Showing 240001 words to 243000 words out of 438336 words
kamar zai lumshe sai kuma ya buɗe a kaina har sai da naji tsigar jikina ta tashi, hannuna dake riƙe da kofin ya ɗan fara rawa-rawa kamar zan saki kofin. Hannayensa dake harɗe a ƙirjinsa ya warware a kasalance, dan haka na ƙara ƙasa da kaina dan bazan iya kallonsa a yanda yaken ba. Jin saukar hannunsa a saman nawa mai riƙe da kofin ruwan ya sani lumshe nawa idon batare dana ɗago na kallesan ba. Ina ƙoƙarin sakar masa amma ya hana hakan, sai ma saukar ɗayan hannun nasa naji akan gefen cikina, a hankali ya fara tafiya da shi har zuwa bayana, kafin ya matsoni ya manne da jikinsa. Sannan ya kai ruwan da ke a cikin hannayenmu saman lips ɗinsa. Yasha kusan rabi ya zare kofin ya ajiye. Ni dai har lokacin ban sake yarda na kallesa ba. Sai dai na furta, “Nagode sosai Ya Awwab. ALLAH ya saka da alkairi, ya bama Ummie lafiya da tsohon rai mai albarka. ALLAH ya kareka da sharrin masu sharri. ALLAH ya yarda dakai”.
Jinai kawai ya ɗora ɗayan hannun nasa ta saman bayana shima ya mannoni da jikinsa gaba ɗaya ya kwantar da kaina a saman faffaɗan ƙirjinsa. Luff nayi ina mai shaƙar narkakken ƙamshinsa mai matukar tasiri da saka nutsuwa a zuciyar mai shaƙa. Munfi mintina biyar a hakan har wani bacci-bacci nake ji yana neman ɗaukata. Sai naji ya ɗagoni a slowly tare da juyamu na koma jikin mirror ɗin shi kuma ya koma inda nake da. Dagowa nai da nufin yin magana ya ranƙwafo ni gaba ɗayansa, daɓas na koma saman mirror ɗin na zauna, shi kuma yamun rumfa hannunsa ɗaya dafe da mirror ɗin, ɗayan kuma ya saukesa akan haɓata ya ɗago fuskata. Cikin matuƙar low voice ya furta, “Open your eyes”.
Jinai Sam bazan iya masa gardama ba, dan haka na shiga yin far-far da idanun kafin na buɗesu da ƙyar na saukesu akan ƙyaƙyƙyawar doguwar fuskarsa dake ƙawace da kwantaccen gashi baƙi siɗik. Kallon juna muke cikin ido da mu kammu bazamu iya fassara yanayin da muke a ciki ba. Sai wani irin tashi tsigar jikina keyi, a hankali a hankali idanuna suka fara tara ƙwalla. Kasa jurewa nayi na lumshesu slowly ina sauke tagwayen ajiyar zuciya. Dan mutumin nan zai kasheni da salonsa. A bazata matuƙar bazata naji saukar abu mai sanyi da taushi saman lips ɗina. Da sauri na buɗe idanuna. Ai babu shiri na maida su da gudu na kulle zuciyata na tsargawa. A salon da yake kissing ɗin nawa yasa gaba ɗaya jikina ya saki har ban san na kai hannuna saman kansa ba nariƙosa. Har ga ALLAH hakan da nayi kawai nayi ne amma bada wata manufa bane, tsabar na rasa ina zan dafa na samu sassaucin ruɗanin dana shiga ne yasa hannuna sauka a saman kan nashi batare dana shiryama hakan ba. Ashe shi hakan armashi ya ƙara masa, dan wajen kicin-kicin ganin na janyesa harda zame band ɗin dake ɗaure da gashinsa na tura yatsuna duk biyar cikin gashin ina yamutsawa. Munfi mintuna uku a haka, kafin ya janye lips ɗin nasa tare da ɗaura goshinsa saman nawa, hancinanmu na gogar juna, kowannenmu na sauke numfashi. Wajen minti ɗaya sannan ya ɗago kansa, kasa kallonsa nayi, sai ma hawayen da suka cika min idone suka ɗan silalo badan ni kaina nasan dalilina nayin su ba, gaba ɗayana ya jawo ya rungume tsam-tsam a jikinsa. Nima samun kaina nayi da ƙanƙamesan dan jikina rawa yake yi.. nan ma mun kwashe wasu mintuna biyun a haka kafin ya kai bakinsa saitin kunnena cikin raɗa ya furta, “Kema baƙi ƙoshi ba ko? A ƙara”.
