Showing 402001 words to 405000 words out of 438336 words

Chapter 135 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2204

kunne da sarƙa da suka kasance zinari. Nasan nayi ƙyau koda ba'a faɗa min ba. Ya Arrahaman na faɗa a zuciyata ni kaina fa nake kallon kan nawa ta mirror. Kwalliya dai kam itace mace. Komai muninka indai zaka gyara sai an kalla an sake kallo. Bare kuma Alhamdullah muna da dai ɗan ƙyan nan dai-dai mu ma. Balle a yanzu da ciki ya sake ƙawatani da fiddoni fam. Flat shoes ɗin da aka haɗo da kayan na sakama ƙafata mai ƙawace da dan kyalli da baƙi. Kafin na haɗa ƴan tarkacena a handbag. Ina warware mayafin ya shigo shima cikin shirinsa. Shaddace baƙa data masifar fiddo da ainahinsa. Sai kawai na tsaya ina kallonsa kamar yanda shima yake kallona. Na buɗe baki zanyi magana sai shima ya buɗe zaiyi muna ƙoƙarin haɗa baki. Duk shiru mukai muna ma juna murmushi. Sai kawai nai ƙasa da kaina har ya ƙaraso inda nake.
Kamar mai tsoron a jisa cikin silent voice ɗin san nan ya furta, “Anya kuwa zan barki fita a haka My Samrh”.
Kaina a ƙasa ina murmushi na ce, “Sabida mi?”.
“Kinyi ƙyau ne fiye da yanda kike tunani”.
“Kaima ai hakan. Dan komai ka saka a jikinka ƙyawunka ƙawatashi yake yi”.
“Ai ke kin mafi ƙyawun ƙyau My helf”. Ya faɗa yana rungumoni jikinsa. Ni dai addu'a kawai nake kada yace na cire ko yace an fasa. ALLAH dai ya taimakeni akai kiransa a waya kan mu ake jira kowa ya tafi har angwaye. Gyalen ya amsa da kansa ya yafa min. Batare da ta sake magana ba ya ɗauka handbag ɗina a hannunsa na haggu na damar ya kamani muka fita. Gidan shiru sai securitys kawai. Sai motar dake fake fara tass mai shegen ƙyau da kuma ta guards ɗinsa guda biyu. Da sauri TJ dake neman faɗuwa saboda kallonmu ya buɗe murfin da sauri, yayin da shi Uban gayyar ya zagaya da ni ta ɗaya side ɗin ya buɗe da kansa ya taimaka min na shiga sannan ya sake zagayowa inda Tj ya buɗe masa ya shiga.. kallona ya ɗan yi ya sakar min murmushi. Nima sai na sakar masa murmushin tare da kwantowa gefen hannunsa....

🤍❤️🤍❤️🤍

A ɓangaren anguna da amaransu kwalliya ce ta kece raini da ko makaho ya kalla yasan naira tayi aiki a wajen. Dan rigunan amare da suka kasance pitch sun musu masifar ƙyau. Hakama angwaye dake sanye da fararen suit kamar ka sace su ka gudu dan ƙyau. Manyan motocin da aka sakasu sabbi ƙal ko ledojinsu ba'a ɗaye ba sunyi matuƙar sake ƙawatasu. To magana ake ta aljihu da manda fa. Ƙannen Maash sunfi gaban wasa a wannan gaɓar.
