Showing 228001 words to 231000 words out of 438336 words
idanunsa yayi a hankali ya kalleni. Sai kuma ya sake maidasu kan abinda yake yi. A taƙaice ya ce, “Uhmm”.
Ajiyar zuciya na sauke da faɗin, “Okay. Amma ban gane tambayar ba. Akan mi kake nufi?”.
“Komai!”.
Ya faɗa can ƙashan maƙoshi. Jimmm kawai nayi ina tunani bayan na sake maimaita komai ɗin a zuciyata. Kai gaskiya ban gane ba, dan duk da ina zargin ahalinsa ai nake ga bai dace na fito fili na nuna ba, tunda ba sanin nasan tarihin gidansu yay ba. Gara idan shine ya sanar min wani abu ai. Fuska na marairaice a sanyaye na ce, “ALLAH kuwa Ya Awwab ban gane ba”.
Komai baice min ba. Yanzu ma ko ɗagowa ya kalleni ɗin baiyi ba. Kusan mintuna biyu ya ajiye kofin coffee ɗin da yake sha sai kuma ya gyara zamansa. Da hannu yay min alamar nazo. Idanu na waro masa alamar mamaki, amma sai ya ɗauke kansa cike da basarwa yana sake tsuke fuska. Banda zaɓin daya wuce bin umarninsa. Dan sam bazan iya musa masa ba. Ina jinsa da wani irin girma da kima fiye da ko yaushe a yanzu. Sannan wani irin shakkarsa nake ji, kwarjinin sa gaba ɗaya ya cika falon har ina jin yama mana kaɗan. A hankali na miƙe kamar wadda tai laifi take tsoron duka. Dan da sanɗa na isa gabansa. Ƙoƙarin kaiwa ƙasan carpet nake ya min nuni da saman cinyarsa. Kaina na maƙe masa alamar a'a, sai ya ɗan taɓe baki ya nuna gefensa batare da yayi magana ba. Dole na canja na koma kan kujerar gefensa dai na zauna. Sai kuma na ɗan saci kallonsa ta gefen ido. Da sauri na maida kaina ƙasa dan dai-dai shima yana ɗagowa ne. Wani irin ratsawa muryarsa ta sake min har cikin kaina, duk da kuwa yayi maganar ne ba cikin tsawa ko hayaniya ba, dan ko a falon kake ba lallai ka jisa ba dan nima na kasance gab da shine. Amma ban sani ba, kodan sai da ya kamo yatsun hannuna cikin nashi tattausan hannun ne sannan yay magana oho. Sake matsa yatsun nawa yay a hankali ina kuma jin kaifin idanunsa har cikin jijiyoyin da jinina ke yawo.
“Idan nace komai ina nufin ina nufin komai da komai. Nasan zuwa yanzu kin san wanene Awwab a zahirance da baɗinance. Dan kinji komai a wajen Mama, kin kuma san komai a makwancinsa”.
Da sauri na ɗago ina ware idanuna duk da zancensa na ƙarshe ya bani kunya. Cikin ɗan rawar lips da nuna mamaki na ƙarara akan fuska na ce, “Ya akai ka sani mama ta faɗa min?”.
Wani ɗan makirin murmushi ya sakar min da lumshe idanunsa sai kuma ya buɗesu luuuu ya zuba su a cikin nawa. Ƙyaƙyƙyafta idanu na fara da ƙoƙarin janye yatsuna dake a cikin nasa har yanzu. Amma sai ya hana hakan ta hanyar sake riƙesu da ƙyau yana girgiza min kansa. Sai kuma ya janye idanun kamar a kasalance ya ɗaura yatsarsa manuniya mai ɗauke da dogon farce fari tass har wani ƙyalli yake tsabar yanda yake fes, akan zobena ya saka yatsan yana wani zagayawa. Zoben na kalla da sauri nima dan sam ban gane inda ya dosa ba. Sai da ya gama zagayesa sannan ya zaresa a hankali daga cikin yatsata. Ɗan jujjuya min shi yay akan fuska, sai kuma ya runtsesa a cikin hannunsa yana kallona gira ɗaya a ɗage.
