Showing 342001 words to 345000 words out of 438336 words

Chapter 115 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2247

mai naƙuda ta samu katifa hahahaha!!!”.
Wani irin kallo Commondo yake ma Baba prof. Cikin zafin rai ya ce, “Oga!!”.
“Don't call me Oga again!!”.
Baba prof ya faɗa a matuƙar zafafe. Wani shegen murmushi Commondo ɗin ya saki da jinjina kansa. Tabbas badan handcuffs ɗin hannunsa ba babu abinda zai hanashi raunata mutanen nan guda biyu, har shi zasu haɗema kai. Amma babu komai zai musu abinda sai sun gwammace inama raunin yaji musu. Cikin tsantsan tsana ya kallesu ɗaya bayan ɗaya, “Lallai ku sani ku dukanku zaku tafka babban kuskuren da sai kun dawwama kuna nadamarsa a rayuwarku. Dan ni Commondo tauraro ne mai wutsiya. Sannan cinnaka nake ban san na gida ba. A tafiyata kuwa bana GUDU DA WAIWAYE. Idan har kaga nayi, abu mai matuƙar muhimmanci na dawo ɗauka. Kada ku taɓa tunanin ƙarfin iko ko faɗa ajin da kuke taƙama da shi zai tserar da ku daga tarkon Commondo. Dan *_TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE_*. Kusa a ranku yanzu ne wasan zai faraaaaaa!!!!”.
Daga Hajiya ƙarama har Baba prof sai da suka ja baya saboda yanda Commondo ya ƙarasa magana ta ƙarshe a kausashe kuma da tsawa. Yayinda Jannifer ta kece da dariya. Sai da tayi mai isarta duk suna kallonta sannan ta dubi Hajiya ƙaramar.........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_


......“Hajjaju wannan duk damuwarku ce dan ku kuka san kanku. Ni a wane matsaya nake? Dan bana buƙatar sake kwana a wannan wajen da ga ni har yara na. Kin san fa ni ba irin Commondo bace, da an cigaba da takura min bakina buɗewa yake caaaaaa!!!!! Da magana”.
Fushin Commondo yasa Hajiya ƙarama watsama Jannifer harara. A harzuƙe ta furta, “In bakin naki bai buɗeba baki cika ƴar halak ba Jannifer. Shashasha kawai ana batun masu hankali kina sako ruɓaɓɓen bakinki. K! har kina da bakin ma jefama mutane maganar banza batare da an sakoki ciki ba”.
“Oh yeer! Hajiya Lawisa amma dai kin san ni tururuwace bana jidon banza ko?”.
“Duk jidon naki kiyi dan iyakarki tsintar gero da dawa amma ƙashi ko nama ƙaryarki”.
“Haka kika ce?”.
“Nama ce fiye da haka. Dan ku dukanku anan zan iya da ku”.
“Ai ba abin mamaki bane dan MAGE taci amanar KARE!!”.
Wata murya a bazata ta daki dodon kunnensu. Gaba ɗayansu suka juya ga ƙofa da basu san yaushe aka buɗeta ba har mai maganar ya shigo musu babu notis. Kusan a tare Hajiya ƙarama da Baba prof sukai baya. Yayinda Commondo yay wata irin zabura da ga zaune yana ƙwalalo idanu waje. Jannifer da bata san ko waye ba kuwa ta ce, “Wannan gaskiya ne ɗan uwa”.
Murmushi Jaga ya sakar mata tare da kashe ido ɗaya yay mata alamar jinjina. Sai kuma ya wani ɗan jujjuya kai yana mai gyara tsaiwa cike da gadara ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Kafin ya tsaida idanun kan Commondo. Rawa jikin Commondo ya farayi sosai. Da ƙyar ya iya furta kalmar, “Jaga! Fatalwa?”.
“Yes I'm. Amma ni ba fatalwa bane JAGA!!!! ne”. Ya ƙare maganar da wani irin kashe ido ɗaya cike da salon iskanci. Lokaci ɗaya Hajiya ƙarama da Commondo suka saki ihu. Yayinda zuciyar Baba prof kawai ta tsarga lokaci ɗaya cikinsa yay wani irin kalar bada sauti sai gudawa tsuuuuuu!!! Daga tsaye. Dariya Jaga ya kwashe da ita. Sai kuma ya nuna Baba prof da yatsa, ya nuna Commondo, ya nuna Hajiya ƙarama sannan ya kai hannunsa kan wuyansa yay alamar yankawa. Tuni itama Hajiya ƙarama fitsari ya ɓalle mata ƙafafunta suka fara rawa.
Cike da mamakin abinda ke faruwa da yanda zakunan dake hanƙoro kusan na mintuna talatin babu mai jin wani duk suka gigice Jannifer ta kalla Jaga cike da rashin damuwa ta ce, “Ɗan uwa halan kai ɗin waye dan ALLAH?!”.
“JaGa!!!! Gawa ta ƙi rami kenan. Sun gina naƙi shiga, ɗan Badamasi ke nan ajiyar ALLAH, mutuwarka sai cikar kwanakinka. Namiji ƙi gudu sa maza gudu. Ki basu shawara, yanzu ba lokacin gardama bane ba lokacin GUDUN CETON RAI NE. Domin gab ZAKI na gaskiya yake da fitowa shawagi. Dan haka mun shiga ƙarnin MAI RABON GANIN BAƊI YA GANI. Maƙiyanka fadawanka. A kafta Yaya Maaaaashhhhhhh!!!”.
Ya faɗa yana tafa hannunsa sai ko ɗiffff wuta ta ɗauke duhu ya bayyana. Wani irin masifaffen ihu Hajiya ƙarama ta fasa dan a zatonta fa Maash ɗinne ya shigo, itama sai gudawa zuuuu. Yayinda Baba prof ya yanke jiki ya faɗi kawai. Commondo kansa a gigice yake dan shi fa kamar su duk sun ɗauka fatalwa jaga yay musu, sannan ganin Maash anan ɗin tamkar ƙarshen numfashinsu ne. Ita kanta Jannifer da bata fahimci tushen zancen ba jin sunan Maash ya saka ƙirjinta fara karkarwa ta kawai fashe da kuka. Ga duhu office ɗin......