Hall ya cika iya cika taban mamaki duk da kuwa duk wanda ya shiga wajen yana da lasisin hakanne. Harka ce ta manyan mutane da ƴaƴan manyan. Ga ƙawayen amare sun fito cikin nasu kalar ta musamman da nunama tsara. Kamar yanda al'adar biki yake bayan sanar da isowar anguna da amare ƙawayen amarya da abokai suka jagoranci shiga dasu cikin tsari da nutsuwar data ƙayatar da kowa. Yaya Musaddiq shine babba. Dan haka yana a gaba shi da amaryarsa Fahad biye da shi maƙale da tasa amaryar da makeup ya ɓoye yanayinta na gumurzun da tasha a jiya hannun angon nata. Dan yanda tafiyarta ma bata gama daidaita ba Falaq ta canja takalmanta zuwa flat gudun matsala. A hakanma dai dan hannunta na cikin nashi ne ya taimaka mata da rufa asirinta. Babu wanda zai ce waɗan nan angwaye da amare basu birgesa ba. Ga shi an musu ɗinki na mutunci da sam bai fidda tsiraicinsu ba. Hasalima maimakon naɗa ɗan kwali a saka net su rolling ɗinsa akai musu ta yanda ya sake mutuntasu matuƙa. Wajen hawa steps Bahijja ta kasa saboda azabar data ratsata. Dan tun takun farko ta tsaya cak. Ai kawai Fahad na fakar ido ya ɗauka kayarsa camak ya ƙarasa da ita har saman kujerar da zasu zauna. Miko za'ai inba dariya ba. Dan yanda yay ɗin dole ya burgeka kuma ya baka dariyar. Shiko ko'a jikinsa fatansa dai asirinsa ya rufu a gama harkar nan lafiya Ummie ko Mama ko Hajiya Mama wani bai ramfosa ba. Dan Hajiya Mammah ma shi zaima iya gaya mata da bakinsa har yanzu ba wani mutunci take da shi a idonsa ba. Wajen zama uku aka tanada. Su suna gefe da gefe na tsakkiya na babban yaya. Sai dai ba kowa ya sani ba, ana daita mamakin ma rashin isowarsa akan lokaci wajen dan har aka gabatar da addu'a da ɗan wasu abubuwan bai iso ba. Sai bayan kusan mintina talatin aka sanar da isowar tashi.
Anan fa wanda basu san Maash ba suka fara baza ido domin ganinsa. Wanda kuma suke wasi-wasin batun aurensa na son tabbatarwa da gaskiyane ko kuwa. Saboda an san dai babu yanda zai ya halarci wannan dinner babu matar. Bayan mc ya gama kirari da wasa shi ya shigo cikin gakun nan nasa na ƙasaita da rakiyar bajiman guards ɗin sa abin zabbirgewa. A gefensa ƙyaƙyƙyawar matarsa da suka gama dacewa a gefensa hannunsa sarƙe a cikin nata ɗayan hannunsa ɗauke da handbag ɗinta.
“Masha ALLAH”.
Kalma mafi girma data dinga fita a bakunan mafi yawan mutanen wajen kenan, dan duk iya hassadarka kasan wannan haɗi ya haɗu. To sai muce mai abu da abunsa ne ya shigo. Dan kuwa dai bakin mc ya gagara rufuwa sai washi yake iya washi kamar zai haɗiye garshensa. Abu mafi birgewa ga anguna guda biyu kuma ƙanne da duniya ta shaida ga MAASH yana taka step ɗin wajen suka miƙe domin girmamawa a garesa. Sai kawai ya tsaya kallonsu shima da murmushin da mutane da yawa zasu iya rantsuwar basu taɓa gani akan fuskarsa ba. Dan har cikin rai yake jin alfaharin kasancewarsu ƙannensa, tare da cika burin kakansa da har ya koma ga ALLAH bazai taɓa mantawa da shi ba. Sai kuma ƙyau da sukai masa matuƙa dan da kansa ya bada design ɗin kayan da ke jikin nasu musamman ma suit ɗinsu. Nuni yay musu da su zauna kafin ya ƙarasa shi da tasa zinariyar mazauninsu. Kamata yay da kansa ya zaunar sannan shima ya kai zaune ya kuma jawota jikinsa da ƙyau tamkar za'a ƙwace masa ita. Aiko abokansa sai kawai suka hau salute nashi.
