Showing 222001 words to 225000 words out of 438336 words
ranar girkinta bane. Haka tunda Hafizzullah yazo take hidima da shi da jansa a jiki shima kai kace ƙaninta ne uwa ɗaya uba ɗaya. Duk yanda Hafizzullah keda ƙin sakin jiki da mutane sai gashi dandanan ya saki jiki da ita. Hatta da jakar kayansa yanzu haka a ɗakinta ya bari dan ɗakin Musaddiq ɗin akwai baƙi maza yan gwarzo da basu kai ga wucewa ba.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
____________
......Lokacin da suka iso airport ɗin su duka sai da ƙwalla ya cika musu idanu. Dan abune da basu taɓa zato ko tsammani ba a rayuwarsu. Sune yau da hawa jirgi daga Kano zuwa Lagos. UBANGIJI al-musawirru mai sassauya al'amura a sanda yaso ga kuma wanda yaso. Da suka shiga jirgin sai Hafizzullah ya rungume yayan nasa yana hawaye. Dole shi ya haɗiye nasa ya dinga lallashinsa. Bayan yayi shiru kuma ya dinga musu video wai dolene ya nunama Aunty Samraah yau sun hau jirgi. Dariya Musaddiq ya dinga masa har ALLAH ya saukesu lafiya garin Lagos. Sunyi mamakin ganin zuƙeƙiyar motar da tazo ɗaukarsu. Amma sai Musaddiq bai kawo komai a ransa ba tuna cewa dafa companyn Maash yake aiki, mai lamba ta ɗaya a Africa, na uku a duniya a matasa. Ai hakan ba komai bane ba. Sunyi da MD dama motar company zata daukesu daga airport ta kaisu duk inda zai je, sannan idan ya kammala gobe idan ALLAH ya kaimu zai kira aje can gidan ƴar uwar tasa a ɗaukesa zuwa wajen GM, daga nan zai wuce kuma....
🩸🩸🩸🩸🩸
Kamar kullum alarm ɗinsa ne ya tashesa. Hannu ya kai idanunsa a rufe ya lalubosa a saman side drawer ya danne wajen kashewar dan shifa ko yaya ƙara take damun rayuwarsa take. Shiyyasa bazaka taɓa ganin wayarsa da ringing ton ba. Kullum cikin vibration phones ɗinsa suke. Hakama television da wahala kiji ya buɗeta caaa tana surutu. Cikin mayen barcin da bai gama isarsa ba ya nufi toilet. Sai da yay wanka kamar yanda abun ke neman zame masa sabo saboda mafarki duk da ba kullum yake tashi a irin yanayin ba sannan ya ɗauro alwala ya fito. A ɗan gurguje ya busar da kansa ya shimfida sallaya yay raka'atainul fijir sannan ya fice masallaci. Ana idar da salla bai yarda sun haɗu da Paah ko Uncle Abdullahi ba ya dawo gidan. Jallabiyarsa ya zare ya ɗauka sports wear ya saka masu kalar blue da rashin white. Sosai kayan sukai masa ƙyau duk da baya sakasu ne domin kwalliya ba. Ya kama gashinsa ya haɗe a tsakkiya tare da ɗauresa da siririn baƙin band. Duk da gudu zai fita sai da ya sakama jikinsa turare ya maƙala bluetooth a kunensa sannan yay zaman saka takalma spots na companyn nike. Yana fitowa falo Laalah dake kwance ya miƙe ya nufosa. Kansa ya shafa cikin lumshe idanu da silent voice ɗin nan tasa ya furta, “Let's go my friend”. Cikin kaɗa bindi kuwa ya bisa abin cike da mamaki. Daka gansu kasan karen ya gama samun training na musamman a hannun uban gidan nashi. Gashi fari tass babu alamar wani dattin ƙazanta a tare da shi. Wanda ma bai sani ba sai ya ɗauka ba kare bane saboda yanda jikinsa ke duguzum da gashi. Yana nufar gate da ɗan gudu Laalah biye da shi ƙafa da ƙafa dan a jere suke tafiya su Sha'aibu dake zaman jiran fitowarsa na take musu baya suka fice yana ɗagama ma'aikatan daketa faman gaishesa hannu. Gudun ya fara tun daga wajen gate ɗin a hankali Laalah a gefensa guards ɗinsa