Showing 351001 words to 354000 words out of 438336 words
ce kika haifi Hafizzullah ba?”.
Kai ta jinjina mata alamar tabbatarwa. Tana hawaye ta ce, “Ɗayar matar Abdul-wahab ce ta haifesu, muma bamu san haka ba sai da Alhaji ƙarami ya auro Samraah.....” nan fa ta shiga bata labarin dalilin haɗuwata da Ya Awwab har zuwa aurenmu. Ai gani mukai kawai Ummie ta tafi zata zube ƙasa. Da sauri duk mukai kanta ALLAH dai ya bama Paah sa'a ya rungumeta a jikinsa. Wani irin kuka ta fashe da shi mai ban tausayi da cin rai. Sai kuma ta ture Paah ta miƙe. Wayar Ya Awwab ta ɗauka. Babu wanda yasan mi take yi ta shiga danne-danne sai kuma ta kai a kunne. Ɗan jimm tai har wayar ta shiga aka ɗaga, bata yi ko da sallama ba a kausashe ta ce, “Kai tsinannen matsiyaci maci amana butulu. Da ni kake TAKUN SAƘAR ka saboda nice jinin Ibrahim. Idan har kai ɗin ɗan halak ne kazo muyi gaba-da-gaba a yau ba kai kidnapping wanda basu da alaƙa da kai ba. Dan haka in har ka cika kai Adamu namiji ne ba mata maza ba. Ɗan halak ne ba ɗan shege ba kazo ka sameni”.
Ƙitt ta yanke kiran tana mai wurgar da wayar. Kamar an saita kuwa Maash ya cafeta cikin hannunsa. Wayar shima ya kai kunensa yana wani makirin murmushi dake nuna tsantsar ɓacin ransa da fusata. Cikin tashi kakkausar muryar shima ya furta, “Nasan kaji mi tace. Dan haka ni Muhammad Awwab El-Mu'azz zan maimaita maka yanzu. In dai kai ɗin ba matsoraci bane. Shashasha lusari mai ɓuya a bayan mace. Kuma cikakken namiji ne ba mata mazan ba kazo ka sametan a cikin Mansion. Idan ba haka ba ni zan biyoka har inda kake, idan kuma hakan ta faru wlhy, wlhy sai kayi dana sanin kasancewata a cikin ZURI'ARKA tsohon banza!!”.
Babu wanda jikinsa baya rawa yanzu kam a falon. Dan kaf ɗinmu ba yara bane. Mun kuma fahimci waye wannan da ake wayar da shi. Ko kallon inda wani yake Maash baiyi ba ya fice a binsa. Hayatu da Fahad suka take masa baya. Sai nima kawai na bisu dan bazan iya kallon yanda jikin Paah ke wani irin karkarwa ba........✍️
Tofa, yau fa ake yinta🤔
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐_
*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._
......Ganin sun tunkari motoci nima sai kawai na bisu. Yau kam da kansa ya buɗe mazaunin driver ya shiga. Dan haka na buɗe side ɗin gefensa nima zan shiga kawai mukaga an wangale gate. Abin mamaki motocin Baba prof ɗinne ke shigowa. Duk tsayawa mukai har suka kammala shigowar aka maida gate aka rufe. Kawai sai ƴan iska masu zubin shaiɗanu na dirgowa a motocin riƙe da mugayen bindigu tamkar sojoji sun tafi yaƙi. Harga ALLAH na tsorata, na kuma sake tabbatar da mutumin nan baƙin shaiɗani ne. Sai da yan barandar tasa suka gama zagayemu tsaf sannan shi ya fito. Sanye yake cikin manyan kaya harda hula kamar wani tsohon kirki. Ya kawo baƙin gilashi ya toshe idanunsa. Wani shegen tsaiwar ƴan iska yayi kafin ɗaya daga cikin yaran su kawo masa kujera tsakiyar compound ɗin alamar zama. Hannu ta ɗaga musu yana masa nuni damu ya wuce ainahin ƙofar babban sashen cike da takun ƙasaita.
