Showing 366001 words to 369000 words out of 438336 words

Chapter 123 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2163

jin zan iya ɗaukar makami akanki wlhy. Jaka jahila butulu kawai. In sha ALLAHU ƙarshenku bazaiyi ƙyau ba. Ummie kuma ta muku nisa mai tazarar zango da har gaban abada bazaku taɓa iya kamota ba. Jinin iyayenmu kuwa daya rataya a kanku in sha ALLAHU bazai barku sake zaman lafiya ba a rayuwarku daga nan har ranar mutuwarku. Dan yana da nasaba da rashin nasarar ku kuketa wahala na shekara da shekaru har zuwa yanzu kun gagara cimma abu guda. Ciwon da Ummie tayi kuwa ƙaddararta ce wawaye, hakama rabata da ƴaƴanta ƙaddararsu ce. Yanzu da UBANGIJI yaso yaye musu ba gasu ba kukuma har yanzu kuna a ƙasan ƙafafunsu. Kai a tunaninka ka bautar da Ya Awwab yana nema muku duniya kuci kai da zuri'arka ko. Hhhhh baka fahimci ƙarshen labarin naka ba yanzu? Shi da kake tunanin ka bautar, da ku ƴan kwanciya a kawo muku kuci matsayin iyayen gida waye ta ƙaremawa? Waye ya faɗi ƙasa wanwar? Dawa ta ɓare? Da ku, ku ɗin nan marasa tawakkali ga UBANGIJI, marasa tauhidi da yarda da ALLAH ba abin wasan wani banza bane. Idan dai har ƙyautatawa zata iya zama wa irinku mutum bazai taɓa fatan ƙyautatama kowa ba. Dan kune kesa bayin ALLAH tsoron ƙyautata ma mutane a wannan ƙarni, kuke saka a gagara banbance na ƙwarai da butulallu irinku. Kaicon bawan da za'a ƙyautatama da tarin alkairi ya maida da sharri. Kaicon bawan da zai dinga kallon hidimarsa ga wani kamar ta fi ƙarfin ƙyautatawar da yake masa koda ya fitar da hakkinsa. Kai kana ganin kun tallafa ma Abie ya tashi saboda ya shigo ƙasarku matsayin baƙo. Ka hidimta masa, ka masa miye, ka masa miye, miye, ko. To amma malam mai hidima idan har da kunya a tare da kai kuwa ya dace ka zauna bamu wannan labarin ma?. A wannan hidimar da kai masa fa, shima shine ya ɗauki nauyin karatunka har zuwa wata ƙasa. Ya baro iyalanka daga ƙauye suma ya ƙyautata rayuwarsu, ya ɗauke su ya kai su ƙasar da kake ya inganta musu rayuwa da ilimi....”
“Ilimi kodai ya lalata musu rayuwa, ta sanadin hakan ɗana ya lalace da neman mata....”
A fusace na ce, “Ban gama magabata ba kada ka sake katseni!!!!”. Babu wanda bai kallan ba a falon, dan nayi magana ne fa like wata boss lady, ni kaina naga ƙarfin hali na. Fahad ya kwashe da dariya tare da faɗin, “Duk wanda ya ƙara katseki Aunty Sam ALLAH sai na kwashe miki ƙafafunsa. Cigaba da basu bayani.”
