Showing 255001 words to 258000 words out of 438336 words
to, dama gajiya tasa banyi ba na kwanta kawai ga yunwa kuma ina ji”.
“Okay”. Kawai yace mata ya cigaba da harkar gabansa. Da ƙyar ta iya samu ta kunna shower tai wankan, cikin son ta birgesa ta fito da ɗan guntun towel. Tako birgesan, dan duk inda tayi biye yake da ita da kallo kamar tsohon maye musamman bayanta. Bayan ta gama shiryawa cikin ƙananun kaya kamar yanda shima ya zuba ƴar shara da wando ta dawo kusa da shi ta zauna. Kamar abin arziƙi suka ci abinci tare tana faman masa shagwaɓa ita a dole ga amarya. Sai da yaci yay nak abinsa yay miƙar ƙoshi sannan ya miƙe a wajen. Barci ya ɗan fara figarsa a kujerar tana jikinsa akai kiran wayarsa. Janyeta yay ya tashi ya fita, kusan mintuna goma sai gashi ya dawo.. Da kallo ta dinga binsa, dan abinda aka ɗirka mata sai tsikarinta sukeyi. So take ko ɗan taɓata yayi, amma mutumin nan bashi da wannan niyyar. Ganin fa wankin hula zai kaita dare ga shi tun a yau take son fara tatsar kuɗaɗe dan Mom taci bashi sosai a bikin nan wajen shirya mata ɗaki tana son ta tura a biya kada asirinsu ya tonu. Tashi tai tsam ta nufi gadon da taga yaje ya kwanta. Cike da shagwaɓa ta faɗa masa a jiki. Shiru yay yana kallonta, itako babu kunya babu kawaici ta fara masa abubuwa. Barinta yay tai kiɗanta tai rawarta, kafin shi kuma ya fara maida mata murtani. Abinka da wadda tasha kayan iri-iri harda wanda bai kamata abama amarya irinta farin shiga ba. Gaba ɗaya ta gama sallama masa har bata ma san mi take ba. Hankalinta ya matuƙar gushewa taji kawai yana ɗaɗɗaureta. Da mamaki take kallonsa. Sai ya sakar mata makirin murmushi. Bata iya ta maida masa ba, dan a yanda ya kifata rufda ciki ya ɗaure ɗin ya sokar mata zuciya. Kafin ta samu damar neman ba'asi ya bita ya taushe. Duk da bata wani nutsu tayi islamiyya ba sosai hanyar da mijin nata ke neman bi a jikinta ya matuƙar firgitata. Cikin tashin hankali ta shiga tambayarsa mi yake sonyi haka? Abinda yake son aikatawa fa haramunne, taya zai yi ƙoƙarin mu'amalatar ta ta baya kamar wasu aladu. Ko kallo bata isheshi ba, tana ji tana gani ya aikata saɓon ALLAH da ita, maimakon bin hanyar da ALLAH ya halatta masa yabi wadda ya harta masa. Babu kuma tausayi babu imani sai da yay mata fata-fata. Tun tana kuka da roƙonsa da magiya harta ma suma dan azaba. Gashi ya ɗaureta duka hannayenta da ƙafafu babu damar koda kare kanta ne.....
❤️🔥✨❤️🔥✨❤️🔥
A ɓangaren Baba prof koda ya koma gida a jiya yaso bama al'amarin lokaci dan yay nazari, sai dai hakan na neman gagararsa. Washe gari duk da uziririn dake gabansa bai iya fita a gidan ba har kusan sha biyu na rana, dan ya kwana da tunane-tunane ne ya tashi dasu. Wayarsa ya ɗauka har ya danna kiran number Maash sai kuma ya yanke yana mai girgiza kansa. Akalar kiran ya maida kan Hajiya Mammah. Harta tsinke ba'a ɗaga ba wai tana waya. Sake kiran yay dan bazai iya jira harta gama ta kirashi ba. Yanzun ma tana wayar, sai dai kuma tana gab da katsewa aka ɗaga. Cikin bada umarni ya ce, “Nafisa ki sameni a gida yanzun nan”. Daga haka ya katse kiran.
