Showing 9001 words to 12000 words out of 438336 words
ba na nufi hanyar ɗakinmu ni da su Bibaa, dan Baby tun muna yara tace bazata zauna dani a ɗaki ɗaya ba. Hakan yasa aka haɗani da Bibaa da auta. Nasha wahalar yaran sosai, dan dukkan nauyinsu kaina ya koma, ga fitsarin kwance. Dole nabar musu katifar na dawo kwana ƙasa saman tabarma. Bayan na fara zama budurwa nazata za'ace nabar cikin yaran na koma ɗakin Baby, amma shiru kake ji wai malam yaci shirwa. Sai ma wani sabon salon iskanci da ita Bibaa kan min yanzu, wai ita tana takura gaskiya a ɗakin dan munyi yawa. Ban taɓa cemata komai a kan hakan ba dai, dan fatana ma a yanzu Mansoor ya fito kawai ayi auren mu a wuce wajen. Shima Yaya Musaddiq yay nasa Hafizzullah ya koma gidansa ba shike nan ba mun bar musu gidansu........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒆𝒗𝒆𝒏_
.......Ina shiga ɗaki kukan da banyi ba a gabansu ya kufce min. Ban yarda nai zaman yinsa ba, na zame kayan jikina kawai na nufi bathroom. Tsayawa kawai nai ina kallon bayin raina a matuƙar ɓace. An masa kaca-kaca tamkar banyi wahalar gyaransa ba kafin na wuce. Nasan Bibaa ce tai masa haka. Dan tsabar iskanci har pad data cire guda biyu ta yasar a bayin da pants ɗinta. Inada ƙyanƙyami sosai a rayuwata, dan abu kaɗan ke ɗagamin hankali, shiyyasa ma nake bugar jikina na tsaftace gidan yanda ta kamata batare da jin ƙyashi ba. Hawaye tab da idona na shiga gyaran bayin, sai da na maidashi ƙal na tattara trash ɗin data tarama mutane na fitar. Har lokacin suna a falon zaune suna kallo har Mum ɗin, kai kace basu ji sallar magrib da akeyi ba. Na jima da fahimtar Mum saita gadama take salla, shiyyasa ƴaƴan nata ma dai gasu nan sai a hankali babu wanda ya damu da ibadar. A da Hafizzullah har ya fara ɗaukar ɗabi'ar, sai da na miƙe kansa ni da Yaya Musaddiq tamkar bama ƙaunarsa sannan. Sake zuwa nai na wucesu na koma ciki. Sai da nayi wanka na saka doguwar riga mara nauyi nai salla. Bayan na idar zaman yin karatun Alkur'ani nayi, ban ɗaga a wajen ba sai da akai isha'i, har lokacin kuma ina jiyo hayaniyarsu a falon, sallar dai bazasu tashi suyi ba. Falon na fito na wuce dan ɗaukar abinci na, amma sai na samu wayam. Banyi ƙasa a gwiwa ba na dawo ina tambayar Bibaa. Wani kallon banza yarinyar ta watsa min duk da kuwa na bata kusan shekara bakwai zuwa takwas, dan kwata-kwata yanzu take a shekara ta goma sha uku, a gadarance ta ce, “Kin bani ajiya ne. Ka jimin rainin wayo dan ALLAH mtsowww!!” ta maida kanta ta cigaba da abinda take yi. Bance komai ba na juya na koma ɗaki, dan hakan da tai na nufin yau banda abinci a gidan tunda na tafi aiki ban kammala miya ba, bayan kuma nayi komai har abinda ba'a sakani ba, miyar ma na barta ne kawai ta gama fidda mai dan karna makara tunda ta soyu. Wajen kwanciyata nakai zaune ina hawaye, dan haka kawai yau naji zafin abinda akai min ɗin duk da