Showing 177001 words to 180000 words out of 438336 words
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_
.......Wajen ƙarfe tara na fito nemawa Ummie abinci, dan nasan tana farkawa shi take fara nema. Ina shiga Hajiya Mammah dake kitchen ɗin ban san mi take yi ba ta aikeni sashensa. Cike da jin haushi na shigo ɗauke da abincin da Hajiya Mammah ɗin ta sani kawo masa. Ko sallamar ma ciki-ciki nayita. Tsaff katafaren falon nasa yake kamar ko yaushe, ga ƙamshin nan dana rasa daga ina yake samunsa dan ya bambanta da duk wani ƙamshi dana taɓa sani ko shaƙa a wajen mutane. Komai nasa dabbane dana saura. Sallama na sake yi a ƙuntace dai-dai isowata tsakkiyar falon sosai. Dan naga alamar basu ji ta farkon ba, inda dan shi kadai ne bazan damu ba. Dan koda yaji zai iya shareni wannan ƙaramin aikinsa ne, amma Hayatu bazaiyi hakan ba duk da takaicinsa da nake, shima kuma ƙwallon kansa ne.
Yanzun ma dai Hayatun ne ya ɗago da sauri alamar dai basu san da shigowar tawa ba da gaske. Cike da kulawa ya amsa min yana wani ɗan rissinar da kansa. Harararsa nayi kawai na ɗauke kai, dan wannan girmamawar da yake min na baƙanta min zuciya. Shiko gogan baima nuna alamar yasan da shigowar tawa ba. Gaba ɗaya idanunsa da ƙyaƙyƙyawar fuskarsa na kan screen ɗin laptop ɗin cinyarsa da takardun hannunsa. Fuskar nan ciɗin-ciɗin babu alamar sassauci kamar wanda ma ke cikin ɓacin rai. Cikin i don't care na laɓe bakinna da dangwarar da tray ɗin saman Centre table ɗin daya ajiye ƙafafunsa masu tsananin tsafta da haske. Gashi cas babu wani girma sosai irin na maza. Dan wata macen ma sai ta fishi girman ƙafa. Da alama dungurarsa da tray ɗin ya ɗanyi ya saka shi ɗan ɗagowa a karo na farko ya ɗan kalleni. Sai kuma ya ɗauke idanun yuuu ya maida ga laptop ɗin. Nima nawa na ɗauke ina sake tsuke tawa fuskar na juya abina da nufin komawa inda na fito.
“Bani ruwa marasa sanyi”. Ya faɗa a dake babu alamar wasa a cikin silent voice ɗinsa. To amma tunda ba suna ya ambata ba bai shafen ba tunda bani kaɗai bace a falon ai. Cigaba da tafiyata nayi dai-dai da yunƙurawar Hayatu alamar zai bashi ruwan.
“Da ita nake”.
Ya katse hanzarin Hayatun cikin gizagonsa. Duk da naji abinda yace ɗin ban kula ba. Ganin na cigaba da tafiyata cike da girmamawa Hayatu ya ce, “Aunt yace da ke yake fa”. Wani irin ɓacin rai ne naji ya ziyarcen. Dan haka na juyo a fusace ina watsama Hayatun mummunan kallo. “Wai malam banace maka ka daina kirana da wannan sunan ba. In ce dai kasan sunana Samraah ai”.
Murmushi kawai Hayatun yayi yana mai rissinar da kansa ƙasa. Sai kuma yace, “Kiyi haƙuri bazan iya faɗa bane. Dan kina da kima da matsayin fiye ma da hakan a wajena”.
Cikin gatse na ce, “Saboda a gida ɗaya aka haifemu?”.
“A'a saboda kina tare da auren boss”.
Duk da furucin nasa yay masaifar tsargani sai na dake. Cike da masifa na ce, “Kaima kasan wani auren boss ai, kar kuma ka sake jinginani da abinda ku ya shafa bani ba”.