Shiru kawai Hajiya Mammah da tun jiya abin duniya ya isa tayi tana bin wayar da kallo. Ita bata motsaba ita bata ajiye ba. A haka kiran Hajiya Rubayya ya shigo mata. Da ƙyar ta iya ɗagawa takai kunnenta. Daga can cikin zumuɗi Hajiya Rubayya ta ce, “Miya faru? Ya kukayi da Baban?”.
“Ca yay na samesa a gida. Ni kuma bana jin zanyi hakan Rubayya. Dan ban san mizan ce da shi ba, kin dai san halin Baba akan ɗan iskan yaron nan”.
“Uhm uhm kar kice haka kije. Ai idan kikaƙi zuwa zai ma yarda da abinda ya faɗa kenan. Wannan fa wata gaɓace da zamu kama mu riƙe. Dan ita kawai ta rage mana yanzu. Dan haka tashi kije. Ki kirani ina jin abinda Baba ke faɗa zan dinga faɗa miki amsar da zaki bashi”.
Matuƙar yarda Hajiya Mammah tama Hajiya Rubayya. Dan haka bata kusa ba ta miƙa ta hau shirin tafiya. Ta fito cikin takun nan nata na isa da taƙama sai dai daka ganta kasan ranta a ɓace yake. Gaisheta ma'aikatan gidan keta faman yi cike da girmamawa. Sai dai gaba ɗaya hankalinta ba'a garesu yake ba. Dan dai-dai nan ɗaya daga cikin ƙosassun motocin Maash da ba kasafai yake fita da su ba sai abu mai muhimmanci ta shigo, sai motar guards ɗinsa ɗaya biye da ita. Da farko ta ɗauka Maash ɗinne ya fita yake dawowa, sai da aka buɗe motar taga wanda ya fito a ciki tai tsaiwar sojan badakkare kamar wadda ta suma a tsaye...
A hankali black beauty matashin saurayin dogo mai tsananin kammani da su Paah sai dai idanunsa sak irin na Maash ya wani yamutse fuska da bin gidan da kallo. Sam gidan baya wani birgesa a zahirance. Amma acan ƙasan ransa yana jin kewar Ummien sa da son kasancewa da ita. Matsala ɗaya ke masa katanga da yunƙurin zuwa gareta, ɗan uwansa. In har Yayansa na waje komai buƙatar da yake ma wajen shi bazai taɓa iya kasancewa ba. Dan yana jin kamar ya soka masa wuƙa ko ɗaukar bindiga ya harbe masa kai kawai.
Sai da ya gama ƙarema gidan kallo batare da hankalinsa ya kai kan Hajiya Mammah ba ya ɗauka side bag ɗinsa irin ta maza matasa masu ji da gayu ya saka. Kansa tsaye babban ƙofar sashen ya nufa, dan sai ya fara zuwa yaga Ummiensa kafin ya ƙarasa sashensa. Yasan dai yanzu su Paah duk basa gida suna office........✍️
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 thirty-two
.......Zaune nake cikin dauriya kan Ummie a saman cinyata ina mata kitso tare da raira karatun Alkur'ani a hankali. Duk da dai Alhamdullah yau ina jin jikina da sauƙi ba kamar jiya ba. Tunda na shigo Mama Balki ta sanar min ai Hafizzullah yazo da safe tare da Hayatu amma sun fita har da Maash sai kawai nace bara nai zaman yima Ummie kitsonta da tun jiya naso yi ALLAH bai ƙaddara ba. Muna fara kitson Mama tace bara taje ta duba su Aunty Falila a kitchen dake girkin rana. Da to na amsa mata na cigaba da kitson ina karatun. Fitar tata baifi da mintuna biyar ba aka buɗe ƙofar ɗakin, sai ban damu ba na cigaba da kitsona ina karatuna da tunanin ko itace ta dawo ɗaukar wani abu. Jin shiru bata ƙaraso ba bata kuma yi magana ba ga wani baƙon ƙamshin turare da ban santa da shi ba yasa na ɗago idanuna na kalla ƙofar.
Cak na tsaya da kitson ina bin black beauty matashin saurayin da kallon mamaki kamar yanda shima ya zubamun idanunsa sak irin na Yaya Awwab. Ganin kallon nasa na neman wuce gona da iri fuska a yamutse na ce, “Malam lafiya? Wanene kai? Miya kawoka nan?”.