biye da su. Haka suka miƙe street ɗin nan. Sosai sukayi nisa bana wasa ba. Jefi-jefi suna gamuwa da mutane da suma suka fito jogging ɗin. Hannu kawai suke ɗagama juna kowa ya wuce. Sai wasu ƴammata ne da suka dai-daita gudun kusan da shi dan suna a ɗan gabansa kaɗan amma ko kallo basu ishesa ba. Sunyi nisa sosai ya jiƙe sharkaf da zufa har yana ɗiga sannan suka sake juyowa bayan ya kalla agogon dake a tsintsiyar hannunsa. Suna isowa kwanar da zata sadasu da gida ya tsaya cak. Nuni yayima Shu'aibu daya bashi ruwa cikin sauke numfashi da sauri-sauri. Da sauri ya nufesa tare da ajiye ƴar jakar da abubuwan da zai buƙata ke'a ciki. Kamar su bottle water, towel da abinda ba'a rasa ba. Ruwan ya amsa ya buɗe murfin haɗaɗɗiyar bottle water ɗin ya kai bakinsa. Kansa ya ɗaga sama ya shiga kwararawa. Wani irin kaiwa da komawa maƙoshinsa ya shiga yi, illahirin ƙofifin gashin jikinsa na buɗewa zufa na fitowa da gudu. Sai da ya sha fin rabi sannan ya sauke gorar yana sauke numfarfashi. Laalah ya zubama kaɗan a jiki, shiko yay wani irin matsawa yana girgiza jiki. Yanda yay ɗin ne ya saka Maash ɗin sakin wani ɗan guntun murmushi yana sake kai goran bakinsa ya ɗan kurɓa sannan ya rufe ta ya miƙama Shu'aibu da suma duk suke shan nasu ruwan tare da masa alamar ya bashi towel. Da sauri ya miƙa masa fari tass ɗin towel ɗin hannunsa dake a linke. Sai da ya fara gogo wuyarsa zuwa gashi dake kwance a kumatunsa sannan yay magana batare da ya kalli su Shu'aibu ba.
“Kira Tijjani ya samemu anan da mota”.
Duk da a hankali yay maganar sarai Shu'aibu ya jisan. Sai dai yayi mamakin jin abinda yace ɗin. Amma bashi da hurumin musawa. Sai ma waya daya zaro yay kiran TJ ɗin. Cikin ƙanƙanin lokaci motocin biyu suka iso. Ta farkon aka buɗe masa ya shiga shi da Laalah. Ta bayan guards ɗinsa ne. Sai TJ da Shu'aibu a gaba tunda ba Hayatu. A ɗan ɗarare TJ ya ce, “Sir ina zamu je?”.
Shiru kamar bazai ce komai ba. Sai kuma can a ƙasan maƙoshi ya furta, “Hospital”.
Da girmamawa TJ ya amsa da, “An gama ranka ya daɗe” yana tada motar. Kansa kawai ya kwantar jikin kujera ya kumshe ido. Har lokacin zufa na faman tsatstsafo masa. Bai ɗago ba har sai da suka isa asibitin. Shu'aibu ya buɗe masa da sauri ya fito. Sai dai banda Laalah shi an barsa a motar. Cikin takun nan nasa ya nufi cikin asibitin Shu'aibu da TJ biye da shi. Tako ina tsirarun ma'aikatan cleaners da ma Nurses da sauransu sai kalonsu suke. Koda suka shiga reception tuni yammatan dake a kan katan sun miƙe bakunansu a washe suna masu Barka da zuwa idanunsu a kansu kamar tsoffin mayu. Ko kallo basu ishesa ba sai su TJ suka amsa musu...
Kuka na gama zabgama mama Balki akan nifa yau ko su sallamen daga asibitin nan kona gudu gida. Dan bazan sake kwana banje naga halin da Ummie ke a ciki ba. Lallashina taitayi akan nayi haƙuri jikina ya ƙara ƙyau tunda doctor tace sai nan da kwana biyu, jikin Ummie kuma da sauƙi sosai. Tirjewa nayi akan nifa sai na tafi. Ganin yanda nake zabga uban kuka yasa Maman cewa shike nan naje nayi wanka idan Alhaji Ƙarami yazo anjima itama zata sake masa magana da kanta. Badan naso ba nabi umarninta. Kamar kullum sai da ta fara taimaka min na shiga ruwan zafi na mintuna goma sha biyar zuwa ashirin da nake yi sau uku a rana. Sannan ta fito akan nayi wankan bara taje ta dawo.
