Showing 291001 words to 294000 words out of 438336 words
min hannayenta alamar nazo gareta. Ai da gudu na ƙarasa na shige jikin nata ta rungumeni tsam. Tana jin motsin tahowar mutane ta sakan da sauri ta nufi ɗaki. Sagade nayi a wajen uwa wadda ta suma. Har sai da Mama Balki ta taɓani sannan na dawo hayyacina. Murmushi tamun da faɗin, “Ko dai nace ya dawo ɗiyata zata bisa”.
Kaina na duƙar ina murmushi yaƙe, sai kuma na nufi ɗakin Ummie da ɗan gudu. Tabbas naji kunyar maganarta, amma ba shine maƙasudin gudun nawa ba. So nake naje na sake tabbatar da abin al'ajabin dana gani. Shin Ummie ɗin ce ko kuma gizo tamun yanzun nan. Kwance na sameta tamkar mai barci, sai gaba ɗaya na sake jin kaina na neman juyewa. Koda mama Balki ta shigo ta tambayan barci take. Kaina kawai na iya ɗaga mata dan ban san abinda zance ɗin ba nikam. Da ga ƙarshe ma sai na fito a ɗakin na haura sama......
💢✨💢✨💢
Maimakon gida guesthouse ɗinsa ya wuce. Inda yakan daɗe baije ba saboda wasu dalilai. Gaba ɗaya ko gani bayayi da ƙyau. Yana shiga ciki Hajiya ƙarama ma na isowa. Dan biye take da shi a baya batare da ya sani ba. Koda ta shigo falon da farko shiru yay baima nuna yasan da zuwan nata ba, sai da taga shirun yayi yawa ta fara magana cikin muryarta dake nuna tsantsar tashin hankalinta.
“Tabbas yallaɓai muna a cikin tashin hankali. Gaba ɗaya a kwanakin nan abubuwa taɓarɓarewa suke neman fara yi. Irin wannan na guda shiyyasa tun samun lafiyar Ummu-Hidaya na farko nace maka muyi abinda ya dace, amma kaƙi fahimtata. Wlhy idan bamuyi wani yunƙuri ba a wannan gaɓar da wuri to fa lallai wankin hula na gab da kaimu dare. Dan zuciyata ta fara kaini ga zargin anya kuwa yaron nan Awwab baya biye da mu? Dan take takensa a wannan gaɓar sun fara bani tsoro. Sannan kaga wannan ifiritiwar yarinyar daya kawo ya ajiye wlhy shaiɗaniya ce. Kuma tabbas aurenta yayi, idan har abinda ya faru a farko ya zama kuskure to bayan faruwar hakan ya aureta dan ya binne abinda ya faru. Idan kuma zamuyi tunani na hankali ance tana da aure, dan ya mata fyaɗe a kuskure kuma zai aureta ne da aurenta? Duk yanda muke son sakama ranmu ba haka ba to tabbas fa tun farko Awwab shine mijin yarinyar nan. Shi kansa Mu'azz abunuwansa na kwanakin nan sun fara bikita min lissafi da har nake ganin dole akwai abinda ya sani, sai dai ban sani ba ko ya shafemu ko ba haka ba. Ka duba yanda yaron nan shima Fahad ya dawo a fetsare kai kai lallai muna buƙatar dawowa cikin hankalinmu, dan wlhy ɗayan biyu ne. Kodai aikin dake jikin kowa ya fara barinsa, ko kuma sun san abinda ke faruwa....”
Wani irin watsi da kayan saman Centre table ɗin Baba prof yayi, kafin cikin matsanancin tsawa ya ce, “Lawusa!! Get out of my house now!!”.
“Yallaɓ....”
“I say get out!!!!”.
Jitai gaba ɗaya illahirin jikinta na rawa. Dan idanun baba prof ɗin sun gama jirkicewa sun juye gaba ɗaya. Fuskarsa ta wani irin canja gaba ɗaya tsufansa ya bayyana kansa. Tunda take da shi bata taɓa ganin matsanancin fushisa irin na yau ba. Tafiya take a gwagwgwame tana waigensa. Tana zuwa compound ta afka motarta ta tada. Ai a guje tabar gidan batare da ita kanta tasan mima take yi ba. Sai da tayi nesa da gidan ta samu waje tai parking. Ruwa ta fisga ta hau kwankwaɗa, sai da ta sha fin rabi kafin ta kifa kanta jikin steering tana sauke numfashi a harɗe. Mike damun tsohon nan ne? Shi indai yana a cikin fushi gaba ɗaya sai kiga ya juye mahaukaci. Tun fa da sauran ƙuruciyarsa haka yake da wannan halin mahaukatan. Ya kamata ace ya nutsu mu tattauna musan mafita amma haukar tashi na neman motsawa. Magana ta gaskiya idan naga zata ƙure bafa zan zauna ta kife da ni ba. Amma shike nan duk wahalar da nayi ta tsahon shekaru ta tafi a banza kenan. Kai impossible.
