Showing 165001 words to 168000 words out of 438336 words

Chapter 56 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2219

A falo ya sami Auta da Bibaa. Auta yazo garesa da gudu yana murnar ganinsa. Bibaa kuwa sai ta ɗauke kanta kamar bata ganshi ba sai da shi da kansa ya kira sunanta sannan ta gaishesa tana faman fushi. Murmushi kawai yayi ya wuce dan ya fahimci kishi take taya uwarta. Hannunsa riƙe dana Auta ya shiga bedroom ɗin Mom. Dai-dai lokacin take fitowa daga wankan da Umma ta sakata yi dole. Sosai ya ƙura mata udanu yana kallon yanda idonta suka kumbura sunyi jazur je dama fuskarta. Itama wani mugun kallo take watsa masa mai cike da tsana da takaicinsa. Dan wani irin ƙyau da kwarjini taga ya ƙara mata. Daka gansa kaga sabon ango shar daya sha sharafinsa. A take abinda ya ringa musu a gida jiya ya shiga dawo mata. Fashewa da kuka tayi tana rarumar kwalbar turare ta jefesa. Da sauri ya kauce yana tura Auta bayansa. Cigaba da rarumo duk abinda ya tare mata gaba tayi tana jeho masa. Tun yana kaucewa har dai ta samesa. Dole ya fito yana dariyar data sake kular da ita. Dan harga ALLAH shifa dariya borin nata ke bashi yanzu. Da Ummanta yaci karo tana ƙoƙarin shigowa da shayi a hannunta. Haɗiye dariyar yayi ya rissina yana gaisheta. Da ƙyar ta iya amsa masa tana wucewa ko kallonsa batai ba dan itama dai al'amarin nasa na jiya ne ya shiga dawo mata a rai tamkar yanzu komai ke faruwa.......✍️