😂Wai miyyasa mutanen ke tsoron Yayanmu haka🤣. Koda yake shifa mara gaskiya ko a ruwa jiɓi yake🥱

🩸✨🩸✨🩸

Gaba ɗaya ya hanani sake sauka ƙasa. Sai shine yaje massalaci. Bai dawo ba sai da akai isha'i. Da wannan damar nai amfani na sauka na haɗo masa abinci. Ummie na ciki saboda Paah, su Hafizzullah ma da alama suna masallaci tare da shi. Aunty Falaq ma na ɗaki dan haka harna gama abinda zanyi babu kowa a farlon. Ina idar da sallar isha'in na kwanta a wajen dan ɗan sanyi-sanyi nake so. Daga azhar har zuwa gabannin asubahi zaka sameni lafiya Lau kamar banda wata damuwa. Ana ce miki asuba tayi da ƙyar nake yin salla sai zazzaɓi da amaye-amaye har sai rana ta ɗaga kuma. Jin an ɗagani na buɗe idanuna, dan nasan mai mun hakan sai dai shi. Kallonsa nayi tare da ɗan tura baki gaba. Cike da shagwaɓa na ce, “Please My Hot ALLAH can yafi daɗi”.
Bai tanka min ba sai da ya sauke ni saman gadon. Yana ranƙwafe a kaina idanunsa cikin nawa yana bina da wani kasalallen kallo da zuwa yanzu na fara fahimtar fassarar halin da yake ciki a duk sanda yake mun shi. Cikin motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta, “Kina son ki haifar min yara da sanyi?”.
Kai na girgiza masa a marairaice kamar zanyi kuka na ce, “ALLAH yafi min daɗi ne fa”.
Bai ce komai ba ya kwanta ta gefena yana mai rungumeni a jikinsa. A tare muka sauke ajiyar zuciya. Nima sai na sake shige masa da sake ƙanƙame shi. Mun jima a haka kafin ya fara canja salon kwanciyar tamu zuwa wani abu daban. Mamaki ya sani ɗagowa na kallesa. Ɗazun nan fa barowarmu falo ya.... Tunanina ya katse jin saukar mitsitsin lips ɗinsa kan nawa. Yanda ya iya bin hanyoyin mantar da mutum kansa yasa tuni ma na saki ragamar duk da nasan wahala ce dai bazan fasa shanta ba. Dan shi ɗin bana wasan yara bane. Marmarine da ga nesa....