Gira ya ɗan ɗage cike da salon iya shege sai kuma ya saki wani faffaɗan murmushi. Hannu ya kai ya ɗan shafi dan tsigigin gemunsa na ɗaukar magana ya wani karkace kai gefe tare da furta, “FAHAD EL-MU'AZZ ADAMS. Kefa ƙyaƙyƙyawa?”.
Maganarsa ta ƙarshe ta sani ƙin cemasa komai duk da naji wani daɗin jin sunan daya ambata ɗin . Sai ma ɗauke idanun nawa da nai na maida kan Ummie. Takowa yay shima a hankali zuwa inda muke. Zama yay kusa da Ummie ta ɗayan side ɗin, kamar wani ƙaramin yaro ya kwanto jikinta yana mai rungumeta. Cikin rawar marya ya ce, “I miss you mom. I love you with all my heart. You are my world and everything.” sai ga hawaye sharr, sake ƙanƙameta yay sosai a jikinsa. Sosai wani irin tausayinsa ya shiga ratsa min zuciya. Kaina na kauda daga kallonsu nima hawayen na zubo min. Da sauri na share su tare da ƙoƙarin cire kanta a jikina ya ɗago.
Da sauri ya ce, “Oh oh beauty sai ki tafi kuma? Ki bari na gama da Ummie na zan dawo kanki”.
Harara na zuba masa. Kafin na girgiza kaina da faɗin, “Ka kama kanka fa.”
Da sauri yako damƙe kan nasa. Sai kuma ya saki murmushi cikin komawa serious saboda hararar dana zabga masa. Hannayensa ya haɗe waje guda. Ya ce, “Am sorry. Barka da rana. Sunana Fahad El-Mu'azz Adams. Autan Ummiensa da Paah”.
Na kula akwaisa da shaƙiyanci, dan haka nayi murmushi da ɗan girgiza kaina. Cikin komawa serious nima nace masa sannu da zuwa. Sai dai yanzu ba kaine autan Ummie ba nice.”
Cikin marairaice fuska ya ce, “A'a dan ALLAH kada kimun haka. Na yarda ki zama aunty na kawai. Daga yanzu ma zan na ce dake aunty beauty”.
“Dama Auntyn taka ce ai”.
Muka tsinkayi muryar Mama a bayanmu. Da sauri ya juya, sai kuma ya miƙe cike da farin ciki ya nufeta. Babu kunya ya rungumeta. Dariya Mama ta shiga yi da ɗan bubbuga bayansa tana faɗin, “Oh ni maigado sai yaushe ne Fahad ɗina zai girma. Haba autan Ummie kafa isa aure”.
“Ina ban isa ba Mama. I miss you wlhy”.
“Muma munyi kewarka sosai Fahad. ALLAH yay maka albarka kaji.” ta faɗa tana ɗagosa. Daka gansu kaga waɗanda ke a cikin farin ciki sosai. Cike da girmamawa ya gaisheta, tare da tambayarta jikin Ummie yana mai bin sashen da kallo. Ta amsa masa da kulawa. Kafin ya tambayeta wai wacece ni dan ya matsu ya sani. Ƙaramar dariya Mama tayi, tare da faɗin, “A'a bakaji a bakina ba. Ka bari zaka sani”.
Cikin yanayinsa na mutum mai sauƙin kai a yanda na fahimta ni dai ya ce, “Okay Mama ba damuwa. Bari naje nayi wanka sai na dawo ALLAH yasa Ummie ta tashi ta ganni na ganta da ƙyau. Ina fatan kin min farvorite food ɗina dai?”.
“Sasai ma kuwa autan Ummie. Dan har sai kaci ka ture.”
Sosai farin cikin sa ya sake bayyana. Ya ɗaga min hannu yana maida bag ɗinsa da faɗin, “Bye Aunty beauty ki jirani nazo muyi hira. Dan sai kin faɗa min wacece ke zan barki.”
