Showing 411001 words to 414000 words out of 438336 words
mahaifiyata........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒆𝒍𝒗𝒆_
*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._
.......Amma sunyi kuskure da suka manta kai sunanka mahaifi, har abada kuma wannan sunan na nan a tsakanin kai da su na mahaifi da ƴaƴa bazai taɓa ya canja ba, dolene ka sauke hakkokin su, suma dolene su sauke hakkokinka. Domin idan UBANGIJI ya tashi hukunci zai hukuntaka ne da kuskuren da kai masa, su kuma bazai zama hujja a garesu ba wajen kare kansu suce ai saboda wancan dalilin ne suka gagara sauke hakkokinka. Wancan kuskuren daban, wannan ma daban. Dan haka ina kira a garemu gaba ɗaya, da mu gyara kuskurenmu tun kafin guri ya ƙure mana. Ruwan Ummu-Hidaya ne ta yafe masa laifunkasa, wannan tsakaninsu ne. Amma ku dai ku nema afuwarsa ya yafe muku, sannan shima ya nema afuwarku ku yafe masa dan ku duka kun tauye juna ta fuskokin kasa sauke hakki. Abinda ya faru kuma a baya ya rigada ya faru, ku daina kallonsa shi da ƴan uwansa da laifin da mahaifinsu ya aikatama marigayi Ibrahim da Abdul-wahab dama sauran mutane. Wancan shima tsakaninsa da sune, tsakaninsa kuma da UBANGIJISA ne. Nasan abine mai wahalar gaske, dan magana ta gaskiya ya kai girman da idan cewa Ummu-Hidaya tai ku fita a rayuwarta gaba ɗaya batayi laifi ba. Adam yayi kurakurai masu yawan gaske da kawai dai sai abar ma ALLAH ikonsa. Domin shine ke rahama, kuma shine ke jinƙai. Ina tayaku jaje da kasancewar sa mahaifi a gareku, ina kuma tayaku addu'ar ALLAH ya hanaku gada daga ayyukansa da kuma halayensa. Dan shi jini ba ƙarya bane, ɗabi'ar iyaye na naso a jikin ƴaƴayensu. Shiyasa masu iya magana suke cewa TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE. Saboda haka iyaye mu kula, mu kula, mu kula da gyara ayyukanmu kodan ƴayanyenmu masu tasowa kada ɗabi'unmu na banza suyi naso a jikinsu. Uba kasan irin uwar da zaka auroma ƴaƴanka, uwa kisan irin uban da zaki sakarwa ƴaƴanki. Ina muku fatan ku tsarkake zukatanku, ku cigaba da gyara halayenku, ku guji ayyukan ɓarna, in sha ALLAHU sai UBANGIJI ya nisantaku da irin waɗan can halaye, wanda muka san kuma munayi a ɓoye muyi ƙoƙari mu gyara. Sannan shi kuma ku cigaba da masa addu'a, sadaƙa mai gudana, ba'a yanke ma bawa hukunci tsakaninsa da UBANGIJIN sa. Amma kuyi haƙuri ku yafema juna, ku dunƙule waje ɗaya kuyi haƙuri da juna, ku manta baya hakan shine zai saka muku salama a cikin zukatanku domin fa babu yanda zakuyi, jini ya riga ya haɗu tunda har an haihu. Idan ke Ummu-Hidaya kin yanke alaƙa da su matsayin ƴaƴan Adam daya aikata laifi mai girma a gareki, su kuma su Muhammad yaya zasuyi a matsayinsu na dangin mahaifinsu kuma ga mahaifin nasu a raye. Dole suma sunada nasu hakkoki a kansu. Idan ku kunce kun janye daga gareta saboda mahaifinku ya mata laifi kuma jin kunyarta, a ganinku yin nesan da ita shine mafita a gareku. Su kuma waɗan ƴaƴan da suka kasance jininku a tsakaninku fa. Wanda sunada hakkoki a kanku kuma. Ita rayuwa duk inda akaje aka dawo tanada sarƙaƙiya, duk ƙoƙarin ka na toshe can dole zaka samu can yanada amfanin da idan ka toshe nan ɗin zaka iya dana sani wataran. Shawarar kawai dazan iya baku shine kuyi haƙuri, kuyi haƙuri, kuyi haƙuri. Waɗanda suka haɗa yau duk sun tafi, sun kuma barku da gwagwarmaya mai wahala gaskiya. Wahalar da haƙurin nan ne kawai zai iya ɗorar da ku matsayin ahali. ALLAH ya farta mana, ya kuma shiryemu baki ɗaya. Yasa hakan ya zama izna a garemu dama na bayanmu masu tasowa.”