Jinjina nai masa da satar kallon Maash, zaune kawai yake kansa a ƙasa ya dafe shi da duka hannayensa. Ummie kam kallona take tana murmushi. Murmushin na mata nima da cigaba da faɗin, “Abie bai lalata maka ɗa ko ɗaya ba. Baƙin halayyarka ce ta lalata su. Ko baka san masu iya magana kance TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE ba. To ka binciki kanka da kanka kaine amsar tambayar abinda ke zagaye da zuri'arka. Abie ya baka gida bayan dawowarka, ya baka motar hawa. Ya ɗauki company guda sukutum ya baka tare da kuɗaɗen da zaka kafa Bussines. Ya ɗauki ƴarsa ɗaya tilo ya bama ɗanka aurenta. Duk da wahalar da take sha bata taɓa iya gaya masa ba ta shanye tai haƙuri, har ma tana tattali da fatan haihuwa da shi, a hakan da yake sonshi take. Duk da halin daka nunama mahaifinta na banza, ka kuma fiddo masa da ainahinka a sanda yake gadon asibiti bai gaya mata wanene kai ba saboda halin dattako. Bai ce ta rabu da ɗan ka ba. Bai ce ta tuhumeka da abinda ka aikata masa ba, sai ma cewa yay duk rintsi ta kasance da shi, duk rintsi ta maka biyayya a matsayin ƙaninsa na jini. Kaji halin manyan ƙwarai masu tauhidi. Dan ALLAH abin bai birgeka ba?. A lokacin da kazoma da Ummie baƙin halinka ɗanta nada wayon da zata sanar masa. Ya ƙullaceka a zuciya har kawo yau. Amma ka duba batace ma kowa komai ba har ka aikata abinda kake ganin damace ta baka ka aikata. Har warkewa tai a lokacin da shekarunsa suka kai yasan komai amma ta shanye bata faɗa masa ba. A hakan bata faɗa masa ba da ilimin da UBANGIJI ya bashi ya gano kai ɗin wanene? Amma duk da haka bai tunkareka ba ya barka da halinka shima. Baka tunanin talala suka maka na barinka da ƙarfin ikon ALLAH har azo irin wannan gaɓar da zaka fallasa kanka da kanka?. Ke ko baƙar tsinanna ai bani ma da abin faɗa a kanki. Dan ke baki da banbanci da dabbobin aladu masu cin kashi matsayin abincinsu. Kuma a cikinku duk ma wanda ya ɗauka min ƴan uwa ya dawo min da su. Idan ba haka ba ni ba Ummie bace da zata iya barinku da halinku, take a yanzu zan sakaku kuyi nadama wlhy, dan kunga wayar nan, komai da kuka faɗa ta kwashe a ciki, yanzu kuma zan tabbatar muku da sunana ƴar jarida ne. Bara kuma ku gani”.
Kaf falon babu wanda bai waro idanu a kallona ba. Yayinda prof ya zaburo kaina jikinsa na rawa. Babu zato kawai mukaga Maash a tsakkiyar mu. Kallonsa yake kamar zai cinyesa da idanu. Cikin matuƙar fusata ya ce, “Mi zakayi”.
A fusace shima prof ɗin ya furta, “Duk abinda zuciyarka take tunanin zan iya. Har yaushe aka haifi ubanta ma balle ita da take tunanin wani abu”.........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑵𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚_


.......“Ai ko da kayi mafi girman kuskuren data faɗa zakayi, dan daka taɓa koda kayan jikin wannan wlhy Gara kaje ka ringume transformer kasan dama tsautsayi ya kaika. Oh kai da tunaninka zakayi duk wannan surutun naka ya tafi a banza yaranka su kashe mu ka fice salin alin zuwa airport ka hau jirgin zuwa Saudia daka gama shiri ko, daga can ka wuce ƙasar da kake so. To ai ka makaro. Dan wannan TSUTSAR NAMAN ITAMA NAMA CE. Idan taƙadaranci kakeji ka iya kada ka manta jininka ne ni, na ɗebo daga wasu ɗabi'unka, sai dai ina bi dasu ta hanya mai ƙyau domin maganin irinka. Idan kuma dattako ne, jinin Ibrahim nake, kaga ko gidan ka taras. Bari na faɗa maka abinda baka sani ba. Tun daga randa na gane kai wanene duk wani motsinka a tafin hannuna kake yinsa. Kaf ma'aikatan gidanka da kake gani aikina suke yi.” ya ƙare maganar da kallon ƙofa ya ce, “Bismillah”.
