Showing 390001 words to 393000 words out of 438336 words

Chapter 131 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2199

da yay na salwantar mana da namu hakkin dake a hannunsa na mahaifinmu dana mahaifiyarmu. Dan gona ɗaya ta rage itama dan tana a hannun Kawu Sabi'u ne yana nomata shiyyasa Abban bai sayar ba, Mom kuma bata san da ita ba. A gaban kowa ya faɗi Mom ce duk ta dinga saka shi yin hakan, shi kuma a lokacin wlhy baya gane komai sai bin umarninta da sabon faranta ma zuciyarta. Kuka ta sanya masa wai ya kawota cikin danginsa dan ya tozartata ashe su sake ɗaukarta a wulaƙance. Babu wanda yabi takanta dama tunda muka zo duk ta kasa sakewa saboda da can ba zuwa take cikinsu ba, ba barin ƴaƴanta take su zo ba. Idan kuma su sunje ta wulaƙantasu da nuna musu ƙyama.
Dangin su Mamanmu ma da mukaje kasa sakewa tayi. Can ma mun samu tarba ta mutuntawa da girmamawa. Haka muka kasance cikin farin ciki a tsakkiyar danginmu. Sai naji kamar a barmu muɗan kwana amma nasan uban gayyar ba yarda zaiyi ba. Dan koda naima Ummie magana sai tace nayi haƙuri idan na haihu ita da kanta zata tsaya har sai nazo nayi sati da ga ni har Falaq. Na ɗan ji sanyi da jin hakan, falaq ma nata murna dan tana son zuwa ta kwana ɗin ko dan sanin kowa yanda ya kamata.
Yini guda muna a can, dan sai bayan sallar la'asar muka barosu suna kewarmu muna kewarsu. Ga uban alkairi naban mamaki da Maash yay musu. Ni kaina sai da naji hawaye sun cika min ido da alkairin nasa. Gashi an tsaida magana gobe idan ALLAH ya kaimu su Kawu zasu zo akai komai na Yaya Musaddiq dan Abba yaje yayi magana da iyayen Ruƙayya sunce su babu wata damuwa suzo kawai tunda dama sun san da maganar Musaddiq ɗin. Sai da muka raka su Abba har gida sannan muka wuce muma. Yau dai kam wajen su Ummie muka wuce. Gajiyar da kowa ya kwaso yasa ba'a zauna falo ba duk muka shige ciki. Ni wankan ma sai da tainakonsa nayi, dan barci kamar zan zube ƙasa nake ji..

WASHE GARI muka samu baƙuncin abokan aikina su Ruƙayya. Abin mamaki harda MD da kansa. Hayatu ne ya saukesu a falon baƙi. Aka kai musu kayan tarba kafin na kimtsa na fita tare da boss. Naji daɗin hakan da yay min, gashi maƙale da hannuna har muka shiga falon ko kunyarsu bai ji ba. Har su Ruƙayya sun miƙe da nufin zuwa su rungumeni suna ganinmu tare sukai surrender. Murmushi na musu cike da nuna jin daɗin ganinsu. Mutuniyata dai sai sinne kai take nasan kunya ce ta isheta. Niko sai na basar na haɗa su duka na nuna jin daɗin ganinsu. Cike da girmamawa MD da su Usman suka gaida Maash, nima muka gaisa harda cemun wai ranki ya daɗe. Ɗan harararsu kawai nayi bance komai ba. Kada na tanka cibi ya zama ƙari dan kafin mu fito harda gargaɗi a kan na kula yanzu ba da bace kada naje ina musu murmushi tunda harda maza. Ni dariya ma ya bani, amma dai na amsa dan a zauna lafiya. Mun ɗan taɓa hira da duk dai mai alaƙa da aiki ce. Shi dai baya saka mana baki sai idan yaso dan kansa. A hirar ne suke sanar min ashe MD yanzu baya wajen, an ɗan samu rikice ne ya ajiye aikinsa. Station ɗin ma yanzu neman durƙushewa take saboda sabon MD ɗinsu bashi da aiki sai wulaƙanta mutane. Ga son yaɗa labaran sirrin mutane, yanzu haka muma wai akan video da yake yawo a media na sayen agwalima da Yaya Awwab yayi yana nan yana shirya abu a kansa. Shiyyasa ma sukai azamar zuwa su gammu tun kwana biyu da suka wuce amma basu samu damar hakan ba sai yau.
