Showing 156001 words to 159000 words out of 438336 words

Chapter 53 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

3459

hura hanci ko a kwalar rigarsu maybe ma basu ƙi ta kwanta ta mutu ba ko ta dawwama a haka cikin halin lalura dan komai ya zama nasu.....”
“Your are vary stupid!!”.
Ya faɗa cikin katseni da daka tsawa. A take kuma idanunsa suka jirkice ƙwayar tsakkiya ta koma siririya, zaibar ta sake duhu exactly na maguna dai musamman idan suna a cikin hasken rana. Har cikin raina naji tsawar tashi ta ratsa ni, a take kwarjininsa da shakkarsa suka sake dabaibaye ni har na gagara sake magana. Sai da ya buɗe ƙofar a fusace ya fice sannan na sauke nannauyar ajiyar zuciya ina mai rumtse idanuna. Lallai wannan mutumin yayi nisan da bai jin kira. Sannan akwai abinda ya kamata na sani dan na fahimci sam baya son abinda zai taɓa ahalinsa kenan. To lallai babbar magana. Dan ni inaji a jikina lallai akwai ɓoyayyen al'amari mai cike da darasi a ƙarƙashin ciwon mahaifiyar nan tasa. Amma in sha ALLAHU koma minene ni *_SAMRAAH ABDULL-WAHAB GWARZO_* nayi alƙawarin sai na bankaɗosa. Uban kowa sai ya kwashi kashinsa a tafin hannunasa cikin MAASH MANSION..
(Tofa babbar magana. ALLAH ya bada nasara Kandala🥱).

Cikin cije baki da tabbatar da alwashina na nufi ƙofar nima. Dan nayi alƙawarin bazan sake bari mutumin nan yaga gazawata ba duk da ina jin shakkar tasa. Abincin rana dana tuna shine dalilin fitowata na ɗibama Ummie yasa hankalina tashi. Harna nufi hanyar barin sashen na fasa, dan sama-sama na ke jiyo magana ata falo. Falon na nufa, acan ɗin kuwa na samesa tare da ɗan kaɗafin PA ɗinsa. Yana zaune hannayensa duka dafe da kansa alamar akwai abinda ke damunsa ko kuma kan nasa na masa ciwo ne oho masa, PA ɗinsa tsaye ata gefensa cikin tsaiwar nuna girmamawa da alama magana yake masa. Ina fitowa yay shiru. Harara na watsa masa dai-dai muna haɗa ido.
“Barka da rana ranki ya daɗe”.
Ya faɗa dai-dai ina isowa inda suken. Wani ƙululun takaici ne naji ya shaƙuremin maƙoshi. Sai dai na danne na watsar da banza tamkar ma banjisa ba. Ledojin dana gani a gaban ogan nasa da bana raba ɗayan biyu abincine na ɗauka. Harna ɗauka ɗaya na sake tattaro sauran biyun ma na kwashe. Dai-dai na ɗago zan bar wajen PA ɗin nasa ya ce, “Ranki ya daɗe ɗaya ne extra, sauran na Boss ne”.
“Ko zaka ƙwatar masa?”.
Na faɗa a kausashe ina watsa masa wani shegen kallo. Da sauri ya girgiza kansa da faɗin, “A'a ayi haƙuri”.
Tsaki naja mai ƙarfi, ina sake balla musu harara su duka biyun. Sai dai har yanzu kan ogan nasa na ƙasa bai ɗago ba, tamkar ma bai san mike faruwa a falon ba. Nima ba shine a gabana ba, dan haka nai gaba abina ina jan tsaki mai ƙarfi..