A tare duk muka amsa da Amin. Yayinda Paah ya miƙe zuwa kusa da Ummie ya zauna. Kansa a ƙasa hawaye na sauka masa ya ce, “Tabbas Ummu-Hidaya ni mai kuskurene a gareki mai girma. Nayi abinda ban cancanci duniya ma ta yafe min ba balle ke dana zalunta ko yaƴanmu. Ke ɗin jarumar mace ce da samunki a wannan duniyar sai an sha matuƙar wahala. Kin shanye, kin kurɓe daga zaluncina. Dan nasan tun daga sati ɗaya na aurenki baki sake jin daɗi daga gareni ba. Kuma hatta da mahaifinki baki taɓa faɗa masa wanene ni ba, sai da ya gano da kansa. Saboda dattako da mutunci na wannan bawa ya sameni batare da saninki ko mahaifana ba yamun nasiha da nuna min illar abinda nake aikatawar. Bai tozartani ba, bai ce na sakar masa ƴarsa saboda ni ɗan iska bane ba. Bai kuma samu mahaifina da zancen ba. Bai kuma gaza wajen cigaba da jawoni jikinsa yana nasiha ba. Badan bashi da ƙarfin ɗaukar mataki a kaina ba. Badan bashi da ƙarfin cewa na sakar masa ke ba. Sai dan kawai shi ɗin jarumin mahaifine mai ƙyaƙyƙyawar zuciya. Wlhy ina ji inama ace Abie shine mahaifina tun a wancan lokacin, inama ace naji nasiharsa naji tsoron ALLAH, kai inama ace mutuwa nai tun ina ƙanƙanina.....” kuka ya sarƙesa. Itama Ummie kanta a ƙasa tana nata kukan. Muma kukan mukeyi, shugaban taurin zuciya ne kawai babu ɗogon hawaye a nasa idanun sai dai sun juye gaba ɗaya alamar dai ana na zuci. Da ƙyar Paah ya ciga da faɗin, “Ummu-Hidaya bamma san ta ina zan fara baki haƙuri ko neman gafararku ke da ƴaƴana ba. Sai dai wlhy ku sani duk duniya ban taɓa son wani abu ba sama da ku ɗin nan ba. Ina muku so da baida iyaka. A yawan lokuta nakan aikata abu gareku batare da ni kaina nasan ta yaya akayi ba, sai daga baya nazo na shiga tashin hankali amma bana iya neman afuwarku. Wlhy ban san irin yanda zan kwatanta miki tashin hankali da ruɗanin dana shiga a waccan ranar ba sakamakon abinda ya faru. Kuma wlhy abinda kike tunanin ya faru bai faru ba, kina faɗuwa kika suma hankalina ya tashi, sai dai tsoro yasa na kasa tsayawa a gidan nima na gudu. Ummu-Hidaya dan girman ALLAH basai anyi tone-tone ba ki yafe min, na roƙeki ko bazaki cigaba da zama dani ba kamar yanda ƴaƴanmu suka buƙata ki yafe min. Dan ALLAH ki yafe min na roƙeki. Muhammad da Fahad kuma ku yafe min dan ALLAH, ku tayani roƙon mahaifiyarku ta yafe min. Bilkisu dan ALLAH ku tayani roƙon ƴar uwarki ta yafe mun. Ƴaƴana Falaq da Samraah da Bahijja ku tayani roƙon mamanku ta yafe min. Na tuba nayi nadama wlhy”. Kuka ya sake sarƙeshi. Itama Ummien kuka take mai ban tausayi da taɓa zuciya. Yayinda illahirin mu muke tayasu. Su duka dole ne su baka tausayi, matuƙar tausayi. Tashi Ummie tayi ta haye sama. Da sauri Paah shima ya tashi ya bita yana kiran sunanta. Suna shiga ɗakin ya zube a gabanta gwiyawu a ƙasa, tare da riƙe ƙafafunta yana kuka sosai. Kukan take itama kanta a gefe har numfashinta na shiɗewa. Haka ya cigaba da mata magiya kusan fin ta minti talati. ALLAH sarki Ummie, zuciyar babu duhu, ita ɗin mai tausayi ce, ta gada daga ƙyawawan halaye na mahaifi. Sai kawai itama ta durƙushe ƙasan ta shiga marin Paah ɗin hannaye bibbiyu suna kallon juna su duka suna hawayen. Tayi masa yafi goma dan harda ƙirjinsa take kaima dukan amma daga marin har dukan ba masu zafi bane ba. Kafin ta faɗa jikinsa tana sake fashewa da kuka. Shima amsarta yay hannu biyu ya rungume yana nashi kukan da sake bata haƙuri....