Ba prof ba mu kammu sai da zukatanmu suka girgiza. Duk da ni Bama sanin ma'aikatan nai ba tunda ba taɓa zuwa gidansa nayi ba. Isma'il Kuku ne farkon shigowa. Sai maigadi, amintaccensa, drivernsa daya taɓa karyawa, bai san sanda ya bar hannun Commondo ba sai dai har yanzu akwai ɗaurin karaya a hannunsa. Amintaccensa, mai bayin filawa, masu share-share da goge etc. Taga-taga prof yay zai zube ƙasa sai da Hayatu ya taresa yana faɗin, “Hankali dai Baba hankali”. A yanda yay maganar kowa yasan akwai shaƙiyanci a ciki. Aiko Fahad ta bushe da dariya da faɗin, “ALLAH Yaya Hayat dama ka barsa ya ɗan sha ƙasa”. Mangare kan Fahad Ummie tayi kaɗan.
Dafe ƙirji Baba prof ɗin yayi. Abin mamaki fuskar Maash da murmushi ya ce, “No no ai lokacin bugawar zuciyar baiyi ba da saura ɗan dakata min.” juyawa yay ya kalla masu bindugun dake zagaye da mu. A take suka sauke bindugun suna murmushi. Sai kuma suka haɗe hanayensu waje guda suka ɗan risina wa Ummie alamar ban haƙuri, nima suka juyo suka rissina min, sukaima Fahad da Hayatu ma haka... A razane Baba prof ya ce, “What?! Ozee. Ni zaku cima amana? Na ɗauki nauyin zuwanku tun daga ƙasarku kuce wani kuke ma aiki ba ni ba?.”
“Dama can bakai mukazo yima aikin ba old man. Dan tun kafin kazo garemu shine ya fara zuwa”. Ozee yay maganar cikin nuna girmamawa ga Maash da harshen turanci. Idanu kawai ya lumshe musu ya buɗe su akan Prof da ya gama diriricewa yana kalle-kalle. Murmushi Maash yay da faɗin, “Oh Mr Paul daya ɗakko maka hayarsu kake nema. Hayat!”. Da sauri Hayatu yay salute ɗin Maash ɗin cike da girmamawa yana fita, sai ko ga Mr Paul bayansa da police biyu ya shigo. Maimakon ya kalla Prof sai ya rissina ya gaishe da Maash.
“Kuturun bala'i, Yaya kana aljanna ina binka da addu'a wlhy, harma Ministar guda a ƙarƙashin komarka yake. Shegiya nera duniya ce”. Fahad ne da wannan maganar yana miƙewa zaram. Ba shi ba mu kammu abin ya matuƙar razana mu. Mr Paul fa da kowa ya sani Minister mai faɗa aji a ƙasar. Eh kam gaskiyar Fahad Naira maganin wata magana. Yanzu kam Baba prof sai da ya kai ƙasa yana nuna Mr Paul da hannu, murya da bakinsa na rawa ya ce, “Kaima munafukina ne dama Mr Paul?”.
Cikin halin ko'in kula Mr Paul ya ce, “Professor magana ce ta kuɗi fa. Sannan magana ta gaskiya Maash yafi ƙarfina, ya wuce da sani na. Bani da zaɓin da ya wuce goya masa baya. Kadai san ni akan kuɗi Mamana ma zan iya badawa”.
“Kutumelacy babarka fa? Shege Ministar yasan takarda hhhhhh!!”. Fahad ne da iskancin nan yanzu ma. Yanzu kam kasa daurewa nayi sai da na murmusa ina mai girgiza kaina. Yayinda Hawaye suka ɓallema Prof a bazata. Nan ma murmushin Maash ya sake saki da faɗin, “Inaa ai lokacin kuka ma baiyi ba. Hayat next level.”
Sake fita Hayatu yayi sai gashi ya shigo da Jaga. Sai wani takun ƙasaita yake ana bubbuɗewa cikin tsadaddun suit Dan yanzu kam Maash ya ɗaure masa ƙugu. Baba prof zai zabura Jaga ya dafesa yana dariya da faɗin, “No tsoho kwantar da hankalinka ba Fatalwa bane JAGUS ne”.