Nako ji a jikina, haka na lafke masa wanka ma sai da taimakonsa. Dan ma yunwar da nake ji ta sa na kasa kwanciya na ce masa abinci zanci. Da kansa ya zubo abincin yazo ya zauna ya dinga bani. Nima sai na amsa ina bashi. Hakan ya ɗan taimaka min na ɗan ci shima yaci. Ina cewa na ƙoshi shima kuwa yace ya ƙoshi. Mamaki yake bani dan ban taɓa gamo da wanda bai damu da zaman cin abinci ba irinsa. Kwance zan kai ya kamani ya zaunar yana girgiza min kai alamar karna kwanta. Cikin shagwaɓa na ɗan tura baki dan kwanciyar nake so. Bai kulani ba sai jinginani da yay da jikinsa kawai ta ɗauki wayarsa yana latsawa. Ajiyar zuciya na sauke kaɗan, idona akan wayar nima nace, “Ya Awwab”.
“Uhhyimm”.
“Yarinyar nan ya kake ganin zamuyi da ita?”.
Shiru kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya ajiye wayar yana furzar da numfashi. “Ki bar komai a hannuna dan zuwa yanzu haka ma tana hannu”.
“What! Ya akai hakan?”.
Na faɗa ina tashi zaune da ƙyau. Kallona yay shima sai kuma ya ɗan lumshe ido ya sake buɗewa akaina. Akan lips ya furta, “Bana wasa da DAMA”.
“Ni shaida ce”.
Na faɗa cikin kashe masa ido ɗaya da kai baki a hankali na sumbaci kumatunsa. Murmushi ya saki mai ƙayatarwa ya jawoni jikinsa ya rungume. Kiran wayarsa ne ya katse mu. Ɗauka yay, kasancewar muna a kusa da juna yasa naji duk abinda Hayatun ke faɗa. Yana ajiye wayar ya miƙe nima na miƙe. Kallona yay na ɗaga masa gira da faɗin, “Lokacin da zan taimaki mijina da tawa basirar yayi. Let's go”.
“My baby”.
Ya faɗa da soft murya yana kallon cikina.
Nima ƙasan nayi da muryata ina mai ɗora hannuna saman cikina na furta, “Yana tare da kariyar UBANGIJI”.
Baice komai ba yay gaba. Nima sai na juya na fita zuwa nawa ɗakin. Babu jimawa na fito, sai naci karo da shi a ƙofa yana niyyar shigowa. Batare da yace komai ba ya kama hannuna kawai.....


💥💥💥

Sai da taimakon Isma'il Baba prof ya koma gida. Tsabar ɗimuwar da yake ciki yasa baima fahimci wanda ya maida shin ba. Hakama Hajiya ƙarama ita kanta bata san a yanda ta dawo gidan ba. Kawai dai ta tsinta kanta a bakin gate. Batako saurari mai taxi daya kawota ba ta afka ciki sai securitys ɗin ƙofa ne dake binta da kallo suna toshe hancin qarin kashin da take suka biya shi. Da ga Maash har Hayatu da Samraah da TJ dake jan motar da zasu fita da kallo suka bita suma.
Nannauyan numfashi na sauke da faɗin, “To ita kuma wannan ƙalau take kuwa? Jibafa jikinta kamar wadda tai kashi, gashi sam bata a hayyacinta”.
Hayatu ne cikin ƴar dariya ya karɓe da faɗin, “Babu tantama aikin Jaga ne wannan”.
“Jaga kuma?”.
Na faɗa ina kallon Maash da yay kamar ma bai san abinda ake yi ba. Yanzun ma bai tanka ba. Sai Hayatun ne dai ya bani amsa da, “Eh, ya kai musu ziyara ne. Kinga ko yanda suke tunanin ya mutu ganinsa a raye ai cakwakiya ce babba. Amma bari na taɓa Isma'il”.
Wayar Isma'il ɗin ya kira. Yana ɗagawa da dariya ya fara daga can. Hayatu shima sai ya fara dariya. Da ƙyar dai cikin dariyar Isma'il ɗin ya bama Hayatun labarin duk abinda ya faru batare da yasan a Hansfree wayar take ba. Shi kansa Tj dariyar yake yi. Yayinda ni kuma nai ƙasa da kaina kawai inayin tawa can cikin maƙoshi. Dan yanzun ma mai gayya da aiki bai tanka ba bai kuma kulamu ba. Cikin ƙanƙanin lokaci muka iso gidan da yay matuƙar ƙayatar dani. Dan ya ginu iya ganin mai kallo, sai ma ka iya ɗauka gilashi ne kawai gaba ɗayansa. Ni dai a zuciyata naita santina har muka shiga ciki.........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_


