Showing 387001 words to 390000 words out of 438336 words
Bibaa yace ai yanada matar aure. Gaba ɗaya sai jikin Abba yay sanyi, Gwaggo Gudidi zatai batun Bibaa yay mata alamar ta bari. Haka dole tai shiru. Bayan la'asar muka bar gidan. Companyn sa mukaje. Daga inda labarin Muhammad Awwab El-Mu'azz Maash da Samraah Abdul-wahab Gwarzo Sam-G ya fara kenan. Sai da naji hawaye sun cika min ido. Dan komai dawo min ya dinga yi tamkar yanzun ne yake faruwa, barema da muka shiga hall na meeting aka saka mana footage na ranar taron. Hatta da inda nake ɗaukar video a wajen gawar Jaga da bai mutu ba. Rungumeni Ummie tayi tana hawaye. Yayinda Maash ya haɗamu gaba ɗaya ya rungume shi kuma. Bamu baro cikin company ba sai goma da kusan rabi na dare. Muna fitowa daga Company tafiyar tamu ta rabu. Su Ummie akai gida da su mu kuma wata hanyar daban. Ƙoƙarin tambayarsa nayi ya hana, dole naja bakin nai shiru har muka iso. Wani irin mugun waro idanu nayi ganin gidan da aka fara kawoni amarya matsayin matar Maash, ni kuma ina ɗauka matar Mansoor. Rasama abinda zance masa nayi, na saki baki da hanci kawai ina kallonsa. Ido ya ɗan kashe min tare da jan mayafina ya rufe min fuska sannan ya ranƙwafo ta bayana hannayensa duk saman kafaɗata cikin kunne ya furta, “Idan za'a kawo amarya rufe fuskarta akeyi”. Ban iya nace masa komai ba. Face murmushi dana saki ta cikin mayafin. Hannuna ya kama har ciki, bai ajiyeni a falo ba ya kaini har bedroom ɗin nan da tarihi bazai taɓa mantawa da shi ba. Sai da ya zaunar da ni a saman gadon sannan ya furta, “One minute” ya juya ya fita. Mayafin na ɗaga ina bin bedroom ɗin da kallo idanuna cike da hawaye komai na dawo min tamkar yanzu yake faruwa. Sai da naji motsin zai shigo mai maza na maida mayafin yanda yake. Abinda ya shigo da shi ya ajiye, na fahimci hakanne saboda ƙamshin daya cika ɗakin. Cikin nutsuwar nan tasa ya kai zaune kusa da ni, batare da yayi magana ba ya kamo hannayena cikin nashi, kaɗan ya murza yatsun da suka sha lalle yau wajen ƙanwar mijin aunty Zakiyya, sai kuma ya ɗagosu duk ya kai mitsitsin bakinsa ya sumbata. Hannayen ya saki ya kama gyalen ya buɗeni ya saka kansa ciki shima, sannan ya sake maidawa ya lulluɓe mu. Cikin wata irin murya mai taushi da sanyi ya furta,
“Mrs Muhammad Awwab!”.
Har cikin tsakkiyar kaina naji wannan kira. A wani irin slowly na ɗago manyan idanuna da ruwan hawaye ya jiƙe na zubasu cikin dara-dara ɗin cat ɗin nasa da blue ɗin ya fito sosai da ɗigo-ɗigon gold. Idan har kaga idanunsa haka to yana cikin matuƙar farin ciki ne babu wata damuwa a tattare da shi........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑯𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅_
Kai jama'a 100 fa 😭
.......Kallon juna muke tsakkiyar ido tamkar zamu cinye kanmu. Ga numfashin juna muna shaƙa a lokaci guda. Cikin matuƙar sanyin murya ya furta, “Samrh! Kece ALJANNAR DUNIYA TA”.
“Nima haka Yaya Muhammad”. Na bashi amsa cikin karyewar murya. Kamoni yay gaba ɗaya na ya saka cikin jikinsa ya rungume tsam-tsam. Kafin ya shiga laluben lips ɗina ya haɗe da nashi. Wani kalar salo yake min mai gigita zuciya da matuƙar nuna sallamawa ga abinda ka yarda kake kuma matuƙar so da bege. Ban wani zauna ɓata lokaci ba na bashi dukkan amanna nima. Sai da ya tabbatar da kansa ya samu yanda yake so kafin ya barni muka sake rungume juna muna mai sauke ajiyar zukata a jere. Munja tsahon lokaci a haka kafin ya ɗagoni yana kallona. Murya a dasashe ya furta, “ALLAH yay miki albarka kinji”.