Dai-dai nan aka fara fito da mutane daga kowanne sashe na gidan ana maidasu sashen masu aiki mazansu da matansu. Ashe tuni ma yaransa sun gama zagayemu da sunan masu decorretion batare da an farga ba. Sai dai ashe nice mai tunanin ba'a fargan ba. Shi gogan yana sane da duk motsin su tunda suka fara aikin. Sai dai ya barsu a ƙarƙashin nasa shirin shima. Ganin ya nufi ƙofar falon shima a fusace muka take masa baya ni da Hayatu da Fahad. Zaune muka sameshi yay zaman ƙasaita, yayinda ƴan iskansa suka zagaye Maash. Muma muna shiga suka zagayemun. Su Azizat dake falon duk sun rikice suna kallon kakan nasu a firguce.
Fito da duk wanda ke sashen yasa ayi. Kusan su Ummie sune ƙarshen fiddowa. Sai Hajiya ƙarama da tai sumar tsaye. Dan ta fahimci shirin wannan makirin tsohon ya danne nata kenan. Sai dai koba komai ta ribantu itama ai, sannan tanada tata nasarar. Ƙananun kukan da su Arwa keyi a wajen yasa ƴan iskan daka tsawa tare da yin harbi. Sake rikicewa falon yayi sai da ƙyar suka lafa. Ta gefen ido na kalla Maash da aka fi zagayewa da bindugun amma babu ko ɗar a tattare da shi. Sai ma tsaiwar ƙasaita ta yay bayansa jingine da bangon falon ya harɗe ƙafafunsa waje guda hannayensa duka biyu cikin aljihun wandonsa. Gefensa Fahad ne shima dai an zagayesan kamar yanda akaima yayansa. Sai Hayatu da ni ma da akaima ƙawanya tun a farkon shigiwarmu. Daga can ma Ummie sun zagayeta haka ma Hajiya ƙarama. Hajiya Mammah da itace ƙarshen fiddowa kasancewar tana ɗaki kwance tana jiyyar hannunta suna isowa wajen ihu ta fasa da faɗin, “Mun shiga uku Baba!”.
Gilashin idanunsa ya cire yana mai binta da kallo. Bakin baya iya shiru cikin rawar laɓɓa ta sake faɗin, “Baba wai mike faruwa ne haka? Wane kalar bala'i ne wannan kuma ni Nafisatu Adams ƴan fashi da ranar ALLAH. Ni wlhy duk na ma rikice ko kidnapping ɗinmu akayi....”
“Ko kuma yay kidnapping kansa ba”. Muryar Ummie ta ratsa kunnen kowa a wajen a bazata. Duk kallonta akayi dan dariyarta take hankali kwance idonta akan Baba prof.. da mamaki Hajiya Mammah ta ce, “Ummu-Hidaya! Ban gane ba. Baba ne fa taya zai yi kidnapping kansa kuma? Kina ganin mutane sun zagayemu da bindigu kamar babu hukuma a ƙasar”.
Haɗe fuska Ummie tayi da watsa ma Hajiya Mammah ɗin wani kallo. “Kamar yanda kika gani mana Nafisa. Ai uban naku lusari ne ba jarumi bane. Sannan mata maza ne ba namijin gaske bane. Dan namijin gaske a filin daga baya riƙe garkuwa. Amma shi harda ƴan baranda ya zo. Adamu kenan, a tunaninka zuwa da waɗan nan wawayen dake hura hanci da bindigu a hannu zaisa ka amsa sunan NAMIJI a gabana? Ai kazo kai kaɗanka ne zan maka kallon ɗan rakkiyar mazan ma. Ka manta na faɗa maka, na faɗa maka in dai ni jinin Ibrahim ce da izinin UBANGIJI sai ka ƙare rayuwarka a ƙarƙashin ƙafafuna kamar yanda tun farko kake a ƙarƙashin ƙafafun mahaifina. Ai na faɗa maka dama bazaka taɓa tsira ba, kuma kafin ka mutu mutuwar wulaƙanci sai ka biya bashin CIN AMANAR da kayi ma mahaifina.....”
