Showing 183001 words to 186000 words out of 438336 words

Chapter 62 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2947

fuskata nima, cikin nuna alamar ɓacin rai, batare dana buɗe idanuna ba cike da tsiwa na furta, “ALLAH ma ya tsari ɗiyar Abdul-wahab da taɓa trash body irin naka, jiki duk ta'addanci da jinin mutane ma. Sannan ma ni ba ƴar iska bace dazan taɓa jikin maza. Kuma wlhy ka tashi min a kai tun kafin kai na saka kai regretting ɗin yanzun nan terror kawai an saba bin na hotels”.
Ban gama rufe baki ba naji saukar yatsunsa a saman lips ɗina. Wata irin masifar azaba ce ta ratsani saboda yanda ya haɗesu ya matse a waje guda, tsabar iya mugunta da baƙin hali ya dinga murzawa. Kusan sakan talatin sannan ya daina murzawar tuni idanuna sun cika da ƙwalla. Yayinda ɗayan hannuna ya shiga kai masa duka akan ƙatoton damtsen hannunsa amma mugun ko gezau. A wata sabuwar bazatar da ruɗani da tashin hankali na sake jin saukar hannunsa a saman cikina. Ihu nake son ƙwalawa amma babu dama ya riƙe bakin. Da bala'i-bala'in ƙarfi na gimtse idanuna da ƙanƙame jikina saboda yanda ya damƙi bindigarsa dana tura a wajen tare da fatar shafaffen cikina. Ai da azabar ƙarfi na dunƙule hannuna na buga masa a damtsensa ina fisge kaina amma yaƙi sakin lips ɗin nawa saima sake matsesu yake. Ɗayan hannuna kuma dana dakesa da shi ya sake zuramin wata handcuffs ɗin itama ya ratayo jikin ƙarfen net ɗin da akai kwalliyar gadon da shi, dan ƙarfene a wajen. Fisge-fisge na farayi, amma ko'a jikinsa saima ya ɗakko salataf ya nane min bakin da shi bam. Tashi yay tsaye sosai akan ƙafafunsa, na fahimci hakan ne a dalilin jin iskar ac na ratsani dan rankwafowar da yay ɗazun a kaina koma jinta banayi sam. Idanuna a rumtse suke dan bazan iya kallonsa ba. Fisge-fisgen na cigaba da yi ina uhum-uhum! Na ƙoƙarin yin magana amma ko uhum banji yayi ba. Hakan ya sakani buɗe idanuna kadan, sai na hangosa can ya nufi ƙofar da nake ƙyautata zaton closet ɗinsa ne saboda labulen da aka saka a wajen fari ne shara-shara kuma ƙofar wajen an yita da girma sosai. Hawaye naji suna ƙoƙarin sakko min, amma nayi ƙoƙarin hana hakan dan bazan taɓa yarda yaga gazawata ba. Kusan mintuna goma sai gashi ya fito. Cikin ƙananun kaya baƙaƙe yana ƙoƙarin ɗora baƙar jacket milk mai ƙyalli a samansu. Ko kallon inda nake baiyi ba, ya ƙarasa gaban mirror ya fesa turare da ƙara kwantar da kwantaccen gashin fuskarsa dama nakan nasa da ya ɗaure waje guda. Boot takalman daya fiddo baƙaƙe masu ƙyau daga sama ya zauna bakin gadon ta kusa dani ya saka. Matsar da jikina nayi baya ina ƙunƙunin da ba'a ji tunda bakin a rufe yake. Sai da ya gama saka takalminsa batare da ya kallan ba ya miƙa hannu ya ɗauka tray ɗin dana shigo da shi, ƙaramin stool yaja gabansa ya ɗora, hankalinsa kwance ya fara kai fruit ɗin bakinsa a nutse tamkar baya so. Ɗauke idanuna nai daga kansa ina ƙwafar da ba'a ji sosai, amma nasan zai iya yajin shi. Sai dai mugun ko a jikinsa yama ƙi nuna yasan dani. Baifi cokali biyar yayi ba ya ture gefe, tissue ya ɗiba ya goge bakinsa yana miƙewa. Yanzun ma ko kallona baiyi ba ya nufi ƙofar fita ya buɗe ya fita duk da buge-bugen da nake uhhhum-uhhhum ɗin dai bai kulanin ba. Fitarsa da minti baifi biyu ba har na fara hawaye sai gashi an sake buɗe ƙofar. Shegen karen nan nasa ne ya shigo. Shi kuma biye da shi, ya tsaya daga bakin ƙofa idonsa akan karen cikin bada umari yay masa nuni da ni yana faɗin, “Ko yinƙurin cire abinda ke bakinta tayi Laalah ka gutsire lips ɗin na bar maka su ƙyauta”.
