Showing 357001 words to 360000 words out of 438336 words

Chapter 120 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2241

tayanda zata fahimta amma ina. Imagen like father like daughter. Kai harma tafi ubanta taurin kai da tsaurin ido. Koda yake ai jini biyu ta haɗa, Rabi'ah ma badaga nan ba a taurin kai. Iya son fahimtar da ita nayi cikin hikima amma ta tabbatar min da itafa tana akan bakanta, idan dai Mu'azz zai zo ya nema aiki ne a companys ɗinta yazo ƙofa a buɗe take, yayi kamar yanda kowa keyi a biyasa albashi, amma batun ta bashi ragamar komai ko ni ta bani sam bazatayi ba. Kai harma da fa su zagina ita ga BOSS LADY jinin Alonso da Rabi'ah masu kuɗi ko. To Rabi'ah ɗin ma dan ubanta saurana ubanta ya samu dan sai da na gama shanye romon a waje kafin shi ya aura abinka da karuwa ƴar mai tuwo-tuwo.....
A zafafe Ummie ta ture Maash ta miƙe tana nuna Baba prof da yatsa, a matuƙar kaushin harshe ta ce, “Karya kake baƙin azzalumi annamimi. Oh surutun da aka barka kanayi taaa!! taaaaaa!! Tun ɗazun yasa kake jin kamar bakinka ne kawai ya iya magana har kake da kalmar yima mahaifiyata sharri. Ka kira Abie ɗina da maci amana, butulu, azzalumi, baƙon haure, kafiri da mine. Yanzu kana son aibanta mahaifiyata da zina. Ƙarya kake yi Adamu. Dan uwarka da bakinta ta faɗi mutunci da martabar da mahaifiyata taje da shi ga mahaifina. Idan kana gani bata raye yanzu ALLAH shine shaida kana da damar ƙaryatata dan dama ba daraja da mutuncinta ka sani ba ai. Sannan kana maganar na zageka, ai sai ka fito ka sanar musu dalilin da yasa na zageka bunsuru ɗan akuya wanda bai san mutunci da kimar kansa ba”.
Ta share hawayenta da nuna shi.“Jama'a kunga wannan, in har bai tuba ba ya mutu, idan har wanda ya kashe basu dawo duniya ya nema gafararsu ba, idan har waɗan da ya zalunta ciki harda mahaifiyarsa da matarsa harma da ƴaƴansa basu dawo duniya ya nema anfuwarsu ba, to tabbas idan kuka gagara ganinsa a WUTA ranar sakamako maybe garwashi ne ya lulkuɓesa acan ƙasan wutar jahannama........✍️

*_“Ya rabba🙏😭. ALLAH ka rabamu da son zuciya. Wace irin rayuwace wannan ka ƙare rayuwarka a bibiyar ta wani. Mutane dan ALLAH mu canja, dan yanzu mafi yawanmu wannan itace rayuwarmu shiyyasa HASSADA take ƙara ƙarfi a zukatanmu wlhy🥲🥲.”_*



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_



*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.