“Ƙarya kike ƙaramar ƴar iska ni ba MACI AMANA bane. UBANKI shine ya fara CIN AMANATA. dan haka shine MACI AMANA, BUTULU, MARA ADALCI, mai son kansa kawai. Shekaru ashirin da shida na ɗauka ina masa bauta da durƙusawa ƙarƙashinsa, alhalin dukiyar da yake taƙama da fankama da ita dani aka tarata. NI!! NI!! nan Adams. Yazo ƙasarmu a matsayin matsiyacinsa faƙirin da baida banbanci da mabaratan kan titi kafiri mai bautar gunki. Mune muka tallafesa ya zama mutum, muka buɗe masa idanunsa ya fahimci a inda yake, musamman ma NI! NI ɗin nan. Uwata ta zama sanadin shigarsa musulinci. Babu irin wahalar daban masa ba, duk da shekarun daya bani ba wasu masu tazara bane haka nake kiransa YAYANA ko YALLAƁAI, idan ya buƙaci aikena jikina har rawa yake domin son ganin na cika masa fiye da yanda ya buƙata. Ko kallon banza wani ya masa zafi nakeji a cikin zuciyata har na ɗauki mataki. Nasha yin faɗa da abokan aikina idan suna gulmarsa. Idan yana ciwo nine tsaye a kansa har ya samu lafiya. Hatta da wankin kayansa da gyaran ɗakin barcinsa kullum nine keyi batare da jin komai ba a raina. Kafin ya furta yunwa na sayo abinci na ajiye masa, haka nake girmamashi a duk wani motsinsa tamkar yayana uwa ɗaya uba ɗaya. A duk lokacin da naga wani abun cigaba da zai ɗaga darajar Company bana baƙin cikin kawo masa shi. Kuma haka za'a gwada a samu nasara. Amma duk da wannan hidimta masan dana ƙare ƙuruciyata inayi a matsayi ɗaya yake kallona har a randa zai bar duniya. Wato YARONSA. Yaronsa da darajarsa kawai yayi aiki a biyashi sai idan wani ya taso a sake nemansa yayi ya biyashi da ƴan kuɗaɗe.
Butulci na farko da tabbatar min shiɗin BAƘON HAURE ne mai rama ALKAIRI da SHARRI shine haɗa baki da budurwata ya turani karatu ƙasarsa bayan tafiyata sukayi aure saboda shi ɗin TSINANNE NE kafirin banza. Na danne zuciyata na ƙyalesa saboda dalilai biyu. Na farko ina masa kallon Yaya ne da zan iya sadaukar da komai a garesa kamar yanda nake tunanin shima zai iya sadaukar min. Na biyu yaci darajar mahaifiyata daya riƙe hannu biyu take masa kallon ɗa jininta. Sai dai nayima kaina alƙawarin komai tsahon lokaci sai na hukunta Rabi'ah da kaina da shi kansa. Dan a lokacin ita nafi kallo a mai laifi, idan shi bai san ina sonta ba ai ita tasan ina sonta. Idan kuma shi bai san ana barin halak dan kunya ba ita ai ta sani. Amma abin duniya ya rinjayeta. Koda yake banyi mamaki ba kasancewar ta ƴar KARUWA mai TUWO-TUWO kuma KARUWAR.