A zuciyarta take ta faman ƙullawa da kwancewar nan ita kaɗai. Tafi awa guda a haka kafin ta tada motar ta cigaba da tafiya. Ba gida ta nufa ba, kai tsaye cikin Agege ta nufa. Ta ɗan yi zurfi a anguwa sosai kafin ta samu waje tai parking. Wayarta ta ɗauka tayi kiran layin Commondo. Kamar bazai ɗauka ba sai tana gab da tsinkewa gashi ya ɗaga.
“Ina anguwarku, ta wajen wani shagon saloon ka sameni Please idan babu damuwa. Gashi zan ɗauka hoton wajen na tura maka ta WhatsApp”.
Banji mi akace da ita tacan ba. Ta dai yanke kiran bayan ta amsa da okay gashi zan tura. Mintuna kaɗan kuwa wani mai sanye da p-cap daya rufe fuskarsa sosai ya buɗe motar ya shigo. Ajiyar zuciya Hajiya ƙarama ta sauke, tare da kallonsa dai-dai yana cire p-cap ɗin. Shima kallonta yayi tare da kashe mata ido ɗaya cike da salon taƙadaranci ya ce, “Yau tsohuwar love ce ta tashi halan Lawy Baby”.
Harararsa ta ɗan yi ta ɗauke kai. Ya wani kwashe da dariyar mungunta tare da kaima kafaɗarta duka ya ce, “Ki gama zagaye-zayenki kema kin san bazaki taɓa ƙara samun jarumi kamar ni ba Lawusa. Dan tunda kike tare da ni kin taɓa kallon wata mace da suffar da kike kallonta yanzu. Jarumi kennan ba irin wannan lusarin mijin naki ba da ko ciki ya kasa baki kusan 18years. Kima shirya aikin nan na zama done no more mata a cikin rayuwar mu”.
“Kai dai ka sani”.
Ta faɗa cikin taɓe baki.
“Kema zaki sani ai. Ina my sweet daughter? Ina fata baki takura min yarinya ko? Dan duk duniya a yanzu banda kowa sai Arwa. Itace farin cikina itace nishaɗi na a itace mafarkina. Dan a yanzu duk wahalar da nake wajen ganin na tara dan ita ne. Ina son duk randa zata kalleni a matsayin mahaifi tasan cewa eh na cancanta.....”
“Hummm kaga ba wannan ya kawoni ba. Akwai matsala fa. Wawan tsohon nan nason raina mana hankali. Tana neman ƙwaɓewa amma ya zauna fushin banza da wofi a maimakon mafitar da zata ɓulle”.
Yanzu kam serious commando ya koma.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒗𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_
.........A cije ya ce, “Miya faru kuma?”.
“Humm! Miye ma bai faru ba”.
Tsaff Hajiya ƙarama ta kwashe labarin komai ta bashi. Har korar da Baba prof ya mata yanzun nan. Ta ɗora da faɗin, “Nifa na fara tunanin tafiya plan b. Kawai mu kauda tsohon nan dan na gaji da harkar nan wlhy. Ina buƙatar zuwa na huta. Tuni da mun gama aikinmu amma tsohon nan sai raina mana hankali yake yana jammu a ƙasa, shi banda ma kansa a toshe yake a shekarun nan nasa an gama barbaɗa masa gishirin mutuwa uwar mi zaiyi da kuɗin nan? Amma yabi duk ya maidamu yaransa, garama kai dama yaronsa ne, amma Ni dan uwar ubansa ba aiki mukeyi kai da kai ba, nafa fara gajiya da raina min hankalin da yake dan yana ganina mace, wlhy na fisa bushewar zuciya”.
“Bake kaɗai bace kika gaji da aiki da wannan mutumin, ni kaina na fara gajiya. Dan na fahimci kansa kawai ya sani. Sannan kuma tunaninsa sam baya tafiya yanda ya kamata. Yanzu ko akan zancen yarinyar nan da ake tayi da kuma Maash na bashi ƙafa ne naga ko zaiyi tunani irin na masu hankali. Sai dai da alama giya ta cinye brain ɗinsa. Sam baya tunani irin na masu hankali. Maash fa ba shashasha bane ba, dan shi yana aiki ne da ƙwaƙwalwa da zuciya a lokaci ɗaya. Idan da bai san wanene shi ba tabbas da alama yanzu ya fara farga, dan idan har zamuyi lissafi irin na masu hankali a bayanin da kikamin yanzu akwai lauje cikin naɗi. In babu rami to miya kawo rami. Ya ɗauke mahaifiyarsa ya maida sashensa duk da azababben asirin da oga ya musu. Ƙaninsa ya dawo, a gaba ɗaya yanda yaron ya dawo kuma an tsarata ne. Mi hakan ke nufi”.