Shegen karen kuwa kamar wani mutum ya wani kaɗa bindi yana nufo ta gefen gadon ta inda zai iya ganina ya kwanta ya zubamin ido. Yanzun kama rawa jikina ke min, dan wlhy tsoron makirin karen nan nake ji over. Ya riga ya masa wani azzalumin training da in akace maka yay wani abun saika ɗauka ma ƙarya ne. Wlhy da ace bakina a buɗe yake haƙuri zan bashi, amma ina zalumin ya rufeshi.
A hankali ya tako cike da ƙasaita inda nake, ya ɗan hawo gadon tare da kwanciya yana facing ɗina. Fuskata na kauda. Amma sai ya saka hannunsa ya maidota ta inda yake. Gira ɗaya ya ɗage cikin ƙanƙance idanun da ƙara maida muryarsa low ya furta, “Kwantar da hankalinki kema yau zaki samu abinda nake bama na hotels ɗin, Ba sai kin nuna jealous ba, ke dai kawai jirani na dawo”.
Baki na cije da matuƙar ƙarfi ina jin kamar na shaƙosa amma babu dama. Haka ina ji ina gani ya tashi bayan ya sumbaci gefen fuskata cike da shaƙiyanci ya rufe ƙofar ya fice abinsa. Sai kawai na sake fashewa da kuka dan bani da zaɓin daya wuce hakan.

Hayatu da ƙin fitowar Samraah ta sakashi yawaita kallon ƙofar jin motsi ya sashi ɗagowa. Akan ogan nasa da sam bama shi yake kalloba shi ya zuba su. Sai dai kwarjininsa da cikar haiba ta cika masa idanun, janyewa yay tare da miƙewa cikin nuna girmamawa ya furta, “Barka da fitowa Yaya”.
Kai kawai Maash ɗin ya jinjina masa yana mai cigaba da kalle-kallensa, can kuwa idanun nasa suka sauka akan abinda yake nema wato Laalah. A can ƙasan maƙoshi da silent voice ɗin nan nasa mai fita a daƙile lips ɗin na motsawa da ƙyar ya furta, “Laalah!”. Azabure karen ya miƙe da ga inda yake ya nufosa da gudu-gudu. Bai masa magana ba yay gaba shiko ya bisa. Da kallo Hayatu ya bisu da ga shi har karen ta ƙasan ido. Yana nan tsaye cikin mamaki sai gashi ya sake fitowa dan bai wuce mintuna biyu da wasu sakanni ba. Yanzun ma bai kallesa ba face nufar ƙofa da yay yana faɗin, “Let's go”.
