Showing 336001 words to 339000 words out of 438336 words

Chapter 113 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2206

cimma burinmu da kai maƙiyanmu ƙasa to sune zasu fara kaimu domin sun ɗakko hanya. Commondo da ga ni har kai ya shirya cin amanarmu ne. Dan yayi kidnapping Mu'azz batare da mun sani ba, bai kuma sanar mana ba saboda yana da wata manufa a zuciyarsa game damu. A binciken dana gudanar yanzun na tabbatar da shine ya gayyaci Jannifer domin su canja ma Mu'azz wajen zama shine aka kama su”.
“Lawisa! Kinsan ko mi kike faɗa?”.
“Niko na sani Yallaɓai, idan baka yarda ba kalla wannan video ɗin”.
Tai maganar tana miƙa masa wayarta. Amsar wayar yay, yayi playing video ɗin data latso masa. Rai-rai kuwa abinda ta faɗa ne a video ɗin. Dan ga Commondo zaune tare da Jannifer suna tsara komai. Dunƙule wayar Baba prof yay a cikin hannunsa zai yi jifa da ita Hajiya ƙarama tai saurin tashi ta riƙe kayarta.
“Please! calm down, yanzu fa ba lokacin fushi bane ba. Lokacin yin faɗan ƙarshe ne kawai. Idan ba hakaba wahalarmu ta shekara da shekaru kuwa zata tafi a banza. Muna da ƙalubale daban-daban dake zagaye damu. Na farko dai Ummu-Hidaya ta warke, na biyu ƴaƴanta Awwab da Fahad dan shima yaron tsagera ne abinda kai musu ya warware. Ga Abdullahi matsayin jami'in tsaro kuma shinema case ɗin su Commondo ke a hannunsa. Ga Commondo ya juya mana baya. Sai dai ban sani ba ko kasan dama shi ɗin Abdullahi ɗan sanda ne?”.
“Ya kamata nasan tun yaushe Commondo ke cin dunduniyata”. Baba prof ya faɗa a kausashe maimakon amsa zantukan data lissafo masa. Tasan wannan mutumin ya gama zarewa, amma bazatayi sake ba dan mugune, dan haka kawai ta saki murmushi. Cikin ɗan laɓe baki ta ce, “Wannan duk mai sauƙine zamu iya bincike. Amma dolene muyi duk yanda zamuyi mu gansa a yau kafin gobe, in ba hakaba yayi magana mun kaɗe”.
Kai kawai ya jinjina mata tare da tabbatar mata karta damu zuwa anjima zataga kiransa akan hakan. Amma ta kasance cikin shiri.. cikin gamsuwa tai masa sallama ta wuce tana wani makirin murmushin nasara. Tana fita daga nan gida ta wuce ranta fes. Dan kaso arba'in cikin ɗari na damuwarta ya kwaranye. Koda ta iso gidan wanka ta farayi, dan zuwa yanzu ta samu ƙwarin gwiwar yin hakan. A'i ta saka ta kawo mata abinci, ta ɗan ci tasha magungunanta sannan ta nemo Rubayya a waya. Ta sake tabbatar mata kada ta bari aikinta ya wuce gobe. Dan haka tayi ƙoƙarin zuwa ta kwana a gidan yau. Bata jira cewarta ba ta yanke kiran.
Tana gama wayar ɗakin Arwa ta shiga domin dubata. A bakinta take jin ai an sallamo Paah a asibiti tun jiya da dare ma kafin su amma yana sashen Awwab suma duk an hanasu ganin sa. Kasa cewa komai Hajiya ƙarama tayi sai idanu data zubama ƴar Tata na tsawon lokaci. Kafin taja numfashi ta fesar tare da miƙewa kawai ta fita........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_