★Tana shigewa Hayatu dake kallon ogan nasa da tunanin zaice wani abu amma babu alamar hakan ya sauke ajiyar zuciya. Cike da kulawa da girmamawa ya ce, “Sir bari to na samo maka wani abincin tunda ta ɗauke wannan ɗin duka ko?”.
Shiru kamar Maash ɗin bazai tanka ba. Dan har Hayatu ya fidda rai da samun amsa sai kuma ya ga ya ɗago ya kalla hanayar da tabi, ɗauke idanunsa yay ya maida ga Hayatun. Cikin yanayin nan nasa a daƙile ya furta. “Barshi kawai. Kaje ku ƙarasa abinda zakuyi. Ina sake gargaɗin ko su Juliet kar su san ina ƙasar nan yau.”
“In sha ALLAHU zan kiyaye Sir. Amma idan mun tafi yau wazai dinga samo maka abinci? Ko dai nayi magana da gidan abincin kullum su dinga kawo order sau uku har cikar sati ɗayan”.
Shiru kamar bazai ce komai ba. Sai kuma miya tuna oho. A hankali ya furta, “Kayi hakan”.
Cikin jin daɗi Hayatu ya ce, “A huta kafiya”. Duk da yana mamakin ogan nasa akan daina cin abincin gidan a ɗan tsakanin nan bazai iya tambayar dalili ba. Dan tun washe garin birthday party ɗin Ummie ya sallami kukunsa dake masa girgiki, duk da ma dai ba ko yaushe bane yake cin abincin nasa yana cin na can cikin gidan a wasu lokutan musamman idan Aunty Mama na gari...

💞⭐💞⭐💞

Tunda suka idar da sallar kanta ke a ƙasa ta gagara ɗagowa ta kallesa. Yayinda shi kuma ya kafeta da idanunsa cike da nazari. Ganin yanda ta takure kanta waje ɗaya ya sashi ɗan sauke ajiyar zuciya. Kafin a hankali yay kiran sunanta..
“Halimatussa'adiyya”.
Da ƙyar ta iya ɗagowa tana amsa masa da, “Na'am”. Dai-dai suna haɗa ido. Saurin maida kanta tai ta sunkuyar. Murmushi ya saki da sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya gyara yanayinsa cikin kame kai ya ce, “Wanene ni a wajenki?!”.
Kasa cewa komai tayi, sai da ya sake maimaitawa. Muryarta na rawa tana sake sunkuyar da kai a hankali ta ce, “Baba!”.
Murmushi yay mai faɗi tare da girgiza kansa. “Halimatussa'adiyya ni ba babanki bane. Mijinki ne ni, nasan kuma kin sani.”
Kanta ta sake sunkuyarwa alamar dai ta san haka ɗin ne. Shima sai ya cigaba da faɗin, “Halimatu nasan ke mai tarbiyya ce da ilimin addini gwargwado. Dan naje har tushenki naga gidan da kika fito. Kema a karan kanki a ɗan zamanki cikinmu gidan nan na tabbatar da hakan. Fatana dai ALLAH yasa abinda na gani yasa ya ɗore har abada. Zuwa yanzu kema nasan kin san gidan da kika shigo. Kin kuma san wanda kika aura. Ni ba yaro bane ba, inada ƴaƴa biyu maza Musaddiq da Abbas da suka girme miki, inada ƴaƴa biyu mata Samraah da Sakina (Baby) da zaku iya sa'anni, inada waɗanda zaki iya girma Hafiz, Nabil, Habiba auta Jamal. Ina roƙonki dan ALLAH ki zauna lafiya da su, ki jasu jikinki matsayin uwa. Kada kiyi dubi da matsayin wadda suka girma ko kuke sa'anni. Mahaifiyarsu karki damu da abinda ke tsakanina da ita. Ki zauna da ita lafiya ki bata girmanta. Dan ALLAH duk wata hanya da zata zama ta raini a tsakaninku kada ki buɗeta. Ni kuma na miki alƙawarin in sha ALLAHU zan ƙare miki mutuncinki tako wane ɓangare. Nima na baki amanar kaina. Ki riƙeni da hannu biyu Please Halimatussa'adiyya. Dan ni da ke duk marayune”.
Cike da mamakin jin kalmar Maraya daya kira kansa yadata ɗagowa ta kallesa.
Cikin lumshe ido ya jinjina mata kansa. “Hakane Halimatu, nima maraya ne da babu uwa babu uba sai Gwaggo na kawai da ku da ALLAH ya bani matsayin iyali, sai ahalina na Gwarzo da sai a hankali zaki san kowa da kowa”.
Kanta ta jinjina masa, sai kuma takai hannu ta share hawayen da suka zubo mata. Murmushi ya saki tare da mika mata hannunsa na dama yana faɗin, “Zo nan”.
Da ƙyar ta iya motsawa zuwa gabansa, sai dai tabar ƴar tazara a tsakaninsu. Dan haka ya kamo hannayenta ya jawota sosai ya manna da jikinsa. Zata noƙe ya sake mannata da jikin nasa tare da zame hijjab ɗinta ya ajiye gefe. Ledar takeaway daya shigo da ita ya jawo gabansu. Ta gefen ido Halime take satar kallon dankareriyar kazar da ƙamshinta ya gama cika ɗakin. Yawu ta haɗiya zuciyarta na zallo, sai dai kunya ta hanata yin ƙwaƙwƙwaran motsi.
Cike da kulawa Abba ya ɗiba naman ya kai bakinta. Babu musu ko kwana-kwana ta amsa sai dai idanunta a rufe dan kunya. Shi dai Abba dariyama ta bashi, amma ya danne abarsa. Sai da Halime tai nak da naman kaji da yogurt sannan ta kauda kanta.......✍️