“Amin ya rabbi, tare da kai Yaya Muhammad”.
Idanu kawai ya ɗan lumshe min ya buɗe murya a ɗashe ya ce, “Salla”. Ban musa masa ba muka shiga toilet. Yanda nake ganin ko'ina ƙal nasan sakawa yay akazo aka gyara. Alwala muka ɗauro kawai muka fito. Kamar yanda ya ambata muka gabatar da salla har raka'a huɗu. Addu'a ya mana sosai dana sake tabbatar da yanada ilimin addini. Bayan mun idar ya buɗe ledar nan daya ajiye. Sai ga gasassun ƴan shila da akaima gyara na musamman a cikin takeaway. Kun san Sam-G ɗin taku yanzu babu abinda ta iya sai kwaɗayi, ai ƙagara ma nayi a fara ci. Da kansa ya dinga bani, shima yana ci, sai da mukai ƙat barema ni (Su Sam-G anga banza🤪). Fuskarsa da ɗan murmushi ya ce, “Na biya bashin kazan al'ada ba?”.
Idanu na lumshe ina murmushi na furta, “Harda gyara ma”.
Sai kawai ya jinjina kai yana sake faɗaɗa murmushin sa shima. Taimaka min yay na cire kayan jikina shima haka muka tafi bathroom wanka. Dan na fara hamma barci kuma yazo. Baya wasa da hakan dan Doctor ya tabbatar masa ina buƙatar dinga samun isasshen barci a ƙalla na awa goma sha ɗaya kowace rana. Bayan munyi wanka da brush mun fito ya ciro kayan barci a wardrobe ya saka min, sannan shima ya fita. Babu wani jimawa ya dawo cikin nasa kayan barcin harna kwanta ma ni. Fitilar ɗakin ya rage shima ya hawo saman gadon yana mai kwantar da kansa a saman filon da nawa yake. Tare da rungumoni jikinsa sosai. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, dai-dai lokacin da yake kai hancinsa saman wuyana yana busa min numfashinsa da shinshinar wajen. Da sauri na ƙanƙame hannunsa dake saman cikina.
“Kin fara barci ne?”.
Kaina na girgiza masa.
“Bayan an kawo amarya ɗakinta, angonta ya bata kazan al'ada. Sunyi sallan godiya ga UBANGIJI miya rage kuma?”.
Jinai gaba ɗaya na daburce musamman yanda yake maganar a cikin kunnena da shinshinar sa yana kuma busa min numfashi duk a lokaci ɗaya. Muryata na rawa na ce, “Ba komai sai suyi barci su huta gajiyar biki”.
“Faɗi gaskiya dai?”.
A shagwaɓe na ce, “Da gaske”.
“Bashin kazan shi fa?”.
Ya sake faɗa cikin salon ruɗa min jiki. Da ƙyar na iya furta, “Ai ba bashi bane ƙyauta ne na tarba”.
“Ni dai nawa bashi ne a biyani”.
Ya bani amsa yana birkitoni jikinsa gaba ɗaya. Bamma san na shige ba kawai na ƙanƙamesa ina masa kukan shagwaɓa da faɗin wannan ai wayone kawai....
💙🩸💙🩸💙
Tari ne ya hanata sukuni cikin dare, ga barci ta kasa saboda abubuwa sunma zuciyarta yawa matuƙa gaya. Gashi yau Ummanta ta wuce gida, tayi zaton Abba zai shigo ya kwana anan sai dai har yanzu babu shi babu alamarsa. Tashi tai ta shiga bayi, kawai sai tarin ya sake sarƙeta. Sai da tayi sosai hannunta a saman bakinta. Tana samu ya tsagaita ta janye hannun mi zata gani. Jini a cikin hannun nata. Wani irin tsargawa zuciyarta tayi. Tai tsai tana kallon jinin al'amarin kamar a mafarki. Jini fa? Mike nan? Mi hakan ke nufi?. Jitai gaba ɗaya tana neman susucewa ma. Tuni ta zame jaɓar ta zauna a ƙasan bayin wani zufa na keto ma illahirin jikinta dake tsumar rawa. Ta jima zaune a wajen batare data san makama ba. Kafin tai ƙarfin halin tashi ta wanke hannunta da bakinta da fuskarta ta fito. So take ko kuka tayi kam yanzu amma hakan yaƙi yiwuwa. Haka ta ɗauki waya batare da duba ƙarfe nawa ba tai kiran Ummanta. Cikin alamun mai barci ta ɗaga daga can, sai kawai ta sakar mata kuka. Hankali tashe Umma ke tambayarta lafiya. Da ƙyar ta iya mata bayanin abinda ya farun. Ita kanta Umman daga can duk ta gigice. Sai maimaita kalmar, “Jini! Jini fa da Jalilah. Miya kawo jini kuma daga tari. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un na shiga uku ni Larai. Kinga yanzu dai ki kwantar da hankalinki dare ya riga yayi, kuma ko mijinki kada ki faɗawa da sassafe zanzo muje asibiti kinji ko”.