Ji nai kamar na tsaga jikinsa na shige dan kunya, sai kawai na sake ƙanƙamesa. Wani irin ratsa kunnena sassanyan sautin murmushinsa yayi a bazata. Sai kuma ya ɗagoni yana ƙoƙarin kallon fuskata amma naƙi yarda yay hakan....
A dai-dai lokacin da acan Maash da Sam-G ke a wata duniya anan falo Mama Balki ce ta iso domin gaishe da baƙi. Cikin fara'arta da kazar-kazar ta shigo bakinta ɗauke da sallama. Amsawa su Musaddiq sukayi dama ransu fal tunanin ganin wannan uba-uban ƙaton gida amma basuga giccin kowa ba sai masu aiki maza. Ɗagowa sukayi su duka a tare da nufin gaisheta, kawai saita ja birki da uban sauri har tana buge ƙafa da kujera. Kallon Musaddiq take kamar zata cinyesa da idanunta, jikinta sai rawa yake yi. Sai kuma ta sake maida kallonta ga Hafizzullah shima. Sai kawai gani sukai ta fashe da wani irin kuka tana faman jan jikinta baya.
A ruɗe duk suka miƙe suna tambayarta lafiya? Mike faruwa?. Sam ta gagara basu amsa, sai sake cin tuntuɓe da tayi da carpet hakan yasata tafiya gaba ɗayanta zata faɗi ta baya suka hau salati da nufarta su duka biyun suka tare a tare....
Cak Maash ya dakata daga yunƙurin sake maida lips ɗinsa da yake saman na Samraah. Itama sai ta buɗe nata idanun da sauri duk suka kalla ƙofar. Dan su dukansu sunji salatin su Hafizzullah ɗin Kasancewar da ƙarfi sukayi. Kallonta yay, itama ta kallesa, sai kuma a hankali ya zame hannayensa da ga jikinta ya ɗaga gaba ɗayanta ya sauke daga saman mirror ɗin daya ɗaurata.
Zan nufi ƙofa da sauri ya riƙoni, fuska na marairaice masa kamar zanyi kuka. Sai yay min nuni da gyalena da ɗan kwali dake yashe a ƙasa. Gyalen kawai na ɗauka dan hankalina ya tashi, kada wani ya cutar min ƴan uwafa a gidan nan? Da wlhy sunga ainahin baƙin halina dan saina gallabi kowa da kowa har uban gayyar tasu bazan bari ba. Dai-dai ina isowa falon suke ƙoƙarin zaunar da Mama Balki a kujera, sai nai turus ina kallonsu. Ruwa Yaya Musaddiq ya bata, yayinda Hafizzullah daya juyo ya ganni yake sanar min abinda ya faru. Da sauri na nufi Mama Balki. Zama nayi a kusa da ita cikin damuwa ina tambayarta mike faruwa?. Dai-dai nan ya fito shima sanye cikin baƙar jallabiya da tai masa wani masifar ƙyau. Muna haɗa ido na kauda nawa da sauri.
Mama dake kallonsa itama fuskarta share-share da hawaye ta nuna masa Yaya Musaddiq. “Alhaji ƙarami dan ALLAH kalla bawan ALLAHn nan. Kalla yanda yake tsananin kama da Babanku. Inda ace mutum na mutuwa ya dawo da ƙuruciyarsa babu abinda zai sa bazan dage Abdul-wahab bane ya dawo Alhaji Ƙarami”.