🥱Gara da kikaci abinki Aunty Halime😂😜.




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_


.......Rashin kowa a falon ya bani damar haurawa saman hankalina a kwance. Sai da na sauke ajiyar zuciyar jin daɗi saboda samun Ummie a yanda na barta tana barci. Ledojin abincin na ajiye gefe, na nufi bathroom nayo alwala. Sai da na gabatar da sallar la'asar sannan nai zaman yin karatun Alqur'ani da ka dan babu Alkur'anin a sashen. Tun ina karatun naji shigowar saƙo a wayarsa dake a hannuna. Ban maida hankali ba har sai da na kammala surar da nakeyi ta Baƙara. Kammalawa ta dai-dai da farkawar Ummie, dan haka na nufeta da sauri ganin tana fisge-fisge tamkar wadda ta farka a firgice. Riƙota nayi a jikina ina karanta mata addu'oi, a hankali-ahankali sai ta fara lafawa. Shiru kusan mintuna biyar kuma ta buɗe idanunta tana kallona. Murmushi na sakar mata, kafin a hankali na ce, “Ummie zaki ci abinci?”. Sai da tai ɗan jimm kamar bazata amsa min ba, sai kuma a hankali ta motsa lips ɗin ta ta ce, “Muhammad yunwa”. Murmushi na ƙara mata idanuna cike da ƙwallar tausayinta. Da taimakona ta ɗan tashi zaune, kamar ɗazun na jinginata a jikina da kaina na dinga bata abincin. Abin tausayi yanzun ma sai taci sosai, hakan ya sakani jin farin ciki, na bata ruwa ta sha, batare da tace min komai ba ta koma ta kwanta kanta a saman cinyata, cikin lokaci ƙanƙani barci ya sake kwasheta. Murmushi na saki ina mai rungumo kan nata a jikina, tsawon lokaci ina hawaye kafin na barta saboda sake shigowar saƙo a wayarsa dake hannuna. Wayar na ɗauka, fuskata a taɓe na buɗe saƙon. _(Ko zan ƙare rayuwata a bibiyar taka rayuwar bazan taɓa gazawa ba ko ƙosawa da hakan tauraron duniya. Zan kuma cigaba da roƙonka ka taimaki rayuwata ka aureni koda na wata ɗaya ne. Wlhy na maka alƙawarin maka hidima tamkar baiwa da uwargijiyarta. Kuma koda kullum kake dukana da zagina bazan taɓa daina sonka da maka biyayya ba Gwarzona.)_ wannan shine saƙon farko da aka turo tun ɗazun. Baki na taɓe tare da jan tsaki sannan na buɗe na biyu. _(Ka taimaki rayuwata Tauraron duniya. In ma bazaka aureni ba ko kwanciya kayi dani koda sau ɗaya dan ALLAH kozan rage ƙishirwarka)_