“Ke yarinya ne Samrh, tsiwanne kawai yayi miki yawa da shegen kauɗi. Shin bakiyi tunanin taya akai kika zo gidan nan ba haka kai tsaye bayan kin gudu min? Nasan hakan zai iya faruwa, amma dai abune da zai zama mai wahalar gaske musamman idan mukai duba da hannun da kika faɗa....”
Kasa haƙuri nayi, cikin tare numfashinsa na furta, “Dama da saninka nazo nan gidan ke nan?”.
Idanu ya ɗan lumshe ya sake buɗewa a kaina. A bazata naji saukar hannunsa kan hancina. Ya ɗan jashi kaɗan da faɗin, “Yanda kike stubborn ɗin nan ai sai da kula. In ba hakaba zaki ɓaro min aiki ne ƴar jarida”.
Duk da naji kunya sai da na ɗan tura masa baki. A shagwaɓe na ce, “Ai ALLAH kaine stubborn a gidan nan. Ni dama nata wasi-wasi, duk da nasan kaɗan daga ikon UBANGIJI hakan ta kasance. Amma dan ALLAH Ya Awwab ya akayi nazo?”.
Shiru yayi kamar bazai tanka min ba. Sai da na marairaice masa kamar zanyi kuka sannan. Yana a kwancensa jikin kujera idanunsa a lumshe yanzu. Hakan ya bani damar zuba masa idanuna ina kallon yanda yake motsa lips kamar abin dole. “Tun a guduwan farko nasan zaki iya maimaitawa. Shiyyasa na samar da zoben nan exactly irin naki ta yanda zan san duk wani motsinki. Kina asibiti a Abuja na sa miki, bayan dinga nuna kin inda kike har magana idan akayi ko kikayi zan iya jinki”. Ya ƙare maganar yana nuna min abinda ke a kunnensa kamar bluetooth sai dai shi ƙarami ne bai kai bluetooth girma ba
Cikin ɗan yarfar da hannu da mamaki na ce, “Bala'i, dama kaje asibiti ka duba ni ne? Wlhy naci kai. Taya ban taɓa ma lura da zoben nan ba nawa bane?”.
Idanu ya ɗan buɗe yana kallona. Kamar bazai ce dani komai ba sai kuma ya motsa small pinkish lips ɗinsa a hankali. “Saboda ke yarinya ce”.
Jinai kamar na harararesa amma bazan iya ba. Sai wani cemin yarinya yake. Amma duk da haka sai da na ɓata fuska. Hannu na miƙa masa na ce, “Bani zoben na gani dan ALLAH”.
Idanunsa ya maida ya lumshe. A taƙaice ya furta, “Ya gama aikinsa. Ina jinki mi kika yanke dan bani da lokaci zanyi baƙi”.
“Ni ban yanke komai ba, akan samun lafiyar Ummie kawai nake da plans”.
Idanu ya buɗe sosai yana kallona. Sai na ɗauke nawa daga kallonsa dan bazan iya jurewa ba. A hankali kamar mai jin tsoro na furta, “Ya kamata Fahad ya dawo gida kamar yanda kowa yake gida”.
“Nooo!!”.
Ya faɗa a tsawace yana ƙoƙarin miƙewa. Duk da yanda ƙirjina ya buga da rawar da jikina yake yi sai da nai saurin kamo hannunsa. Muryata a karye kamar zanyi kuka na ce, “Dan ALLAH kayi haƙuri ka zauna. Bafa kaji ƙarshen maganata ba Please”.