bawai yau ɗinne farko ba, amma kasancewar na dawo da yunwa sai abin ya zafeni. Tun muna yara idan Mum ta bushi iska takan hanamu abinci, haka Hafizzullah zaita kukan yunwa dan ni da Yaya Musaddiq mukan daure, ko zaiyi kukan mutuwa kuma bazata bashi ba sai dai Yaya Musaddiq ya fita ya samo masa a waje koda da bara ne, yanzu kam da muka girma idan aka hanamu zai sayo ya jamu ɗakinsa muci mu ƙoshi muna hirarmu. Sai kuma hakan ke ba Mum haushi take kai ƙararmu ga Abba wai muna haɗe kai muyita zaginta a ɗakin Yaya Musaddiq. Wani lokacin Abban kan mana faɗa, wataran kuma ya mata shiru, sai dai ta ƙaraci masifarta ita kaɗai. Ganin zaman bazai amfaneni da komai ba na miƙe ina share hawayena. Ƙaramin hijjab ɗina na zaman gida na ɗauka na saka, na ɗauki jakata dana fita aiki da ita na fito. Suna a falon har yanzu suna kallo, banko kalla kowa ba a cikinsu na fita zuwa ɗakin Yaya Musaddiq. Sai da na ƙwanƙwasa tare da yin sallama ya bani izinin shiga sannan na shiga. Tashi yay daga kwancen da yake a tabarmar barcinsa, dan koya sayi katifa amshewa Mum take ta bama su Bibaa su kasheta da fitsari ko a bama su Abbas. Kusan sau uku tana yin hakan shiyyasa ma ya bar saya shima. Murmushi yay min yana mai bina da kallo, na ɗan tura baki gaba ina zama a gefensa da ajiye jakar kamar a yanayin gajiye. Yaya Musaddiq mutum ne mai sauƙin kai sosai, da wahala ka iya ganin fushinsa a zahiri. Cike da kulawa ya ce, “Kandala miya faru kuma ake kumbura wannan cat face ɗin?”.
Sake tura bakin nayi da faɗin, “Ni ba komai, yunwa nake ji”.
Ɗan jimm yay yana kallona, sai kuma ya ɗauke kansa da sauke ajiyar zuciya ya miƙe. Rigarsa ya ɗauka ya saka a saman singlate ɗin jikinsa. “Ki jirani ina zuwa”.
Kaina na jinjina masa ina kaiwa kwance a tabarmar tasa. Yana fita na ɗan lumshe idona. Kusan minti huɗu ina a haka sai kuma na miƙe zaune. Jakar tawa na jawo gabana, tare da zuge zip na ciro mujallar nan da MD ya bani ɗazun. Yanzu kam kai tsaye na zubama mujallar ido, sosai nama mutumin kallon ƙurilla a karo na biyu, badan baiyi haske dau irin na larabawa da indiyawa ba da tabbas zan iya cewa daga cikinsu ya fito. Dan daga suffar jiki har zuwa ta halitta fuska bai yi kama da ƴan Nigeria ba. Sai dai kuma abin mamaki fatarsa zamu iya cewa irin tamu ce. Duk da kuwa ba baƙi bane wulik, idan ma za'a kira farare za'a iya nunashi mu anan Africa, sai dai kuma farin nashi yasha banban, koda yake maybe camara ce ta maida shi hakan. Sake maida idanuna akan kitson kansa dake ɗaure a tsakkiyar kai kamar wani mace, sai kawai naja sirrin tsaki, banda ƙarshen duniya dai ace namiji da kitso da ɗan kunne. Kai ALLAH ya ƙyauta, inaga dai ɗan daudu ne gaskiya. Dangwarar da mujallar nayi gefe na sake komawa nai kwanciyata. A dai-dai nan Yaya Musaddiq ya shigo ɗakin da sallama. Amsa masa nai ina tashi zaune. Ya ajiye min ledar hannunsa yana faɗin, “Oya tashi kici”.