Shiru kamar bazaice mata komai ba, sai kuma ya ɗan nisa a hankali tare da kaiwa zaune cikin kujerar dake facing ɗinta. Zaman ƙafa ɗaya kan ɗaya yay yana mai kwantar da kansa a jikin kujera tare da lumshe idanunsa. A haka ya furta, “Please Mama relax. Wannan ba Baba bane, dan Baba ya tafi ya barmu tafiya ta har abada.” ɗagowa yay da kansa ya ɗan zuba mana idanu mu duka sai kuma ya sake furzar da iska kaɗan yana ɗan mana nuni da Mama Balki. “Wannan matsayin uwa take garemu mu duka. Ban sani ba ko kun san Baba yana da mata a zamansa na Lagos harda yarinya ɗaya. Itace wannan”.
Da sauri Yaya Musaddiq ya kalla Mama, sai kuma ya juya ya kalla Maash ɗin. Sake gyaɗa masa kai yay cikin lumshe idanunsa tabbacin haka ɗin ne. Ni ko da Hafizzullah a ruɗani muke kallonsu. Gwarama ni dama na jima da wannan al'amarin a zuciya. Sai kawai mukaga Yaya Musaddiq ya duƙar da kansa yana hawaye. Kafin ya miƙe a hankali yaje gaban mama Balki ya tsugunna. Hannunta ya kamo cikin nasa hawaye na cigaba da masa gudu a fuska ya furta, “ALLAH na gode maka daka saka inada rabon ganin wannan rana kafin nabar duniya. Mama dan ALLAH kiyi haƙuri, kiyi haƙuri kiyi haƙuri. Tun daga randa nasan kaina, tare da labarinki a wajen Gwaggo Gudidi ban taɓa fashin addu'ar ALLAH yasa kafin nabar duniya na haɗu da ke da ƴar uwarmu da akace tana tare dake ba. A dalilinki sau biyu ina zuwa Lagos bayan na tuhumi iyayena akan kuskuren da sukayi suka nuna min nadamarsu suma, sai dai dan basu san ina zasu ganoki ba suma shiyyasa suka cigaba da zama da damuwar a rayukansu. Tabbas mama an cutar dake. Muma kuma an cutar damu, tunda da mun sanki na tabbatar bazamuyi kukan rashin iyaye a duniya ba. Dan ALLAH mama kiyi haƙuri ki yafema ahalinmu kada hakkinki ya cigaba da hanasu kwanciyar hankali a rayuwarsu. Kuskure ne sukayi a wata gaɓar da mu kammu bamu tsira ba. Dan mu ɗin ma komai sai da ya ƙwaɓe tsawon shekaru tsakaninmu dasu babu wani jituwa sakamakon amsata da ƙanin mahaifiyar mu yayi ya riƙe bai bar musu ba, duk da dama tun raduwar mahaifiyarmu ita Samraah da Hafizzullah suna a hannunsa ne. To nima sai yace zan koma hannunsa, amma suka nuna basu amince ba suma su Samraah sai a dawo musu da su. Kowa ya fahimci gadon da aka barmana sukemawa shiyyasa dangin mahaifiyarmu suka dage shine akai rabuwar tashin hankali suka manta damu sai da ga baya naita bibiyarsu har komai ya dai-daita. Zamma iya cemiki dawowarsu garemu sosai-sosai lokacin amsar kuɗin auren Samraah ne”. Kuka yaci ƙarfinsa.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_
......Muma kukan muke ni da Hafiz sosai. Hakama Mama kuka take har tana siƙewa. Sai da ya mana magana cikin gyaran murya sannan kowa ya ɗan tsagaita. Cikin yanayinsan nan na rashin son hayaniya ya furta, “Kuka ba shine alama ta godiyar ALLAH ba. Abinda ya faru ya riga ya faru, ku fuskanci wanda yake a yanzu itace rayuwa. Ya kamata bayan magrib itama Falaq kuje can dan ta ganku tunda tana fama da kanta bazata iya tazo nan ba. Gashi babu wani lokaci shi Musaddiq zai wuce gobe in sha ALLAHU”.
Duk mun gamsu da zancensa, yayinda Mama ke jinjina kai ta ce, “Alhaji Ƙarami dama kasan inda suke kenan? Shiyyasa ka auro Samraah?”.