Ƙin zaman yay har tsawon lokaci. Sai faman huci ma yake yi abin mamaki da tsoro. Hatta da gashin jikinsa duk sun mimmiƙe. Muryata na rawa cike da magiya na sake faɗin, “Dan ALLAH dan ALLAH. Burinka fa shine samun lafiyar Ummie, kuma wannan hanyar da zan faɗa maka in sha ALLAHU ina fatan zata taimaka mana. Kayi haƙuri ka danne duk abinda kake ji game da ɗan uwanka. Dan wlhy komai bazai yiyu ba sai mun haɗa ƙarfi da ƙarfe. Ni, kai, shi, Hayatu, Mama, Baba, da duk wanda ka aminta da shi a cikin yaranka. Idan har wanda baka haɗa komai da su a duniya ba zasu ci arziƙinka yanda suke so har su bama ƴan uwansu kai mi kake jira akan naka gudan jinin ɗaya tilo. Kana ganin idan lafiyar Ummie ƙalau zata barku a cikin wannan halin? Ko a yanzu da take a cikin halin jarabawa wlhy maybe tana jin zafi da kewar rashin ganin ɗan uwanka dan bata san taya zata furta bane kawai. Karfa ka manta shima nan gidansu ne Ya Awwab. Yanda kake da iko da komai na cikinsa shima haka yake da iko da shi dan ko'a addinance matsayin magada masu kaso kai ɗaya kuke amsawa. Duk duniya fa baka da kamarsa, kamar yanda shima baida kamar ka. Duk mu ɗin nan da muke zagaye da kai son zuciya ko wani dalili zai iya sakawa mu gujeka, amma shi komi ka zama bazai daina jin ƙaunarka a zuciyarsa kamar yanda kaima nasan kana ƙaunarsa. Wannan ƙiyayyar dake tsakaninku ƙirƙirarriyar ƙiyayya ce, kune kuma ya kamata kuyi yaƙi da zukatanku wajen ganin kun canjama abokan gaba nasararsu. Kaifa ka tunatar dani ba'aima maƙiyi gaggawa, idan ba haka ba zai rigaka kai inda kake hari harma ya juyo kai baka kai ba. To kenan in har zaka tafin sai ka kasance mai kula gudun kar ya saka maka tarkon da zai riƙeka ya hanaka isar kafin shi ɗin ya iskoka kuma. Dawowar Fahad gidan nan shine first target ɗin mu akan kowa da komai wlhy. Amma na baka dama kaje kayi tunani ka gani, sannan ka nema zaɓin ALLAH. Ni kuma na maka alƙawarin duk abinda ka yanke zanyi biyayya a kansa sai muje plan na gaba, ni dai fatana kawai Ummie ta samu lafiya ne”. Daga haka na saki masa hannu a hankali. Kaina na duƙar na saki kuka. Dan harga ALLAH yanzu wani masifar tausayi yake bani. Bawan ALLAHn nan yana cikin wani irin bahagon ƙulli ne mai tsaurin gaske. Shiyyasa aketa amfani da shi ana azabtar da mahaifiyarsa da ɗan uwansa. Nayi zaton tafiyar tasa zaiyi, sai naga a hankali ya koma ya zauna cikin kujerar tare da dafe kansa da duka hannayensa yay masifar cije ɗan ƙaramin lips ɗinsa kamar zai hudashi da haƙori. Ha jima a haka kafin ya ringa sauke wasu irin zafafan huci da naji ƙarin tsoronsa a raina. Dan tuni na maƙure a cikin kujera kamar mage taga ƙare a lungun mai hanya ɗaya tal.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒆𝒆𝒏_
.......Mun jima zaune a hakan kafin ya mike a fusace. Taku ɗaya biyu ya tsaya cak, batare da ya juyoba cikin kaushin murya ya furta, “Daga yau zaki cigaba da zama anan”.