Babu musu na tashi zaune, ina ƙoƙarin buɗe ledar shima yana kaiwa zaune ya ɗauki mujallar. “Tofa! Ke kuma ina kika samo _Maash_ haka kandala?”.
Baki na taɓe da fara kai lokar indomie ɗina. Kafin na ce, “MD ɗinmu ne ya bani yau wai zanyi aiki a kansa”.
“Aiki kuma?”.
“Eh Yaya, so suke wai nayi hira da shi a ranar bikin buɗe Companyn sa”.
“Kai lallai sun haɗaki da aiki. Amma ALLAH ya bada nasara”.
“Amin” na amsa masa ina sake jin karaya. Sai kuma na kallesa, batare da nasan ya akai bakina ya suɓuce ba na ce, “Yaya amma dai shi ba musulmi bane ba ko? Sannan ba ɗan Nigeria bane?”.
Sosai ya waro idanu waje da faɗin, “Kai! K waye ya gaya miki ba musulmi bane?”.
“To Yaya wane musulmi ne zai zauna ai masa kitso a saman kai ya ɗaure haka kamar wani mace. Ga ɗan kunne kuma a kunne ga tattoo a wuyansa. Sannan kalli idonsa kamar na mage fa. Ni wlhy banji ya birgeni ba abu kamar ɗan daudu”.
Dariya Yaya Musaddiq ya saki yana girgiza kansa. Ya ce, “Banda abinki Samraah dan mutum yayi duk wannan sai a fiddashi a musulunci ko a kirashi ɗan daudu. Wannan abun da kika gani yanzu shine samari suka ɗauka matsayin gayu da wayewa wai, baki ganin kuma shi ɗin mai lokaci ne da duniya ke ji da gani. Idan kuɗi na ɗibar mutum ai komai ma sai ya yi ba komai bane. Sannan shi ɗin kamar ance ruwa biyu ne. Tsakanin kakansa da kakarsa akwai wadda ba ɗan Nigeria ba, anan ma ya kwaso waɗan nan kamannin da kowa ke ganin ba ɗan 9ja ɗin bane ba. Amma asalin mahaifinsa ɗan kwanar Mashi ne ma, Kinga kuwa shi cikakken bakano ne, anan ma aka haifesa shi”.
Baki na taɓe akan maganar yaya ta kusan ƙarshe, sai kuma na ce, “Humm, to ALLAH ya rabamu da irin wannan kuɗin masu mantar da bawa shi waye kuwa. Ni yanzu Yaya yaya zanyi to. Wlhy duk kaina ya gama kullewa fa?”.
“Karki damu in sha ALLAHU zamu samo mafita. Ke dai kawai ki saka a zuciyarki zaki iya. In dai shi ba aljani bane nasan duk taurin kan Maash bazai gagari Kandalata ba ai. Dan itama tauriƙiƙin kantace ga naci akan abinda tasa gaba”.
Dariya na ƙyalƙyale da shi da faɗin “Kai yaya?”
Ya ce, “ALLAH ai nasanki ne fiye da yunwar cikina kandala”.
Nanma dariyar nayi shima yana tayani, tuni Yaya ya mantar dani baƙin halin mutanen gidanmu. Ya kuma bani ƙwarin gwiwa sosai data bani karsashi akan tunkarar wannan aiki da MD ya bani, ban baro ɗakin ba sai da na fara hammar barci....