Da sauri Hayatu ya kwashi kayan daya zube a Centre table wanda duk takardu ne yabi bayansa. A maimakon ƙofar baya da sukafi bi yau ta babban falo suka bi. Duk da abin ya ɗan bama Hayatu mamaki sai baice komai ba, dan yasan ogan nasa yakan iya haɗa shekara ma baibi ta babban falon ba da sunan fita a gidan. Sai dai in zaije duba Ummie, ita ɗin ma sashenta na a jikin nashi ne shiyyasa akwai ƙofar da yake bi basai ya fito tanan ɗin ba, dan wannan kullum ne safe da yamma, idan ma ya yini a gidan zai iya zuwa biyar bai gaji ba.........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_


.......Babu kowa a falon sai television dake aiki kasancewar dare ya fara duk al'ummar gidan sun shige ciki, hatta uwar dabar gidan Hajiya Mammah da alama yau bata kusa. Dan dama dai itace zaka zo ka iske a falon koda yaushe saboda sa idon masifa da son nuna ita a dole boss ce. Tuni guards ɗinsa da TJ sun gama shirya motocin fita. Fitowar tasa ta sakasu duk miƙewa da barin abinda suke yi. Gaishesa suka shiga yi da girmamawa. Hannu kawai yake ɗaga musu dan yau sosai ƴan miskilancin ne a kusa, ga abinda ya faru tsakaninsa da Samraah yanzu. Da sauri Hayatu ya buɗe masa bayan farar zananniyar motar da TJ ya fiddo, wadda ko makaho ya shafa yasan eh lallai kuɗi yay aiki wajen sayen ta. Dan sai wani irin sheƙi take da ƙyalli mai ɗaukar ido. Gata nan wata ƴar ƙumbula bata cika hayaniya ba, ba kuma ta cika mamaye waje ba. Tsaf take kala da yanayin matasan zamani irinsa da ke gara kan kuɗi ta yanda suke so saboda amincewar UBANGIJI garesu. Sai da ya zauna Hayatu ya maida ƙofar ya rufe sannan kowa ya zabura ya shiga mazauninsa. Hayatu da TJ na gaba kamar koyaushe. Securitys ɗin sa na'a wata motar kamar ko yaushe suma. Da dasu uku ma kawai zaiyi fitar. TJ na ƙoƙarin tada mota ta fito da ɗan saurinta. Kamar kullum tana a cikin kwalliya dake ƙara fidda mata ƙyawunta da bayyana wayewarta. Hayatu ne yay ma TJ nuni daya dakata, dan haka ya tsaya ɗin harta ƙaraso, kallo ɗaya tai musu ta ɗauke kanta, dan direct bayan ta nufa saitin inda Maash da bai san ma da fitowar tata ba yake. Dan hankalinsa nakan takardun daya ɗauka a gefensa da Hayatu ne ya ajiye masa su dan ya duba. Cikin shagwaɓaɓɓiyar muryata data haɗe da gayu ta furta, “My bro.. please zan bika, nasan dai club zaka je”.
Idan kujerar motar nan ta motsa shima ya motsa duk da kuwa muryar tata tazo masa a bazata tunda shi bai san da fitowar tasu ba. Ƙara narke murya tayi cikin nuna damuwa da shirun nasa ta sake cewa, “Please mana Yaya Awwab na shigo?”.
“Kai kana jiran miye?!”.
Ya faɗa cikin yanayin fusata batare daya ɗago ba. Ai jikin Tj har rawa yake wajen murzama motar key dan ko kallonsu ogansu yayi sun san mi yake nufi balle magana da baki. Da wani kalar mayen kallo Azizat tabi motar, ga wani irin sanyi ƙalau da jikinta ke komawa kamar an zubama bread ruwa. Dai-dai motocin na isa katafaren golden an black gate ɗin gidan da aka wangale musu wasu hawaye masu zafi suka shiga rige-rigen sakkowa saman ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Bata motsasu ba, bata kuma yi yinƙurin barin wajen ba. Ashe turaren da Mammah ta bata duk na ƙarya ne tunda gashi tazo gabansa amma bai kulatan ba. Arwa dake ta bayansu ce laɓe ta tako zuwa inda take bayan ta gama cin dariya, dan tun fitowar Azizat daga ɗaki tabiyo bayanta, dama kuma itace ta ɗauke turaren da Mammah ɗin bama Azizat ɗin dan a kunnenta komai ya faru sanda take bata batare da su sun sani ba. Hannunta ta kama kawai tare da janyota ta faɗa jikinta. Rungumeta tayi cikin sigar nuna lallashi batare da tace mata komai ba, sai dai shafa bayanta kawai da takeyi dan babu wani abu da zata faɗa mata kuma wanda ita bata sanshi ba. Sai dai kawai taƙi yarda ne kamar yanda kowa ya sani. Dan tunda yayansu yaface bayayi tofa babu ubanda ya isa cewa yayin sai Umminesa, itako batama da cikakkiyar lafiyar hankalin fahimtar abinda ake a gidan, a shi kansa ma bata masa kallo irin na mutum face ojujun dake sake hargitse lissafin brain ɗinta. Bata ganin laifin Azizat wani lokacin, dan wlhy ko ita da suke kamar uba ɗaya da Yaa Awwab ɗin a lokuta da dama takan ji inama-inama. Amma yanda tasan yana mata kallon ƙawa uba ɗaya yasa take dannewa kawai. Sun ɗan jima a wajen kafin ta kama hannunta su koma ciki...