Maimakon Maash ya tanka akan batun sai ya shiga yima MD tambayoyi akan ainahin masu companyn. Cike da girmamawa ya dinga bashi amsa. A mamakin mu da zasu wuce sai kawai yace MD ya fara shirin komawa aiki on Monday. Ba su ba hatta ni sai da na kallesa. Amma sai ya basar. Bayan wucewarsu naso muyi maganar sai bata yiwu ba saboda zuwan Yaya Musaddiq. Shi kuma suka fita shi da Hayatu. Bayan la'asar koda suka dawo ya shigo ɗaki na biyosa da ruwa sai na samu ya shiga wanka. File ɗin daya ajiye a side drawer na ɗauka ina dubawa dan haka kawai yaja hankalina ganin tambarin gidan TV ɗin mu. Ba ƙaramin razana nayi da ganin sunana ba matsayin mamallakiyar gidan tvn. Zufa naji tana keto min, da ƙyar na iya controlling kaina na maida na ajiye yanda ya ajiye abinsa. Koda ya fito ban nuna masa na gani ɗin ba sai taimaka masa da nayi ya kimtsa muka fito falo dan yace zai ci abinci. Koda ya kammala cin abincin kuma hira da su Ummie dake falon ya ɗauke hankalinsa. Sai kuma ga kiran Uncle Abdullahi yana sanar musu ai ALLAH yay ma Arwa rasuwa yanzu babu jimawa. Ashe yarinyar jiyya take sosai zuciyarta ta kumbura. Sunƙi sanar mana ne saboda kunya da nauyin abinda mahaifinsu ya aikata mana da nata iyayen. Shi kuma Maash ko shigowa yay ƙasar baya zuwa asibitin ta yanda zasu gansa. A ɓoye yake zuwa ya duba Paah kawai ko shi Paah ɗin ma bai san da haka ba. Harga ALLAH bai taɓa maida hankalinsa kan yarinyar ba dan shi yama manta da ita sam. Iyayenta kuwa dama bai yaɓa sha'awar dubasu ba da Kakansa. Paah ɗin ma dan ya zame masa dolene yana kuma fatan sauke hakkinsa dake kansu matsayin mahaifi. Shiyya dukkan ɗawainiyar asibitin shike ɗaukar nasa batare da shi kansa Uncle Abdullahi ya sani ba. Dan bai hana a amshi kuɗinsu ba, amma yace su ajiye duk randa aka sallami Paah ɗin su basu abinsu.
Wannan rasuwa ta shigemu. Dan haka a ranar muka fara shirin wucewa dan Ummie ta roƙo Uncle Abdullahi da a jinkirta jana'izar har zuwa safiya ayi a Mansion. Ita yarinya bata da laifi, bata san komai ba akan abinda ya faru itama tsintar kanta tayi a tsakanin hakan. Idan ma za'azo dubi ta wani fannin ita aka cutar Haka kuwa akayi bayan sallar isha'i jirginmu ya wuce Lagos badan mun shirya hakan ba. Dan sati guda muka zo da niyar yi a Kano. Sai dai kana naka ne ALLAH yana nashi. Daga airport dai duk gida muka wuce, kowa kuma makwanci ya nema domin hutama rayuwarsa. Sai washe gari bayan sallar asuba aka kawo gawar Arwa gidan. Dangin iyayenta guda biyu sun iso daga ƙauyensu kasancewar tunda wancan zancen ya fasu ashe sunzo dama. Sai dai Uncle Abdallahi ya hanasu zuwa Mansion, da suka dawo kuma a lokacin mu mun wuce Spain. Mama Balki tai mata wanka da kakarta data haifi Hajiya ƙarama. Aka shiryata aka kaita makwancin ta na gaskiya. Duk da Arwa yarinya ce sannan uwarta kawai ta sani a gidan mutuwar ta shigi su Mama Balki sosai. Ita Ummie ba wani shaƙuwa sukai ba amma taji rasuwar. Ni kaina da ban taɓa damuwa da shirgin yarinyar a gidan ba sai da rasuwar ta dakeni. Hakama Maash bai dai ce komai ba face yimata addu'a amma nasan koyaya zai ji, dan yarinyar harga ALLAH tana masa kallon ɗan uwane kamar uba ɗaya. Duk da itama ya jima da fahimtar take-takenta na son shi. Abin mamaki sai ga su Azizat sun zo daga Niger suma a washe gari. Azizat tayi kuka sosai dan kowa yasan a gidan suna shiri matuƙa da Arwa. Duk da shirin nasu baya wuce akan a ƙuntatama Malika ko yanda za'a shawo kan Maash dai. To koma dai yayane ita dai ta tafi ta huta kuma. Sai fatan ALLAH ya gafarta mata kurakuranta da namu dana iyayenmu baki ɗaya...
