Showing 354001 words to 357000 words out of 438336 words
riƙe masa Ummu-Hidaya ba miye-miye. Kai ko ga ƴar gwal an haifi a Nigeria. Komai bance masa ba a randa ya kawo min wannan zantukan banzar nashi. Na koma kawai gefe na shiga na fita shege a dawowa ta biyu baima san sanda ya amince ba jikinsa na rawa. Suma duk da akwai shaƙuwa a tsakaninsu na sake ƙulle zukatansu a waje guda suka nuna suna son junansu. A zatona wannan haɗin auren zai sa ya dunƙule dukiyar ya bama Mu'azz matsayinsa na mijin ƴar tasa tilo da yake taƙama. Kokuma ya tattara duka aikin ya bama Mu'azz ɗin. Ya cigaba da jagorantar companyn. Amma shegen mutumin nan sai ya ɗauki ƴarsa ya ɗorata akan komai. Tana wata ƙasar tare da ɗana da aka maida hoto amma tana juya kan dukiyar duk da ƙananun shekarunta.
Wannan abu ya ƙara ƙona min zuciya matuƙa. Wato ni na ɓata ƙuruciyata a banza wajen hidimta masa ɗana ma zai koma ɗan amshin shata mijin Hajiya. Haba never. Tuni na je na kunno musu wutar da Mu'azz ya fara cin ubanta. Dan a lokacin data samu cikin farko ya jajibemu domin dubata da shirina naje. Na banka masa maganin da Malamina ya bani bamu baro ƙasar ba sai da ya zubar mata da cikin da ake ɗogafi da shi. Da matuƙar farin ciki na dawo a lokacin har kashi biyu kuwa. Na zubar da cikin da Mu'azz yay mata da ƙararshi data kawo min wai bata son ubanta ya sani ai masa faɗa akan neman matan da yake da dukanta da yake yi. A zahiri na amsa mata da to kawai, amma ko uhun bance masa ba. Yo neman mata sai na hanashi ya more ƙuruciyarsa ya ƙare kanta iya kaɗai kenan ma, ko kuwa tana matarsa bazai jibgi shegiya ba yanda yake so a kuma sanda yake so. A dawowar tamu ma dukkanin baya nai ina samu akan zaman nasu. Ubanta yake ci gwargwadon iko shine ma dalilin da yasa tana kammala karatun ta saka suka dawo Nigeria da zama. Duk da dai tana dojewa wai ta dawo ne tai aiki a kamfanin babanta. Ƙaryar banza kenan. Koda ta dawo ɗin nasan Mu'azz na aikata duk abinda yake acan bai fasa ba. Ban kuma tsawatar masa ba. Babban abinda ya fara saka min tsanar shegiyar yarinyar nan bayan wadda nake ma ubanta ta shafeta shine ɓoye zancen cikinka da tayi tare da wannan munafukar annamimiyar da mijinta. (Ya nuna Mama Balki) Ban tashi sanin tana da ciki ba sai da ya shiga watan haihuwa, shiyyasa ashe ubanta ya tura Mu'azz wata ƙasa aikin watanni har shida. Ni kaɗai nasan a halin dana tsinta kaina a wannan lokacin, dan haka na nutsu domin nemo mafita akan yanda ko ta haihu za'a maida abinda ta haifa lahira dan ubansa. Ƙawarta da naga tana yawan zirga-zirga a gidan ce tazo min rai. Dan haka na nemeta amma sai taƙi bani haɗin kai a lokacin da yake Lawisa shegiyar makira ce. Tata yawo da hankalina duk da barazanar da nake mata da kurari, sai da ta latsani da ƙyau har bayan an haifeka sannan ta yarda mukai magana. Wannan shine mafarin alaƙata da Lawisa duk da bata da wani ƙarfi sai idan dalili ya taso. Jawota jikina yasa na fahimci itama shegiyar tana kwana da tashi da baƙin cikin Ummu-Hidaya ɗin. Amma tana dannewa kullum tana jikinta. Kamar dai yanda nake ma ubanta wahala, itama tanata yima ƴar wahala. Duk da mun haɗe kai da Lawisa tako ina mun gagara samun nasara akan kauda kai a duniya. Dan koyaushe idon baƙar matar nan da mijinta na kanka. Ya nuna Mama Balki cikin tsana.