Wani irin zabura nayi yan hanjin cikina na wantsalawa tare da bugun zuciyata. Bamma san sanda na furta, “Anan kuma?”. Ko kallon inda nake baiyi ba yayi wucewarsa hanyar bedroom ɗinsa. Wani irin bugawa zuciyata keyi diff-difff!! Dan har ga ALLAH maganar tashi tayi masifar ratsa min ƙashi da bargo. Wane irin neman bala'ine haka dan ALLAH. Taya zan cigaba da zama a side ɗinsa bayan Mama Balki ta sanar min babu wanda yasan akwai aure tsakanina da shi. Sannan yan uwansa ma abinda ya faru kallonsa suke ama tsayin fyaɗe. “Na shiga uku ni Samraah mutumin nan zai kasheni. Ni wlhy koma ba duk wancan ba bazan iya zaman anan da shi mu biyu kacal ba. Mutumin daya nema kusan kasheni ina gaskiya bashi yiwuwa. Gara ma tun kan wankin hula ya kaini dare na kama gabana. Inama laifin yace na koma sashen Ummie dan ALLAH. Zaram na miƙe, har haɗawa nake da sassarfa na nufi ƙofar fita. Sai dai kuma gam take alamar an kulle. Idanuna ne suka cika da ƙwalla. Ji nake kamar na saki ihu. Na jima a wajen kafin na yanke shawarar zuwa na bashi haƙuri tare da fahimtar da shi illar wannan hukuncin nasa dan bazai haifar mana da ɗa mai ido ba daga ni har shi ɗin....
🌜🌜💮🌛🌛
“Nafisatu ai ba amsar bane matsalar. Maganar kuma zamowarmu kuma family na farko a jihar nan a tunanina tuni muna ɗaya daga cikin masu wannan matsayin ama Nigeria ba jihar Lagos ba. Ɗanki ya jima da samo mana wannan sunan ama duniya ba'a ƙasar haihuwarmu kawai ba. Siyasa ta wuce duk yanda kike tunani, cike take da rikice-rikice da matsaloli iri-iri. Bazaki gane hakan ba sai mun farata. Amma dai ki bari zan tattauna da Awwab. Kin sanshi yanada experience akan irin waɗan nan abubuwan”.
“Baba yanzu nan duk mu yawan yaranka har mu huɗu cif babu wanda zaka iya shawara da shi a shekarunmu sai jika. Awwab har wani hankaline da shi wanda ko aure baiyi ba.”
“Humm Nafisatu, aure ai lokacine da shi ko?”.
“Baba yana da lokaci, amma kuma kaima ya kamata ka motsashi, yanzu irin wannan abun daya faru idan da maganar nan ta fita mi muke tunani? Ni yanzu ma tsorona ALLAH tsorona yaji daɗi ya cigaba da aikatawa tunda ba kunya garesa ba. Ballema yaga ba'a ɗauki wani mataki ba akai ai kaga abun bamusan kuma ina zai tsaya ba. Tun fa yana taɓa ƴan aiki wlhy wataran kan ƙannensa zai dawo. Dan Awwab yariga yayi gaurin da macen kawai yake buƙata fa. Ya kamata a duba wannan zancen Baba. Idan yana akan bakansa shi baiga wadda yake so ba ai ga ƴar uwarsa nan Azizat. A haɗasu mana kawai tunda Ita dai bazataƙi bin umarninmu ba. Shima kuma idan yaga kowa yaƙi saurarensa ai dole ya amince a wannan karon tunda koba komai yana son asirinsa ya rufu kar duniya ta sani”.
Jinjina kai kawai Baba yake. Sai da takai har ƙarshe sannan ya nisa. “Shawararki abar dubawace Nafisatu, kuma zan duba. Awwab ɗinne sai a hankali, yaro ne mai shegen taurin kan tsiya. Yanzu fa ki duba ki gani saboda yasan abinda yay ba dai-dai bane sam yaƙi zuwa gidan nan. Idan naje can duk yanda zai zame ya gudumin ya sani. Amma barshi nasan mi zanyi. Zanzo yau da dare na ritsashi in sha ALLAHU. Da zarar ya shigo gida ki kirani kawai”.
