce, “No ALLAH ba haka bane. Kawai an samu kuskure ne ni yazan harareka”. Na ƙare maganar a matuƙar karyar da kai. Ɗauke idanun nasa yay cike da basarwa ya cigaba da shan coffee ɗinsa. Naji tamkar na fasa ihu kona kamashi da duka. Amma duk babu dama. Sai kawai na dake tunda na fahimci ƴan wulaƙancin ne a kansa....

🌜💮🌛

Kamar kullum tsaff ta fito cikin gayunta. Arwa ce riƙe da handbag ɗinta tana mata shagwaɓar ta bata kuɗi. Itako sai faman latsa waya take tana tafiya kamar ma bata jin ɗiyar tata. Sai da suka gama sakkowa da ga upstairs ɗin sannan ta miƙa mata hannu alamar ta bata handbag ɗin. Sake marairaicewa Arwa tayi da maida hannunta baya ta ɓoye jakar. “ALLAH Ummy ni bazan baki ba, just 200k fa nake so bawani kuɗi masu yawa ba. Gift da zan sayama Lubnah yau birthday ɗinta. Kuma motana fa nace miki duk friend ɗina sun sanni da shi, dan ALLAH ki bani baƙin naki, ALLAH bazanyi tuƙin banza ba i promise ”.
“Riƙe promise ɗinki. Dan bazan baki motana ba. Ga dai 100k nan na saka miki je kiyi manage da shi banda kuɗi yau. Give me my bag jare. Kuma ki tabbatar kin dawo gidan nan kafin ten na dare. Dan karna shigo ban sameki ba. Zan ɓata miki rai”.
Baki cike da iska Arwa ta miƙa mata handbag ɗin, babu ko godiya ta juya fuuuu ta koma sama. Kai kawai Hajiya ƙarama ta girgiza ta juya tai tafiyarta. Babu kowa a falon sai su A'i dake gyarawa. Gaisheta sukeyi cike da girmamawa. Itako tana amsa musu a nutsen nan nata babu alamar hayaniya a tattare da ita. Daka ganta kaga mace mai haƙuri da iya zama da mutane. Compaund ta fita, kai tsaye tai wajen motarta dan ita sam bata da driver. Bata yarda da kowa ba ita ke tuƙa kanta, tana ƙoƙarin ajiye handbag ɗinta a side ɗin mai zaman banza dai-dai nan Hajiya Mammah ke fitowa itama cikin wani shegen shiga na manyan mata dake ji da kansu. Kallon juna sukai, amma sai Hajiya Mammah ta watsar da Hajiya ƙaramar tamkar bata ganta ba ma. Lips Hajiya ƙarama ta cije tare da faɗin, (zanyi maganinki ne) a zuciyarta. A zahiri kam sai ta saki murmushi tare da nufar Hajiya Mammah ɗin cikin girmamawa ta gaisheta. A ɗage Hajiya Mammah ta amsa tana ƙoƙarin shigewa motar da drivern ta ya buɗe mata. Itama sai Hajiya ƙaramar tai murmushi ta juya ga tata motar ta shiga. Kusan a tare suka fice a gidan. Sai dai suna fitowa babban titi kowa yay hanyarsa. Ita Hajiya Mammah gidan Baba prof ta nufa, itako Hajiya ƙarama asibiti ta nufa...