Tako ina sun rufe komai sun katantane. Daga baya ma sai na fahimci shi Abdul-wahab kamar ya sakama motsina ido. Dan bawai ga Ummu-Hidaya ba hatta da uban gidan nasa wanni kaffa-kaffa yake da shi idan har ina waje. Rana ta farko dana zuba ma Ibrahim wasu ƙwayoyin da Lawisa ta samo mana ta kuma tabbatar min da in har Ibrahim ya shasu bugun zuciyarsa zai ƙara ƙarfi da ga ƙarshe ta buga ace heart attack ne ya kashesa bayan na gama wahalar zuba maganin a cikin shayinsa kawai matsiyacin yazo da wani salo ya ɓarar da shi as mistake. Ya kuma katantane shi da kansa ya haɗo masa wani ya bashi a gabana. Wannan abu yamun ciwo na fara ninka tsanar da nake masa a raina tare da saka masa alamar tambaya. A karo na biyu ma dana haɗa wutar lantarki a office ɗinsa kawai bamma san ta yanda akai ba kawai shi yaje ya kama wayar ya hana Ibrahim kamawa. Satinsa guda a asibiti yana jiyya a maimakon Ibrahim. Wannan ma ta wuce bance da shi komai ba na sake kafa wani tarkon a cikin gidansa da fetur nan ma Abdul-wahab ya wargaza min. Haka ya dinga bina kafa da kafa yana wargaza min ayyukana akan Ibrahim. Daga ƙarshe na fito ƙuru-ƙuru na masa gargaɗi da barazana. Amma da yake shi taurin kai ya masa yawa sai ma ya maida abun rainin hankali, har yana wani sanar min cikin gadara wai in ma ina wani tunani a kansa ne na canja dan TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE shi ɗin ba kanwar lasa bane. Idan kuma zan shekara dubu ina ƙulla makircin kashe Ibrahim zai kasance a bashi kariya da izinin UBANGIJI. Kar kuma na ɗauka zai faɗa masa ne ya ɗauki matakin hukuma shi da kansa zai cigaba da bashi tsaro da tsarewar ALLAH batare da ya taɓa sanar da shi wanene ni ba har sai idan shine ya gano da kansa. Alwashi na ɗauka masa kan nima mu zuba ɗin, ni da shi ɗan halak ka fasa. Muka ko zuba ɗin ba tare da sanin Ibrahim ba. Tabbas Abdul-wahab ya nema zamenim bala'i a rayuwata. Dan haka na shirya shirin ƙarshe da shi a ciki dan ya cancanci irin hukuncin Ibrahim shima.
“Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, Baba yanzu har wannan ya kai ka kashe Abie da ya inganta rayuwarmu. Shine fa sanadin barowarmu ƙauye”. Hajiya Mammah ce ke maganar cikin matsanancin kuka. Hakama Hajiya Mama da Paah kansu kawai suka duƙar suna hawaye.
Cikin kaushin murya da zafin rai Baba prof ya daka mata tsawa da faɗin, “Oh dan yayi sanadin barowarku ƙauye bada wahalar ubanku bace Nafisatu. Ko a banza yasa na kawo kun badan ya cigaba da amfanuwa da ƙuruciyar mahaifinku bane. Kar wanda ya sake katseni ki bari nakai ƙarshen zancena mana kafin kiyi alƙalanci!!!”. Ya ƙare maganar a tsawace yana wani irin huci kamar bajimin sa. Kafin ya cigaba da magana a zafafen nasa.