🌜❤️🌛

A yanayin da ya shigo duk yanda Dad ke ɗauke kansa akan al'amarin nan sai da ya zuba masa ido cikin tashin hankali. Hakama Attahir da ke zaune jigum zaram ya miƙe akan Mansoor. Sai dai yana kamo hannunsa da ya dafe kansa da shi Mansoor ɗin ya kaɓe. Sai kuma ya zube cikin kujera. Amamkinsu ji kawai sukai ya fashe musu da kuka. Dole Dad ya miƙe shima. Su duka biyun sukai kansa da tambaya. Bai iya ya amsa musu ba, face kukan da yake yi da sambatun faɗin, “Shike nan na rasata. Ta auri wani bani ba. Kun cutar dani. Da kunsan irin son da nake mata da baku aitaka abinda kuka aikata ba”.
Hannu Dad ya sanya a bakinsa ya rufe, kafin cikin kulawa da tausayawa da lallashi ya shafa kansa. “Please Mansoor cool down. Nasan an maka badaidai ba. Nima kuma ina ji a raina mun cuta maka. Amma yanzu in sha ALLAHU a shirye nake na gyara kuskurenmu”.
“Taya zaku iya gyarashi Dad? Ta yaya? Bayan wadda kuka rabani da ita ta min nisa?. Iyayenta sun mata aure Dad, Samraah tayi aure, ta auri wani bani ba. Wlhy Dad ina sonta so na gaskiya da ban taɓa kwatanta yima wata ɗiya mace irinsa ba”.
Gaba ɗaya jikin Dad sanyi ya ƙara yi, sai ma ya rasa abinda zai sake faɗa. Kusan mintuna biyu kowa yay shiru a falon sai kai-kawon zuciyoyi kawai sukaji an faɗo musu babu ko sallama balle excuses. Hajiya Sakeena ce ke faman huci da cika da batsewa. Ta watsa musu wani mummunan kallo su duka sannan ta dire idanun nata akan Mansoor. “To mara mutunci haƙarka bata cimma ruwa ba. ALLAH bai karɓi rayuwar Husnah ba kamar yanda kaso kayi fata. Kaje ka gaggaya min magana son ranka har gidan mijin aurena. To yanzu ko zakaji amsa...”
Kamar an jeho Mamy itama sai gata. Kai tsaye kan Hajiya Sakina tayi. Cikin tashin hankali da mamaki ta zube a gabanta tana kuka da roƙonta ta rufa mata asiri. In sha ALLAHU indai batun auren Husnah ne zata saka Attahir ya aureta. Wata shegiyar dariyar rainin hankali Hajiya Sakina ta sanya. Kafin ta tafa hannaye da faɗin, “Iye nanaye caras-cass. Ai daga baya kenan, kema kin sanni bana manta bashin gaba ai Aunty. Ɗanki yaci zarafina ga ɗiyata ɗaya can tilo kwance a asibiti rai a hannun ALLAH. Dama na faɗa miki, in har Mansoor ya saki Husnah wlhy kema sai kin rasa naki igiyar auren dan sai na fallasa abinda kike binnewa”.
“K!! Sakeena!!”.