Acan falo ma su Uncle Abdullahi da Hajiya Mammah da Aunty Mama haƙuri suke bama Maash da Fahad. Tare da neman afuwarsu. Musamman ma Hajiya Mammah da tasan tayi abubuwa a gidan. Ba kuma ta ɓoye ba komai da tayi ta sanar musu. Hatta abinda ta saka a abinci ta bama Samraah takai masa yaci da ga ƙarshe abinda ya faru ya faru, ta sanar musu da manufarta tayin hakan. Ashe hatta su kansu su Uncle Abdullahi ba ƙyalesu tai ba. Tayi musu na mallaka ta yanda duk abinda zatai a gidan zasu kasance cikin shakkarta. Sosai al'amarin nata ya sake bama kowa mamaki, amma tunda dai komai ya wuce batun neman gafara ake yi sai suka yafe mata, tare da fatan ALLAH ya yafe musu baki ɗaya. Daga ƙarshe suka bata shawarar ajiye ɗabi'arta ta je ta roƙa mijinta yafiya shima ta koma wajen ƴaƴanta. Ko kuma ta samu miji tai aure dan shine babban mutuncinta da kimarta. Ta kuma dukufa neman gafarar ALLAH tayi tuba na gaskiya da alkawarin bazata sake aikata abinda ya aikata a baya ba. Daga nan malam ya mana nasiha tare da shawarwari akan muma tamu rayuwar da namu mazajen. Suma mazajen namu ya musu a kammu. Har dai aka rufe taro da addu'a Ummie da Paah basu fito ba. Babu wanda yace komai a kan hakan. Amma fa Yaya Awwab ficewarsa yay a gidan bayan wucewar su Malam...
★Har dare bai dawo ba. Tun ina ɗaukar al'amarin da sauƙi har na fara shiga tashin hankali. Gashi na kirashi yaƙi ya ɗauka. Sai na nema Yaya Hayatu. Kwantar min da hankali yayi, ya tabbatar min na shirya dan yanzu dama ya kira shi yace ya kaini inda yake. Banyi mamakin hakan ba, dan na fahimci Yaya Awwab akwai taurin kai. Sai dai ta wani ɓangaren bana ganin laifinsa. Yana ƙaunar mahaifiyarsa ne sosai. Sannan duk wani ɗa na ƙwarai irin abinda zai yi kenan, ko nice ma abinda zanyin kenan magana ta gaskiya. Shiryawar nayi dan ina matuƙar buƙatar ganinsa nima. Abinda zan iya buƙata kawai na ɗauka, koda na fito sai na kasa tafiya sai na nufi sashen su domin sanar ma Ummien. Nayi mamakin samunta a falo ita da mama Balki. Ganin yanda nake sim-sim ta miƙomin hannu cike da kulawa tana faɗin, “My darling miya faru? Zonan naji”.
