Showing 264001 words to 267000 words out of 438336 words
na kallesa. Amma sai na janye ina amsar kofin da girgiza masa kaina na ce, “A'a ka barsa haka ka ɗan ci abincin ko kaɗanne. ALLAH ko zama da yunwa ya saka ciwo. Baice komai ba har na ɗakko tray ɗin na aza saman cinyata na buɗe plate ɗin. A take Ƙamshin taliyar ya gama cika wajen. Ba wani dahuwar ƙaƙale na mata ba. Dan attaruhu ne kaɗan sai vegetables da kifin gwangwani dana saka a ciki. Kodan ƴar kaɗan ce dama na dafa sai ya bani wani kalar ƙyau a idon mai kallo. ALLAH dai yasa tayi dadi ma a baki. Tray ɗin na ɗaga zan maida jikinsa ya dakatar da ni. Da mamaki na kallesa, shima kallona yake yi. Cikin wani irin luuu da idanun kamar zai lunshe hannayensa harɗe a ƙirjinsa ya min nunin na ajiye a saman jikin nawa. Nan ma kasa Musa masa nayi, sake min nuni yay da spoon ɗin shima. Nan ma na ɗauka babu musu. Ya nuna min abincin tare da buɗe mitsitsin bakinsa alamar na bashi. Sosai na ɗan waro idanuna waje, sai ya ɗan ɓata fuska da ƙoƙarin zamewa zai koma ya kwanta.
Riƙosa nayi da sauri cikin marairaicewa na ce, “Yi hakuri to zan baka”. Ƙaramar harara ya ɗan mun sannan ya koma ya zauna. Niko sai mita nake a zuciyata. Mutum kamar kurma sai iya shege fal cikinsa. A zahiri kam abincin na fara bashi a nutse. Shiko ya zuba min idanunsa kawai yana wani taunawa tamkar baya so. Sai da yay kusan lauma uku sannan ya wani lumshe min idanunsa cike da salo tare da haɗe babban yatsarsa da manuniya 👌alamar yayi. Bamma san na sakar masa murmushi ba nima. A mamakina shima sai ya murmusa kaɗan. Zuba masa ido kawai nai ina kallonsa, dan tabbas murmushi yanama bawan ALLAHn nan ƙyau, sai kuma a kaf rayuwarsa, inaga abinda yafi masa wahala kenan sai magana.
“Samrh”.
Ya kirani a hankali. Firgigit na dawo hayyacina. Sai kuma na ɗan ɓata fuska dan na fahimci na saki layi da yawa. Ƙoƙarin dojewa nake dan a tunanina zai min magana ne akan kallon nasa. Sai naji saɓanin hakan. Sake kiran sunan nawa da yay can ƙasan maƙoshi da silent muryar sa ɗin nan yana sake narkar da cat eyes ɗinsa kaina ya sa na amsa nima idanuna a ƙasa.
“Minene burinki a duniyar nan?”.
Ƙaramin murmushi nayi, tare da ɗebo abincin nakai bakinsa. Buɗewa yay ya amsa, na ɗan janye hannuna batare dana kallesan ba dai na ce, “Yaya Awwab! Ina da burika da yawa. Sai dai dukansu sun ta'allaƙa ne a ƙarƙashin dai-daiton rayuwa da samuwar dunƙulalliyar tafiya a yanzu. Dan na jima da shafe babin burikan da wauta da ƙuruciya ta ƙirƙira a baya saboda wasu dalilai.” abincin na ƙara ɗiba zan bashi ya girgiza min kai alamar ya ƙoshi, fuska na marairaice ina kallon abincin, sannan na sake kallonsa na ce, “Please kaɗan fa kaci. Ka daure ka ɗan ƙara sai kasha magan...”