*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._


.......Bari na faɗa muku wani abu, duk da ya fito ya nunama mahaifina ainahinsa har yabar duniya bai nuna min wanene shi ba. Ko zaman meeting da mukai ana gobe zai bar duniya abinda kawai ya nuna min shine yana son ya tattara komai gareni, dan akwai wasu abubuwa daya ware na Muhammad da Fahad a cikin dukiyarsa. Sauran kuma nawane a matsayina na mai gadonsa. Ya ƙara da min nasiha game da kulawa da duk wanda zanyi mu'amala, ya tabbatar min dana tsaya akan gaskiyata, na kuma rungumi ƴaƴana na horar da su ta yanda sune zasu zama gatana kuma garkuwata koda anan gaba. Ya faɗakar da ni kada na cuci kowa, koda ma'aikaci na ɗauka mai hidimta min a cikin gida na sauke hakkinsa na kuma bashi darajarsa irin ta ɗan adam. Yace dani na cigaba da girmama wannan wawan, dan shi ɗin kamar ubane a wajena, yana kallonsa matsayin ƙani jininsa kodan riƙon da mahaifiyarsa ta masa da raino irin na uwa. Sannan mijina, duk rintsi kada na barsa, kada na masa ɗagawa, kada na ƙasƙantar da shi. Na ƙyautata masa, na masa biyayya matsayin sa na miji, shugaba, uban ƴaƴana, ta wani fanin tamkar yayana. Ya nuna min yasan halin Azz na neman mata, karna damu na cigaba da masa nasiha da addu'a watarana zai daina in sha ALLAHU. Daga ƙarshe ya bani amanar Bilkisu da Falaq tare da ɗora min nauyin nemo sauran iyalin Abdul-wahab na haɗasu na riƙe tare da ɗaukar nauyin rayuwarsu. Sannan ya danƙa min takardun Companynsa na robobi yace na bama iyalan Abdul-wahab ya mallaka musu duniya da lahira. Dan bazai taɓa iya biyan mahaifinsu abinda yay masa a rayuwa ba koda da dukkan abinda ya tara ne. Na amshi komai da hannu biyu, tare da masa addu'a da fatan samun lafiya. Daga nan mukayi zaman meeting komai lauyoyinsa suka saka hannu muma muka saka ni da Muhammad. Fahad kam da pinger print ɗin sa akai amfani dan bashi da wayon yin abinda ya kamata. Takardun Company daya mallakama zuri'ar Abdul-wahab akwai saka hannun Abdul-wahab ɗin sai dan ban san lokacin da ya sakashi yayi ba. Shima dai lauyoyi suka saka hannu na ajiye akan sai na samo sauran iyalan nashi sannan na damƙa musu. Nayi mamakin rashin cewar Adamu komai a wajen, da kuma yanda Abie bai sakashi a maganar ba ko sau ɗaya. Dan har muka gama cike-ciken takardun nan kallonmu kawai yake yi. Wannan abu ga tsaya mun a rai har na ƙudiri aniyar tambayar Abie idan mun kasance mu kaɗai. Amma sai labarin ya canja washe gari na rasa Abie na. Mai yankewa ta raba a gaɓar da nafi buƙatarsa.....”
Kuka ya sarƙeta. Da yawan wanda suke a wajen suma hawaye suke najin tsananin tausayinta. A hankali na rarrafa inda take na rungumeta, sai shima Maash yazo ya haɗamu ya rungume mu duka. Ƙwacewa shima Fahad yay yazo ya rungume Yayansa. Haka mukai kuka sosai idan ka cire Maash da idanun ne kawai suka juye sai jijiyoyin kansa da suka tashi sosai. Hakan yasa na sake tabbatar da taurin kansa. Da ƙyar Ummie ta cigaba da faɗin....
