Showing 294001 words to 297000 words out of 438336 words
TJ da saƙo wai inji boss. Ina buɗewa sai ga waya, harda sim card a ciki da cajinta da komai. Nayi farin ciki sosai kowa kuma ya tayani har Mama.
Samun wayar nan ya matuƙar sakani a farin ciki. Dan ji nai kamar na taka rawa. A falon na barsu nacema aunty Falaq zanje nayo shirin barci nazo a ɗakinta zan kwana. Kai tsaye ɗakinsa na wuce na ɗakko flash ɗin nan. Ɗakina na koma jikina har rawa yake. Kamar mai tsoron a kamata sai da na kulle har windows bayan ƙofa sannan na haye gado na saka flash ɗin jikin wayar.....
🌟🌟🌟🌟
Karan farko a rayuwarsa da tun cuɗewar abubuwa ya zauna yin nazari. Sosai abubuwan dake faruwa a gidan ke dawo masa dalla-dalla. Tabbas lokaci yayi da zai gyara mu'amalarsa da ƴaƴansa. Ya kuma tsaya tsayin daka wajen ganin lafiyar matarsa rufin asirinsa. Baya ganin laifin Awwab da Fahad, dan suna da hujjojin da zasu juya masa baya a rayuwa. Suna son mahaifiyarsu, babu kuma wani ɗa na kwarai da za'a wofantarwa da mahaifiya ya iya kawaici koda kuwa mahaifinsa ne. Tun suna masa alkunya da tunatar da shi muhimmanci mahaifiyarsu a garesa har sun daina sun wofantar da shi kawai. Dan gara-gara ma Muhammad na ɗan rangwanta masa sai idan ta ƙurane yake magana. Amma Fahad ko kallo bai siheshi ba. Yanzu haka tunda ya dawo ko hangosa yay sai ya canja hanya. Jiya ne ma data ƙure suka haɗu babu yanda zai yi ya ce masa ina yini. Bai ko jira ya amsa ba yayi wucewarsa...
Shigowar kira ya katse masa tunaninsa. Kamar zai share sai kuma dai ya kalla wayar. Ganin Baba ya sashi sauke ajiyar zuciya. Ɗagawa yay cike da girmamawa ya gaishesa duk da kuwa bai jima da barin gidan ba. Baba prof kam dako amsawa baiyi ba kai tsaye yace yazo ya samesa a gida yanzu nan. Ya amsa masa nan ma da girmamawa. Bai kuma ɓata lokaci ba ya shirya ya fita amsa kiran mahaifin nashi...
Kusan a tare suka shigo gidan, har shi Paah ɗin ma yayi mamaki dan da'alama tunda Baban yabar Maash Mansion sai yanzu ne yake dawowa gidan. Sai da ya dakata Baban ya fara shiga ciki sannan shi yabi bayansa. A falo ya samesa, duk da basu jima da rabuwa ba ya sake gaishesa yana mamakin ganin yanda duk fuskar mahaifin nasu ta birkice. Daga ƙarshe ma kasa haƙurin yayi sai da ya tambaya.
“Baba kana lafiya kuwa?”.
Murmushin yaƙe Baba prof ya ɗan yi, sai kuma ya jinjina ma Paah ɗin kai cikin furzar da numfashi ya ce, “Idan nace da kai babu komai Mu'azz na maka ƙarya.”
Cikin tashin hankali paah ya ce, “To baba miya faru?”.
“Ba daga ni bane Mu'azz daga kune. Al'amarinku ya fara tayar min da hankali musamman kai da ƴar uwarka. Sai kuma Awwab. Yanzu kuna ganin a matsayina na mahaifin ku da mahaifiyarku ta tafi ta barni da ku kun min adalci kenan ku dinga cima kan ku mutunci?. Yanzu har kun kai girman da zaku dinga gorantama kanku akan ƴaƴanku. In ce kamata yay ni da ku mu nutsu mu fuskanci abinda Awwab ke ɓoye mana dangane da yarinyar nan. Ko kuna ganin zancen fyaɗen nan ba komai bane....”