Ai tun kafin ma na ƙarasa kalmar maganin ya wani yamutse fuska da ɓata rai. Dariya naji ya bani, wai namiji babba kamarsa da tsoron magani. Bance da shi komai ba face maida abincin na rufe na ajiye. Maganin dana riga na ɓalla nasa a ƙaramin plate na rufosa na buɗe na ɗiba. Ina juyowa yaga abinda nayi kawai yay saurin jan bargon zai kwanta na ɗane gadon ina dariya. A saman cinyarsa na zauna na hanashi kwanciyar tare da riƙo fuskarsa. Kansa ya shiga jujjuya min kamar zaiyi kuka.
“Please my tiger wlhy bana so. I hate medicine! leave me alone I beg”.
Hancinsa na ɗan ja da faɗin, “Noo sai fa My Lion ya sha maganin nan zan barsa. Ni ina son naga ka samu sauƙi, jikinka ƙara zafi ma yake”.
“Pleaseeee”.
Ya sake faɗa fuskarsa a yamutse kamar zai fasa ihu.
“Nima Pleaseeee manya fa basa tsoron magani. Haba ɗan Ummiensa. Bafa wani wahala da yanzu ma kasha. Zakafi samun sauƙi da wuri”.
“No kawai ki rungumeni zan daina ji”.
“A'a, sai kasha sannan zan rungumekan. Rufe idonka ka gani ka buɗe bakin haba mana, be a good boy my Lion. Hhaaah”.
Kafaɗa ya maƙe mun duk ya marairaice abin dariya. Kamar ba stubborn Maash ɗin nan ba mai yin komai cike da rashin mutunci ba. Cikin ƙoƙarin sake dabara na ce, “To yanzu yaya kake son ayi?”.
Bakin ya buɗe zaiyi magana kawai na shammacesa na cusa maganin. Na saka tafin hannuna na danne bakin. Duk ƙoƙarin turewa da yake yana yunƙurin amai ban barsa ba saida na ɗauka ruwa, ina janyewa zai ɓaro maganin na danna masa kofin kan baki tare da riƙe masa hacci da yatsuna dole ya zuƙi ruwan. Sai da na tabbatar ya shanye ruwan maganin kuma ya wuce gaba ɗaya sannan na saki masa hanci ina dariya. Ganin yanda yake riƙe wuya yana yunƙurin amai yasa na daina dariyar dan na fahimci abin nasa fa na gaske ne. A hankali na riƙe fuskarsa da tafukan hannuna duk biyu tare da kai lips ɗina saman small nashi duk da yanda zuciyata ke dukan tamanin-tamanin ga kunya amma na daure. Cak kuwa ya tsaya da kakarin ya shiga sauke numfashi. Kusan minti ɗaya na tabbatar nutsuwarsa ta dawo jikinsa na janye bakina ina mai tusa kaina cikin ƙirjinsa dan harga ALLAH kunya naji sosai. Abu goma da ashirin gani a saman cinyarsa kuma zaune ɗane-ɗane kai ni Kandala ansha abin kunya. Saukar hannayensa akan bayana da yanda ya wani irin rungumeni tsamm ya sani lumshe idanuna dake rufe tare da jan numfashi a hankali. Mun kusa mintuna uku a haka kowa na sauraren bugun zuciyar ɗan uwansa kafin ya kwantar dani a hankali shima ya kwanta yana jan duvet ya lulluɓemu. Sosai yanzu kam gabana ya faɗi. Dan raba jikina nai ƙoƙarin yi da nashi ya girgiza min kansa, cikin mugun low voice a kunnena ya furta, “Please! stay, I need hakan babu abinda zanyi”.
Ajiyar zuciya na ɗan sauke mukai shiru. Har ma na ɗauka barci ya kwashesa a bazata na sake jin muryarsa a cikin kunne na. “Tell me mine burinki?”.
Sai da nayi ɗan murmushi kafin na sake shigewa jikinsa, dan yanzu kam zafin jiki nasa daɗi yake min kasancewar nima kamar na fara jin sanyin abinka da wadda bata saba shiga ruwa ba. A hankali nima nace, “Yaya Awwab”.
“No faɗin yaya Awwab again. Sabon sunana nake so”.