Hummm yanda Ummien ke treating namu mukanji kammu like babys ne, ƴan shagwaɓa a gaban iyayenmu, musamman ma ni da ban tashi da uwa ba. Ban samu irin wannan gatan ba. A hankali naje gabanta zan durƙusa, amma sai ta jawoni kusa da ita ta zaunar. Sake tambayar tawa tayi, a ɗarare na sanar mata. Murmushi tayi da sake shafa kaina, sai ka rantse bata da wata damuwa. Amma ko makaho ya kalleta yasan tana cikin ta, dan idanunta sun yi bala'in kumbura saboda kuka. Har ina jin sake karyewar zuciya da kallonta a yanayin. Cike da dakiya ta ce, “Karki damu kinji Baby na. Kije wajen mijinki, ki lallashesa ki tausa masa zuciyarsa. Nasan yayi hakane domin samun daidaituwar kansa. Dan Muhammad bai iya fushi ba, idan yana cikin fushi baya iya controlling harshensa ma. Shiyyasa na koyar da shi yin hakan tunƙuruciya, dan idan yabar inda akai masa kuskuren sai kiga ya huce. ALLAH yay muku albarka, ya kuma saukeki lafiya kema dan na ƙagu naga wannan miji na Bilkisu ko Kishiya ne ma dai to”.
Dariya Mama Balki tayi, nima na ɗan murmusa kaɗan. Haka nai musu sallama na wuce batare dana iya kallonsu ba........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DsaV9faJPfULbIJBU7TS72
https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq
*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._
_
......Ina a baya kaina jingine da kujera na lumshe idanu, yaya hayatu na daga gaba yana driving dan shine zai kaini. Muryarsa a sanyaye ya ce, “Auntynmu dan ALLAH ki lallaɓa Yayanmu ya yi haƙuri komai ya wuce Ummie da Paah su cigaba da kasancewa tare. UBANGIJI ma muna aikata masa laifuka da sukafi wannan girma, ko mushiriki ka kasance ka dawo ka tuba garesa tuba na gaskiya yana yafe maka duk da ƙin shirka da yake balle mu mutane masu fatan gafara daga UBANGIJIN. Paah yayi laifi, amma yayi nadama, al'amarin sa kuma ya ta'azzara ne bisa jagorancin zaluncin shaiɗanin tsohon can. Amma wlhy Ummie na son shi, shima kuma yana sonta sosai. Koyaya Ummie na buƙatar abokin rayuwa a wannan gaɓar, tana buƙatar mai ɗebe mata kewa da tausasa damuwarta ta tsahon shekaru. Sannan batai tsufan da zata gagara wani auren ba. Ba kuma zasu bari ta auri wani mijin ba saboda dole kishin mahaifinsu na nan a tare da su. Kinga ita ai an tauyeta, sannan ko doctor ya bada shawarar mijinta ya kasance da ita yanda ya kamata hakan zai cigaba da daidaita matsalarta komai ya koma dai-dai game da abubuwan da suka dinga bata, in ba hakaba ta cigaba da shiga damuwa wataran brain ɗin nata zata sake birkicewa ne. Nasan duk son da Ummie kema Paah in har Yaya Awwab bai yarda su koma tare ba itama bazata amince da shi ba. Haka ma Fahad, amincewar Yaya Awwab ce kawai zata rissinar da shi ya haƙuran. Ke kuma rissinar Yaya Awwab a yanzu kamar tana a hannunki ne. Kinada tasiri matuƙa da rawar da zaki taka a wannan gaɓar komai ya koma normal. Mu dawo full family har ƴaƴanmu su taso suma su mora haƙuri da juriyar mu”.
Hawayen dake zuba min na share. Cikin jinjina kai na ce, “In sha ALLAHU zanyi ƙoƙarin hakan Yaya Hayatu, amma kaima sai ka tayani da su Mama kuma. Dan wlhy ina tsoron fushinsa matuƙa. Yaya Awwab nada murɗaɗen hali mai ban tsoro. Amma yanzu dan ALLAH ina Paah ɗin?”.
“Paah ya koma can gidan wajen su Uncle Abdullahi. Amma ki