.......Daga station Maash guesthouse ɗinsa suka wuce. Da ga shi sai Hayatu da Jaga suka shiga ciki. Sun fi zaman mintuna talatin Maash ɗin baice komai ba yana dai zaune ƙafafunsa a harɗe ya jingina kansa da kujera idanunsa a lumshe da alama ya tafi dogon nazari ne. Jaga zaiyi magana dan ya matsu Maash ɗin yace wani abu Hayatu yay masa nunin yay shiru cikin alamar yin zipping lips nashi. Ajiyar zuciya Jaga ya saki da rufe bakin nasa ruff ya koma ya zauna yanda yake. Maash ya jima a haka har akai kiran sallar azhar sannan ya buɗe idanunsa. Miƙewa yay ya nufi bedroom yana ce musu suma suje suyi alwala. Hakan kuwa sukayi, bayan sunyo duk suka wuce massalaci.
Koda suka dawo daga massalacin ma sai da yay waya da matarsa babu ko kunya a gabansu kuma. Shi dai Hayatu murmushi kawai yake. Yayinda Jaga keta wani sinne kai shi ga ɗan duniya (😂😝). Wayar Maash ya ajiye fuskarsa da alamun murmushi, yana kallonsu yaga yanayinsu sai ya gimtse cike da basarwa ya gyara zama da faɗin,
“Muktar!”.
Ɗan sosa kai Jaga yayi dan in ba Maash ɗin dake kiran ainahin sunansa yanzu ba mantawa ma yake da sunan sa wani Muktar can. Cike da girmamawa ya ce, “Na'am babban yaya”.
“Ina ganin lokacin da zaka fara naka aikin yayi”.
Wani irin miƙewa Jaga yay ya taka rawa sai kuma ya ware baki zaiyi ihu. Da sauri Hayatu yay gyaran murya. Baki jagan ya dafe da hannu biyu shima da sauri yana waro idanunsa waje. Sai kuma ya koma ya zauna kansa a ƙasa ya ce, “Afuwan babban yaya. Kasan hankalin bai gama zama ba sai kun haɗa da addu'a”.
Komai Maash baice masa ba sai ma maida hankalinsa da yay akan tab dake hannunsa. Sai Hayatu ne ya ƙumshe baki yana ƴar dariya ciki-ciki. Shima ɗagowar Maash ya sashi saurin haɗiyewa ya daidaita yanayinsa.
“Wa zaka fara kaima ziyara?”.
Cike da zumuɗi Jaga ya ce, “Commondo”.
Murmushi ya nema suɓuce ma Maash amma sai ya gimtse yana mai ɗan taɓe baki cike da basarwa ya ce, “Okay good and fine. Kanada damar yin hakan a yau. Dan Iyayen gidan nasa na shirin ganawa da shi a daren yau suma. Kana da damar basu assignment lokaci ɗaya.”
Wani irin daɗi ne ya ratsa zuciyar Jaga. Nan take ya shiga sambatun godiya kamar wanda aka yima wata ƙyauta. Ga shi dai a zahiri da shiga kamar ba shi ba ya shiryu. Dan bayan an gama jiyyarsa daga suƙar wuƙa Maash da kansa ya kaisa Rihab akan matsalar shaye-shayensa. Ya zauna tsahon watanni har ALLAH yasa aka dace batun shaye-shaye ya zama tarihi. Shine ya sake ɗaukarsa zuwa ƙasar Canada aka sakashi wata makaranta domin fara sanin minene ma amfanin rayuwa. Yayi wata biyu acan aka sake maidashi ƙasar Saudiyya a yanzu haka yana ɗaukar karatun addini dana zamani. Wannan zuwan nashi Nigeria ma anyi amfani da hutun makaranta da suka samune. Yanzu kam a rayuwarsa ji yake babu ya Maash. Shine uwa shine uba. Komai ya sakashi zai iyayi barema akan waɗan nan mutanen da shi kansa burinsa ɗaukar fansa a kansu musamman ma Commondo da ya zama sanadin ta'azzarar lalacewar rayuwarsa. Sannan ya shirya kashesa a gaɓar da yake ganin zai kuɓuce masa duk da wahalhalun bashi kariya daya kasance yana yi a tsahon shekaru.
A duk ta yanda zai ziyarci cell da taimakon Isma'il Maash ya tsara masa. Da ga haka suka ɗan ƙara tattaunawa sannan suka fito. Wani wajen suka sake zuwa shi da Hayatun, shi kuma Jaga ya tafi masaukinsa. Daga nan gida suka wuce, inda suka tarar su Fahad baje a falo anata tsara yanda shagalin bikin sunan gobe in sha ALLAHU zai kasance. Dan zasuyi walima kawai anan cikin Mansion ɗin. Duk sannu da zuwa sukai musu. Hayatu ne kawai mai amsawa. Mai gayya da aiki kam hannu ya ɗaga musu kawai idonsa akan Samraah dake goye da baby a baya tana cin abu a bowl da bai san ko minene ba. Itama dai ɗan kallonsa tayi, sai kuma a hankali ta sauke idanunta muryarta can ƙasa ta ce, “Sannu da zuwa”.
Kai kawai ya jinjina mata tare da janye idanunsa a kanta a wani kalar slowly. Sai kuma ya nufi ɗakin Ummie cikin takun nan nasa.....