Da mamaki nace, “Wane sabon suna? Yaushe ka samoshi”.
“Yanzu da za'a mun muguntan bani magani mana. In ba hakaba ni gaskiya zanbi takan dokan likitar nan”.
Ai harda ƴar zabura nayi, amma sai ya maidani ya sake matsewa da faɗin, “Toki faɗa”.
A shagwaɓe na ce, “Nifa nama manta”.
Sai da ya ɗan mintsineni sannan ya ce, “Mai zafinki”.
Jinai gaba ɗaya kunya ta gama kamani ma. Ko yaushe nayi wannan irin ɓaranɓarama haka. Irin wannan bama auntys ɗina na DANDALIN TSUTSAR NAMA kunya (🤣😂😜).......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚-𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_
......Firgigit na dawo hankalina jin hannunsa a cikin jikina. Hannun na riƙe tare da marairaicewa na ce, “Please Yay... Uhmm uhmm M..y Ho..t” na faɗa kamar mai koyan magana ina ƙara cusa kaina cikin ƙirjinsa. Ina jin motsawar ƙirjinsa alamar yin murmushi. A zuciyata nace mugu ɗan masa.
“You are my Hot too Aljannar duniyata. Faɗa min minene burin naki?”.
Gaba ɗaya jinai tsigar jikina na tashi saboda yanda yake min magana a cikin kunne a wani kalar hankali. Ajiyar zuciya naja cikin dauriya da nuna juriya a hankali nima na ce, “Babban burina yanzu a duniya shine Ummie ta samu lafiya. Na biyu Yaya Musaddiq yay aure. Na uku ku daidaita kaida Yaya Fahad Please Yaya Awwab. Nasan ba son ranku bane. Amma kaine baba, kana amsa tamkar sunan uba ne a garemu baki ɗaya. Komi kake ji a ranka ka dinga daurewa dan ALLAH. Sannan ka yawaita ambaton sunan ALLAH da istigfari, salatin ANNABI da ambaton Hasbinallahu wa-ni'imal wakil akoda yaushe. In sha ALLAHU zamuyi nasara. Dan haɗuwar kanku shine tsanin samuwar lafiyar Ummie, idan ba hakaba zamu cigaba da zama a ƙarƙashin igiyar tufƙa da warwara ne. A yanzu haka mataki na farko da nake so ka fara ɗauka bayan canja mata doctors ɗin nan da kayi shine maidota nan sashen. Tunda samanka babu kowa a maidata can, ko kuma kai ka koma can ita ta zauna nan ƙasa idan zaifi mata sauƙi. Hakan zai bamu damar kulle kowacce irin ƙofar nasarar cimma buri daga duk mai mummunar manufa. Bani da wani buri a yanzu daya wuce tabbatuwar waɗan nan abubuwan guda uku wlhy”.