Baki ya sake buɗewa zai yi magana, sai dai hakan bai yiwu ba, dan kamar a ɗan fusace silent voice ɗin boss ɗin nashi ta daki kumnuwanmu.
“Hayat! Kaje zan nemeka”.
Abinda yay niyar faɗar ya haɗiye. Batare da wata jayayya ba ya miƙe zumbur. Takardun jikinsa ya tattara ya kai gabansa. Hakan yasa na watsa musu harara su duka na cigaba da tafiyata. Sai dai kafin nakai ƙofar har Hayatu yazo ya wuceni, yana fita ya wani rufo ƙofar. Ban damu ba na kama handle ɗin nima zan buɗe na jita gam. Wani irin takaici ne ya ratsa zuciyata. Dan na fahimci mutanen nan neman maida min rayuwa suke wata sha katafi. Shiru nayi tsaye a wajen har kusan minti ɗaya. Sanin banda wata mafita saita wajensa ɗin ya sani nufar dining room ɗin sa. A cikin haɗaɗɗen freight ɗin dake a wajen na buɗe na ɗakko goran ruwa masu sanyi sosai saɓanin wanda yace marasa sanyi. Batare dana ɗora a saman tray ba ko ɗaukar kofi na fito. Har yanzu yana a yanda yake hankalinsa a laptop ɗin. Ruwan na dangwarar masa kawai ina tura baki. Ganin yaƙi nuna yasan dani ma a wajen ya sani faɗin, “Ga ruwan nan zan tafi”. Shiru bai kulani ba. Baima ko motsa ba. Takaici ya sake riƙemin maƙoshi, sai dai nasan fushi na bazai haifar min da komai ba sai ma sake tunzurashi. Sassauta muryata nayi a hankali na ce, “Please ka bani key na fita”.
Nan ma shiru bai da niyyar kulani, tuni idanuna sun fara cika da ƙwalla. Kusan minti ɗaya sannan ya magantu ciki-ciki.
“Ban hanaki shiga cikinsu ba?”.
Da farko ban fahimci abinda ya faɗa ɗin ba. Sai daga baya na fahimci akan ma'aikatan gidan nan ne maza da ɗazun a compaund. Dan haka cikin son manna masa rainin wayo na ɗan duƙo kansa kaɗan duk da yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri cikin dakewa na furta, “A matsayinka na wa?”.
Wani irin lumshe idanunsa dake yawo a fuskata yayi, yayinda ni kuma na yunƙura da nufin barin wajen kawai naji an bugi ƙafafuna. Gaba ɗayana na tafi, duk yanda nai ƙoƙarin son riƙe wani abu hakan bai yiwu ba sai da na faɗa kansa na zauna daram a cinyar tasa. Yanda na faɗo ɗin fuskokinmu suka kasance gab-gab da juna. Wani irin kallo yake min cikin tsakkiyar ido daya hanani iya koda motsi, kafin a hankali ya sake matso fuskar tasa gab da tawa. A take gaba ɗaya tsigar jikina ta mimmiƙe. Sai kawai na lumshe idanuna a hankali dan nagama sadaƙarwa akan nawa lips ɗin zai sauke nashin. Amma a maimakon hakan sai jin saukar yatsarsa nayi a saman lips ɗina ya shiga zagayawa a hankali, tare da sassanyar muryarsa cikin kunnena ya furta, “I'm not interested”.
Da sauri na buɗe idanun tare buge hannunsa dan har yanzu yana zagaya yatsarsa akan lips ɗin nawa. Bamma san sanda na watsa masa harara ba da ɗora hannayena akan ƙirjinsa na turashi baya. Ni kuma nai yunkurin tashi zumut. Amma tsabar mungunta sai ya sake taɗeni da ƙafar na sake komawa kan jikin nasa. Hannun na sake kaiwa jikin nasa zan turashi naji saukar nasa a bayana. Matsoni yay gaba ɗaya sai gani kwance a ƙirjinsa. A fusace na buɗe baki zanyi magana ya rufesa rufff da mitsitsin nashi. Waro idanun nawa waje nayi gaba ɗaya cikin tashin hankali da rikicewa, shima ya ɗan waro nasa kaɗan sai kuma ya kashe min ido ɗaya cike da salon iskanci. Ai ruff na sake rufe nawa idanun jikina na rawa.