_🤣Maganin mai zama gidan suruki kenan ai Umma._


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_


.......Alhamdullah sati biyu kenan da fara maida akalar al'amurana sashen Hajiya Babba. Tun ina ɗari-ɗari har na fara sakin jikina. Nayi tunanin Hajiya Mammah ko sauran matan gidan wani zai hana amma sai naji shiru. Sai ma jana da Hajiya Mammah ɗin ta farayi jikinta yanzu. Dan ta daina min faɗa sosai. Aikin sashenta ma idan naje yi iya bedroom take cewa na gyara kawai. Tun al'amarin nata naɗan bani mamaki har dai na tattara na watsar da tunanin ALLAH ne ya amsa addu'ata na fara samun sauƙi daga kowa.
Abinda na fara fahimta ga lalurar Ummie shine tana ƙarfafa ne a duk sanda Awwab ya shigo inda take ko kuma yama zo gidan zance. Dan a kwanki ukun nan da yake a gidan gaba ɗaya mun kasa gane kanta. Yau da safe har ciwo ta jimin da ƙyar aka fito dani a wajenta. Dalilin hakanne ma na yini a sashenmu da zazzaɓi shine nake kwance har yanzu. Ban samu ɗagawar jikin ba sai dare. Kwanciyar ce ta isheni na tashi na fito. Shiru sashen dan kowa har ya kwanta. Harna zauna a falo sai kuma na tashi na fita gaba ɗaya. Ko'ina akwai haske a gidan kai kace rana ce, sai dai babu hayaniya mai ƙarfi dan wanda ma basuyi barci ba duk sun nutsu a ɗakunansu. Tsamin da jikina yay ya sani ɗan fara tattakawa ko zai sake min, duk da ina kwaɗayin zuwa na duba Ummie sai dai babu yanda zanyi dan yau ɗin kam zuwa kusa da ita haɗari ne babba. Cinkushewar zuciya da son mantar da kaina damuwata ya sani nufar garden ɗin gidan. Shi kam akwai ƙarancin haske a cikinsa, amma ko ɗar banji tsiro ba na samu kujera na zauna ina mai ƙurama korayen gayyakin cikinsa da ƙarancin haske ya sakasu yin duhu ido. Kamar da ga sama naji ana wata ƙara mara daɗin ji, gabana ne ya faɗi. Sai kuma na fara jin sambatu dake fita da wasu irin kalamai marasa daɗin saurare. Neman rikicewa nayi, da sauri na kai hannu na toshe kunnuwana. Ban san adadin mintinan dana ɗauka ba a haka kafin na buɗe kunnen. Yanzu kam shiru babu ihun, sai magana ƙasa-ƙasa da akeyi cikin raɗa. Miƙewa nayi cikin sanɗa na nufi inda nake jin maganar. Hango mutane tsaye mace da namiji, namijin na ƙoƙarin sakama macen kaya a jikinta ya sani lafewa jikin fulawoyi.
Cikin shagwaɓa macen ke faɗin, “Wlhy ni na faɗama ban gaji ba. Miyasa yau duk baka son kasancewa da ni ne? Ko dai ka samu wata ne a cikin sabbin masu aikin nan?”.
Da ɗan kaushin murya namijin ya bata amsa da, “Miyasa kike da zargi ne wai? Kin san fa minene matsalar. Muhammad na gidan nan ke miyasa baƙya lissafi ne! Kije sai da safe bana son damuwa”.
Magana ta yunƙura zata sake masa ya ɗaga mata hannu. Sai naga ta faɗa jikinsa ta rungumesa. Niko tunda ya ambaci Muhammad zuciyata ke wani irin rawa. Dan kuwa a bakin mutum ɗaya ne nake jin sunan nan. Kuma ɗansa kawai yake kira da shi wato Awwab. “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un” na faɗa cikin rawar baki sakamakon ganin wanda zuciyar tawa ke ayyana min. Paah tare da Siyama a garden suna aikata z... kasa ƙarasawa nayi, sai ma wani irin kuka daya kufce min. Dole nakai hannuna na toshe bakina har sai da suka fice sannan na durƙushe a wajen nayisa. Wannan wane irin zubar da mutunci ne. Mutum mai daraja da kima kamar Paah ace yana bin masu aiki. Kai ya Arrahaman. Gaskiya ya kamata nasan tarihin wannan gida, ko hakan zai taimakeni wajen fara rarrabe ƙarya da gaskiya. Tare da kallon kowa na gidan nan da siffarsa.

Bayan kamar tazarar mintuna ashirin da fitarsu sannan na fita. Sashenmu nayi nufin komawa, amma sai naci karo da Mama balki da alama daga sashen namu ta fito. Idanu ta waro sosai a kaina. Sai kuma ta kama hannuna cikin sauke ajiyar zuciya tana tambayata “Daga ina haka? Yaya jikin naki? Badai sashen Hajiya Babba kika koma ba?”.
Kaina na shiga girgiza mata. Hawayen da nake makalewa na kufcemin. Sake tashin hankalin ta yayi. Babu shiri taja hannuna. Siririyar hanyar sashensu da mijinta tabi dani. Sai gamu a madaidaicin falonsu da yau ne shigowata cikinsa na farko. A saman kujera ta zaunar dani itama ta zauna. Sai da ta bani ruwa nasha sannan ta fara jeramin sabuwar tambaya.
Kaina na girgiza mata kawai. Tare da faɗin, “Mama babu komai. Amma dan ALLAH idan bazaki damu ba ki bani tarihin wannan gida a yau”.
Ɗan jimm tayi kamar mai nazari. Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Wani abune ya sake faruwa kuma?”.
Kamar zan faɗa mata sai kuma na fasa saboda kwaɓar da zuciyata tayi min. “Babu komai Mama. Kawai dai ina son jine saboda nasan ta hanyar dazan ɓullo wajen taimakon Ummie game da wannan ciwon nata.”
Nan ma shiru tayi kamar bazata tanka min ba. Kafin ta nisa tana mai jinjina kanta. “Zan sanar miki duk abinda na sani Kandala. Saboda harga ALLAH tun randa na fara ganinki a gidan nan zuciyata ta sami nutsuwa dake. A kuma kwanakin nan da kikayi na gwadaki ta hanyoyi da dama banga wata alamar cin amana ko kasancewarki ba mutuniyar kirki ba. Amma duk da haka ina roƙonki ki riƙe min dukkan abinda zan faɗa miki amana dan ALLAH. Sannan zan taimakeki da abinda zan iya domin ganin munyi wani yunƙuri akan Hajiya Babba ko ALLAH zaisa mu dace.”
“Nagode Mama.”