Sosai ya bani dariya. Hakama Mama Balki dariya take yi. Yana gama ficewa na dubi Mama fuskata da sauran dariyar na ce, “Mama wannan ɗan naki akwai dai rashin ji a jikinsa”. Dariya ta sake yi sosai tana kaiwa zaune. Ta ce, “Humm bar Fahad inda kika gansa ya dai so yin barkwancin ne. Amma shima da kike ganinsa wani lokacin akwai miskilancin. Sai dai bai kai Alhaji Ƙarami bane kawai. Halinsu ma sam ba iri ɗaya bane ba. Dan shi Fahad na surutu sosai, shiko Alhaji ƙarami maganar ma aiki ce. Nan fa ta shiga bani labarin Fahad da halayensa. Wani nayi mamaki wani nayi dariya wani al'ajabi. Surutunmu ya tada Ummie ma. Tana farkawa ta fara kiran “Yunwa Muhammad! Yunwa”. Aikin kenan yanzu, daga taci abinci sai barci. Idan kaga ta farka yunwar ce ta sake tashinta. Shiyyasa jikinta yake wani irin murjewa tana ƙiba kwarjininta na sake fitowa. Kwana biyu dai Alhmdllh bata wannan bige-bigen. Bamu sani ba ko hakan nada nasaba da canja mata magunguna da akayi ne. Dan a ranar da jikinta ya motsa sosai ina asibiti a yanda Mama ke bani labari anzo da wani baƙon likita tun daga ƙasar RUMAN (Dole mu tuna Shahan-shan namu na Iffan😘😀). shine ya dubata tare da canja mata allurai da magunguna. Acewarsa a gwada waɗan nan sabin samfir ne da a shekarar nan aka samar dasu akan masu matsalar ƙwaƙwalwa. Ya bada wata ɗaya zai sake dawowa yaga idan an dace. Amma duk da haka a kullum sai doctors daya bari zasu ke kula da ita zasu dinga aika masa da cigaban da ake samu. Sannan ya dakatar da su Hajiya ƙarama da sauran doctors ɗinta a komai acewarsa shi baya haɗa aiki da waɗanda ba wanda yake tare ba.
Sosai naso ace sanda abin ya faru ina wajen. Dan ina buƙatar fahimtar yanayin kowa a cikin doctors ɗin nata na baya. Dan nasan ko suna da gaskiya hakan bazai musu daɗi ba. Amma ko yanzu na ɗauki ɗamarar yin hakan.....
🌛🌜❣️🌛🌜
Ya ALLAH🙏 Wanda ke da rabon shiriya a masu ɗakkowa, da masu yaɗawa, da masu jiran a ɗakko su karanta a matsayin bati, ya UBANGIJIN al'ashi. Ya mai RAHAMA da jinƙai. Ya mai fidda rayayye a cikin matacce, ya fidda matacce a cikin rayayye. Nayi tawasalli da sunayenka masu tsarki, waɗanda ka kirayi kanka da su ka kuma sanar damu, da wanda ka barwa kanka saninsu ka keɓancesu gareka. Nayi tawasalli da ɗan gatan nan naka, wanda kace idan muka so shi, mukabi abinda yazo mana da shi na shiriya ka gafarta mana. Ina roƙonka ka shiryar dani da su. Ya rabbi kafisu sanin wahalar da nake sha a yayin rubutun nan. Nakan hana kaina barci domin sauke hakkin masu saya a lokacin da su suke barcin, nakan yini da ciwon kai, ina fama da ciwon idanu, ina fama da ciwon yatsu. Ina fama da ciwon baya. Wataran nakan wayi gari banama jin farin ciki ko sha'awar rubutun, wataran na tashi da uzirin baƙi ko fita. Amma duk nakan kuntata kaina domin naga nayi. Idan har ban kasance na cutar dasu da komai ba a rayuwarsu, ya rabbi! ya rabbi! ya rabbi!! ka shiryar dasu su guji taɓa hakkin daba nasu ba. Ka shiryar dasu su guji ɗaukarma kansu nauyin da zasuyi dana sani a ranar da ake fansa da lada da zunubi. Ya rabbi ka gafarta mana kurakuranmu. Ka shiryar damu, ka nisanta mu ƙuntata zuciyar kowa koda kuwa dabbace. ALLAH kasa mu samu sauƙaƙƙen hisabi batare