Washe gari ban ɗaga ko tsinke ba a gidan, dan banma tashi a barci ba sai ƙarfe bakwai. Salla nayi nai wanka nai shirin office nai tafiyata, dan har lokacin babu wanda ya tashi suna can suna barci ana jiran jaka ta gama girkawa a fito a ci. To ai na fisu iya tsiya, dan kamar yanda na saba in har aka gunziga min baƙin ciki a gidan sai na maida murtani. Yaya Musaddiq bai san tsiyar dana shuka ba ya ɗaukeni muka wuce a mashin ɗinsa. A hanya nake roƙonsa wannan weekend ɗin muje muga Hafizzullah a Katsina dan ALLAH idan baida aiki da yawa. Bai musa ba yace min in sha ALLAHU zamuje ranar asabar sai mu dawo lahadi. Sosai naji farin ciki, harma na manta da damuwata balle na sanar masa banyi breakfast ba na gudo yau. Yana sauke ni ya miƙamin 1500. Amsa nayi ina masa godiya da yima iyayenmu addu'ar samun rahama. Daga haka na shige shi kuma ya wuce.
Kasancewar yau inada gabatar da program banfi zaman mintina talatin ba na tashi na fita tare Khalid. Kusan cin karo mukai da Mansoor dake ƙoƙarin fitowa. Baya naja da sauri, sai hakan ya sakani tuzguɗewa na tafi zan faɗi. Kusan tare suka kawo hannu shi da Khalid domin taimaka min, niko nai saurin sake maida jikina baya ta yanda kowannensu bai samu damar taɓanin ba, dan na gwammaci na faɗin kawai. Aiko faɗuwar nayi, na kuma ji zafi sosai, duk da kuwa na fuske Mansoor sai da ya fahimci hakan. Cike da damuwa yakai duƙe gabana tare da sake kai hannu zai riƙo nawa na ɗan hararesa. Murmushi kawai yay ya janye hannunsa yana kaisa saman kansa ya shafa cike da basarwa. Sai kuma ya sake maida idonsa gareni, a hankali ya ce, “Yanzu har kina da damar yin masifa babie. Naga dai hannun ai nawa ne”.
Sake hararsa nayi tare da ɗauke kai ina ɗan murguɗa baki, na ce, “Sai ka bari sai ka biya ai”. Ina kai ƙarshen maganar na miƙe abina. Dariya ya saki mai sauti da faɗin, “Rigimammiya kawai ai saura ƙiris dai, mi kike ci na baka na zuba. Wata uku bazaki ƙaraba sai da igiya uku na ciff a kanki”.
Murmushi kawai nayi ina ɗan murguɗa bakina dake cikin face mask ɗina na wuce na barsu a wajen Khalid na tayasa dariya. Sai da na gaishe da kowa kafin na wuce na ɗan ƙara gyara fuskata gaban mirror, suma su Mansoor sun shigo, dama mu zaije kira ashe. Hakama baƙonmu na yau ya iso tuni, dan haka babu ɓata lokaci aka fara gabatar da program ɗin........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑬𝒊𝒈𝒉𝒕_
__________________
Kuzo na kawo muku cookbook me recipe sama da 60 a farashi mai rahusa, kunsan azumi ya gabato ya kamata adinga canzawa Habibi abinci. Kar a dinga bawa maigida kullum doya da kwai, ko chips, nace ko kin san zaki iya sarrafa dankali ya baki sama da abinci kalla 5, kin iya? Ko de kullum chips kike bawa habibi? To ga cookbook na kawo ki zo ki saya ki saye zuciyar maigida ga kuma drinks and smoothie's shima kalla kalla, kai har da bonus din yadda zaki iya homemade yogurt and mayonnaise.
Wannan cookbook din zaku same shi a farashin 2k amma first 10 people zasu bada 1k each.
https://wa.me/message/MLUBB6FMKURYH1
__________________
.......Yau ma kamar kullum Mansoor ne ya ɗaukeni zuwa gida bayan an tashi. Mun ɗan fara tafiya nake sanar masa aikin da MD ya saka ni. Da mamaki ya juyo yana kallona da faɗin, “What! Dama ke ya bama aikin nan? Taya zai haɗaki da wannan aikin mai wuya bayan yasan wanene wannan mutumin. A tarihinsa fa bai taɓa yarda yayi hira da ɗan jarida ba har yanzu. Kuma karki ɗauka wai ƴan jaridar nan gida Nigeria kawai. A'a har manya-manyan ma irinsu BBC, VOA, Aljazeera da ire-iren su. A duk sanda aka buƙaci hira da shi sai ya haɗa mutane da P.A ɗinsa...”