Wasu irin hawaye ne masu zafi suka silaloma Ummie. Yayinda jikin Maash ya fara rawa na tsantsar fusata. Yana motsawa ƴan iskan nan suka sake attacking ɗin sa da bindugun. Amma duk da yasan zafa su iya harbin nasa ya mutu har lahira tuni ya watsar da su ta hanyar hankaɗe bindugun ya nufi mahaifiyarsa. Dan a duniya bai haɗa al'amarinta da kowa ba. Da sauri suka ɗana kunamin bindugun su da wanda ke zagaye da ita amma sai Baba prof ɗin ya ɗaga musu hannu yana murmushi. Kamo Ummie Maash yay jikinsa, maganar da babu wanda ke ji yake mata ƙasa-ƙasa cike da kulawa da tattali. Dariya Baba prof ya kwashe da ita kamar ba tsoho mai shekarun girma irinsa ba. Jinai zuciyata na ƙuna. Bamma san lokacin da nima na furta, “Wawa jahili”. ba
Ai gaba ɗaya waɗanda ke zagaye da ni, da wanda ke zagaye da Maash ɗin sukayo kaina...
“Duk wanda ya taɓa min MATA a cikinku wlhy! Why UWARSA ma sai tayi dana sanin HAIHUWARSA!!!”.
Razananniyar muryar Maash ta ratsa kunnen kowa dake a wajen sai da muka firgita. Dan hatta da kamaninsa sai da suka sauya. Cikin nuna Baba prof da yatsa ya furta, “Kai kuma kafi JAHILAI JAHILCI tunda har kake iya maida FARI ya koma BAƘI. WULAƘANTACCE kawai da bai san girma da kimar HALLACI ba, mai faɗa da ƙaddara ɗan son banza. Kai har kana da bakin zaman yima mutane wannan surutan banzar naka soki burutsu. Duk abinda kake lissafin ka masan ai badan ALLAH kayi masa ba, kayine daman dan ka shiga jikinsa ka cimma wata manufarka baƙin annamimi. Idan kace duk ya maka wannan, inganta rayuwarka data ƴaƴanka da yayi fa. Bai kuma ji ƙyashin ɗaukar ƴarsa ɗaya tilo ya aurama ɗanka da ke a gurɓace ba. Sannan ya kama UWARKA ya riƙe da hannu biyu fiye da yanda ma kai kake riƙon nata. Sai ka gaya min UBAN mi kake so ya maka bayan duk wannan?”.
“Ni kake zagi Awwab?”.
“An zagekan, zan maka ma mafiyin wannan ɗin ne. Dan ni wlhy tuni na daina maka kallon MAHAIFIN UBANA. Na tsaneka”
“Kamar yanda nima ban taɓa maka kallon ƊAN ƊANA ba tun ranar haihuwarka naji bana sonka”.
“Alhamdullahi hakan yamun daɗi ai, dan ka taimaki kanka wajen gane abinda yafi ƙarfinka har abadan yafi ƙarfin naka. Kai ko kunya bakaji ba a duk wannan surutan naka ka faɗi ta inada Abie ya cutar da kai...”
“Oh so kake kasan ta inda ya cutar dani mara kunya. To zakaji yanzun nan kuwa. Dan zan ko gaya maka idan ita uwarka ta gagara sanar maka. Ko aure da kake faɗin ya ɗauka uwarka ya bama Mu'azz ni na sakashi yin hakan ta ƙarfin tsiya ba hallacinsa bane ba........”✍️
Hummmmmmmmmm🏃
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._
......Dukkan ƙuruciyata a wajen hidimtawa rayuwarsa na ƙarar da ita, amma da yake shi kansa kawai ya sani haka ya tattare dukkan dukiyar da aka tara da gumina a ciki ya rubuce sunan ƴarsa akai da naka, kai ɗin nan ɗan mitsitsinka dama baka san kanka ba balle waninka. Niko ya haɗani da wani tsohon companyn da ya gama mutuwa ya manna min ƴan kuɗaɗe wai ya sallaman naje na gyara. Tun daga lokacin na fara tunanin ta yanda zan mallake dukkan abinda ya handame ɗin nima tunda naga kowa kansa ya sani kawai. Haka na shiga na fita na kwaɗaita masa haɗa aure tsakanin Mu'azz da uwarka. Tsabar mutumin nan shi butulune nunawa ma yay kamar bai da wannan ra'ayin. Baya son wannan haɗin saboda Mu'azz baya jin magana. Rashin jinsa yayi yawa. Bazai iya