🌿✨🌿✨🌿

Tun Commondo da Jannifer na saka ran zuwan iyayen gidansu har al'amarin ya fara basu mamaki. Musamman ma Commondo. Dan yayi tsammanin in har ya kwana Baba prof bazai barsa ya yini ba. Amma sai gashi har ana shirin fuskantar wani daren babu Baba prof babu Lawisa. Koda yake yasan ita bazata zo ba. Saboda gaba ɗaya ya haɗa lissafinsa akan shirinta na turo masa Jannifer. Tun kuma daren jiya ya gama kitsama kansa yanda zai wargazata. Har shine zata shirya ma tarko. Ashe shirin nata ba'a kan yallaɓai kawai yake ba har da shi. Lallai zata san ta taɓo gidan rina wlhy. Dan ko bai fita a wajen nan ba akan lokaci yayi alƙawarin sai ya tarwatsa rayuwar Lawisa tazo ta samesa anan kusa...

A ɓangaren Jannifer ma dai hakanne. Dan zuciyarta ta fara bata Hajiya ƙarama na shirya wani abu ne tayi amfani da ita. Idan kuma ba haka ba tsautsayine ya faɗa mata. Amma ya kamata ace Hajiya ƙaramar tazo dan fitar da ita. Sai kuma gashi shiru wai malam yaci shirwa gashi oganta bai san tama amshi wannan aikin ba. To wlhy ta ɗauki alƙawarin in har Hajiya ƙarama batayi wani abu daga nan zuwa gobe ba har wani daga cikin sirrinta ya fito lallai itama sai ta kaita ƙasa dan sai dai suyi mutuwar kasko wlhy.....

💥💥💥💥

Muna zaune a inda ya barmu sai gashi ya fito. Narasa miyyasa yanzu idan ya shiga ɗakin Ummien bai wani jimawa. Kuma haka zai fito fuska ciɗin-ciɗin. Ina ji a raina kamar hakan nada nasaba da Paah dake a ɗakin yanzu. Ko saboda mi babu jituwa tsakaninsu da mahaifin nasu oho? Dan in batun sihiri ne zuwa yanzu ai Alhamdullah. Amma in sha ALLAHU shima Paah ɗin zanyi ƙoƙarin fara shayar da shi ruwan addu'ar da muke sha tunda ALLAH ya dawo da zamansa nan ɗin. Ganin bai kalla kowa a cikinmu ba ya haye sama nima sai na miƙe riƙe da bowl ɗin madara da sugern dana haɗa waje ɗaya nake sha. Dama Ya Hayat ya amshi Baby. Ruwa na ɗauka nasa a tray sannan na nufi ɗakin nasa. Tsaye ba samesa da ga shi sai dogon wandon jeans ɗin jikinsa ya cire rigar har singlet ɗin ciki. Wandon ma ya kwance belt ɗin amma bai zaresa ba. Wayata ce a hannunsa yana dannawa, da mamaki na ɗan kallesa na ɗauke kaina. Dan wannan jikin nasa a bubbuɗe sam bana son ganinsa sai inji duk ina ƙara tsorata da shi. A hankali na ajiye tray ɗin ruwan ina faɗin, “Sannu da dawowa.”
Wayar ya ajiye tare da ɗan kallona ni da tray ɗin. Ban damu da kallon da yake min ɗin ba na kai zaune ina ɗaukar bowl ɗin madarana da shuga na cigaba da sha. Shima zaman yayi yana mai ɗaukar goran ruwa dana ajiye na addu'oi ya ɓalle murfin ya kai bakinsa. Sai da ya shanye tass ya ajiye goran sannan na kauda kaina a kansa. Yunƙurin miƙewa nake na wuce bathroom haɗa masa ruwan wanka a bazata matuƙar bazata naji saukar muryarsa yana furta, “Wacece ita?”.
Sosai naji ƙirjina ya motsa. Amma Abinka da ƴar jarida sai na dake na kallesa cikin nuna mamaki da rashin fahimta na furta, “Wake nan?”.
Shiru bai da alamar sake tanka min, sai kuma ya ɗago ya zuba min idanun nan nasa masu firgitarwa. Babu wasa a tattare da shi ya ce, “Samrh! Who is she?”.
Baki na murguɗa kaɗan, sai kuma na marairaice fuska da faɗin, “My hot ban ga gane wa kake magana ba Please. Naga dai tunda ka shigo iya mu kaɗai ne ka samu zaune”.
“Hummm!”.
Yace kawai yana miƙewa. Murmushi na saki a karo na farko, sai kuma na matso inda yake nasha gabansa ganin niyyar barin wajen yake. Kallona ya tsaya yi kamar yanda nake kallonsa nima cike da shauƙi. Sai kuma na matsa a hankali na shige jikinsa na rungumesa. Ajiyar zuciya muka sauke a tare, na sake ƙanƙamesa da faɗin, “Yarinyar jiya kake magana?”.
“Uhmm!”.
Ya faɗa acan ƙasan maƙoshi.
“Labarin mai tsada ne. Sai idan nima zaka gaya min wanda nake son ji na maka alƙawarin faɗa maka. Dan tabbas abinda ya shafi yarinyar a garemu mai muhimmanci ne”.
Shiru kamar bazai ce komai ba. Har ma na fidda ran ji sai naji saukar hannayensa saman bayana ya sake rungumoni da ƙyau. A cikin wani kalar salon rikita ni ya fara shinshinar wuyana. Ji nai ina daburcewa dan haka na mintsinesa ta re da ƙoƙarin janye jikina na ce, “Wayyo ni My Lion please”.
“Anƙi please ɗin faɗa min”.
“Anƙi wayon nima sai ka fara faɗa min”.
Numfashi ya ɗan furzar tare da ɗagowa ya sake rungume ni. “Naji”.
Ya faɗa a takaice kamar abin dole. Duk da naji haushi sai na daure. Musamman ma ganin la'asar ta gabato. Kamar yasan mike a raina shima sai ya kalla agogon. Kallona yay idanunsa a ƙanƙance. Cikin motsa lips ɗinsa ya ce, “Salla first”..
Nima sai na ce “Wanka fa?”.
“Na gaji ki mun”.
Kafaɗa na maƙe masa alamar a'a.
Kansa ya nuna alamar wai shi ɗin?
Na ɗaga masa gira ina murmushi. Hannu ya kai zai damƙoni na goce da sauri ina dariya. Sai ya ɗan ciza lips irin zaki gane idan na kamakin nan ya wuce bathroom ɗin.........✍️