“Baba kayi haƙuri bana katseka bane. Amma bana tunanin Muhammad zai aikata wannan mummunan aikin da gangan. Mu zauna mu auna maganganun Addah da abinda ya faɗa mata ranar. Dole akwai abinda ya kamata musani.”
“Humm banƙi ta taka ba, amma dai ni da kai duk munsan wacece Nafisa ko. Tunda mun san ita fitina bata mata wahala mizai hana mu mata uziri. Ƙaramin abu kaɗan daga aikinta ta maida shi babba.”
“To amma Baba su kuma sai a dinga musu adalci ai. Bai kamata ace muna ƙara musu zafi ba a rayuwarsu. Sun rasa mahaifiyarsu tun suna ƙanana. Duk da bawai ta bar duniya bane amma banbancin kaɗan ne. Ni kuma a matsayina na mahaifi son zuciya ya hanani fuskantar su, na kasa rungumarsu na zame musu madadin uwa na kuma amsa sunan uba. Birinƙyaɗuwata kawai nake yi kuma a matsayinku na iyayena da ita dake matsayin yaya a gareni kun kasa nuna min kuskurena. Badan ALLAH ya kiyaye yaran nan ba wlhy tuni sun iya faɗawa criminals rayuwa. Dan kaine ma mai ɗan jan Muhammad a jiki da, sannan ya samu tattalin Abie kafin yabar duniya. Amma Fahad sam bai samu gatan nan ba. Baba mufa duba al'amarin nan da mahangar adalci.”
Kai kawai Baba prof ke jinjinawa kamar tsohon ƙadangare. Sai da Paah yay shiru kafin yaja gwauron numfashi da faɗin, “Shike nan na yarda duk munyi wannan kuskuren. Sai muyi fatan haɗuwa mu gyara mu duka a yanzu. Amma ita wannan yarinyar da Fahad yace ɗiyar Sarkin mota ce ita da ɗan uwanta kai dama kasan da hakan?”.
“Wlhy sam ban sani ba sai yanzu nima daya faɗa ɗin na sani. Amma nakega ai hakan ba komai bane ba. Dan Abdul-wahab ya cancanci kowane irin ƙyautatawar mu. Ka kuma san shaƙuwar dake tsakanin Abdul-wahab da Muhammad zai iya yin komai domin ganin ya binciko sauran zuri'arsa. Tunda mu bamuyi hakan ba. Da kuma Ummu-Hidaya na lafiya na tabbatar da tuni tayi hakan. Shiyyasa ni sam ban wani yi mamakin hakan ba sai ma daɗi da naji dan sun tabbatar da su ƴaƴan halak ne da basa manta alkairi”.
“Hakane”.
Baba Prof ya faɗa cikin ɗacin rai. Kafin ya nisa da cigaba da faɗin, “Hakan da Awwab yayi na jawo yaran jiki abin a jinina masa ne kam. To amma batun maganar fyaɗen da ake zargin ya mata kuma fa?”.
“Wannan batun Baba yana buƙatar bincike. Kuma shine maƙasudin zargina akan akwai abinda ita Adda ta sani akan al'amarin. Ya kamata kuma ka binciketa, tanan ne kawai zamu iya kamo bakin zaren.”
Nanma kai Baba prof ɗin ya jinjina. Yana dai ta danne zuciyarsa. Sai can yace, “Amma baka tunanin aurenta Awwab yayi?”.
“Aure fa Baba? Yayi aure shi Muhammad ɗin batare da mun sani ba? To waye zai masa walicci? Minene kuma dalilin da zai sa ya aikata hakan? Tunda yasan mu dukanmmu burinmu shine yayi auren?”.