Wankan na ƙarasa batare da tunanin kowa zai iya shigowa ba na fito ɗaure da towel kawai. Dan masu shara tun sanda zan shiga cikin ruwa Mama Balki ke cemin sun shigo aikinsu. Haka dama sukeyi, kullum tunda sassafe zaki gansu, wani lokacin ma ana idar da sallar asuba. Daga nan kuma sai da rana, sai kuma yamma. Fes kuwa na samu ɗakin harda turaren wuta sun kunna. Jikina na goge da ɗan hanzari. Bana son Mama Balki ta shigo ban saka kaya ba duk da nasan ko tazo ɗin tsayawa take bakin ƙofa sai ta tambayi na shirya sannan ta shigo, dan kunyarta nake ji matuƙa. Ƴar jakar kayanmu na buɗe na ciro b&p da zan saka dan ni ina amfani da kayan asibitin ne. Bra ɗin na fara ƙoƙarin sakawa da sauri-sauri, na saka hannu ɗaya ina ƙoƙarin saka ɗayan kawai ya zaro ta baya. Fuska na ɓata kamar zan fasa kuka, abinda dai nake gudun sai ya faru, tunda dole na jira Mama Balki tazo ta maƙala min ko kuma na cire na sake sakawa tazo ta sameni, amma bari muga na gwada dai kozan iya nawa ƙoƙarin. Kicin-kicin maidawa na fara ina famar cizar lips, sai kawai naji saukar lallausan hannu mai bala'in sanyi akan nawa dake riƙe da hannun bra ɗin. Tabbas wannan ba mama Balki bace, dan wani irin mayataccen ƙamshi ne ya shiga ratsa ƙofofin hancina. A birkice na juyo gaba ɗaya na nama manta da wani batun saurin da nakeyi. Saukar idanuna cikin lulu cat ɗin nashi ya sani ja baya jikina har tsuma yake. Shiko ko gezau, sai ma wani irin kallon ƙurilla yake bina da shi idanunsa a shanye. Inda naga ya kafama idanun nima na kalla da sauri, ai da sauri na naɗe hannayena a wajen ina tura baki kamar zan fasa kuka. Kafaɗa ya ɗan ɗage tare da taɓe baki irin shi baiga abin kallo ba, ina ƙoƙarin sake juya masa baya sai kawai ya shiga takowa a hankali. Baya na sake jan jikina yana cigaba da biyoni duk na ruɗe. Jin na dangane da abu yasa na juya da sauri na kalla, sai naga bangone, tashin hankali anzo the end kenan inji bature. Banda zaɓin daya wuce kawai na juya masa baya na kalla bangon. Idanuna a runtse murya na rawa na ce, “Wai da ALLAH minene haka kake yi? Ni dai ka fita kayafa zan saka, sai Mama ta shigo ta ganka”.
Maimakon amsa min ko ya fitan sai kawai naji ya saukar hannunsa akan kafaɗata, da ƙarfi na sake matse idanun nawa jin yanda yake wani irin tafiya da yatsun kamar mai yi da gayya........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒆𝒆𝒏_
.......Hannun bra ɗin ya maƙala min a inda ya zare, a tunanina zai matsa ne sai naji saɓanin hakan. Matsoni ya sake yi ta yanda har nake jin saukar numfashinsa a saman wuyana, sai kuma ya saƙalo hannun nasa ɗaya ta saman cikina. Yanda na sake matsewa a bangon bai hanashi jawoni baya ba a hankali, kansa ya ɗoro a saman kafaɗata tattausan gashin kumatunsa dake da laimar da nake ƙyautata zaton zufa ce tunda sports wear ne a jikinsa na gugar gefen fuskata. Ɗayan hannun ya ɗaura a saman nawa dake rufe da ƙirjina har yanzu zai zame, aiko naƙi yarda na sake ƙanƙamewa.
“Na cire towel ɗin kenan?”.
Soft voice ɗin sa dake fita low sosai cikin maƙoshi ta ratsa kunnuwana. Kaina na girgiza masa alamar a'a idanuna na cika da ƙwala.
“Oya remove your hand kona ciresa tas”.
Nasan zai iya, dan kaɗan daga ƙaramin aikinsa ne. Dan haka na shiga zamesu a hankali hawayen da nake maƙalewa na sake taruwa cikin idanun. Sake matsesu nayi jin yanda yake jan towel ɗin a hankali, har ya gama sauke b ɗin kan jikina babu kunya babu tsoron ALLAH ya gyarata ta zauna da ƙyau sannan ya maida min towel ɗin a sama.
“I love white musamman yanda wannan ta miki ƙyau”. Ya faɗa cikin kunnena cikin raɗa.