Ɗan luuu yay da idanunsa kamar abin dole ya saki murmushi. Babu wanda ma yay zaton zai amsa a cikinmu saboda yanda ya jima baice komai ba. Sai kuma ya ɗan furzar da iska cikin sauke numfashi. Kansa ya girgiza a daƙile ya furta, “A farkon ganina da ita ban san ita wacece ba. Ban kuma taɓa kawo wani abu game da ita ba. Sai dai sunanta ya ɗan so ya ja hankalina har ya tunamin da Baba a ranar. Abubuwa ne da yawa suka faru da suka alaƙanta wannan auren Mama, dan har ga ALLAH ni banje da nufin ɓata mata aure ni na aureta ba. Kawai na hana wancan ne dan na kuɓutar da ita daga halin banza na mahaifiyarsa. Sai kuma Uncle nata yace ya bani, naso kawo musu wani dalili sai kawai naci karo da fuskar Musaddiq nima a lokacin, shine kawai nace na amsa. Bayan barina wajen kafin a ɗaura auren na saka akamin bincike shine na gano su ɗin yaran Baba ne”.
Sosai kowannenmu ke jinjina iko da hikima ta UBANGIJI. Hafizzullah da bai fahimci komai ba a zancen yay tambaya. Nice na masa bayani. Sai kawai ya hau murna wai muma ashe munada Mama. Abinda yay ɗin ne ya sakamu darawa mu duka. Hatta shi uban gayyar ina kallon sanda yay ɗan munafukin murmushin nan nasa dai-dai yana miƙewa. Ciki ya koma ya barmu anan da Mama. Aiko sai labari ya ɓalle a tsakaninmu, dan Mama wayayyar mace ce mai kuma tsananin kirki da dattako. Fita tayi sai gata tazo da Malam Baba. Mahaifin Hayatu kenan, mijinta kuma a yanzu, aminin mahaifinmu. Shi kansa ya shiga mamaki matuƙa, ya kuma yi farin ciki da ganin ƴaƴan amininsa. Duk da ya jima zuciyarsa na masa wasi-wasi a kaina ashe. Shiyyasa tun ranar farko daya ganni agidan yake kallona. Dan duk da bana kama da Babanmu, gaba ɗaya komaina na mahaifiyarmu ne idan ka cire ɗan duhun da nake da shi dan mahaifiyarmu farace tass, su su yaya Musaddiq duk sun ɗakko farinta amma kamanin Baba. Maganar aure kuma dake a tsakanina da Maash ya sani Hayatu ya faɗa masu dama.
🌺🌺🌺🌺
Ganin har gab da magriba bai sake fitowa ba munata hirarmu da Mama a falo Yaya Musaddiq yay min nuni da hanyar bedroom ɗinsa cikin hikima. Jinai duk kunya ta gama kamani, sai dai bazan iya musa masa ba. Dan haka na tashi sum-sum na wuce. Yanzun kam ban tsaya knocking ba na murɗa handle ɗin ƙofar a hankali na shiga kaina a ƙasa. Dan har yanzu ina jin nauyi da kunyar abinda ya faru a tsakaninmu ɗazun. Jin ɗakin shiru kamar babu motsi ya sani ɗan ɗagowa ina kallon ko ina. Sauka idanuna sukai a kansa. Yana zaune a cikin sofa sanye da bathrobe alamar bai cire ba tunda ya fito wankan, bowl ne na glass a saman cinyarsa da uban chocolates a ciki. Da mamaki nake kallon chocolates ɗin kafin na ɗan ɗaga idanuna akan fuskarsa. Da farko na zata ma barci yake a hakan, sai da naga gashin idonsa dogaye sosai sun ɗan motsa alamar kallona yake ƙasa-ƙasa. Kauda nawa idanun nayi kamar zan juya naji ya furta, “Zo nan”.