“Sai da na gama shirya komai sannan na tunkari Ibrahim da sigar neman alfarmar aron kuɗi da zan inganta bussines ɗina. Amma shi da yake butulu ne, kansa kawai ya sani sai shegiyar ƴar nan tasa da kai dake matsayin jikan da ni nama fisa matsayi da ƙarfi a wajenka domin ubanka na haifa. Haka ya nuna min baida waɗan nan kuɗin. Sannan ko yana da su ma bazai bani ba dan sunyi yawa. Naje na cigaba da juya na hannuna wai fara kasuwanci da kaɗan yafi albarka. Kuji min shegen makiri, shi bada manyan ya fara ba. Na zafafu ranar da ƙyar nai controlling kaina. Ban sake masa magana ba sai bayan wasu kwanaki na sake zuwa masa dai da wannan buƙatar amma na rabin abinda na nema a farko nan ma ya nuna min sam shifa bazai bani ba tunda ya sallameni. Idan ma dukiyar da nake kallo a hannunsa ce shima ba tashi bace mallakin ƴarsa ce da jikokinmu. Kam babbar bala'i kenan. Wai abinda aka tara da gumina ake min gadara da shi hahaha yaro bai san wuta ba kenan sai ya taka. Daga haka ban sake masa batun ba sai bayan kusan wata ɗaya naje masa da tayin sayen Shere a companyn nawa dan nayi amfani da kuɗin na tada companyn da ke neman durƙushewa. Abin mamaki wai azzalumin nan a wannan ɓangaren babu musu ya amince. Ya sayama ƴarsa kaso ɗaya bisa uku na Shere ɗin company na. Ya kuma biya akai duk abinda ya dace ya amshi takardu a gabana ya damƙa mata. Daga wannan ranar nai alƙawarin sai na ɗanɗanama Ummu-Hidaya azaba da wutar dalma a tafin hannunta. Matakin farko kuma shine kashe ubanta. Anyi haka da ƴan kwanaki kawai a bazata akace min wai tana naƙuda. Imagen matar ɗana nada ciki ban sani ba a karo na biyu. Hakan na nufin akwai abinda take shiryawa kenan itama ko ubanta ya kitsa mata a kaina, domin idan babu rami miya kawo rami? Ta ɓoye na farko na biyu ma haka........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_
*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._
.......Banyi magana ba dai sai shi Mu'azz ɗin na samu na ci masa ƙaniya sai da ya koma yana rantsuwar shima wai bai san da cikin ba sai da ya kai watanni kusan huɗu. Ta kuma roƙesa kada kowa ya sani idan kuma ba hakaba zata gudu tabar gida har sai ta haihu ta dawo saboda ta fahimci baya son haihuwa shine ya zubar mata da cikin farko. Na Awwab ma shiyyasa ta saka mahaifinta ya turashi wani aiki na watannin rainon cikin nata da tayi bayan ta tabbatar mai idan wani abu ya samu cikinta sai ta kaisa kotu. Sosai raina yamun zafi da lusarancin Mu'azz. Dan a zahiri baya jin magana, sannan yana da zafin rai idan aka ƙuresa amma bashi da yawan hayaniya da kwaramniya tamkar ba mune muka haifesa ba. Kaf halayensa na mahaifiyata ne ya kwaso shi. Barshi dai da fitinar neman matansa kawai. Takaicinsa ya sakani korashi dan mun gama shirya kawai tafiya matakin ƙarshen ni da Lawisa. Sai dai dole sai mun sami point. Munata neman point bamu samu ba har sai da tafiyarsa jihar Katsina ta taso. Amma zaiyi landing a Kaduna ya ƙarasa Katsina ta mota. Hahaha wannan abu yay min daɗi matuƙa. Hakama Lawisa. Babu ɓata lokaci ta samar mana wanda zai mana aiki a kaduna. Abinda ya ƙara sakamu a farin ciki da tafiyar ta kasance da shegen makirin driver ɗinsa mai cika bakin zai iya ƙare rayuwarsa yana bashi kariya. Anyita ta ƙare, raina yayi sanyi FANSA ta tabbata akan Ibrahim da Drivern sa Abdul-wahab, sai dai wai Ibrahim bai mutu ba. Hakan bai wani ɗaga min hankali ba, dan nasan zan iya ƙarashi da hannuna abu mai sauƙi. Amma kuma zan iya bashi damar rayuwa koda a kwancen ne ta yanda yana kallo ina juya abinda ya cutar dani a kansa amma babu yanda zai yi dan ubansa.....