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_



......Bayan idar da sallar la'asar ɗin ya jima bai shigo ba. Harma nai zaton ya gudu ne sai gashi ina falon saman zaune ina waya da Gwaggo Gudidi da miss call ɗinta dana sake gani ya sakani kiranta naji ko wani abu ne ya faru. Bedroom ɗinsa ya wuce babu jimawa sai gashi ya fito. Zama yay a kusa da ni tare da zame jikinsa ya kwanta kansa a saman cinyata. Ɗayan hannuna ya kama ya riƙe kan nasa ya ɗaura a saman shafaffen cikinsa ya harɗesa cikin nashi da yay folding a ƙirji. Jinai gaba ɗaya wayar ma na kasa cewa komai. Amma dai na dake har muka kammala. Sallama nake ƙoƙarin mata ya buɗe idanunsa da mun nunin na bashi wayar. Sai da na waro ido sosai amma sai bai sauraran ba ya kai wayar kan kunnensa. A mamaki na sallama yay cike da girmamawa da gurɓatacciyar hausarsa da sai anyi da gaske ake gane wasu kalmomin. Shiyaysa ma ni nafi ganewa muyi magana da turanci a koda yaushe. Shima yama fi yin hakan. Amma a raina na ɗauri ɗammarar koya masa Hausa in sha ALLAHU.
Nasan ba gane maganarsa Gwaggo keyi ba dan haka hirar bai tsaho ba ya bani wayar. Sallama nai mata batare dana saurari tsogumin da take akan rashin gane abinda yake fada ba na yanke kiran. Wayar na ajiye da kai hannun nawa cikin sumarsa daya warware na fara tausa masa kan nasa da yin wasa da gashin. Idanunsa ya lumshe da ƙanƙame hannuna dake a cikin nasa har yanzu. Cike da sanyi na ce, “My Hot!”.
A can ƙasan maƙoshi ya ce, “Umyim”.
Ban damuba na ce, “Abinci fa?”.
Kansa ya girgiza min alamar bazai ci ba. Cike da damuwa na ce, “Miyyasa?”.
Idanunsa ya buɗe ya kafeni da su. Sai kuma ya lumshe da sake buɗewa cikin motsa lips ɗin sa ya furta, “later”.
Kaina kawai na jinjina masa da gyara zamana. Dan nasan tunda yace bazaicin ba ba cin zaiyi ba fa ko miza'ayi. Sakin batun abinci nayi na kama mai muhimmanci. A ɗarare na ce, “Na maka laifi fa. Amma dan ALLAH kayi haƙuri ka yafe min tun kan na faɗa”.
Shiru kamar bazai ce komai ba sai zuwa can ya ɗan buɗe idanunsa da suka sirka yanayi, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya da miƙa hannu ya ɗauka laptop ɗin sa daya ajiye saman Centre table. Filo ya ɗauka ya ɗaurata a saman cikinsa duk yana daga kwancen, sai da ya fara ƙoƙarin kunnata ya ce, “Ai nasa zaki ɗauka ki sake dubawa shiyyasa na ajiye miki inda zaki gani”.
Da mamaki na ce, “Kasan akan mi kuwa nake magana? Flash

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login