Mom na sharar hawaye ta ce, “To Umma sai kinzo”.
Koda ta yanke wayar sai ta faɗa saman gado kawai ta saki kuka, dan bata da abinda ya rage mata kuma sai dai kukan kawai. Al'amarin yaran nan su Samraah da Haihuwar nan ta Halime yayi masifar tsaya mata a zuciya fiye da komai. Dan shi kansa Musaddiq yaron gaba ɗaya ya sauya ya canja tamkar bashi ba. Sai ka ɗauka ama can ƙasar wajen yake rayuwa ba watanni kawai yay da tafiya ba. Hafizzullah ƙaraminsu na baya-baya da bama ta damu da shi ba shi kansa yaron baka gajiya da binsa da kallo yanzu. Balle kuma babbar giwa. Yarinya ƙarama jiba yanda take gara kan babban mutum irin Maash da manyan ƙasa ma ganinsa garesu aiki ne babba. Ai dolene ma a wannan al'amarin akwai aikin asiri. Bata yarda da tsohuwar nan ba Gwaggo Gudidi. Akwai abinda suka nemawa yarinyar nan ta mamaye Maash da danginsa. Kuma wlhy sai ta tona mata asiri dan sai inda ƙarfinta ya ƙare auren nan sai ya tarwatse. Bari dai tasan inda Baby take tukunna”. Sai kuma hawaye sharrrrr.....
Hummm Mom! Mom!! Mom!!!!!!🤨
❣️❣️❣️❣️
Barci na sha sosai da safe dan tun bayan sallar asuba dana koma ban tashi farkawa ba sai sha ɗaya. Nayi mamakin ganinsa gefena shima yana barcin. Sai duk ya bani tausayi. Babu wanda baya buƙatar hutu a rayuwarsa. Sai dai kawai dan babu yanda za'ayi dole a haƙura. A gefe mutane sha'awarsa suke ya tara, a rayuwarsa kam cike take da ƙalubale da buƙatu kamar kowa. Na tabbatar inda zai samu dama zai kwanta a gida ya huta koda na tsawon sati ɗaya ne. Amma sam bashi da wannan damar. Koda ya gwada yin hakan bashi yiwuwa garesa, ni kaina matar tasa lokacinsa ƙayyadajjene a gareni. Numfashi na sauke a hankali, tare da kai lips ɗina saman small nashi na sumbata. Sai kuma na shige jikinsa kawai na rungumesa sosai. Saukar hannunsa a saman kaina, da yanda ya tura yatsun cikin gashin yasa na sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Muryarsa a raunane cikin yanayin wanda ya tashi a barci ya furta, “Kin tashi?”.
Kaina na jinjina masa tare da sake shigewa jikin nasa na ce, “Amma kai bana son ka tashi yanzu”.
“Why?”.
“Saboda ina son ka huta Please. My Hot wlhy jikinka na buƙatar hutu sosai. Ka duba hanlin daka shiga wata huɗu da suka wuce saboda stress. Shike nan kullum kai ina zaka neman kuɗi, ina ka dawo neman kuɗi. Daga jirgi sai zaman mota. Ko lokacinka bana wani samu. Please kuna hutawa mana, duka rayuwan nawama yake wai. Mu gama nema da tara dukiyar mutuwa ta zo ta tsamemu a cikinta mu tafi kamar ba'a taɓa yinmu ba. Sai ma mun dace da haihuwar ƴaƴa na ƙwarai ne zamu tafi mubarsu da dukiyar su mana addu'a, wasu bishashar gabansu kawai itace damuwarsu. Please mu kasance tare kawai ni basai kaje ko ina ba”.