Duk yanda naso ƙwace jikina hakan ya gagara, dan yayi masifar min irin riƙon da ban isa ƙwatar kan nawa ba. Da wani irin kalar salo yake sarrafa halshena cikin bakinsa. Duk mintsinin da nake masa babu alamar yana jina ma. Sai da yay mai isarsa dan ko kiran wayarsa da ake faman yi bai kula ba, gaba ɗaya jikina ya gama saki. Koda ya sakan sai kawai na duƙunƙune a jikin nasa ina sauke numfashi a gwagwgwame jikina sai rawa yake. Shima cikin furzar da nasa numfashi da shaƙaƙƙiyar murya har tana siezing a hankali ya furta, “Na miki abinda kike buƙatar ai. Sai yaushe za'a ɗaga ni”.
Bai ma gama rufe baki ba na miƙe zumbur. Batare dana kallesa ba na fisgi ɗan kwalina dake a jikinsa. Cikin haɗa hanya na nufi barin wajen, dan duk masifar da nake ji zan masa akan abinda ya faɗa min ɗin yanzu bazan iya furtawa ba.
“Ribbon”.
Ya faɗa ƙasa-ƙasa muryar tasa a shaƙe har yanzun.
Kamar zan sharesa sai kuma dai na Juyo dan bana buƙatar barin komai nawa a sashen, ribbon ɗin nawa na hanga akan jikinsa. Sai da na runtse ido sannan na nufesa, hannu na kai zan ɗauka amma sai ya gyara zama ta yanda ribbon ɗin ta koma tsakkiyar ƙafafunsa. Kauda kaina nayi da sauri, tare da juyawa cikin sassarfa nabar wajen dan ni kaɗai nasan abinda idanuna suka gane min. A mamakina ina kaiwa ƙofa na murɗa handle ɗin sai gashi ta buɗe. Ƙoƙarin juyowa nayi na kallesa sai naga yana ajiye remote alamar shine ya buɗe ɗin kenan. Harara na watsa masa dayin ƙwafa cike da tsiwa na ce, “Kuma ALLAH ya isa na, sai na gayama Ummie”. Na ƙarasa fita da sauri har ina bugewa da ƙaton flowers base dake gefen ƙofar anyi decorretion da su.......✍️
_🤣Koba ALLAH ya isa ba. Muma to ALLAH ya isanmu jikinmu da aka hau🥱😜. Bara na ware kafin danginta su caskala ni🚴🚴🚴._
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_
.....Tana fita ya runtse idanunsa da karfi, sai kuma ya fisgi gorar ruwan data ajiye masa ya ɓalle murfin tare da kafa bakinsa ya hau kwankwaɗa. Tass ya shanye ruwan yay jifa da robar tamkar itace tai masa abinda ya harmutsasan, sai kuma ya miƙe da hanzarinsa ya nufi side ɗin da bedroom ɗinsa yake yana famar haɗa hanya da furzar da huci a jajjere da taunar lips kamar zai huda su da haƙori.
★Kai tsaye nima side ɗinmu na nufa maimakon komawa ƙarasa abincin Ummie. Ko kallon waɗanda ke a falo banyi ba na afka bedroom. Karo mukaci da Bahijja, dan haka ta riƙeni gam cikin kiɗima da ganin yanayina ta ke furta, “Aunty Kandala lafiya kuwa? Mike faruwa dake na gankai haka a birkice? Ko hajiya babba ce?.”