⭐⭐⭐

Gidane babba mai ƙyau kuma sosai. Ga masu aiki tako ina nakai kawo maza kai kace akwai wasu mutane da yawa a ciki. Guri drivern Hajiya Mammah ya samu yayi parking, sannan ya fito cikin rawar jiki ya buɗe mata, sai faman cika take da batsewa wa ma'aikatan dake ta faman gaisheta da girmamawa. Ko sau ɗaya bata amsa musu ba, sai ma tana fitowar tuni wani yazo ya amshi handbag ɗin hannunta dan sun san halinta sarai. A yatsine take bin jibga-jibgan motoci ukun dake fake a compaund ɗin wanda bata san da su ba a gidan da kallo. Cike da isa ta dubi wanda ya amsa mata bag ɗin ta ce, “Waɗan nan motocin fa?”.
Muryarsa har rawa take wajen bata amsa da, “Na baƙine da Alhaji yayi ranki ya daɗe”.
“Baƙi?”.
Ta maimaita da sigar tambaya, sai dai kuma kafin ya bata amsa tayi gaba bakinta a taɓe. Bayanta yabi da sauri. Kanta tsaye ta shiga ta main perlor ɗin gidan ta shiga ainahin falonsu. Babu kowa a ciki, sai ƙamshin air fresheners dake tashi da kuma ɗan sanyin ac kamar ba safiya ba. Baba kam akwai son tsafta. Duk da rayuwarsa yake shi kaɗai a gidan babu mace zaka samu komai tsaf-tsaf. Dan tunda mahaifiyarsu ta rasu bai sake aure ba. Suma kuma ko yace zai yi ɗin bazasu bariba wlhy. Dan yanda ba'ama uwarsu kishiya tana raye ba bayan ta mutu ma baza'ai mata ba. Zaune takai saman luntsuma-luntsuman kujerun falon. Tuni ta wani lume a ciki dan sunada bala'in taushi. Baban nasu ɗan gata ne, dan duk shekara sai Awwab ya canja komai na gidan an sake masa sabon fenti. Kukun gidan daya fito ne yana gaidata ya katse mata tunani, a ɗage shima ta amsa masa fuska a yamutse. Har zai juya ta dakatar da shi, umarnin haɗa mata breakfast ta bayar. Cike da girmamawa ya amsa mata yana komawa ciki. Babu jimawa kuwa ya kammala komai ya kawo ya ajiye gabanta. Zama ta gyara da ƙyau ta fara kwasar girki tana chart da Rubayya dake ƙara tsara mata yanda zata tunkari Baban. A haka Baba prof ya shigo falon ya sameta. Kanta dake duƙe ta ɗago ta kallesa, yana sanye cikin farar jallabiya tas data ƙara fiddo tsufarsa. Dan bashi da wani jikin kirki, gashi dogo masha ALLAH kamar dai su Paah dan duk shi suka biyo har su Maash duk tsahonsa ne. Kanta ta ɗan rissinar tare da faɗin, “Barka da fitowa Baba”.
“Yauwa Nafisatu kece a gidan?”.
Ya faɗa yana kaiwa zaune. Murmushi tayi, tare da sake rissinawa ta shiga gaishesa. Da kulawa ya amsa mata yana tambayarta mutanen gidan da jikin Ummie. Cikin ɗan ɗage kafaɗa ta ce, “Da sauƙi to Baba. But ba shiga nake ba dan tun dai randa ta faɗin nan gaskiya”.
Fuskarsa a ɗan ɗaure yace, “Ban gane ba?”.
Fahimtar katoɓarar da tayi yasa ta ɗan ƙaryar da kai gefe. “Baba ba wani abu nake nufi ba fa. Wlhy ina jin tsoro ne shiyyasa. Kasan idan Ummu-Hidaya na'a wannan yanayin akwai haɗari shiga inda takene. Amma nasan da sauƙi gaskiya, tunda kaga ba'ai kiranka ba”.
Kansa ya jinjina cikin nuna gamsuwa. Ita kuma ta sauke numfashi. Sai kuma tayi murmushi da sake ɗan dubansa. “Baba wai motocin suwaye na gani haka a gidan nan?”.
Hannunsa ya ɗan yarfar da taɓe baki, sai kuma ya ɗauka black tea ɗin da kuku ya kawo masa ya fara kurɓa, sai da yay kusan sau uku kafin ya kalleta. “Shugaban jam'iyyar ACC ne na ƙasa da wasu ministoci guda biyu. Suna damuna a kwanakin nan akan son na shiga siyasa. Ni kuma abinda bai taɓa birgeniba kenan Nafisatu. Yanzu ma shugaban ƙasa ne da kansa ya turosu. Ni dai na faɗa musu gaskiya ina akan bakana. Amma sun dage matuƙa. Shine nace suje zanyi shawara”.
Cike da zumuɗi da zamala Hajiya Mammah ta gyara zamanta. Gaba ɗaya 32teeth ɗinta washe suke. “Amma Baba mizai hana ka amshi tayinsu. Ni banga wani aibu ba a siyasa ai. Sannan kowane irin sharuɗɗa ka cikasu da ko ɗar bazakaji na shiga ba. Tayinfa kujera suke maka mai matsayin farko a jihar nan. Zamu kasance cikin matuƙar farin ciki a kiramu first family na wannan state mai girma irin Lagos. Baba dan ALLAH ka amsa”. Ta ƙare faɗa cikin shagwaɓa. Ajiyar numfashi ya sauke tare da gyara zamansa.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏_


*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG


https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

____________


.......Tsahon lokaci muna zaune shiru batare da ya sake magana ba. Coffee ɗinsa kawai yake sha a hankali yana kuma daƙilar tab da ke a saman ƙafarsa da yay crossing.
“Wane hukunci kika yanke?”.
Tambayarsa ta iso cikin kunnena a bazata. Ɗan ɗagowa nayi na kalla inda yake, dan da farko ma banyi zaton shine yay maganar ba. Yanzu ɗin ma daƙilar tab ɗin kawai yake, dan haka na ce, “Wai kaine kayi tambaya?”.
Ɗago manyan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login