“Abinda naso ya fahimta kenan ai amma shi jaki ya wani kironi. Nifa yanzu wannan duk matsalarsa ne. Kawai mu tafi plan b. Dan bazamu cigaba da zama yana juyamu ba. Idan bai sani ba shine a tafin hannunmu ba mune a tafin hannunsa ba. Sannan muke juyashi, ba shike juya mu ba. Duk randa kuma yasan su waye mu wlhy sai zuciyarsa ta buga”.
Dariya sosai Commondo ya kece da ita, sai da yayi mai isarsa kafin ya kalleta yana wani rausayar da kai irin na manyan ƙwari. “Barsa wasa yake da wuta, amma bai san itace zata ƙona shi ba. Na yarda dake kaiwa mu tafi plan b”.
Idanu ta kashe masa tare da bashi hannu suka tafa. Sai kuma ta ce, “Kai tsaya! tsaya! Kayi maganar akwai alaƙa tsakanin yarinyar nan da Awwab. Kana nufin akwai abinda kake ɓoyema yallaɓai akan binciken daya sakaka akan ta ne? Danni fa na gama yarda da gasken gaske yarinyar nan Awwab ya aureta”.
Wani shegen murmushi Commando ya saki, a zuciyarsa yace (Shegiya tsuntsuwar kanari mai wayo. Ai kema bazaki sani ba dan da wannan makamin zan yaƙeki. Yanda zamu haɗu mu kauda yallaɓai haka nima zan kaudaki, kudai gama yimin wahalar, ɗiyata kuwa sai ta dawo hannuna) a fili kuwa sake faɗaɗa murmushin yayi har haƙoransa na bayyana ya ce, “Karki damu zaki sani idan ma akwai in babu sai nan gaba. Yanzu dai ina da uziri. Amma mu haɗu zuwa gobe kamar zai fi.”
(Matsiyaci tabbas akwai abinda kake ɓoyewa. Amma zanyi maganinka. Mudai gama da Yallaɓan kaine next. Dan ku dukanku sai na goge muku hadda. Badai Arwa ce mai gadonka ba, ka gama amsar kason ka kaima na kaudaka dan har abada ƴata bazata san kaine mahaifinta ba. Kamar yanda na sanarma iyayena ka jima da mutuwa da itama kanta har abada a haka zamu cigaba da tafiya) Hajiya ƙarama ce ke wannan zantuka a zuciyarsa. A zahiri kuwa sai ta saki murmushi da faɗin, “Yanda kace ai haka za'ayi Abban Arwa. Kadai tabbatar ka kirani da wuri dan muyi mu gama kasanshi baya tsayawa waje ɗaya. Dan yana ganin yanzu tana neman ƙwaɓewa wata hanyar zai nemo balle ga Awwab ɗin yayi tafiya”.
“Baki da matsala kema kin sanni ai. Na barki lafiya”. Ya ƙare maganar yana buɗe ƙofar ya fice abinsa. Yana gama fita ta dallama bayansa harara tare da taɓe baki. Mamaki ma take yanda akai ta auri guy ɗin nan. Babu yanda Ummu-Hidaya bata bata shawara ba amma a lokacin ta dage akan itafa taga miji. Haka tayi zaman shekaru kusan biyu da shi suka haifi Arwa. Arwa nada shekara ɗaya aka kamashi akan laifin kisan kai. Prison aka kaisa ɗaurin rai da rai. Hakan yasa kawai ta yanke hukunci da tsarama iyayenta da duk danginta cewar yayi haɗarin mota ya mutu dan ba'anan Lagos aka kama shi ba a arewa ne. Kowa ya yarda da ita dan yanda ta tsara komai dole ne ma a yardan, balle ita ba cikakkiyar bahausa bace tana da yare. Anyi zaman makoki da komai da akema mamaci tayi basajar yin takaba. Bayan nan da shekara ɗaya da wasu wattani sannan Arwa nada kusan shekara uku ta auri Alhaji El-Mu'azz, kusan shekara huɗu da aurensu kwatsam sai ga Commondo ya dawo, ba kuma kowane ya fiddosa ba sai Baba prof.. fitowar commondo taso zame mata matsala, dan ya ta mata barazana akan indai bata bar Paah ba sai ya tona mata asiri ya kuma halaka ta. Barazanar nan yasa ya dinga cin kuɗi a hannunta na hauka, har sai da taga abin ya tasarma gurguntata sannan ta zauna ta sanar masa planning ɗinta na auren El-Mu'azz. Tun daga lokacin suka shirya sabon plan akan yallaɓai kasancewar shi commondo yaron yallaɓai ne na ammana kusan ma yana ɗaya a cikin waɗanda suka ƙara kangarar da shi a sanda ya fara rashin ji. Dan haka ɗan amana ne na Baba prof matuƙa shiyyasa suke ganin zasu kadashi cikin sauƙi. A mafi yawan lokuta idan ya ƙulla sukan warware masa batare daya sani ba. Hakama Hajiya ƙarama idan ta ƙulla commondo na warware mata batare data sani ba. Shima kuma commondo ɗin Hajiya ƙaramar kan warware masa. Haka dai suke wannan rayuwa tacin amanar juna amma a zahiri su amintattun juna ne....