“Nima irin waɗan nan tambayoyin naka sune a raina Mu'azz. Amma tabbas mu zauna muyi tunani irin na masu hankali. Idan har mun tabbatar Awwab zai iya nemo zuri'ar Sarkin mota dan ƙyautatawa taya zai haikema yarinya batare da dalili ba. Gashi nan yin hakan ya zame masa matsala, ya kuma zame mana muma ahalinsa. Duba nan ka gani, na tabbatar zuwa gobe wannan labarin shine zai zama latest”.
Jikin paah har rawa yake wajen amsar magazine ɗin da Baba prof ɗin ke bashi. A shafin farko yaci karo da abinda ya nema rikito masa zuciya waje. A take rawar jikinsa ta ƙara ƙarfi. Idanunsa suka kaɗa jazur. Muryarsa na rawa da yatsarsa dake nuna abinda Mujallar ta rubuta da kuma hoton Maash da yarinyar (Samraah) ya ce, “Bab....ba ya akai wannan maganar ta fita?”.
“Taya zan sani Mu'azz, ni kaina wannan tashin hankalin yasa ka ganni haka. Ina fitowa da Mansion na samu kira. Wani ma'aikacin Mujallar ne ya min gulmar tare da turo min ita. Ya kuma tabbatar min nayi gaggawa kafin su saketa yau ɗin nan. Sai dai ashe na makaro, dan ya turo saƙon ne tin daren jiya ban lura ba sai a yau. Koda na isa gidan Magazine ɗin aikin gama har ya gama.”
“Aiko wlhy Baba sun takalo rigimar da bazasu iya maganinta ba. Dan yau ɗin nan ba gobe ba sai na saka an kama duk wani shege dake aiki a gidan wannan mujallar” ya miƙe a matuƙar fusace ya fice batare da ko sallama ya sake ma Baba prof ɗin ba. Wani shegen murmushi baba prof ɗin ya saki har haƙoransa na bayyana. Sai kuma ya jawo waya ya hau danne-danne tare da kaiwa kunnensa. Ana ɗagawa cike da bada umarni ya furta, “Duk su saki labarin. Ina son daga yanzu zuwa safiya kaf Nigeria dama duniya su san da wannan labarin”. Ƙitt ya yanke kiran, tare da kwashewa da dariya tamkar ba baba prof ɗin nan ba da tsufa ya gama cinyema rayuwa gaba ɗaya sai abinda ya sara kuma. Kai duniya ɗan adam abin tsoro. Idan har jininmu basu tsira daga zaluncinmu ba, to waye kuma zai tsira daga garemu. ALLAH ka gafarta mana kurarenmu, ka hanemu son zuciya da zalunci ga waninmu koda dabba ce😭🙏......✍️
_Masha ALLAH kowa na buƙatar samun lokacin kwalliya a gobe idan ALLAH ya kaimu, jibi kuma suyar mama😋, (to kar dai a manta da ni gaskiya ɗan hanji-hanjin nan na gobe ina jira). ALLAH ka karɓi ibadunmu da wanda sukaje hajji, ALLAH ya dawo mana da su gida lafiya. ALLAH kuma ya maimaita mana da rai da lafiya. ALLAH ya rufama kowa asiri ya hana kowa cin bashi. Mata ƴan uwana dan ALLAH kada a takurama maza yin abinda basu da shi. Duk abinda suka kawo mu amsa kuyi haƙuri mu sanya albarka, ALLAH sai ya bamu ladan haƙuri._
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
........Wani irin suya ta bala'i zuciyar Paah keyi. Kai tsaye ya bama driver ɗinsa umarnin wucewa da shi DSS office. Sai dai me suna ɗaukar hanyar a tafiyar da bata fi ta mintuna biyar ba kawai wata mota tasha gabansu, ga titin baida yawan mutane haka sosai sai jefi-jefi. Rai ɓace Paah ya fito ganin drivern sa na ma mai motar magana amma bashi ma da niyyar gyara musu balle fitowa ya basu haƙurin ɓarnar da yay musu dan ya gogi musu mota sosai. Saitin drivern yaje yay knocking glass ɗin wajen. Ana buɗewa kawai aka huro masa abu a fuska. Babu shiri ya haɗiye abinda yake son faɗa ɗin yay baya yana kai hannu a fuskarsa ya share abinda aka huro masan, yana ɗagowa kawai luuuu ya tafi zai faɗi. Ihu drivern sa ya ƙwala yana yo kansa da kiran, “Alhaji! Alhaji!!” kawai suka harbesa har sau biyu. Kafin wani lokaci mai tsayi sun saka Paah a mota sun bar layin driver kwance cikin jini yana magowar mutuwa dan sun samesa ne a ƙirji da cikinsa......