*_Alonso_* aƙon haure daga ƙasar Spain zuwa Nigeria. Kwara-kwara, bature-batture, balarabe-balarabe gashi nan dai bamu san takamaimai ɗan wane ƙabila bane ko yare, kawai dai daga ƙasar Spain yazo. Abinda kawai kowa yake kallo a tattare da shi shine bashi da alaƙa da Africa sam. Alonso ba musulmi bane ba, baya kuma jin hausa ko zo na kasheka, daga turanci sai yaren Spanish. Da farko harkar kasuwanci ce ta shigo da shi ƙasar Nigeria. Dan yana kawo irin dish ɗin nan na kwanika kala-kala da mutanen da ke jere da su. Kafin a hankali ya samar da wajen yinsu anan cikin garin Lagos ya ɗauki yaranmu aiki yana kuma koyar dasu. Sannu a hankali kamfani ya fara bunƙasa kafin cikar shekara biyu duk yaran daya hora sun gama ƙwarewa har suma suna koyar da wasu. Adams shine kusan babban yaron Alonso saboda ƙwazonsa, ga biyayya da ya kema uban gidan nasa tamkar yaya da ƙane duk da kuwa Adams nada mata acan ƙauyensu dake Kano mai suna kwanar-mashi harda ƴaƴa biyu. Dan neman kuɗi ne ya kaisa garin na Lagos. Ƙyaƙyƙyawan halin Adams yasa Alonso yanke hukuncin kaisa ya ƙaro ilimi acan ƙasarsu ta Spain tunda ya faɗa masa yayi sakandire, sai dai bai kammala duka ba saboda matsala ta rashin kuɗi ga nauyin iyayensa da matarsa da duk ke a kansa. Alonso shine ya saka Adams dawowa da iyalinsa da mahaifiyarsa nan Lagos da zama. Tare da saka yaransa biyu mace da namiji a makaranta. Nafisa da Mu'azz, sai ciki da matar tasa ke da shi tsoho. Ganin a yanayin da take Alonso ya bama Adams shawarar tafiya da ita amma sai mahaifiyarsa ta hana. Ganin haka yasa Alonso neman wadda zata kula da ita matsayin mai aiki saboda mahaifiyar Adams bata da wani ƙarfin yin hakan saboda tsufa. Sai dai duk wadda aka kawo sai a samu matsala saboda masifar matar Adams. Dan mace ce azababbiya matuƙa...
Rabi'atu yarinya ce budurwa da bazata wuce shekaru goma sha shida ba. Ɗiyace wajen mai abinci dake gab da kamfanin Alonso Kuma duk a wajensu suke cin abinci. Tayi matuƙar sabo da Adams harma wasu na ganin ko son juna suke. Sai dai sam ba haka bane ba. ALLAH dai ya haɗa jininsu ne kawai kasancewarta yarinya nutsatstsiya mai hankali ga ilimin addini da girmama na gaba da ita. Ba Adams kawai ba kowa a gurin Rabi'ah nada ƙyaƙyƙyawar alaƙa da shi har shi kansa oga kwata-kwatan wato Alonso. Ganin tafiyar Adams na matsowa ga matarsa taƙi kwantar da hankalinta ta zauna lafiya da masu aikin da ake ɗauka mata sai Adams ya roƙa Rabi'ah akan ta dinga zuwa tana ɗan mata gyare-gyaren