Kalmar JAGUS ɗin nan daya faɗa ita ta sakamu dariya. Dan hatta Maash ɗin sai da yay ɗan girgiza kansa. Cike da izza Jaga ya cigaba da faɗin, “Kun zata na mutu ko? To kwana basu ƙare ba old man. Kasan mu ƴan gidanmu ALLAH ya bamu tsahon rai. Kakana na goma ance shekara ɗari huɗu yayi a duniya, hakama na tara dana takwas dana bakai. Na shidda ne yay ɗari uku da uku, na biyar kuwa ɗari uku da arba'in. Na hudu yay ɗari biyu, na uku kuwa ɗari da hamsin, shine ya fara rage mana mudu. Wanda ya haifi ubanta ɗari da arba'in yayi, babana kuwa har yanzu yana raye ya kusan cika ɗari da hamsin shima. Ya kake tunani akan ni JAGA, ai maybe ma kakana na goma zan gado nayi four hundred inji turawa, larabawa kuma sukace أربعة مئة.
Wani tsugunne gayu yay a gaban Baba prof ya kamo gemunsa yana wasa da shi fuskarsa da murmushi ya furta, “To ya kake ganin zaku kasheni tashi ɗaya na tafi tsoho? Abinda fa baku sani ba shi wannan bawan ALLAHn KAINUWA ne, sannan DUTSENE na rimi bashi fargaba ko ta ruwa. KWAI NE kuma CIKIN ƘAYA ajiyar ALLAH. Idan har munanan hallayarku zaku iya jan ra'ayinmu ku lalata mana rayuwa da bamu kuɗi da kayan maye, ta yaya kuke tunanin adali irinsa dake ƙoƙarin ƙyautata rayuwarmu bazai iya janye ra'ayinmu daga gare ku ba. Kai ka godema ALLAH a Muktar nazo nan ba Jaga ba, da wlhy sai na jajjage maka hanjin cikinka tsaf da wuƙa. Kasa a kasheni kai da yaronka da waccan ƴar iskar karuwar yar karuwa”. Ya nuna Hajiya ƙarama. Idanu ta waro waje da faɗin, “Ni ce karuwar ƴar karuwa?”. Muryarta na rawa. Murmushi Jaga yay yana miƙewa cikin wani ɗan iskan rangaji ya isa gabanta, sai da yay mata wani kallon sama da ƙasa sannan ya furta, “Oh maimaici kike buƙata kenan. To aike kin wuce karuwa ma. Matar datai aure kan aure jama'a miya kamata a kirata”. Yay maganar yana juyawa ya kalla kowa a farlon. Cike da shaƙiyanci Fahad ya ce, “Sai dai Uwar ƙaruwar Ya Muktar”.
“Oh oh I love you my ƙani. Nima na zama babba”.