“Na shiga ruɗani matuƙa na rashin Abie, amma haka nai tawakkali ina addu'a da fatan dangana wajen UBANGIJI. Badan zuciya ta saba ba, ba kuma dan gangar jiki da ruhi sun haƙura ba na fara dawowa dai-dai. Kwatsam sai ga azzalumin nan yazo min da fuskar yaudara akan na mallaka komai a hannun Azz yana kula da shi. A lokacin ban kawo komai a raina ba, sai dai ina akan nasihar mahaifina. Sannan bazan iya mallaka komaina ahannun Azz ba kodan halinsa akan mata. Za'a iya amfani da wannan damar a lalata komai dan nasan matan banza da dukiya basa taɓa rayuwa a muhalli guda. Dole wataran sai an rasa guda a ciki. Kodai dukiyar ta kakkaɓe a dalilin matan, ko matan su gudu a dalilin ƙarewar dukiyar. A zatona ya fahimceni zai bar ni, amma sai ya cigaba da kawo wasu hanyoyin cikin salon damuna. Kawai sai na fara shan jinin jikina, anya kuwa mutumin nan babu wani abu a ransa. Musamman idan na haɗa yanayinsa da zaman meeting ɗin da akayi na rashin cewarsa komai, da yanda ko wata mahaifina baiyi da rasuwa ba amma yake wannan kai-kawon na son na mallaka dukiya ga ɗansa duk da yasan hallayarsa. Kai akwai abinda ya kamata na sani. Na ɗauki ƙudirin wannan bincike kawai sai ma ya sauƙaƙa min ta hanyar fitomin da mummunar manufarsa. A wata ranar juma'a da na gama kammala shirin komawa office a litinin ɗin satin da zamu shiga ina falo zaune Muhammad na kusa da ni yana homework ina gyara masa, sai Hayat, Falaq, Fahad dake ta tsalle-tsallensu kawai sai gashi ya faɗo mana. Nayi mamakin hakan, babu neman izini babu sanarwar irin wannan shigowa haka. Duk da abin ya sosa raina sai na daurema zuciyata saboda Abie yace na masa biyayya tamkar ƙaninsa na jini, sannan koba komai shi ɗin mahaifin mijina ne. Hijjab dake ajiye a gefena kawai na ɗauka na saka ina masa sannu da zuwa. Bana jin ya amsa min yanda ya kamata, dan ko gaisuwar da su Muhammad sukai masa bai kulasu ba. Fahad ma da ya nufesa yana murna bai taɓa yaron ba ya waske. Nan ɗin ma dai bance komai ba, sai Muhammad nama magana akan ya tattarasu suje wajen Mamansu Fateema (Maman Hayatu) dan lokacin Bilkisu bata da lafiya.
Yaran na gama fita na maida hankalina kansa. Cikin sauƙaƙa harshe na ce, “Baba lafiya dai kuwa? Yanzu nake zancen zuwa ni da yara gida mu muku barka da juma'a na sanar maka zan koma zuwa office in sha ALLAHU Monday”.
Wani mummunan kallo ya jefeni da shi, cikin ɓacin rai ya ce, “Ummu-Hidaya kina son nuna min kema mai taurin kai ce kenan?”.
Cikin nuna mamaki na ce, “Baba taurin kai kuma? Mizaisa na maka taurin kai. Kai fa uba ne a wajena. Ka cancanci sakani ko hanani akan abinda kaga zanyi ba daidai ba. Karka manta ko sanda Abie na raye yakan saka kamin faɗa ko gyara akan wani kuskure idan nayi balle yanzu da banda kowa sai ALLAH sai ku”.
“Ƙarya kike Ummu-Hidaya, in da abinda kika faɗa haka yake da baki bijirema umarni na ba. Da baki nunama duniya ni ban isa ba. Idan ma wani abu ne a ranki to bara na fito miki a mutum. Baki da ƙarfin hanani abinda nayi niyya. Na biyo miki ta hanyar lalama ne domin na baki damar rayuwa cikin salama ke da yaƴanki. Dan haka zan miki gargaɗi ba ƙarshe da zai iya taimakonki. Kada kice zaki bijirema umarnina. Idan kuma har kikai hakan kiyi kuka da kanki akan abinda zai iya biyo baya. Ban kuma amince da komawarki office ba ranar litinin ɗin, idan har kallon uban kike min da gaske”.
Sosai raina ya sosu da waɗan nan zantuka nashi. Bamma san fushi ya taso min ba na furta masa, “Baba ai baka da hurumin hanani zuwa aiki, inaga Azz ne kawai keda wannan damar matsayinsa na miji. Shima idan naga akwai tauye hakki a cikin al'amarinsa bai zama lallai na masa biyayya ba saboda tun farko ya ɗaukama mahaifina alƙawarin barina, nima kuma ya ɗauka min, idan har yasan hakkin alƙawari da muhimmancin sa kaga bazai bijire ba”.