Rasuwar Arwa tayi matuƙar jijjiga iyayenta. Musamman ma Hajiya ƙarama. Dan a wannan ranar likitoci kwana sukai kanta tanata wani irin kuka da aman jini. Ɗayan ɓarin jikin ya ida mutuwa. Dama ga allurar poison ɗin da Prof yay mata ta fara aiki kaɗan-kaɗan kamar yanda wadda tai masa shi tuni ma ta gama masa illa. Haka dai aka sakata barcin dole har washe gari da aka bizne Arwa bata farko ba. Shima dai Commondo yaci kuka rurus. Dan duk da bai taɓa nuna damuwarsa akan ƴar tasa ba yana matuƙar sonta da ƙaunarta. Yana gani ko wahalar da ya sha a rayuwa zata tafi a banza a ƙalla dai ya bar mai masa addu'a. Dan koda ta masa abinda ya sakashi shiga a wannan halin bai taɓa jin soyayyarta ta ragu masa a zuciya ba. Ashe itace zata fara tafiya ta barsu, inama shine ya tafi ba ita ba. Kaicon wannan mummunar rayuwa tasu mara ƙyaƙyƙyawan tarihi da alƙibalar gani a koya........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑯𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒐_


......Har akai sadakar uku jikin kowa dai a sanyaye babu wani ƙarfi. Dangin su ma sukai shirin kama gabansu. Dan sun san anmusu halacci. ALLAH sarki Ummie, bata barsu haka ba sai da ta musu alkairi. Suka tafi suna mai sanya mata albarka da addu'oin fatan alkairi har ma damu kammu. Sun wuce da safe gidan ya sake komawa shiru. Dan su Azizat dama ba'a nan suke kwana ba can wajen mahaifiyarsu gidan Prof da safe su zo su koma can da yamma. Batare da mun sani ba washe gari akace mana sun wuce. Ita dama Hajiya Mammah tun randa akai jana'iza da tazo bata sake zuwa ba saboda kunya ne ko munene dai oho mata. Da yammacin ranar tafiya ta tasowa Yaya Awwab, haka ina fushi da kumbure-kumbure suka wuce shida PA ɗinsa da ƙandarariyar baturiyar nan dana tsana. Yanda take wani kwarkwasa da iyayi agaban Yaya Awwab na ƙona min zuciya. Bandai ce komai ba amma ALLAH idan bata kiyayeni ba sai na mata zanen yarabawa. Bayan wucewarsu gidan sai ya sake koma mana shiru, sai kawai na tattara na koma sashen Ummie dan bazan iya zaman sashen ni kaɗai ba. Ashe can ma Aunty Falaq ta gudo wajen Ummie ɗin. Dariya Ummie taita mana wai mu ragayen mata ne. Daga maza sun tafi sai mu gudo wajen Mamanmu. Shagwaɓa muka dinga mata tana biye mana. Ita dai Mama ido kawai take saka mana.