Attahiru daya gama kaiwa maƙoshi da abinda ke faruwa ya dakama Hajiya Sakina tsawa tare da yunƙurowa kamar zai mareta. Cike da rainin wayo tai wani irin ja baya tana ɗaga duka hannayenta sama alamar surrender. Sai kuma ta kwashe da dariya tana tafasu. Tsitt falon yayi kowa na kallonta har Mamy. Sai da tai Mai isarta kafin ta nuna Attahir ɗin tana haɗe fuska. “Oh lallai ashe kaima ka girma Attahiru? Ai ban sani. Sai ka saurara bada kai nake yi ba yanzu da tsoffinku nake”. Ta wani ɗauke kanta ta maida kan Dad da ya zuba mata ido kawai. Sai kuma takai zaune zama irin na ƙasaita da ƙularwa.
“Kayi haƙuri Yaya idan kaga an ɗaure alƙali a kotu tofa ɗaurowa tayi. Nasan zaka so sanin yanda akayi matarka ta dage dan hana yiwuwar aure tsakanin ɗan ka da budurwarsa. Da kuma ƙullawa tsakanin Husnah da ɗanka.”
Cikin ɓacin rai Dad ya tareta da faɗin, “Sakeena ki tafi maganarki kai tsaye kin san bana son shashanci”.
“Uhhm hakane Yaya kayi hakuri”. Ta faɗa tana maida kanta kan Mansoor da Attahir da suka gama cika da batsewa. Kamar bataga a yanayin da suke ba ta fara bayaninta. “Idan Mansoor da Attahir basu manta ba a ranar da matashin ɗan kasuwar nan da sunansa ya shahara a ƙasar nan dama duniya yay bikin buɗe Companynsa a garin kano wato *_Awwab El-Mu'azz Adams_* da akafi sani da *_MAASH_* kun tattauna wani batu akansa da daddare daya shafi video recording da budurwar Mansoor tai masa”.
Da wani irin sauri Mansoor ya ɗago yana kallon Attahir. Saurin girgiza kai shima Attahir ɗin yayi zai fara rantsuwa Hajiya Sakina ta dakatar da shi. “Kwantar da hankalinka Mansoor ba Attahir bane ba. A sanda kuke tattauna batun wannan video Aunty ta shigo sashen naku saboda damuwar rashin cin abincin kirki da Mansoor yayi. Ta kawo masa kunun tsamiya data dama masa akan ko zai sha tunda tasan yana sonshi sosai. Sai dai tana ɗaura hannunta akan handle ɗin ƙofar ta tsinkayi Mansoor yana sanar ma Attahiru batun video tare da nuna masa shi, ya kuma roƙesa akan dan ALLAH ya rufe wannan sirrin har sai sun gano gaskiya. Ya kuma taimaka musu akan tabbatar da gaskiyar saboda shi yana da abokai ƴaƴan manyan ƙasar nan da sukayi karatu tare a us masu alaƙa da Maash. Cikin jimami Attahir yay masa alƙawarin bincikawa. Sai dai ya tabbatar masa da sam baya jin Maash zai aikata wannan al'amari da gangan in ma harfa ya aikata ɗin. Dan ya ɗan san Maash ɗin shima sama-sama duk da ba wata mu'amala mai ƙarfi bace ta haɗasu face zaman makaranta ɗaya a us. Ya kuma gargaɗi Mansoor ɗin akan ya gargaɗi budurwarsa ta adana video ɗin da ƙyau gudun kada wani ya gansa har yayi tunanin yin wani abu na cutarwa ga Maash. Dan yanzu mutane sun lalace. Ganin Maash mutum mai tarin dukiya za'a iya amfani da video dan yimishi barazana. Ɗari bisa ɗari Mansoor yaji wannan shawara ta ɗan uwansa, ya kuma tabbatar masa da zai nema itama Samraah ya gargaɗeta a daren nan ma basai gari ya waye ba.
Da baya da baya Aunty ta bari sashen, ta samu kai kanta falon, ta samu ka shige sai su Amal kawai na kallo, dan haka ta samu damar shigewa ɗakinta da sauri itama. Kai kawo ta shiga yi zuciyarta na ayyana mata abubuwa da yawa akan abinda ta jiyo. Kaima dai Yaya kasan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login