🌿🌿🌿🌿🌿
Ranta a ɓace yake har ƙololuwar zuciya. Ta kuma gama yankema kanta koyama Fahad da yarinyar nan dama Awwab ɗin hankali. Hatta da ɗan uwanta bazata ƙyale ba. Waya ta ɗauka tai kiran Auta. Kamar itace ta mata laifin cikin masifa ta zayyane mata komai. Mashi'a sam bata da son fitina. Sai kawai ta shiga bata haƙuri da tabbatar mata cewar tana nan tafe in sha ALLAHU. A satin nan zata shigo Nigeria dan sutukarta ma babu lafiya. Jin hakan ya ɗan sakama Hajiya Mammah nutsuwa. Amma duk da hakan sai da tai kiran Rubayya da rabon da suyi waya harta manta. Da farko Rubayya masifa ta balbaleta da shi. Sai da itama Hajiya Mammah ɗin ta hayayyaƙo mata sannan suka koma dai-dai. Amma duk da hakan ita Rubayya tace bazata zo Maash Mansion ba sai dai ita taje gida ta sameta. Da yake itace ke so kuma a ƙage take ko gardama batai mata ba tace tana jirata gata nan zuwa.
Hakan kuwa akai, ta tashi tai shiri cikin shiga ta alfarma da fariyya data saba ta fita drivern ta ya jata suka wuce gidan aminiyar tata....
To ALLAH yasa a ƙulla alkairi ƙawar o'e🥱😵.
🩸💦🩸💦🩸
Na jima a kwance ina ƙullawa da kwancewa akan rayuwa da kwamacalar gidan nan, tare da abinda na gani game da Ummie. Sai kewar mijina data addaban, dan kona faɗa kona ɓoye haka dai al'amarin yake ina jin kewarsa matuƙa. Hirarsa ta jiya da mutumin nan a office ce ta sake dawo min. Tuna abinda ya bashi flash da file yasa na miƙe na fito. Ɗakinsa na shiga, komai tsaff kamar yanda na gyarashi a ɗazun. Bincike na fara a closet ɗinsa dan tabbas ina son sanin mike a cikin flash ɗin nan. Duk inda nai hasashen zai iya ɓoyesa ban ganshi ba, sai a ƙarshe a banza na samosa ata inda ma mutum bazai taɓa tunanin an ajiye ba. Ganin harda file ɗin yasa na yarda shine. Iya flash ɗin kawai na ɗauka, dan nafi damuwa da son ganin abinda ke'a cikinsa. Sai dai yanzu damuwar a ina zan samu waya ko laptop na kallonsa? Badan babu wayoyi a gidan ba, sai don komai na son sirri ai a rayuwa. Musamman ma wannan shima bazai so ace na saka a wayar wani na kalla ɗin ba. Ban samu makamar kamawa ba. Dan haka na maidashi na ajiye a wajen na fito akan sai na samu mafita. Ƙasa na sauka domin nema mana abincin lunch, amma sai da na leƙa Ummie. Na samu Mama na kwance mata kai sai kawai na fito nima na shiga kitchen ɗin. Ban jima da farawa ba sai ga Fahad da Hafiz. Nan fa sukai zaman tayani munayi muna hira. Ni harma mamakin shaƙuwar Hafiz ɗin da Fahad nakeyi. Sai ka rantse sun san juna tuntuni. Muna kammala abincin salla muka nema, daga nan kowa yayo wanka muka fito.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐_
......Bayan mun kammala lunch su Fahad suka tafi ɗakko Aunty Falaq. Basu wani jimaba kuwa sai gasu. Matuƙar farin ciki duk muka tsinta kammu. Yanda naga Falaq ta rungume Ummie tana kuka da yanda Ummien keta faman shafa kanta da cikinta yasa na sake shiga ƙaulani. Tabbas akwai shaƙuwa a tsakaninsu daka gani, amma duk mai hankali zai iya sakama yanayin Ummien alamar tambaya. Daga baya kuma da taga kamar zamu farga sai ta canja yanayi tama kwanta. Dole muka dawo falo aka buɗe babin sabon hira, salla kawai ke tada mu. Kamar wasa da dare sai ga