kafin a samu wata. Babu musu Rabi'ah ta amince, dan akwai ƴar ƙyaƙyƙyawar alaƙa tsakaninta da matar Adams ɗin a dalilin kai musu abinci da take kullum gida saboda basu fara girki ba. Fara aikin Rabi'ah baifi da sati guda ba Adams ya wuce ƙasar Spain bisa ƙoƙarin uban gidansa Alonso. Bayan wucewar Adams Rabi'ah ta cigaba da ɗawainiya da matarsa Uwani har ALLAH ya sauketa lafiya. Bawai bata mata masifar bane ita, kawai dai tanada haƙuri ne sosai shiyyasa kowa ke ganin babu matsala. Bayan haihuwar matar Adams da wata biyu wani rikici ya taso, dan zuwa yanzu kanta ya ƙara wayewa tayi sabbin ƙawaye. Duk wahalar da Rabi'ah kemata da jaririnta da sauran yaranta biyu ta rufe idanunta ta mata rashin mutunci wai tana soyayya da mijintane. Rantsuwa sosai Rabi'ah ta shiga mata tana kuka akan ita bata da wata alaƙa da Adams face ta mutunci kamar kowa. Amma sam sai taƙi saurarenta har ta kaita da fusata ta watsa mata ruwan zafi dake akan risho da Rabi'ah ɗin ta ɗora zata mata girki. Hankali tashe aka kwashi Rabi'ah zuwa asibiti.
Alhamdullah anyi sa'a ƙunar batai nisa ba. Dan ta iya hannunta zuwa gefen ciki ce kawai ta tashi. Ta fuska ALLAH ya taƙaita mata wahala. Hankalin Alonso ya tashi, dan haka ya shirya matar Adams da yaransa biyu suma ya turasu ƙasar Spain inda mijinta ke karatu. Shi kuma ya maido tsohuwa mahaifiyar Adams ɗin gidansa dan yayi alƙawarin kula da ita har su Adams su dawo. Ƴar shaƙuwar da Rabi'ah tayi da tsohuwa yasa bayan warkewarta ta cigaba da zuwa gidan Alonso tana mata hidima duk da kuwa an ɗauka mata masu aiki. Rayuwar yarinyar da ƙyawawan ɗabi'unta ya fara jan hankalin Alonso kanta. A hankali sai ya fara sanyama duk motsinta ido idan tazo gidan. Tun tsohuwa bata lura ba harta fuskanta. Tausayi ya bata sosai, dan tasan da kamar wuya a bashi auren Rabi'ah tunda shi ba musulmi bane. Amma dai tana kan masa addu'a itama na ALLAH ya shiryesa kodan kyawawan ɗabi'un da ALLAH ya zurtashi da su. Zamu iya cewa ALLAH ya amshi addu'ar tsohuwa akan gaɓa. Dan kuwa randa Alonso ya gagara daurewa ya amayarma Rabi'ah sirrin dake a ransa ta tabbatar masa bazai yiwuba saboda addini ya bambantasu a ranar ya musulunta. Wannan al'amari yay matuƙar yima tsohuwa daɗi, dan haka ta sanar da Adams ta hanyar telephone da ake amfani da ita a lokacin kuma sai a gidan ma wane da wane. Shima sosai ya tsinta kansa a farin ciki mara musaltuwa dan dama burinsa kenan.........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚_