Na faɗa ina sake shigewa cikin jikinsa sosai. Shima sake ƙanƙameni yay yana sauke wasu irin ajiyar zuciya a jajjere. Kamar yanda nai tsammani baice komai akan batun ba. Sai taimaka min da yay mukayi wanka. Bayan mun gama kimtsawa falo muka dawo, banyi mamakin ganin an kawo mana abinci ba sai dai naji kunya dan daga gani daga gida ne. Haka na zauna muka karya koma nace ni na karya dan shi kam bana ɗaukar cin abincinsa cin abinci. Yanda bai nuna zamu bar gidan ba nima sai nake jin daɗin zama a cikinsa. Salla kawai ke fitar da shi. Ina ganin kiran su Aunty Falaq naƙi na ɗaga dan nasan tana can ta haɗa kai da Fahad iya shege zasu min. Hafizzullah dai gida muka barsa yaga Yaya Musaddiq ya nane masa.
Ba ƙaramin farin ciki na tsinta kaina a ciki ba da zaman gidan nan na yau. Sai la'asar muka fita, nazata ma gida zamu koma sai naga mun nufi wani waje daban. Ashe gidan Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain muka nufa. Acan muka samu su Ummie. Aiko sai naji duk na daburce. Ga Aunty Falaq ta sakani gaba da tsokana. Ummie dai da Mama murmushi kawai suke. ALLAH ya taimakeni Fahad ya shigo tare da Bahijja sai tsokanar ya koma kansa. Har dare muna a gidan Malam, koda muka baro can gidan dai muka koma ni da shi su Ummie kuma suka wuce can. Yau kam a ɗakinsa muka kwana, katifa ce kawai a cikinsa ƙatuwa. Nan ɗin ma mun kasance cikin farin ciki sosai. Washe gari babu barcin safe mukai shirin tafiya Gwarzo. A gidan Abba muka haɗu da su Ummie, nayi mamakin ganin harda Mom, sai dai daga gani bada son ranta bane ba. Dan ina ganin Abba na mata masifa, ga Ummanta tsaye galala tana bin Abban da kallo.
Mota duk muka shiga, dama shi Maash tunda ya fito ya gaida Abba ya koma ciki abinsa. Su Ummie kam bama su fito ba. Wajensu Gwaggo ta shiga. Aunty Falaq da mijinta sai Yaya Musaddiq. Hafizzullah da Fahad motarsu daban. Ni da uban tafiya sai TJ dake jan mu. Abba shi da Mom da su Bibaa sai Kawu Jafaru da muka ɗauka a hanya. Gaba da bayanmu motar guards ce. Ɗan kwanciya nayi a jikinsa dan shi yanata aikinsa ne a laptop. Tun ina kallonsa ina cin chocolate ɗin hannuna harna fara barci. Sai da ya ɗan motsani zai gyara min kwanciya na ɗan buɗe ido. Lumshe mun nasa yayi ya sake buɗewa da faɗin, “Sleep” akan lips ɗin sa. Maida idanun mai kawai na rufe dan barcin nake ji sosai.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑯𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒐𝒏𝒆_
*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._
......Mun iso tushe asali abin alfahari. Tarbar da muka samu ya sake tabbatar min da ansan da zuwanmu. Dan mun sami gidan Kawu Musa cike da dangi ƴaƴa da iyaye kamar ba safiya ba. Bayan gaishe-gaishe da ƴan koke-koken tuna mahaifinmu suka sake neman gafarar Mama Balki da Falaq. Kai tsaye sukace su sun yafe komai ya wuce. Suka kuma nuna farin cikin kasancewa a cikin ƴan uwa da yanda aka musu tarba ta mutuntawa da nuna ƙauna. Falaq nata kuka dan ita kaɗai tasan a kalar farin cikin da take a ciki yau ɗin nan. Abinda ta gama fidda rai da samunsa yau gata tsundum a cikinsu wato dangin mahaifinta, kuma kowa na nuna mata soyayya da ƙauna kamar za'a cinyeta dan kulawa, hakama little Awwab kowa nata ma yaron addu'a.
Su Kawu sun damƙa mata gadonta a hannu, yayinda Ummie ta damƙa mana alƙawarin mahaifinta. Sai zuciyar Abba ta sake karaya yau ma harda kukansa yana bamu haƙuri akan kuskuren