Muna waya da ƴan Kano, Musamman Yaya Musaddiq da Hafizzullah da Abba. Sai aunty Halima sabuwar ƙawarmu. Dan yanzu mun ɗinke da ita kamar ba matar Abbanmu ba. Bahijja ma na Kano maƙale bata dawo ba. To batun dawowar tatama dai sai da aure a kanta. Dan an gama tsaida magana bikinsu za'ai kawai da Fahad a huta kafin mu koma. Sai yanzu ne ma nake jin batun komawar tamu Spain. Harga ALLAH na ɗauka mun dawo gida kenan. Kasancewar a gari ɗaya Abba ke cemin an saita bikin Yaya Musaddiq da na Fahad ɗin rana ɗaya. Nan kuma da kwana goma ne idan munada rabon kaiwa. Ba ƙaramin farin ciki na tsinta kaina ba da wannan labari. Na kira Ruƙayya naita mata tsiya, dan yanzu muna waya kullum da chart amma bata sanar min ba. Shima Yaya Musaddiq ɗin ya mun bayani duk yanda sukai da Yaya Awwab. Ya ɗauki komai na bikin ko naira ya yace baya son wani ya sanya. Harda hawayensa dan video call muke a lokacin, sai nima kawai na sanya masa kukan. Dole ya danne nashi ya koma lallashina.

Kasancewar biki a ƙurarren lokaci mukai tunanin fara shirye-shirye ni da aunty Falaq. Dan ango dai Yaya Awwab ya tasa ƙeyarsa da shi aka tafi. Sai dai kwanansa uku sai gashi ya dawo. Maimakon Lagos sai ya sauka a Kano. Da daddare sai gashi tare da Hafizzullah. Mamaki ya kama mu dan munsan dai Hafiz na Kano. Sai cewa Fahad ɗin yay yaje ya ɗakkosa ne su fara shirin biki. Cikin harara nace “Wannan ɗan yaron? ina abokanka”.
Sai kawai ya nuna Hafiz ɗin, wai ai shi shine babban abokinsa. Rasama abin cewa mukayi, sai Mama da Ummie ne ke mana dariya. Babu yanda muka iya dole muka shiga hidimar tsare-tsaren bikin tun a ranar. Washe gari da yamma Yaya Awwab yay kirana wai mu shirya za'a kaimu airport zuwa dare. Da mamaki na ce “Airport kuma Yaya Muhammad yin me?”.
Kai tsaye ya bani amsa da, “Zaku same mu a Dubai ke da Falaq”.
Rasama abin cewa nayi nikam. In ba masu abu da abinsu ba irin wannan yanke wannan hukunci kamar wanda ke Katsina zashi Kano. Babu yanda muka iya muka shiga shiri. Ummie nata faɗa wannan wace irin tafiya ce ni ina fama da kaina falaq ga ƙaramin yaro. Mama dai ta bata haƙuri akan tunda sunce muje mu tafi ɗin kawai. Haka dai Ummie ta barmu. Babu abinda muka ɗauka daga mu sai kayan jikinmu da handbags. Hafizzullah da Fahad suka kaimu airport. Fahad sai lallaɓamu yake wai mu zaɓoma matarsa kaya na kece raini. Muna isowa bamu fi mintuna talatin ba aka ɗauke mu. Banyi mamakin ganin mu kaɗai ba a jirgin sai wasu tsirarun mutane. Dan zuwa yanzu na sake fahimtar wanene mijina. Tabbas ALLAH ya musu baiwa ta dukiya, sai dai fatan ALLAH ya kaimu aljanna kuma...