“Hu'umm, to amma shi miyyasa yake yin haka? Kamar ba wayayye ba? Ko kuma bashi da gaskiya ne shiyyasa yake gudun hakan?”.
“To ALLAH kaɗai masanin gaibu, sai kuma shi da ya barma kansa sanin dalilin. Amma dai wasu na ganin girman kai ne kawai da giyar kuɗi dake ɗibarsa. Dan a yanzu fa shine matashi ɗan kasuwa na biyu a duniya dake juya manyan kuɗaɗe, anama hasashen nanda shekara mai zuwa zai iya zama na farko. Wasu kuma na ganin akwai dai wani babban dalili nashi, dan in har da girman kai ne ai zaiso ƙara bayyanama duniya shi ɗin wanene ta hanyar ƴan media ɗin. Wasu ko na ganin ko dodon tsafinsa ne yace kar yay hakan, kin san dai mafi yawan ƴan kwasuwar nan dake shahara a ƙanƙanin lokaci sai a hankali, shiyyasa ake yawan ɗora musu zargi, ALLAH dai masanin gaibu. Amma gaskiya al'marin dai nasa akwai ɗaure kai”.
“Ƙila to aljanu ne da shi da basa son hira da ƴan jaridar. Ko kuma dai da gasken dodon tsafinne da shi. Dan ni naga yanda kowa ke misalta dukiyar tasa akwai ban tsoro kam”. Na faɗa cikin halin ko in kula. Dariya sosai Mansoor ya sanya, tare da faɗin, “Kai Babie baƙya rabo da wauta ALLAH. Aljanu kuma? Namiji da aljanu? Adai tsaya a dodon tsafin”.
“To inba aljanu ba shi kam ai abin nasa yayi yawa, dodon tsafin ma kuma ai aljanu ne. Yanda yake nuna kansa a matsayin wayayye irin haka ai ya kamata ace an wuce wannan ajin. Amma ni kam in sha ALLAHU sai na sakashi ya magantu, ni halin nasa ma sai ya ƙara min ƙwarin gwiwar tunkararsa.”
Sosai Mansoor ya juyo ya kalleni cikin nuna mamakinsa a fili. Sai kuma ya maida kansa ga titi yana faɗin, “Anya yarinyar nan kin san wanene *_MASH!?_* kuwa? Babu sauƙi fa a ɗaukar wannan alwashin naki. Ni dai ina gargaɗarki da kar kiyi wani abu mara ƙyau dan ALLAH. Idan kin samu dama kamar yanda kowa ke fata fine, idan baki samu ba ba faɗuwa bace. Dan haka be careful sweetie. Kar ki biye ta MD kujerarsa kawai yake yunƙurin saitawa”.
“Karka damu, ni ba wani abu mara ƙyau zanyiba ALLAH. Kuma duk ma tambayar da zan masa ai sai na kaima MD ɗin ya duba. Kaima kuma zan baka ka gani kafin ma na turama MD ɗin har ma Yaya Musaddiq. Kawai dai ina fatan karya masa wannan alfaharin nasa ne”.
Kansa ya jin jina min, ya ce, “To ALLAH ya bamu sa'a, dan zanfi kowa kasancewa a farin ciki ace kece kika karya ɗin kam. Dan har ƙyauta sai na miki na musamman”.
“Tami?”.
“A'a ai ba sai na faɗa ba. Yanzu dai ajiye ma wannan batun. Su Alhajina fa zasu zo wannan weekend ɗin. Dan haka yau ina buƙatar ganawa da Abba yaya za'ayi kenan”.
Da sauri na juyo na kallesa, ya jinjina min kai alamar tabbatarwa. Kaina