......Da sauri saurayin da muka samu zaune a falon ya miƙe tsaye cikin nuna girmamawa. Sai budurwar dake ƙasan carpet bakinta a ɗaure da seletep hannunta ma a ɗaure. A kallo ɗaya da nai mata na gane Murjanatu ce. Sai da na ɗan waro idanuna waje ina kallon Maash. Amma sai ya ɗauke nasa cike da basarwa ya cema saurayin da ya kira da Muktar ya kwance mata abin hannunta dana bakinta. Kamar yanda aka bashi umarni yayi, sannan ya koma ya zauna yana mai dakawa Murjanatu data sanya kuka tsawa alamar taima mutane shiru. Shirun kuwa tayi tana hawaye da kallona. Duk sai naji ta bani tausayi. Murya a sanyaye na cema Hayatu su bata ruwa. Babu musu kuwa yaje ya kawo mata. Tako sha sosai tana sauke ajiyar zuciya.
Sai da naga ta ɗan samu nutsuwa sannan na tashi na koma kusa da ita. “Murjanatu”. Na kira sunanta a taisashe. Amsawa tayi muryarta na rawa sosai da jikinta. Kafaɗarta na dafa da kulawa na ce, “Ki kwantar da hankalinki. Bamu kawoki nan domin cutarwa ba. Sai domin mu kuɓutar da ke. Kamar yanda kika sani na faɗa miki sunana a waccan ranar. Sannan kin mun sani na tsakanin mai jiyya da ma'aikaciyar asibiti a wancan karon.”
“Hakane Aunty”.
Ta faɗa muryarta na rawa. Kaina na jinjina da kallon Hayatu na ce, “Yaya Hayat ko zamu samu hoton matar can a wajenku”.
Kai tsaye ya ce, “Abu mai sauƙi”.
Tab dake gefen ogan nasa ya ɗakko, yay ɗan danne-danne ya miƙo min. Hoton Hajiya ƙarama ne rangaɗaɗau kuwa. Anci ado na fariyya kamar kai mata magana ta amsa. Janye idanuna nayi daga kan hoton na maida kan Murjanatu da har yanzu ta kasa nutsuwa da ƙyau. “Murjanatu ina son ki kwantar da hankalinki ki kuma amsa min dukkan tambayar dazan miki. Hakan da zakiyi shine zai kuɓutar da a halinki dan bamu kawoki nan ba sai da muka san komai a kanki”.
“Dan ALLAH aunty kuyi haƙuri kada ku cutar dani, wlhy zan amsa muku duk abinda kuke buƙata. Bana son komai ya samu iyayena”.
“Babu abinda zai samesu. Sai dai ki sani a yanzu haka suna a hannunmu. Idan kin amsa mana abinda muke buƙata babu gargada to tabbas zaki samesu cikin aminci harma mu fidda mahaifinki ƙasar waje yaga likita akan ciwonsa.”
Da sauri ta jinjina min kai cikin ɗokantuwa. Hoton Hajiya ƙarama na nuna mata. Duk yanda taso dakewa sai da muka fahimci razanarta. Muryarta na ɗan rawa ta ce, “Shugabar asibitin da nake aiki ce. Sunanta Doctor Lawisa.”
“Micece alaƙar dake tsakaninki da ita bayan wannan?”.
Baki ta buɗe zata fara rantsuwa na girgiza mata kai da faɗin, “Gaskiya kawai Murjanatu. Dan da kunnena naji tana cin mutuncinki saboda kin sanar da wani cewar an cirema patient appendix. Wlhy kinji na rantse miki, idan baki faɗan gaskiya ba zan tafi na barki da su”. Na ƙare maganar ina nuna mata su Hayatu da Maash da yay wani zaman kasaita yanzu ya kwantar da bayansa da kujera ido a lumshe sai ka ɗauka ma barci yake. Amma ni nasan idonsa biyu mu yake kalloma. Cikin ruɗewa ta shiga roƙona akan karna barta da su zata faɗa. Zama na gyara alamar ina saurarenta.
Sai da ta shaƙi numfashi da kukan da ke mata kai-kawo sannan ta ce, “Aunty zan faɗa miki komai dana sani. Amma dan girman ALLAH ki taimakeni da iyayena in ba hakaba wlhy zata iya halakamu. Dan akwai wani da yaso yin irin wannan kuskuren na fallasa sirrinta har yanzu bamu sake jin labarinsa ba. Hakama mahaifiyarsa wayar gari akayi ta ƙone a gidansu ƙurmis akace gobara ce. Again wata ta taɓa bijirema umarninta a gabanmu ta mata allurar poison ta faɗi a wajen ciwon ciki ranar batai kwanan duniya ba sai akace wai ciwon hanta ne ya kasheta dama ta daɗe da shi a jikinta. Still wata mata ta taɓa fahimtar an cutar da yarinyarta a asibitin tazo na rantse miki tana barin asibitin basu isa gida ba mota ta take napep ɗin da suke ciki sai gawarwakinsu aka dawo da shi asibitin.”
Ba ƙaramin tashi hankalina yayi ba. Amma cikin dauriya nace mata, “In sha ALLAHU Murjanatu mun miki alƙawarin baki dukkan tsaro da kariyar UBANGIJI. Shiyyasa ma muka ɗauke iyayenki kafin ma mu kawoki nan ɗin”.
“Shike nan aunty zan faɗa muku

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login