da an jinkirta mana ba saboda hakkin wasunmu da mukaci a duniya. Dan ALLAH, dan ALLAH. Dan girman ALLAH mu saukaƙama kammu kunji bayin ALLAH. Ni kaɗai nasan a yanayin da nake wannan rubutun musamman a ɗan tsakanin nan, kada ki bari UBANGIJI ya kamaki da laifin hakkina nima bazan so haka ba. Dan bana son akai gaɓar da zan iya tashi tsakkiyar dare domin miƙama UBANGIJINA ƙararki ko ƙararka. Dan ALLAH, dan ALLAH, dan ALLAH. In har da gaske ke masoyiyar MANZON ALLAH ce kina fatan tashi a tawagarsa ranar da kowa ke fatan hakan, idan har da gaske kin yarda da mutuwa da ranar hisabi, idan har kin yadda wannan rubutun hakkina ne ALLAH zai iya cirar min hakkina a jikinki, idan har kin yarda ban taɓa cutar dake da komai ba, idan har kina fatan kema ALLAH ya kiyaye hakkinki ko hakkinka, ku daina ɗakkowa a inda na killacesa, ki daina yaɗawa, kema ki daina karantawa. Wannan itace maganata ta farko kuma ta ƙarshe in sha ALLAHU, ALLAH ya yafe mana kurakuran mu baki ɗaya.🙏
🪴🪴⭐🪴🪴
Ran Baba prof a ɓace yake kallon Hajiya Mammah dake gaishesa. Bai amsa ba, sai nuna mata agogon dake falon nasa mai shegen ƙyau da ɗaukar hankali yayi. “Kalla time, sai yanzu ne kike zuwa bayan tun 12 da wasu mintuna nai kiranki Nafisa?”.
“Kayi haƙuri Baba. Wlhy na fito zan taho sai ga Fahad. Bamma ko tsaya ya ganni ba na taho dan kar kaita jirana. Wlhy duk a tsorace nake, kada su sake ƙoƙarin ƙona mu a cikin gida kamar wancan karon. Ban san wace jaraba ce ta dawo da yaron nan ba ana zaune lafiya.”
Ɗan jimmm na wucin gadi ne ya riski Baba prof.. kafin tamkar mai koyon magana ya ce, “Wai wane Fahad ɗin?”.
Cikin rashin damuwa Hajiya Mammah ta ce, “Fahad namu mana Baba. Wlhy gashi can ya dawo abinsa. Abinda ma dai ya ɗan bani mamaki shine ganin a motar fitinannen ɗan uwan nasa aka ɗakkosa. Ko sun shirya ne bamu sani ba. Idan ma hakanne ta kasance ai mu abin farin ciki ne a garemu, dan wlhy tsoron tashin hankalin nan nasu nake suzo wataran su ƙonemu ƙurmus mu da gidan kana dai ganin wancan karon da ƙyar muka sha suka so sakamu a tara. Kai ai nikam wannan jini na Ummu-Hidaya ai ba'a cewa komai. Bala'i kala-kala daga wannan sai wancan”.
Yanda Baba prof yay shiru da alama ba fahimtar zantukan Hajiya Mammah yake ba ma shi. Dan sai da ta ɗan kai hannu ta taɓashi sannan ya dawo firgigit. Murmushi yayi zai yi magana dai-dai nan akai knocking ƙofa. Tsaki Hajiya Mammah tayi tana hararar ƙofar dan tasan bai wuce ma'aikatan gidan ba. Cike da wulaƙanci ta bada izinin a shigo. Ilai kuwa cikin ma'aikatan ne. Kansa a ƙasa da girmamawa ya kai durƙushe yana sanarma Baba prof yana da baƙo.
Agogo Baba prof ya kalla, cikin ɗan ɓacin rai yace, “Bani da apartment da kowa yau, koma su waye a sanar musu suje sa dawo next time”.
Kai hadimin ya jinjina. Har zai miƙe sai kuma ya koma ya durƙusa. Kansa a ƙasa cikin ɗari-ɗari ya furta, “Ranka ya daɗe Commando ne fa, kuma kaine kace ko baka gidan nan yazo nemanka a sanar da kai”.
Cikin masifa Hajiya Mammah ta juya zata fara danna masa zagi Baba prof ya dakatar da ita. “Uhmm Nafisa kinga barshi umarni na ne. Kinga jeki gida kawai idan na gama da shi zan zo na sameki. Komi ke faruwa ki dinga sanar dani ta waya. Sannan kiyi