“Kitttumelecy kice ɗan iska ne ashe shima, shiyyasa yayta wani fiki-fiki da idanu uwa na kifi tarwaɗa, kamar wani ustazun ƙwarai hummm” na faɗa a fili bayan na ƙare karanta saƙo na biyu. Ai tini na shiga komawa sama ina karanto na tun daga farko, kaɗanne da alama ana gogewa, ko sau ɗaya kuma bai taɓa bada amsa ba. Koda yake munafukin maybe gogewa yake. Fitowa nayi na shiga masa bincike a messages ɗin nasa, sai gashi na ci karo da wanda sukafi nama farkon ƙazanta daga ƴammata da ban da ban. Ina cikin karanta wani daya firgitani matuƙa dan har na gagara daurewa ina surutai fittt naji an fige wayar. Da sauri na juyo nima a firgice. Sai kawai na gansa tsaye a kaina ƙiƙam yana faman mazurai, fuskar nan tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa. Sai da ya kalla wayar sannan ya sake ɗagowa yana watsa min wani kallon dana kasa bama fassara. Baki na murguɗa masa tare da gallara masa harara nima na ɗauke kaina na maida kan Ummie dake kwance kanta a saman cinyata. Ya daɗe tsaye a kammu batare dana san mi yake yi ba dan ban sake ɗagowa na kallesan ba nima. Kafin ya kai durƙushe gaban mahaifiyarsa ya ɗan ranƙwafo kanta yana mai kai ƙyaƙyƙyawan hannunsa mai ɗauke da dogayen fararen akaifa saman fuskarta ya shafa. Ɗan ɗagowa nayi na kallesa, a mamakina sai naga kamar ƙwalla a cikin idanunsa. Jinai tsigar jikina ta tashi, da sauri nai azamar ɗauke kaina ina sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. Saukar hannunsa akan nawa dake a saman kanta ya sani juyowa na sake kallonsa, dai-dai nan ya ture min hannu ya maye nasa a gurbin nawan yana shafa kitson da nayi mata. Baki na tura nima na ture nasa hannun ina harararsa. Ɗagowa yay ya kalleni cikin yanayin kamar harara shima. Sai kuma ya sake ture nawan, ban bar masa ba na sake ture nasan nima ina hararar tashi.
“K baki da kunya ko!”.
Ya faɗa a dakensa a daƙile kuma. Sai da na taɓe baki sannan na ce, “Yo ni rashin kunyar mina maka. Bana rigaka ba kazo kana nemana da faɗa alhalin ban kulaka ba. Kaje kaji da ƴan iskan ƴanmatanka kwartaye ma ya isheka tunda ba'a gayyaceka ba anan ɗin”
Wani irin kallo yake min da ya saka tsigar jikina tashi gaba ɗaya. Bamma san sanda na murguɗa masa baki da gatsinawa ba na janye nawa idanun da ƙyar.
“I will teach you to be smart”.
Ya faɗa a lalace yana ɗauke kansa. “Ka fara koyama kanka da ƴan iskan ƴammatanka”. Na bashi amsa nima ina ɗauke nawa kan gefe. Daga haka shima ya miƙe tsaye batare daya sake kulani ba. Nima sai ban sake kulashin ba har ya gama dube-dubensa a ɗakin ya fita...