Wani irin matseni yay a jikinsa har sai da na saki ƙaramar ƙara ya sassauta min. Yanda naji jikinsa na rawa yasa gabana faɗuwa. Da sauri na ɗago tare da yaye duvet ɗin. Hannunsa yake ƙoƙarin kaiwa saman kansa ga wani irin juyewa da idanunsa ke neman yi. Da masifar sauri na tashi zaune jikina na rawa. Gaba ɗaya bargon na yaye, na wani irin ɗaga kansa na maida saman jikina tare da fisgar gorar ruwa na ɓalle murfin. Ɗiba nayi cikin hannuna na shafa masa a fuska, sannan na saka masa kan baki hawaye na rige-rigen sakko min. Da ƙyar na samu ya sha kaɗan, banyi magana ba na fara karanto addu'oi ina tofa masa. Tamkar wani mai aljanu sai ya fara lafawa a hankali a hankali har barci ya ɗaukesa. Tagumi kawai nayi na zuba masa ido, nama rasa wane kalar tunani zanyi. Ina nan zaune shiru na fara jiyo kamar hayaniya da dukan ƙofa. Jinai gabana ya faɗi, a hankali na zame kansa a saman jikina na maida saman fillo tare da gyara masa bargon na sauka. Har nakai ƙofa na dawo, dan bathrobe ce a jikinmu daga ni har shi kasancewar daga swimming pool muke, sai ƙaramin towel da kaina ke naɗe a ciki. Sauri-sauri na canja zuwa doguwar riga na saka hijjab kawai na fito. Babu kowa a falon, daga waje ne ake hayaniyar. Buɗe ƙofar nayi na fita gaba ɗaya. Turus na tsaya jikina na rawa ina kallonsu. Fahad ne riƙe da wani shegen kaifaffen wuƙa irin na chinis ɗin nan da zakaga suna faɗa da shi a films, sai faman riƙesa ake yana rantsuwa sai ya kashe ɗan uwansa da hannunsa. Shi ya tsanesa, baya sonshi baya son ganinsa sai ya kashesa. Abinda yay matuƙar bani mamaki kaf ahalin gidan idan ka cire Paah da Uncle ɗin nan nasu kowa yana nan. Amma duk sunyi tsaitsaye Baba ne kawai mijin Mama Balki ke ƙoƙarin ma Fahad magana, sai Mama dake roƙonsa itama tana kuka. Sai kuma Hayatu da guards ɗin Maash dake rirriƙe da Fahad ɗin. Sai Hafizzullah da ban san ma yana gidan ba na ƙoƙarin amsar wuƙar a hannun Fahad ɗin cikin lallashi da dabaru. Ido muka haɗa da Hajiya ƙarama dake faman taɓe baki, da sauri ta wayance ta gyara fuskar tata takai hannu tana sharar hawaye ita a dole kukama take yi. Kaina na girgiza na maida kan Hajiya Mammah. Waya ce a hannunta yanayinta da alamar damuwa da gani akwai wanda take son kira ko kuma tanata kiran ba'a ɗaga ba. Na maida kan Maman Malika. Kanta a ƙasa tana hawaye. Sai su Azizat da Arwa da yanayinsu ya nuna yanzu ma suke shigowa gidan suma sunyi tsuru-tsuru a cikin yanayi mai wahalar fassara. Sai masu aiki da fuskokinsu ke nuna yanayi mabanbanta. Bahijja dake kuka sosai kamar zata shiɗe na zubama ido fiye da kowa, A'i na riƙe da ita itama tana sharɓan hawayen. Idanu na ɗan lumshe na buɗe ina mai sauke ajiyar zuciya.. Nayi alƙawarin bakina bazai taɓa furta ni matar Maash bace, sai dai in har shine da kansa ya sanar musu. Amma lokaci yayi da zan fara buga nawa acting ɗin nima a cikin wasan nan. Sai da na karanto addu'a tare da dawowa ainahin Sam-G ɗita da kowa ya sani.
Cikin dakiya fuska a ɗaure da ɗan ɗaga murya kaɗan na ce, “Ku sake shi!”.
A tare gaba ɗaya, da wanda suka ganni tun ɗazu, da wanda basu san da fitowata ba duk suka ɗago suna kallona da matuƙar nuna mamaki a fuskokinsu. Ganin basu da niyyar sakin nasa a kausashe na sake faɗin, “Ku sakesa nace ko”.
Hayatu ne ya fara sakinsa a hankali, sai Hafizzullah dake min wani irin kallo idanunsa duka a waje. Bamma nuna na gansa ba ni sam, ganin Hayatu ya saki Fahad ɗin suma guards ɗin Maash duka sakesa, sai dai daka gansu kasan a tsorace suke. Hannayena na warware daga ƙirjina, kafin na shiga takawa a hankali na sakko a ɗan steps ɗin dake gaban ƙofar sashen nasa. Dai-dai nan Hajiya Mammah ta wani irin zaburo a masife da nunani da yatsa ta ce, “Kai! To ke kuma fa a waya kike wannan maganar a gadarance haka?”.