Cike da farin ciki Hajiya Mammah ta amsa da, “To in sha ALLAHU kuwa Baba. Amma maganar siyasar nan itama dai dan ALLAH a duba mana. Yaya kaga Nafisatu Adams K/Mashi ɗiyar gwamnan jihar Lagos”.
Yanda tai maganar tasa baba ƙyalƙyalewa da dariya. Itama dariyar takeyi....
❤️❤️❤️❤️
Kamar mai tsoron a jita a hankali nai knocking ƙofar, shiru babu motsin komai. Sake yi nayi har fin sau uku. Ganin dai bazai kulani ba na yanke shawarar buɗewa kawai ma shiga. A hankali na murɗa handle ɗin kuwa. Sai ko gashi ya buɗe. Sai da na sauke ajiyar zuciya tare da tsayawa na daidaita kaina sosai sannan na tura na shiga da sallama. Turus na tsaya ina kallonsa dan zaune yake akan sofa daga shi sai towel da waya a hannunsa yana magana cikin yanayin nan nasa a daƙile kamar wanda akama dole. A hankali na maida ƙofar na rufe ina mai duƙar da kaina dan bazan iya jurar kallonsa a yanda yake ba. Nafi minti biyu a wajen ina sauraren wayar tasa dana fahimci da Hayatu yake yinta. Sai dai abinda ya ɗan ja hankalina jin yana faɗin idan sun huta Hayatun ya kawosu nan gida. To ko su waye keda irin wannan matsayin haka. Dan na fahimci tunda nazo gidan nan ban taɓa ganin wani baƙo daya shafesa ba yazo. In banda ranar birthday ɗin nan da Bahijja tace min wanda suke zaune a waje ɗaya abokansa ne, kuma duk ba'a ƙasar suke ba idan ka cire ɗan sarkin Lagos ɗin. Ganin har ya kammala ya miƙe yana ƙoƙarin nufar mirror ya sani gyara tsaiwata. Dan ya wani basar tamkar baima ganni ba. Kuma na san yasan na shigo ɗin rainin hankalinsa ne kawai. Kaina a ƙasa daga ƙofar ɗakin na furta, “Dan ALLAH ina son muyi magana”.
Bai tanka min ba, bai kuma fasa abinda yake ba. Sai da ya mula dan kansa kusan minti biyu sannan ya magantu. Cikin silent voice ɗin nan tasa a daƙile ya furta, “Ki wuce wanka baƙi zasu shigo”.
Ji rainin hankali, ina masa wata maganar yana min wata. To ina ruwana da wasu baƙinsa. A zahiri kam sai na ƙara sauke murya har lokacin kan nawa a ƙasa. “Dan ALLAH kayi haƙuri ka barni naje can inda na saba. Ko kuma na koma sashen Ummie tunda dama a yanzu kusan acan ɗin nake. Ya Awwab taya zan dawo nan bayan kasan akwai matsala. Babu fa wanda yasan akwai wani maganar aure a tsakaninmu a gidan nan. Mi kake tunani zasu fassara zaman nawa?”.
“Su fassara duk yanda yay musu! Idan kuma kina buƙatar su sanin ne, yanzun nan sai na tarosu su sani”.
Da sauri na ɗago ina kallonsa. Yanda yay maganar kansa tsaye babu wani alamun ya ɗauki zancena da muhimmanci. Kai wlhy stubborn mutumin nan ya fara isata. Da ƙyar na iya dannewa muryata na ɗan rawa na ce, “Idan kai zaka iya fuskantar su ka kuma ɗauka komai wlhy ni bazan iya ba. Sannan ba wannan rigimar nake so ba yanzu lafiyar Ummie ce damuwata. Dan ALLAH ka duba zance na yana da muhimmanci...”
“Kin dameni Madam wuce wanka kafin nazo kanki”.
Ya faɗa da ɗan kaushin harshe yana ajiye cumb ɗin hannunsa yana barin wajen. Karan farko naji hawaye sun gangaro