Mun iso Dubai lafiya. Sai dai ni naɗan jigata kaɗan dan banda juriya yanzu sosai, dama kuma tun jiya bana jin daɗi dauriyar kawai. Hayatu ne yazo ta ɗaukemu, sai naji haushin rashin ganin ogan nasa. Amma dai bance komai ba har muka iso gida. Gidane mai ƙyau sosai da yaji kayan more rayuwa. Shima Hayatun na ajiyemu yace zai koma wai meeting suke can ma ya bar ogan nasa kuma yana jiransa ne. Takaici yasa naƙi tanka masa. Sun san basu da lokacinmu suka kwasomu zuwa nan kara tsaye. Yanda nake kumbure-kumbure yasa Aunty Falaq tambayata lafiya. Cikin ɓacin rai na amsa mata da, “Aunty dan ALLAH wane kalar wulaƙanci ne haka. Sun san suna da abin yi suka kwasomu. Nifa ALLAH bazan jure wannan abun ba. Kayi aure dan ka kasance da mijinka akoda yaushe amma sam bashi da isashen lokacinka. Yau yana wannan ƙasa, gobe waccan, jibi meeting, gata taron ƴan kasuwa. Citta kaza, kanumfari kaza”.
Dariya sosai ta sanya min, ta ce, “Oh oh little sis.. irin wannan lissafi haka. Lallai akwai aiki kenan. Ashe ke bazaki iya jure abinda na jure ba. To wlhy Yaya Hayat ko satin amarci bai cika mun ba suka bar ƙasar nan. Kwanansa biyar inaga. Da ya tafi ban gansa ba sai bayan sati uku. Nana ma sukai kwana ko huɗu ne da ƙyar suka sake tafiya. Nifa a ɗan zaman rikice-rikicen nan ne ma zance miki mun taɓa zaman sati ciff yana gida sai dai ya ɗan fita ya dawo sabgar wuni. Ya xamuyi tamu ƙaddara kenan, mata a waje gani suke mun gama morema duniya da komai na cikinta. Nan ko mu muka san ƙalubalenmu. Samraah kafin nayi aure babu abinda nake buri kamar naga koyaushe ina tare da mijina muna tattalin juna. Sai dai da safe na shiryashi ya ɗan tafi harkokinsa zuwa la'asar ace ya dawo mun kasance tare har wata washe garin, weekend kuwa ya zama salla ce kawai zata fitar da shi. Amma a satin farko na fahimci wannan burin nawa ya zama tarihi ba kuma mai tabbata bane. Tun ina damuwa da yawan fushi harma na haƙura dan bani da yanda zanyi. Dan haka kema haƙuri zakiyi, a hankali zaki saba da duk wannan rashin kasancewar tasu tare damu mu itace babbar ƙaddararmu a gidan aure. Muma godema ALLAH da ya kasance yanzu gamu a tare, ga kuma iyayenmu guda biyu ga Baba suna ɗebe mana kewa.”
Ta ƙare maganar tana ja min kumatu na. Baki na sake tunzurawa, dan nikam gaskiya bana jin zan iya dauriyar nan. Kawai azo ayita da wajewa ga lokacin tafiya gana zaman gida. Amma dai bance mata komai ba. Wanka muka farayi muka ɗan tsakuri abincin da muka samu an kawo mana. Ni kawai ma sai na kwanta abina dan barci nake ji sosai.

Ba ƙaramin ƙarin takaici naji a zuciyata ba sanda har na tashi naga babu shi babu alamarsa. Sai ma Aunty Falaq ce ta shigo tace na shirya wai Yaya Hayat ya kirata nan da awa ɗaya za'azo a ɗauke mu mu sameshi kasuwa. Baki na buɗe kamar zanyi magana sai kuma nai shiru saboda ƙwallar da suka cika min ido. jinake kamar nace babu inda zanje sai dai na daure kawai nai shirin cikin doguwar rigar data kawo min. Amsar little Awwab nai a hannunta muka fito, babu wanda yay magana a cikinmu bayan amsa gaisuwar Balaraben da yazo ɗaukar mu ya buɗe mana bayan motar muka shiga. Tafiya ce ta ƴan mintuna ta kaimu haɗaɗɗe kuma makeken shagon da baida iyakar labartawa. A can muka samu Yaya Hayat. Bayan mun gaishesa ya amshi Awwab a hannuna yana tsokanarmu. Murmushi kawai nayi ni dai bance komai ba, sai aunty Falaq ce ke kare mana. Saka Awwab yay a irin ƴar jakar goyon nan ta ƴan gayu a ta cikinsa, mu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login