Hannunta na ture daga jikina batare dana iya magana ba. Cikin sassarfa na nufi bathroom ɗinmu dan bana fatan taji ƙamshin turarensa daba ɓoyayye ba a gidan a jikina. Ina shiga kai tsaye ƙarƙashin shower na shige na sakarma kaina ruwa kawai. Dan bani da wani zaɓin daya wuce hakan. A jajjere na dinga sauke ajiyar numfashi sai ga hawaye sharrr-sharrr kamar an buɗe fanfo....
💦💦💦💦
Tun fitowar Samraah da ga sashen Maash Hajiya Mammah dake laɓe ta bita da kallo. Duk da ƙamshin turarensa da yanda Samraahn ta fito ya sata farin ciki dan ta tabbatar akwai abinda ya faru koda ba wanda sukayi fata bane. Amma dai ba haka taso ba. Taso a yau komai da suka shirya ya faru kawai dan itafa tafi son idan ta saka abu a gaba kawai tayisa a wuce wajen. Har ta nufi barin wajen sai kuma ta fasa. Part ɗin Maash ɗin ta nufa, kanta tsaye ta buɗe ƙofar ta shiga da sallama. Babu kowa a falon sai uban ƙamshinsa da sanyin ac. Sai television dake aiki sai dai babu ƙara sosai. Idanunta ne suka sauka akan tray ɗin abincinta. Trayn ta zubama ido na tsawon sakanni, sai kuma ta nufi inda yake. Tana gab da kaiwa ta tsaya cak, tabbacin jin motsi ya sata komawa da baya da sauri ta fita a sashen gaba ɗaya.
Sai kuma abinda tayi ɗin ya sakata dariya. Kaɗan ta dara tana nufar nata part ɗin.
Da kallo Hajiya ƙarama da komai ya faru akan idonta ta bita. Lips ɗinta ta cije da ƙarfi sai kuma ta saki ƙwafa. A zuciyarta tana ayyana lokaci fa yayi da zata amshi kayanta kafin wannan matar ta mata shigar sauri. Amma dolene ta bincika mi take ƙullawa akan Maash ɗin haka ne. Gaba tayi da yanzu bata da wannan lokacin asibiti ta nufa. Tanada aikin da zatayi na kuɗaɗe masu nauyin gaske. Dan haka tai ficewarta cike da takun kasaita irin na manyan mata gogaggun kuma ƴan boko...
Hajiya ƙarama ke kuma....🤔 (To Bara dai nayi hiru.🥱
✨💫✨💫
A ƙofar gate Mansoor yaci karo da Mamy. Ɗauke kansa yay tamkar bai ganta ba zai wuce. Amma sai ta riƙo masa hannu cikin tashin hankali. “Mansoor mika aikata?”.
Kansa tsaye ya bata amsa da, “Sakinta nayi. Dan bazan iya koda zaman minti ɗaya da ita ba Mamy”.
“Baka da hankali Mansoor. Kasan muhimmancin auren nan a garemu baki ɗaya?”.
“Bana son na sani Mamy kiyi haƙuri”.
Daga haka ya zare hannunsa yay gaba abinsa yana ƙoƙarin shiga taxi ɗin da yazo. Dan dama bai sallamesa ba. Binsa kawai Mamy keyi da kallo komai ya ƙwace mata. Har motar tabar wajen bata iya taɓuka komai ba. Sai da motar su Hajiya Sakeena da zasu wuce asibiti ta fito sannan ta dawo firgigit. Ƙoƙarin isa ga motar tai tana tambayar mike faruwa. Dan taga Hajiya Sakeenar na kuka. Cikin masifa da hayayyaƙowa tamkar ba yayarta ba ta ce, “Koma miya faru ba huruminki bane ba. Kije ki zauna gida ki jirani. Dan wlhy in har yarinyata ta mutu kota nakasa sai ke da ɗanki kunyi dana sani” daga haka ta dakama driver tsawa akan su je. Nan ɗin ma sake sumar wucin gadi Mamy tayi, ba kuma ta dawo a hayyacinta ba har sai da sukai nisa.