Idanuna na ɗan rumtse, dan duk sanda saukar muryarsa zai shiga cikin kunnuwana sai na jisu har tsakkiyar brain ɗina. Sai da na ciza lips da sauke numfashi sannan na juya kaina a ƙasa na nufesa. Ban zauna a kujerar da yake ba doguwa sai na zauna akan ɗayar dake gefensa dan guda uku ne dama. Doguwa ɗaya sai biyu masu zaman ɗai ɗai a gefe da gefen ta.
“Mi kike buƙata?”.
Ya faɗa a daƙile yana kai sauran chocolate ɗin hannunsa ƙaramin bakinsa. Satar kallonsa nayi ina mamaki a raina, namiji da cin chocolate, ai kayan yara ne da mata, duk yau banga ni dai ya ci abinci ba, sai dai ko da suka fita yaci. Ganin ya zuba min ido na ɗan girgiza masa kaina da faɗin, “Ba komai, kawai na jika shiru ne baka fito ba. Ga kuma abinci duk yau naga baka ci ba”.
Shiru bai tanka min ba tsahon kusan mintuna biyu, kafin ya ɗago a nutsensa zaune sosai tare da ajiye bowl ɗin chocolates ɗin nashi a Centre table. Murya can ƙasa ya ce, “Gashi ina ci”. Yay maganar yana nuna bowl ɗin chocolates ɗin. Da mamaki na ɗago idanuna sosai na warosu a kansa. Tare da furta, “Chocolate ne abinci? Abin kwaɗayin yara ne fa. Kai kuma ƙatoto da kai ka zauna kana ci, kuma amma ce fa maza basa cin zaƙi hak.....”
Ganin yanda yake kallona da mayatattun idanunsa na kasa ƙarasawa, sai ma na miƙe cikin wayancewa na ce, “An kira magrib bari na shirya kar su zo suna jirana”. Na wuce bayi da sauri.
Da kallo ya bita harta shige, sai kuma ya girgiza kansa shima yana miƙewa zuwa closet ɗinsa yin shirin massalaci.
💕💕💕
Bayan sallar magrib Hayatu da kansa yazo ɗaukarmu. Ogan nasa bai dawo ba. Amma tunda shi yace zamuje dama sai ban damu ba na shirya tsaff cikin atamfa riga da skirt a kayan daya kawo min. Ni da Hafizzullah da Mama a baya, Yaya Musaddiq da Hayatu a gaba. Yanda naga bakinsa yaƙi rufuwa saboda farin ciki nasan Mama ta gaya masa komai ko mahaifinsa. Nayi matuƙar mamakin ganin ƙayataccen gidan da shima yake a ciki. Sai na sake yarda da batun Mama Balki da tace su suna zaune a Maash Mansion ne kawai saboda Ummie. Shine gaba muna biye da shi, sosai ta ciki ma gidan yay ƙyau da tsaruwa. Sai da muka zauna ya kwala kiran mai aikinsu wata ƴar budurwar yarinya ta fito. Gaishemu tayi sannan ya bata umarnin kawo ruwa da abinci shi kuma yay sama. Babu jimawa sai gashi ya fito riƙe da ƙyaƙyƙyawar matashiya, gaskiya zata iya girmata koda shekara uku ne, da ƙyar take tafiya saboda cikin jikinta da yay girma sosai. Duk da fuskarta ta ɗan yi fushi irin na masu ciki hakan bai ɓoye kammaninta da Hafizzullah ba. Yanda muka zuba mata ido haka itama ta zuba mana nata. Lokacin da suke isowa gab da mu jikinta har rawa yake yi. Haka ta dinga bimmu ɗaya bayan ɗaya da kallo, kafin ta maida kan Mama da ke kallonta itama fuskarta ɗauke da murmushi. Cikin langaɓar da kai ta ce, “Mama ina ji a jikina su ɗin jinina ne. Dan ALLAH Mama kada kuce dani ba haka bane ba. Yaya Hayat yace bazai faɗa ba sai dai na gani da ido na”.
Murmushi mukayi mu dukanmu, kafin Mama ta gyaɗa mata kai. “Tabbas su ɗin jininki ne Falaq. Ga babban yaya Musaddiq, sai Samraah ban ƙanwa, sai auta Hafizzullah”.
Kuka ta saki a hankali idonta akanmu