Dariya ya ɗan yi da mun kallon sama da ƙasa, cike da gadara ya furta, “Ga fili ga mai doki”. Yay ficewarsa. Wannan al'amari ya gigitani ya kuma ƙwaɓe min lissafi. Gaba ɗaya komai naji ya ƙwace min. Hankalina yay matuƙar tashi. Mutuwar Abie ta dawo min sabo fil a zuciyata. Nayi kuka irin wanda bazai misaltu ba a wannan yini. Dole na keɓance kaina daga kowa domin yin nazari. Sai ya zamto gaba ɗaya weekend ɗin ya koma min na bincike da nazarin manufarsa. Duk da gargaɗin nashi a monday ɗin haka na tashi da shirin fita aiki. Amma mi sai Azz ya birkice min a wannan safiya kan bazan fita ko'ina ba. Na tambayesa dalili yace ban isa ya faɗa ba. Fita dai office ya soketa har abada. Ko dai na bashi komai ya cigaba da kulamin da shi, ko kuma na bama Baba. Murmushi nayi kawai na takaici, dan na fahimci ɗora shi akai akan keken ɓera. Sai kawai ban kulashi ba na cigaba da shirina. Na gama zan fita ya hanani fita ta hanyar kulle ƙofa. Da farko roƙonsa na farayi da son fahimtar da shi kuskuren da yake neman yi. Amma yaƙi saurarena sai ma sake hawa da yayi. Hakan ya baƙantan rai da zuciya nima na hau sama muka fara rikici. Kamar yanda ya saba duk da tunda muka dawo Nigeria hakan bai sake faruwa ba ya ware ƙwanji ya hau dukana. Da ƙyar na shiga bathroom na rufe kaina ina kuka. Abinda yasa kowa bai sani ba saboda yaran duk sun fita makaranta. Bilkisu kam tana wajen mahaifiyarta saboda damuwar abinda ya faru na zuwanta can dangin Abdul-wahab suka ƙi saurarenta bata da lafiya ma. Abinda yasa a lokacin ban shiga maganar ba akwai shirin da nake yi ya kuma haɗa da nima ina a cikin damuwar ne. Ya cigaba da banbamin masifarsa akan na buɗe ƙofar na masa banza naci kukana sosai a toilet ɗin sannan na wanke ciwukan daya jimun. Haka ya gaji dan kansa ya fita ya bar gidan batare dana fito ba. Nima sai da naji fitar motarsa sannan na buɗe na fito. Bana son yarana su fahimci baƙar rayuwar da nake ciki tsakanina da mahaifinsu na tsawon shekaru, musamman ma Muhammad mai fushi da ƙin duk abinda zai taɓa ni. Dan haka na daure na gyara komai na gyara jikina nasha magani na fita zuwa office ɗin cikin ƙarfin hali kamar yanda nayi niyya tun farko.......✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒔𝒊𝒙_


*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.

*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._


......Wannan shine mafarin komai. Fita ta office kuma ta sake fusata shi ya cigaba da kunnomin Mu'azz da abubuwa iri-iri ya zamto a tsakanin nan sam babu zaman lafiya ko tausayi a tsakanina da shi. Duka, zagi, gori, har akwai wani dare da yazo min da w.....
Kuka ya sarƙeta ta kasa ƙarasawa, sai da tayi sosai sannan ta cigaba da faɗin, “Da wata har ɗakin barci na, ya hanani fita a ɗakin sukai abinda suka so. Zan iya cewa ban kai wayewar gari da numfashi ba. Dan sume musu nayi tsabar tashin hankali, mijina da wata a ɗakina gadon mu na aure. Lokacin dana farfaɗo naga Fatima (Maman Hayatu) da Lawisa a kaina. Tambaya ɗaya na musu ina yarana? Suka bani amsa da suna lafiya kawai na maida idona

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login