Farin cikin Ummie baya musaltuwa a wannan rana. Sai da ta share hawaye ta sake sharewa sau babu adadi. Yayinda ita ke kukan farin ciki anan acan asibiti Baba prof na ƙunar zuciya yake yi shi da ƴarsa Lawisa. Dan kuwa saboda su Maash ya ɗauki nauyin gidajen tv masu yawa suke nuna wannan dinner live. Ya kuma saka aka saka musu tashoshin dan su gani kamar yanda kowa ke gani.
Wani irin zafafa da hanƙoro zuciyar prof keyi a cikin ƙirji. Sai dai babu damar motsa ko ɗan yatsa dan shi da dutse basu da banbanci a yanzu ƙasancewar sai an motsashi dan haka yake turum. Rashin makama ya sakashi fashewa da kuka kawai. Hawaye masu azabar zafi da ƙona zuciya suka dinga bin fuskarsa. Yayi kiran azo a kashe masa tvn amma babu kowa a kusa. Sai faman taunar lips yake yana fasasu da gaƙori tare da antayi ashariya manya-manya kamar ba tsoho ba.
A ɓangaren Commondo kam dariya ya dinga yi, dan shi ba taron bane ya zame masa abin kallo prof ne. A kwanakin nan dama a tsakaninsa da shi sai dai ƴar tsinema juna da yin ALLAH ya isa. Prof ɗin yayi-yayi a raba musu ɗaki anƙi ko kulashi. Daya damu mutane ma dan bakinsa ras na magana da ga shi har commondo ɗin. Sai securitys ɗin dake tsare da su sukace bashi da wannan isar ai a yanzu. Kalmar nan ta masa masifar ciwo. Ai ko ya dinga surfa musu zagi a wannan rana amma babu wanda ya kulashi...

★★
A wajen dinner bayan mc ya gabatar da isowar Maash da tashi amarya aka sake addu'a. Kafin aunty Mama ta fito ta gabatar da kanta matsayin ƙanwar mahaifin anguna. Ta kuma buƙaci nutsuwar kowa dan acewarta tana da bayani mai muhimmanci da babban saƙo ga duk wanda ke a hall ɗin dama wanda ke gani a wajen ta hanyar television. Tsitt kuwa hall ɗin ya sake yi fiye da da. Itama sai ta sake nutsuwa da juyawa ta fuskanci Maash dake gyarama Samraah mayafinta suna magana ƙasa-ƙasa. Cike da kulawa ta kira ainahin sunansa.......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_


........Dara-dara ɗin cat eyes ɗinsa ya ɗago ya kalleta. Tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya amsa mata da girmamawa. Da sauri mc ya kawo masa mic dan kowa na buƙatar jin abinda zai faɗa. Hakan ya sake gamsar da mutane. Hajiya Mama ta cigaba da faɗin, “Muhammad Awwab wacece a tare da kai?”.
Juyawa yay ya kalla Samraah da tai ƙasa da kanta. A hankali ya ɗaura hannunsa saman haɓarta ya ɗagota. Kallon juna sukai cikin ido kafin a hankali ya kai mic ɗin saitin small pinkish lips ɗinsa ya motsasu cike da ƙasaita idanunsa a cikin na Samraah ɗin itama nata a cikin nashi har lokacin ya furta, “Aunt! Ita ɗin MATATA CE!”.
Ya Arrahaman, irin wannan salo haka mai kashe zuciya. Sai kawai hall ɗin ya ɗauki tafi. Da ƙyar aka samu ya lafa. Hajiya Mama ta sake faɗin, “Yaushe ka fara sonta?”.
Yanzun kam idanunsa ya lumshe tare da sake juyawa ya buɗe su akan Samraah da ita kanta wannan tambaya ta sakata jin zumuɗi tana kallonsa. Cikin tsakkiyar idonta ya sake saka nashi. Cikin wani irin soft voice ya furta, “Ranar dana fara GANINTA”.
“Yaya akai haka bayan kowa yasan Maash ba ma'abocin shiga sabgar mata bane?”.
“Saboda ita ta kasance ta MUSAMMAN”.
“Uhmmm Masha ALLAH ta musamman kam. Muma shaida ne. Amma zamu so musan yaya akai haka da sauri?”.