Ko kallon inda take bayi ba, na cigaba da takawa har gaban Fahad dake wani irin huci da ƙarasa zaro wuƙar dake cikin kufenta dan dama bai gama cireta duka ba kasancewar Hafiz ya riƙe masa hannu. Saurin riƙeni Hajiya ƙarama tayi batare dana san sanda tama zo inda naken ba. Cikin girgiza kai ta furta, “No Please ƴammata. Zai iya jimiki ciwo baki ganin bashi da hankali”.
Kaina na ɗan karkata na kalleta da ga sama har ƙasa cikin ɗage gira, sai kuma na ɗan girgiza kan nawa da gyara tsaiwata na ce, “Ayya ashe mahaukacine shima”. Daga haka na ɗauke kaina na maida ga Fahad dake ƙoƙarin gittamu. Babu alamar wasa a tattare da ni na ce, “Yaya Fahad!”.
Cak ya tsaya kamar wanda ake sarrafawa da remote. Sam banyi zaton zai tsaya ɗin ba, kawai na gwada sa'ata ne ƙasan raina ina roƙon UBANGIJI akan ya hanani jin kunya. Dan haka tsayawar tasa ta sakani wani irin jin sanyi a raina, ban damu da kallon da Hajiya Mammah da Hajiya ƙarama kemun ba, kai dama kowa na wajen. Da baya na ɗan ja na koma gabansa. Ganin yanda yake hucin da cika da batsewa jikinsa na rawa ya sakani sakin murmushi. Batare da nayi magana ba na miƙa masa goran ruwan hannuna. Ƙin karɓa yayi, dan haka na sake sakin murmushin da raunana murya nace, “Haba dai Autan Ummie, ko sokake na saka rigima ban yarda na bar maka autancin ba. Dan dama fa haƙuri nayi kawai amma ina son autancina. Kasha kaji, muje mu duba Ummie na tabbatar tana matuƙar buƙatarmu a kusa da ita. Shiko Yaya Awwab da kaina zan maka maganinsa. Yau sai ya bar mana gidan nan dan bazamu zauna da shi yana sakaka fushi ba. Ina dalili ina ɗan mafari Yayana yafi gaban raini ai, ungo kasha kaji”. Na ƙare maganar ina ƙara miƙa masa ruwan da miƙa ɗayan hannuna kuma alamar ya bani wuƙar. Kamar mai shakkun yin hakan ya amshi ruwan ya bani wuƙar. Bamma san wani wawan ajiyar zuciya ya kufce min ba. Da ƙyar na danne hawayen da suka cika min ido ina satar kallonsa. Tuni ya ɓalle murfin goran ya kai bakinsa yana sha da irin salon da ɗan uwansa yake shan ruwa a wasu lokutan. Sai da ya shanye tas ya miƙomin roban. Amsa nayi ina murmushi da faɗin, yauwa yayana you are the best Yaya in my life. Oya let's go wajen Ummien mu kafin ƙuda ya rigamu”.
A hankali ya saki murmushi. Muryarsa a ɗashe ya ce, “Kema you are the best ƙanwa in my life”. Ya ƙare maganar yana miƙa min hannunsa wai na kama. Kafaɗa na maƙe masa tare da girgiza kai. A hankali na furta, “Wanan hannun na sarki ne”. Alamu yay min na bai ji minace ba wai. Sai kawai na sakar masa murmushi da nuna masa hanya. Kafaɗa ya ɗan ɗage sama da taɓe baki...
“Na shiga uku ni Nafisa. Wai mi nake shirin gani haka ne nikam? Ke kuma naki salon kenan kibi wa kibi ƙani. Jama'a karuwanci a cikin gida”.
Kallonta na ɗan yi na kashe mata ido ɗaya.
“Iyeeeh!! Dan ubanki ni kike ma wannan abun? Kin san ko matsayina a wannan gidan?”.
“Ƴar cin arziƙi mana”.
Na faɗa a hankali dai-dai zamu gittata. Wani bala'in zaburowa tai kaina tare da kai hannu