Jaga ya bama Fahad amsa yana wani tsuke baki kamar zai yi kiss da girgiza kai like yanama ɗan yaro wasa. Dariya mafi yawanmu a falon mukayi, dan hatta Ummie sai da ta murmusa. Uban gayyar dai yanzu ma kai kawai ya ɗan girgiza. Jaga ya cigaba da faɗin, “Yawwa to kinji sunanki MAGAJIYAR KARUWAI. Bara na baku labarin wannan matar, dan nasan da yawanku baku sani ba hatta shi ogan nata kansa. A ƙauyenmu akan haifeta, kuma bata da uba, dan tsohuwarta a yawon tazubar ta samota itama. Bayan ta haifeta aka rirrima akama uwar aure da wani saurayinta da aka laƙama ƴar duk da shi ya rantse ba ƴarsa bace. Oho musu dai haka suka zauna taren ita lawisa na girma, tsangwamar mutane da hantarar da ake mata duk inda ta gitta ana kiranta ƴar shege, ko talla ta ɗakko babu mai saya yasa, a makaranta yara dunya dukanta kenan ƙanwar uwarta da itama take zaman tazubar ɗin anan Lagos ta ɗakkota ta taho da ita aka nema mata gidan aikatau. Tana fara aiki taga yaran gidan na zuwa makaranta itama tace tana so, haka mai gidan ya sakata amma da sharaɗin bazasu na biyan kuɗin aikinta ba. Tako amince, daga ita har ƙanwar uwar tata. Da yake tayi primary a ƙauyen namu, sai dai bata kammala ba. Amma shi mai gidan nan yay duk yanda yay aka sakata a aji ɗaya na sakandire. Daga nan ƙaddara da tsautsayi suka haɗata da Ummien mu ALLAH ya ƙara miki lafiya da nisan kwana. Ya rissina yana haɗe hannunsa wa Ummie. Murmushi ta sakar masa. Yayinda Fahad ya ce, “SARAUNIYA UMMIE ƳAR IBRAHIM MAMAN MUHAMMAD AWWAB DA SAMRAAH DA FAHAD ta amsa maka babban Yaya”.
“Godiya nake my ƙani”.
Cewar Jaga. Sai kuma ya cigaba da faɗin, kada na jaku da nisa. Tunfa Lawisa na aji biyu ta fara sanin maza, shiyyasa ma ta laƙema kakanmu Alhaji Ibrahim ALLAH ya gafarta masa. Sai dai bata samu nasara ba. Yawon tazubar ɗin nata ya fara yawa bayan ta gama makaranta. Wanda ya auri babarta tana zuwa ƙauye yace ya mata miji da Laminu, idan kuma har bata amince ba zai saki uwarta. Itako uwa bata son barin gidan miji, tacema Lawisa idan bata auri Laminu ba zata tsine mata. Da alama dai bata son tsiniwa, dan haka ta amshi Laminu da hannu biyu akan zata aure amma sai ta gama makaranta. Babu wanda yace a'a, dan a lokacin shima Laminu yana makarantar almajirci bai koma gida ba. Bayan kamar shekara huɗu sai ga Laminu ya dawo, lokacin Lawisa na nan Lagos wai ta zama a malamar asibiti, da akace tazo batun aure ya taso sai ta bijire, ai ko dai aka ɗaura mata aure da Laminu, sannan innarta ta ɗauketa da ƙarfin tuwo takai ƙauye. To abin mamaki kuma bamu san yaya akai ba Lawisa na zuwa ta faɗa soyayyar Laminu, wasu dai na ganin aikin asiri ne ba wani abu ba. Haka dai aka tarkatasu suka taho Lagos dan tace bazata bar aikinta ba. Abinda Lawisa da danginta basu sani ba shima Laminu shegen kansa ne, dan a inda yake ma ya addabi mutane matuƙa, aiko tana kawoshi Lagos idonsa ya buɗe ya fara mu'amula da manyan mutane a riga irinsu su Prof sai ya sake bushewa, dan kuwa wanda ya kashe yaje prison kamashi yay da Lawisa suna ikkanci a ofishinta na asibiti, shine ya bisa har can garinsu ya kashe aka kamashi aka kaisa kotu daga can aka wuce dashi magarƙama. To nadai takaice muku Lawisa taje ƙauye tace Laminu ya mutu a haɗarin mota. Haka akaita kuka da ƴan sadake-sadake musamman iyayensa harna kwana bakwai. Ita kuma ta shiga takaba wai. Bayan ta dawo ta cigaba da harkokinta daga ƙarshe ta auri ɗan oganta”. Ya nuna prof. “Abinda Lawisa da Prof basu sani ba shine. Laminu shine ya koma Commondo kuma yaron prof ne, ita kuma Lawisa mijinta ne uban ƴarta waccan”. Ya nuna Arwa. Wani mugun zabura kuwa Arwa tayi jikinta na rawa. Hannunta dafe da ƙirjinta ta ce, “Na shiga uku ni ɗin?”.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_


*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login