“Wlhy kai jahili ne. Wato ɗauka ma kake rayuwarsu da mutuwarsu duk a hannunka take?”. Fahad ya faɗa a matuƙar zafafe yana kuka. Cikin tsawa Prof... Ɗin ya watsa masa harara da faɗin, “Nace a daina katseni sai naje ƙarshe. Kai yaushe ma aka haifi uwarka balle kai zaka katseni. Idan kai baka san rayuwarsa a hannun nawa take ba ita uwarku ta sani dan taga kaɗan daga abinda zan iya bayan tamun irin wannan gadarar. Haka shima uban nata. Ni ɗin dai daya wulaƙantar ni ne na shiga na fita aka kawosa Lagos ɗin yana a tsakanin rayuwa da mutuwa. Inda naso da tun a can zan kashesa amma ba haka nake buƙata ba alokacin. Ni na tsaya tsayin daka akai treatment ɗinsa har ya fara samun sauƙi. Kaga ko ai rayuwar tasa a hannuna take mara kunya (Wa'iyazubillah😭). Naje masa da jarabawar ƙarshe, wadda da ace ya cita da har yanzu yana rayuwarsa dan ba itace a gabana ba ni. Yana a gadon asibitin naje masa da batun duk halin da yake a ciki nine na sanya shi, na kuma gaya masa kuskurensa, tare da tabbatar masa idan har ya mallaka min abinda nake so a lokacin tofa zai tsira, hakama ƴarsa zata tsira. Hakama jikokinsa. Idan ba kuma ba haka ba, zan kashesa kamar yanda na kashe uwar matarsa da matarsa. Na kuma kashe ƴarsa da jikokinsa abinda ya hana nin ya dawo nawa gaba ɗaya dan babu mai cin gadonsa sai ni. Hhhhhh!!! Kun san miya faru? Da yake mutumin nan ƙasurgumin shegen Bature ne kai tsaye yace min bazai bayar ba. Har ma yana iƙirarin idan ya bar asibitin nan sai ya wulaƙanta rayuwata. Dan sai ya kaini hannun hukuma na faɗa masa dalilin kashe masa mata da mahaifiyarta. Hahaha ni sai ma ya bani dariya, dan haka na haɗa masa da abinda naso barinsa a duhu saboda wasu dalilai, amma tunda zai iya ɗaukar fansar matarsa da uwarta nashi iyayen fa?. Dan haka na fito na faɗa masa ai suma ni ne na kashesu. Nayi hakanne kuma a dalilin hukuncin auren budurwata da yayi, cikin sauƙi na shirya matsalar data zama gobara har yau ake ɗauka daga sune. Tofa wai wanda ke a gadon asibiti a tafin hannuna ke nuna fusata har gado na jijjiga. Sai famar hura hanci yake shi a dole sai ya ɗau fansa. Kaji Bature ɗan balaja'u. Kazo ƙasata kace zaka nunan gadara. Barinsa nai ya gama bige-bigen nasa sannan na siburbuɗa masa allurar poison. Hhhhh karfa kuga laifina dan alokacin bata mutuwa bace. Ina da makarinta a hannuna, na kuma nuna masa idan har yay min abinda nake so zan masa ita mu rabu lafiya ya cigaba da rayuwarsa zaɓinsa ne. Na koma gida ina jiran feedback. Washe gari kuwa na samu kira daga wajensa. Ganin ƴarsa da jikansa a wajensa har ma da lauyoyinsa yasa na fahimci gargaɗina ya amsu kenan. Dan haka na samu gefe naci dariyata son raina sannan na koma. Sai dai tun a farkon zaman meeting ɗin na fahimci baifa sallaman ba, lallai taurin kai baiyi ba, da ace mutumin nan yasan mizan iyayi da wlhy baiyi jayayya ba. Da bai zaman tattare komai da komansa a gabana ya mallakama ƴarsa da jikokinsa ba. Da bai ajiye shaidu akan hakan ba har kuma ya gayyaceni zaman. Dan wannan shine mafi girman kuskure daya taɓa aikatawa a rayuwarsa da shima yasan ya tafi yabar BAYA DA ƘURA. Dan nayi alwashin sai na tabbatar masa da TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE koda yana kwance a cikin kabarinsa. Yanda bai saka ni cikin zancen ba an ajiyeni ne matsayin hoto ko dan yamun gadara ne oho mas nima sai banyi magana ba har akai zaman meeting ɗin aka tashi. Abu ɗaya nai masa shine lokacin da zan fita a ɗakin nai masa kallon (Kayi kuskure) nai ficewata. Dan banda sauran kuma dil da shi wasan ya koma tsakanina da ƴarsa ne. Yes ni da ƴarsa dan allurar poison ɗin da nai masa kawai ta wadatar ta ƙarasa min rayuwarsa. Hakan kuwa ce ta kasance, washe gari aka shafe babin rayuwarsa. Ya zama tarihi. Alonso Ibrahim ya shuɗe kamar bai zo ba.
Adalcina yasa na tsaya akan komai na jana'izar sa komai akayi yanda ya kamata. Ai koba komai baƙonka Annabin ka inji masu iya zance. Baƙunta yazo ƙasarmu, ya kuma tattara ya bar mana miya rage ai gaba ta ƙare kuma sai wadda aka barma JINI. Banyi ƙasa a gwiwa ba dan bana son na cigaba da jan al'amarin na samu Ummu-Hidaya da batun ta bama mijinta komai na dukiyarta ya cigaba da juya mata a matsayinta na uwa ta cigaba da tarbiyyar yaranta da kula da mijinta. Kun san buɗar bakinta mi tace dani kuwa? Hahahhhh!!! Kawai sai cewa tai wai (Baba karka damu, zan cigaba kamar yanda na fara wannan shine burin mahaifina). Banyi fushi ba na cigaba da nuna mata