What you need to start making $500 from PromptEarn Dollar Affiliate 👇. 📍A smartphone 📱. 📍 Internet Connection. 📍Access to your AIM Course. 📍 Atleast 2 hrs of your daily time. If you still don’t know what this is, click the link below to know how you can start 👉https://wa.link/6f3908

________

.....Musuluntar Alonso daya koma Ibrahim Khalil bai sa Rabi'ah ta amince da shi ba har sai da ta tabbatar yayi tubane domin ALLAH badan soyayyarta ba. Biki akayi na bajinta duk da kuwa kowa bai san iyayen Alonso (Ibrahim Khalil) ba. Sai Adams dake acan yana karatu. Shedar daya bada akan asalin Alonso (Ibrahim) yasa ba'a zurfafa bincike ba aka bashi kodan musulunci daya amsa ai ya zama ɗan uwa. Rayuwar Rabi'ah da Ibrahim rayuwace mai sauƙi da ƙayatarwa. Ga tsohuwa a gefe na ƙara ɗorasu kan ƙyaƙyƙyawar tirba. Shekararsu ɗaya da aure ya ɗuketa sukaje ƙasarsa. Acan suka iske Adams da iyalansa. Sosai Adams ya nuna farin cikinsa, sai dai ga matarsa sam ba haka bane ba. Banda harara da kallon banza babu abinda take bin Rabi'ah da shi har sai da Rabi'ahr ta tattarata ta watsar itama sannan tasha jinin jikinta. Satinsu biyu suka dawo Nigeria dan Ibrahim ya riga ya saba da rayuwar sabuwar ƙasarsa. Dawowarsu da watanni biyu iyayensa suka samu iftila'in gobara suka ƙone ƙurmus. Dole ya sake tattara Rabi'ah suka koma cikin tashin hankali. Sai dai zuwan nasu bai canja komai ba dan anyita ta ƙare Ibrahim ya rasa ahalinsa.

Wannan shine dalilin dawowarsa Nigeria gaba ɗaya. Adams ma ya dawo shi da iyalansa. Har lokacin kuma Rabi'ah bata taɓa ko ɓatan wata ba. Hakama matar Adams bata sake haihuwa ba tun Abdullahi. Dawowar Adams yasa Ibrahim sake sakar masa ragamar kamfani sosai. Aiko cikin amincin ALLAH sai sake bunƙasa yake har sun fara buɗe wasu reshikan a jahohi. Kwatsam sai ga Rabi'ah da ciki. Musalta farin cikin Ibrahim da su Adams da suka zama ahalinsa a yanzu ma ɓata lokaci ne. Haka aka shiga jelar tattalin cikin nan har ALLAH ya sauketa lafiya aka haifo ɗiya mace ƙyaƙyƙyawa mai tsananin kamanni da mahaifinta. Yarinya taci suna Ummu-Hidaya kamar yanda Rabi'ah ta buƙaci a sanya mata. Duk wani gata Ummu-Hidaya na samunsa ga kowa. Sai dai hakan bai hana Rabi'ah tsayawa akan tarbiyyarta ba. Dan haka ta tashi yarinya mara kwaramniya ga kuma gatan iyaye da na yayu su Mu'azz da a yanzu su take kallo matsayin zuri'ar iyayenta. Tana da shekara huɗu Rabi'ah ta sake samun ciki. Nan ma anyi farin ciki matuƙa. Cikin nada watanni biyar tsohuwa mahaifiyar Adams ta rasu. Ibrahim yaci kuka dan sai ma ka ɗauka itace ta haifesa shima. Hakama Rabi'ah ta shiga ɗimuwa. Ba'a gama kukan mutuwar tsohuwa ba mahaifiyar Rabi'ah itama tai accident ta rasu. Ai sai Rabi'ah ta ƙarasa birkicewa. Dan bata san kowa ba a danginta a duniya sai mahaifiyarta. Tun bata da wayo take mata nacin sanin ina babanta da ƴan uwansu dan daga ita sai ita ta buɗe ido ta sani a Lagos sai masu tayasu aikin abinci amma bata sanar mata ba gashi har rayuwa ta ƙare. Sam lafiya taƙi samuwa ga Rabi'ah. Ga cikin na matuƙar bata wahala ƙwarai da gaske. A haka dai aka kai watan haihuwa da ƙyar. Sai dai kuma ranar haihuwa anta shan fama haihuwar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login