“Saboda tayi abinda wani bai taɓa kwatanta yi ba a sunan ma'aikacin jarida harda Mazan. _(“Sir a matsayinka na matashi da za'a iya shiga mamakin ganin yanda ka gina katafaren kamfani irin wannan da ya zama na farko a Africa, a duniya na uku kuma bama shi kawai ka mallaka ba, akwai wasu manyan cibiyoyi daka kafa a ciki da wajen Africa ma ba Nigeria kawai ba, ko nace duniya, shin ko zaka iya jan hankali matasa irinka dake tasowa dangane da neman na kai da asalin tarihinka dan su san kaima ba daga kwance ka kai wannan matsayin ba, sai da kai aiki tuƙuru, tare da tsallake ƙalubale masu yawan gaske kuma duk kai haƙuri ka jure har gashi a yanzu ka zama wani babban ginshiƙi tauraron duniya dake haska yankinsa da ƙasarsa, yarensa harma da addininsa?)_
Sune kalmomin data furta masu girgiza zuciya da rarrabesu suka zama masu wahalar gaske da sanya razani, tare da jan hankalin Muhammad Awwab El-Mu'azz Maash gareta. Dan shine lokaci na farko, kuma karo na farko da naga tsantsar JARUMTA da iya aiki da ƙwarewar iya sarrafa harshe na ƴan jarida a tare da yarinya ƙarama kamarta. Idan nace muku TSORONTA naji, har na amince batare dana shirya hakan ba karki musanta min”
Kutumaddu-madu. ai wani irin sowa da ihu da hall ɗin nan ya ɗauka na matasan samarin dake wajen dama abokan uban gayyar su kansu kai kace wata gagarumar ƙwallo da duniya ta dasa ma idanu gaba ɗaya ce a kaci. Ya ilahil alamin. Maash ya gama buɗe aiki yau. Ita kanta Samraah jikinta tsuma yake yi. Babu shiri ta shige jikinsa ko zata samu nutsuwar fuskantar mutane. Sai da aka samu hall ɗin ya lafa bayan mc ya warware sautin waƙar da aka rairama Maash ɗin da Samraah sannan tambaya ta koma kanta.
Cikin tsareta da ido Hajiya Mama ta ce, “Daughter Samraah wanene wannan tare da ke?”.
Kallonsa na ɗan yi sai kuma na duƙar da kai ina murmushi. Mic ɗin ya kawo gab da bakina, a hankali na furta “Mama Miji”.
“Oh Woow Masha ALLAH. A ina kuka fara haɗuwa?”.
“Wajen taron buɗe Company naje a matsayin mai ɗaukar rahoto.”
“Kenan kema tun a ranar ki ka faɗa a soyayyarsa?”.
Shiru nayi kamar bazance komai ba. Hakan yasa hall ɗin yay tsitt sosai. Sai da Hajiya Mama ta sake furta, “Muna sauraren Mrs Maash”.
Ɗagowa nayi na ɗan kallesa sai naga ya wani tsareni da shanyayyun idanunsa. Ɗan hararsa nayi kaɗan na maida kaina na rissinar. Kamar mai koyon magana na ce, “Mama kawai dai....”