🤔Waye da wannan aiki kuma??.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
Gaba ɗaya ji nake tsigar jikina na tashi sosai. Dan har ga ALLAH zuciyata ta ƙara girgiza da ganin Baba prof ɗin da Hajiya ƙarama. Duk da ba komai na fahimta ba game da zantukansu. Amma kenan hirar da yaje nayi da ni a wancan lokacin tana da manufa kenan. No wander naji duk zuciyata bata aminta da shi ba. Shine harda zuwa ya dinga ɓarin kuɗi harda kuma bani mota. Bama wannan ba, a cikin zantukansu shi da Hajiya ƙarama akwai wajajen da nake buƙatar yima nazari. Kamar...
_(Tabbas nayi kuskuren ƙin bibiyar bayan Abdul-wahab kamar yanda nake biye dana Ibrahim Alonso...)_ “Abdul-wahab dai Baba fa kenan. Alonso Abie ɗin Ummu. To miye ribarsa idan ya bibiyi bayanmu?. Sannan su kansu bayan Abie dai na nufin Ummie, Maash, Fahad ko. Ikon ALLAH to mi hakan ke nufi kuma? Tunda dai Fahad da Awwab ai jikokinsa ne da ɗansa na cikinsa ya haifa”. _(Yallaɓai wlhy zan haukace wane irin ruɗani da tashin hankali ne haka yazo mana a rana ɗaya?. Gashi mun gagara magance batun likitocin nan abu sai ƙara nisa yake, duk da dai ba wannan bane kaɗai hope ɗinmu wancan ma zasu iya mana illa tunda ko ganinta bamayi a yanzu balle sanin halin da take ciki)._ Furucin Hajiya Ƙarama ya sake min amsa kuwwa a zuciya. “Sun gagara magance batun likitoci, sannan basa ganinta, Ummie kenan ko wa? Anya kuwa mutanen ba sune keda hannu akan al'amurin Ummie ba?”. _(Dole akwai abinda Awwab ya sani. Dole shine ya shirya komai. Ta ya yarinyar dake a Kano zata dawo Lagos? Ta ya ɗiyar Abdul-wahab zata shigo Maash Mansion matsayin ƴar aiki? Ta ya! Ta ya! Ta yaya?!)_ “Wannan magana ma alamar tambaya gareta, Maash nada dalilin ɓoyeni matsayin matarsa kenan?. Ya ALLAH wai wannan wane irin ruɗaɗɗen gidane haka? Na gagara fahimtar komai, gaskiyar Mama da tace kowa ma abin zargi ne, gida kamar jinin sarauta, koda yake miye banbancin gidan masu dukiya da sarautar. Su waɗan can mulki da dukiya suke ma farauta da yaƙi. Su kuma waɗan nan dukiya da ƙarfin iko suke ma farauta. Idan za'a auna ai ɗan juma ne da ɗan jummai. Gane mai gaskiya kuwa ta hanyar bincike ne kawai dan nasan Maash bazai faɗa min ba. Dole ne zuwa gobe na ziyarci asibitin can, amma bari na fara magana da aunty Falaq....