💫💫💫💫💫

Baƙuwar Hajiya Mammah ta iso. Kasancewar kowa yasan ita dama baƙinta ba'a saukarsu a falon ƙasa yasa Mama Balki mata rakkiya har can sama na part ɗin Hajiya Mammah ɗin. Sannan ta koma ta kawo kayan motsa baki. Ta ajiye tana ƙoƙarin fita cike da isa Hajiya Mammah ɗin tace ta turo mata yarinyar nan. Ɗan jimm Mama Balki tayi na shakku, sai kuma dai a ɗarare ta ce, “Tana a sashen Hajiya Babba Alhaji ƙarami ya sakata aiki”. Dan gara ta faɗi haka ɗin kafin wani yazo mata da gulmar sake ganin Samraah a sama abin ya zama babbar matsala.
Shiru Hajiya Mammah bata amsa ba. Sai dai fiskarta ta nuna tsantsar ɓacin ranta. Fahimtar hakan yasa baƙuwarta sallamar Mama Balkin. Tana fita ta kamo hannun Hajiya Mammah ɗin cikin nata.
“Relax mana Hajiya Nafee. Ina gaya miki a koda yaushe ki ɗan dinga controlling fishinki akan al'amarin gidan nan. Ki daina barin ana gane miki haka da wuri musamman ma masu aikin nan naku munafukai. Yanzu dai ina son kimin bayanin mike faruwa?”.
Shiru kamar Hajiya Mammah bazatayi magana ba. Sai kuma cikin ƙunar rai ta shiga ma aminiyar tata bayani tun daga farkon zuwan Samraah gidan har kawo yau ɗin nan kamar yanda dai ta sanar mata ta waya. Ƙawar tata ta jima batace komai ba alamar nazari, kafin ta saki murmushi da kallon Hajiya Mammah.
“Ni ina ganin mafitace tazo mana ai akan yarinyar nan. Za muyi amfani da ita dan ta zame mana zaren ƙulla auren Awwab da Azizat. Kinga cikin sauƙi kema zaki samu cikar burinki”.
“Ban fahimceki ba Rubayya. Ita wannan abar har wacece ita da zata zama zaren cimma burukana? Sai dai burin kore ƙishi”.
“Yamzu kuwa zaki ji. Badai kince yarinyar na shishshige masa ba? Sannan tana shigema uwarsa duk da wahalar da taci a hannunta?”.
“Hakane”.
“Wannan salon nata shine ai makamin namu. Dan dashi zamuyi amfani da ita mu sarƙo wuyan shegen yaron nan mai taurin kai da rashin mutunci. Yanda yake nuna shi mata basa gabansa da ita zamu tabbatar ma duniya munafunci ne.”
“Kinfa san bana son kwana-kwana a zance Rubayya. Fito fili ki faɗa min inda kika nufa dan ni ban fahimci komai ba”.
Dariya sosai Hajiya Rubayya ta saki harda ƙyaƙyƙyewa. Kafin ta ce, “Daɗina dake rashin haƙuri Aminiya. Bari to na kaiki. Fyaɗe zamu saka ya mata na rashin imani. Mu kuma mu dinga masa barazanar yaɗa zancen ta yanda sai ya tsani kansa. A cikin tsakiyar rikicin muyi duk yanda zamuyi ya auri Azizat. Inada tabbacin bazai mana jayayya ba a lokacin dan bashi da wata mafita neman ma wajen tsira yake yi..”
“Humm to idan kuma yarinyar ta samu ciki fa? Ko kuma shi ya ce zai aureta saboda faruwar al'amarin?”.
“Mu dama ai cikin muke buƙatar ma ace ya matan. Dan aikinmu zai fi tafiya dai-dai. Idan kuma yace ma zai auretan mu dai-dai ne. Hakan kuma zai sake ƙarfafa aikinmu.”
“Ta yaya?”.
“Idan yace zai aureta kuma ga ciki ai dole dai zai bari ta haihu. Ku kuma ai ba yarda zakuyi ba matsayin iyaye musamman ma ke. Mu kuma zamuyi amfani da hakan mu zubar da cikin, a wajen zubar da shi zata bar duniyar. Sabon zance zai tashi akan shine ya kasheta, dama zuwa lokacin Azizat na tare da shi. Sai muyi amfani da wannan rikicin da yanayin da zai shiga shi da sauran mutanen gidan naku kema ki samu cikar burinki,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login