Da sauri na toshe kunnena tare da ture masa kai dan bana ma son ji. Maimakon ya barni kamar yanda naso sai ma ya sake nanne ni da jikinsa tare da sumbatar wuyana da hannun dana toshe kunnen. Ni kaɗai nasan kalar masifaffiyar kunyar da nake a ciki da mamakin tasa rashin kunyar dan shi komai yana yinsa ne kansa tsaye. Mun kai tsahon mintuna biyu a haka sannan ya janye jikinsa a nawa tare da kama hannuna. Ban buɗe idanuna ba, sai alamar zaunar dani da naji yayi a bakin gado. Jin kamar ya jawo kujera ya zauna gab dani dan har ƙafafunmu na a cikin na juna ne ya sani buɗe idanuna dake mar-mar. Kamar yanda nayi hasashen hakanne kuwa. Ya jawo kujera gab da ni ya zauna hannunsa ɗauke da rigar asibitin da aka ajiye min a saman gadon. Idanunsa kan p ɗin dana ajiye. A zabure na kai hannu na ɗauke ina ɓata fuska kamar zan yi kuka na cikukuyesa a hannuna na tura ƙarƙashin cinyata. Mayatattun idanunsa ya zuba min tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Hand”.
Bani da zaɓin daya wuce miƙa masan kawai, dan nasan ko cewa nayi bana so bazai barni ba. Inaji ina gani ya saka min rigar sannan ya miƙar dani a gabansa kamar wata ƴar yarinya ya zare towel ɗin ya ajiye gefe. Hannu ya miƙa min wai na bashi p ɗin dana sake saurin ɗaukewa. Kafaɗa na maƙe masa ina juyar da kaina gefe. shima sai ya taɓe nasa bakin kawai. Turaren dana ajiye gefe ya ɗauka ya ɗan duba jikinsa, sai kuma ya ɗan sake taɓe baki kaɗan, batare da yace komai ba ya ɗan fesa min ya maida ya ajiye. Ni dai uffan bance masa ba, kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hannuna. So nake na tambayesa yaya Ummie amma duk ya dabaibaye ni da salon da ban taɓa zaton gani daga garesa ba. Gashi duk abin nan da yake fuskar nan na'a tsukenta kamar bashi keyi ba. Da ƙyar na iya dauriyar faɗin, “Ina kwana? Yaya jikin Ummie?”.
Jin shiru bai amsa ba ya sa na ɗago idanu na a hankali kamar wata matsoraciya. Kamar yanda nayi zato shima nasan a kaina suke, dan haka da gudu nai yunƙurin kauda nawa amma sai ya riƙo haɓata da yatsunsa biyu.
“Ina miki aiki bazama kince kin gode ba”.
Baki na tura masa. Cike da ƴar jarumtar dana tattaro a tsiwace nace, “To ni dai ai bance ina so ba”.
Maimakon ya bani amsa sai naga ya saki wani shegen murmushi. Cike da suɓutar baki da mamaki na ce, “Lah yau ma kayi murmushi”.
Janye hannunsa yayi, tare da tsuke fuskar. Ni sai ma abin ya bani dariya. Sai kace wani ɗan yaro. Dariya nayi ina ƙoƙarin kare bakina na ce, “Ikon ALLAH, to kai baka so ace kayi murmushin ne? Sai kace wani abun mugun abu. ALLAH idan ma kayi murmushin kafi ƙyau. Amma kullum fuska a ɗaure kamar wani ma'aikin mutuwa.” na ƙare maganar ina haurawa saman gadon gaba ɗaya tamkar banga irin kallon da yake faman bina da shi ba. Sai da naja bargon na rufe ƙafafuna sannan na kuma marairaice fuska. A hankali na ce, “Yaya Awwab!”. Shiru yaƙi amsa min, sake maimaita kiran sunan nashi nayi a shagwaɓe. “Yaya Please answer me”.
Nan ɗin ma kamar bazai amsa ba. Na sake ƙoƙarin yin maganar cikin harara ya katseni da faɗin, “Ba kunni ke ji ba ne”.
Baki na tura sosai. Na ce, “To ai dai ba daɗi mutum yayi magana aƙi amsa masa.”
Banza yay min bai tanka ba. Nima sai na cigaba da faɗin, “Dan ALLAH ka taimaka a sallaman yau a asibitin nan. Idan ba hakaba ALLAH zan gudo gida. Ina missing ɗin Ummie sosai. Ni wlhy na warke fa”.
“Na gani”.
Ya faɗa kamar bashi ba yana ƙoƙarin yaye bargon dana rufama ƙafafun nawa. Da sauri na waro idanuna ina riƙe hannunsa. Kaji mun mutum to mizai gani?. Shanyayun idanunsa ya ɗago ya zuba min, ni kuma na marairaice fuska har idanuna na tara ƙwalla. Hannun ya janye kawai batare da yace min komai ba. Nima sai na sauke ajiyar zuciya dan al'amarin wannan mutumin yasha kan nawa ƙaramin tunanin gaskiya. Sake matsar da kujerar da yake zaune yayi gaban side drawer.