Sai kuma nayi shiru. Sai da na sake jan wasu sakanni da saka ƙaguwa a zuciyar kowa na kuma ji a raina ajin da naja ya jawu. Dan shi kansa uban gayyar a ƙagare yake sannan na furta, “Addini, nagarta, Ƙyawawan ɗabi'u, kama mutuncin kai, yakana sune suka fara jan hankalina bayan aure. Aduk wanda ke gefe idan akace masa Maash abinda zai faɗa ko ya fara kawoma ransa, ko ya kallesa a bangon mujallu ko jaridu da fuskar television matsayin matashi da ake makallo da wasi-wasin dukiyarsa ko ta halak ɗin ce ko kuwa akwai wasu dabaru. Tantiri da baya jin magana, mai izza, fariyya da dukiya. Mai tsananin ɗagawa da girman kai wanda baya son arewa da mutanen yankin. Sai dai kuma sam ba haka bane, na fahimci hakanne nima a lokacin da muka kasance kusa da juna. Maimakon waɗan can halayen da ake masa kallo da ga nesa. sai naci karo da kishiyarsu a tattare da shi. Hasalima da matasanmu zasuyi koyi da halayensa da sun matuƙar ribantuwa. Mutum ne mai addini da kula da shi fiye da yanda muke zato. Yana da ilimin addinin sosai. Mutum ne mai sauƙin kai da son sauke hakkin na ƙasa da shi cikin tausayawa. Mutumun ne jarumi ba malalaci ba. Akoda yaushe ƙoƙarin neman nakansa yake ta hanyar HALAL da kuma guminsa. Sannan ba arewa bace baya so manyan arewan ne da ya kamata su jawosa jikinsu arewar ta amfanu da shine ruɓaɓɓu. Dan ta aljihunsu kawai suke yi su. Wannan nagartar tasa itace tushe kuma mafarin komai. Idan har za'aso MAZAN da basu da ko quarter ɗin waɗan nan halayen nasa shi mizai hana a so shi”. Na ƙare maganar a hankali ina mai ɗago idanuna na kallesa. Shima ɗin kallona yake, dan haka na ɗan kashe masa ido ɗaya kamar yanda yake min ina wani sassanyan murmushi. A hankali na motsa lips ɗina idanun nawa a cikin nasa na ƙarasa furta, “Dan haka shine ALJANNAR DUNIYA TA”.
Sosai hall ɗin ya kaure da tafi, yayinda dj ya saki cool music na masoya mai ratsa zukata. Shiko jikinsa kawai ya jawoni ya rungume sosai. Tare da faɗin, “NIMA ITACE ALJANNAR DUNIYA TA”.
Sake hargitsewa hall ɗin yayi kuwa. Kusan mintuna goma kafin komai ya nutsa. Aunty Mama ta cigaba da faɗin, “Nasan wasu dayawa zasu ce muda mukazo taron sabbin amarya da ango mun ƙare kuma ga tsaffin aure. To ayi haƙuri, suma wannan taro harda su. Dan nasan mutane da yawa kafin sanin Maash yayi aure sukan saka a ransu duk ranar da zata kasance ta bikinsa sai ya nema fasa Nigeria da wajenta na ban mamaki. Sai kuma komai ya faru batare da an sani ba, hakan yasa daga baya da abin ya fito wasu suka shiga ruɗani. Shiyyasa mukai amfani da wannan damar domin tabbatarma da mutane gaskiyar da suke son sani. Muhammad Awwab El-Mu'azz Maash dai mijin Samraah Abdul-wahab Gwarzo ne. Wadda akafi sani da Sam-G. Muna musu fatan alheri da zuri'a ɗayyaba tare da dawwamammen farin ciki. Yanzu zamu dawo kan angunanmu da amarensu suma. Mc bissmillah”.

Taro ya cigaba da gudana cike da birgewa da ƙayatarwa. Tarihin angwaye biyu dana amarensu sai san barka. Yayinda aka warware sautin mawaƙa da aka gayyato daga arewaci da kudancin ƙasar. Kai da kaga yanda ake zuba liƙi da manyan kuɗaɗe zaka san bikin na girma ne. Su Alhaji Fahad babu yakana babu ɗaga ƙafa yasha rawarsa. Yayin bada cake ya tsotse lips ɗin Bahijja tsaf dan sai da ya saka a nashi bakin sannan ya bata. Lokacin da Ummie tazo tana musu liƙi su dukansu bayan an saka mata waƙarta ta girma itama Mama Balki da Hajiya Mammah biye da ita Maash da Samraah sukazo suka fara liƙeta da daloli🤪 itama. Ai tuni suma aka zo ana zuba musu nasu. Yayinda Ummie ta juyo garesu suma. Hakama Yaya Musaddiq da Fahad da amaren biyu suka fara zuba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login