Mansoor kam kai tsaye anguwar su Samraah ya nufa. Ya ɗan jima tsaye a ƙofar gidan sai ga wata mata ta fito tana ƴar dariya. Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Jikin gate ɗin ya matsa zaiyi knocking sai ya jiyo kamar hayaniya. Fasawa yay yayi ɗan jimm alamar saurare. Masifa wata mata keyi harda zagi, sai kuma wata siririyar murya na dariya cikin shaƙiyanci. Mamaki hakan ya basa, sai dai yaji nutsuwa a cikin muryoyin babu na Samraah. Amma kuma bai taɓa zuwa gidan nan yaji haka ba. Yana tsaye a wajen sai ga matar ɗazun ta dawo. Daurewa yay ya gaisheta ta amsa masa da ɗan kallon mamaki. Dan kuwa dai ta ganeshi sosai. Ai Mansoor ɗin Samraah ba ɓoyayye bane a layin nasu kodan aikin gidan tv da sukeyi tare.
“Ihmm niko kamar Mansoor?”.
Cikin jin daɗin ta ganesa ya amsa mata da cewar shine. Tare da roƙonta ta turo masa Samraah dan ALLAH”.
Murmushi tayi tana ɗan girgiza kai. Sai kuma ta amsa masa da, “Ayya Mansoor ai Samraah bata nan tana Lagos ne ko Abuja naji ance. Amma dai kamar Lagos ɗin”.
Da mamaki yace, “Lagos? To yin me?”.
Ɗan jimm tayi alamar tunani. Sai kuma ta kaɗa kanta da faɗin, “Tare da mijinta mana. Amma dai ka nema Abban nasu ko ƴaƴanta Musaddiq mana”. Daga haka tayi shigewarta tabar Mansoor da sakakken baki....
❤️💦❤️💦❤️
A ciki kam Mom ce ke fitina akan Halime bata isa yin girki a gidan ba yau. Dan tun randa ta tabbatar itace sukai uwar fitina da Abba har takai ya shashsheka mata maruka tare da gargaɗi mai ƙarfi akan iskancin kai hannu jikinsa da take sonyi a kwanakin nan, zata shaƙe masa kwala, ko zata cutar da shi. Acewarta gara ta murɗe kowa ya huta. Wannan mari ya girgiza Mom har ma da Ummanta. Yayinda Halime take ɗaki tana kwasar dariya. Bawai marin bane ya bata dariya itafa. Firgicewar Mom da ganinta matsayin matar mijinta ne kawai ke bata nishaɗi. Dan a take abubuwa data ɗan sani a gidan na ƙarfin Mom ya shiga dawo mata. Tana ji Abba zai shigo ta haɗiye dariyar ta.
Umma itace ta killafa Mom ta ƙarfi, ta kuma tabbatar mata idan fa bata kwantar da hankalinta ba har aurenta ya mutu to gaskiya kada tazo mata gida. Wannan hauka har ina aita tarota tana ƙwacewa kamar wata ƙaramar yarinya. Su nutsu su fuskanci abinda ya dace suyi amma ta zauna yin hauka akan wanda shi sam hankalinsa ma baya a kanta yanzu. Wannan faɗa ya sakata nutsuwa. Har Abba ya gama kwanakin angwanci a ɗakin Halime bata sake kula kowa ba. Da ya dawo ɗakinta kuma yaso nuna ɗaukar fishi da ita. Sai dai roƙon da Musaddiq yay masa ya sassauta abun. Dan haka ya haɗasu su duka gidan har Nabil dake makaranta yay musu nasiha tare da tabbatar musu da Halime itama yanzu ɗaya daga cikin family ɗinsu ce, sannan baya buƙatar damuwa daga kowa.
Abbas da Musaddiq da Nabil ne kawai sukai magana da amsar Halime. Amma Baby da Bibaa ko kallon uban ma basuyi ba. Watsar dasu Abba yayi, sai ma maganar bikin Baby daya tabbatar musu ya gama tsayar wa nan da wata biyu, tare da sanar musu