Da wannan tunanin nai shirin barci. Wayata kawai na ɗauka sai hijjabin salla na wuce. Na samu kuwa Mama har sun kwanta. Aunty Falaq ce kawai ke zaman jirana. Muma sai muka kashe komai muka wuce ɗakin da akai mata masauki. Ɗaki ne babba da komai na buƙata a cikinsa. Zama nayi saman gado ita kuma ta wuce bayi. Kamar jira ina zama kira na shigowa wayar hannuna. Shiru nayi ina kallon no ɗin dan bata Nigeria bace, sai da tana gab da tsinkewa na ɗaga dan zuciyata ta gama bani Maash ne. Koda na kai kunne shiru babu magana, nima sai kawai nayi shirun. Munfi minti ɗaya a haka ganin baida niyyar magana na ce, “Assalamu alaikum wanene Please? Dan kana kiran matar aure ne”.
Nan ma shiru kamar bazai tanka ba, sai can ya ɗan motsa a ƙasan maƙoshi sosai dan da ƙyar nake iya jinsa ma ya ce, “Nima mijin aure ne”.
Murmushi nayi a karo na farko, a fili kam na bashi amsa da, “Uhhyim to wa kake nema?”.
“Mrs Maashhhh”.
Ya wani jaa h ɗin ƙarshe har sai da naji tsigar jikina ta tashi. Da ƙyar na iya saita kaina na ce, “kayi ɓatan kan number wannan Mrs Muhammad Awwab ce”.
Ina jiyo sautin murmushinsa sai dai baice komai ba. Dan haka nima na murmusa ina kaiwa kwance. Yaja wasu sakanni kafin ya amsa ni da, “Miya hana ki barci har zuwa wannan lokacin?”.
A hankali na ce, “Ba komai”.
“Kin tabbatar?”.
“Uhmm! Kai miya hana to?”.
Ɗan shiru yayi sannan ya ce, “Kewarki”.
yanda ya faɗa ɗin ya sakani ɗan lumshe idanu, gudun karya fara ɓaromin manya-manyan magana ya sani cewa,
“Naga waya nagode sosai ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara buɗi mai albarka. Ya yaye maka dukkan damuwarka. Ya maida maƙiyanka ƙasan takalman ƙafafunka. Ya ɗaukaka darajarka a duniya da lahira”.
Maimakon amsa ƙitt naji ya yanke kiran. Mamaki ya kamani nai zuru ina kallonta kawai. (To addu'ar ce baya so ko mi) kafin na samo amsata sai ga video call ya shigo. Ajiyar zuciya na sauke kafin na tashi zaune na jingina da gadon sannan na ɗaga. Ƙaramar ajiyar zuciya na sauke da ɗan binsa da kallo. Kafin na ɗan rissinar da idanuna ƙasa dan babu riga jikinsa sai raɓar ruwa da yake alamar wanka ya fito. A hankali ya furta, “Cire wannan hijjab ɗin”.
Idanuna na ɗago cikin ɗan warosu waje na ce, “Saboda mi?”.
“Haka nake so”.
Ji nai kamar na kwafɗesa, amma yaya na iya dole na cire ɗin bayan na kalla ƙofar bayi kada aunty Falaq ta fito. Da ga baya ma sai na miƙe na fita gaba ɗaya na koma falon sama. Sai da na zauna sannan na kallesa na ce, “Sorry”.
Komai baice min ba sai wani shegen kallo da yake bina da shi har ina jin kunyar kaina da kaina duk da rigan ba wani ya nuna min jiki bane, wando ne da riga amma ta ciki best ce sai yar jacket ɗin samanta da take har gwiwa. Ta cikin ta kama min jiki sosai saboda ta wajen a buɗe take. Baki na ɗan tura na ce, “Wai mi kake kallo?”.
Maimakon bani amsa sai ya ɗan sakin murmushi da faɗin, “Ina jinki maimaita”.
“Mi kuma?”.
“Du'a”.
Sai naji kunya ma duk ta kamani. Amma sai na daure na maimaita masa kamar yanda na faɗa a farko. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke mai nauyi lips ɗinsa na motsawa. Dai-dai nan na fara jiyo hayaniya na tashi sosai a gidan, hanyar down stairs na kalla da sauri, kafin na miƙe da sauri ina faɗin, “Ya Awwab gidan nan fa