Showing 297001 words to 300000 words out of 438336 words

Chapter 100 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2248

kamar babu lafiya”. Banma jira amsawarsa ba na katse kiran na sauka da sassarfa. Na samu har Mama da Aunty Falaq ma sun fito, har buge juna muke wajen ƙoƙarin fita. Sosai hankalinmu ya tashi lokacin da muke ƙarasa fitowa ganin police ne sai ma'aikatan gidan zagaye da wani abu, mace ce ke kukan da alama itace aka zagaye. Kusan a tare muka iso da Hajiya Mammah. Sai yazam tsawar da tayi ma'aikatan sun buɗe hanya. Hakan ya bamu damar ganin abinda ke faruwa. Falilah ce rungume da mijinta tana kuka kamar ranta zai fita. Jikinsa duk jini har mayafin da aka rufa masa data yaye. Sosai gabana yay mummunar faɗuwa. Ita kanta Hajiya Mammah idanu ta waro sosai da maida kallonta ga police ɗin, sai dai ta kasa cewa komai sai Baba ne yay ƙarfin halin tambayar lafiya..
Kai tsaye ɗan sandan ya bashi amsa da sun tsincesa ne a bakin hanya yashe a ƙasa babu jimawa. A dalilin number motar suka gane daga gidan nan yake. Dan da zasu wuce da gawar ta shi asibiti suga dai ya dace su fara zuwa da shi nan ɗin su tabbatar.
Muryar Baba na rawa ya ce, “Tabbas na nan ne. Drivern Alhaji ne, kuma tare suka fita ɗazun ai. Ina shi Alhajin?”.
“Gaskiya shi kaɗai muka samu, kuma harbinsa akayi”.
Sosai hankalin kowa ya tashi, Hajiya ƙarama ta fashe da kuka tana kiran ta shiga uku. Driver tare yake da Paah. A take aka fara neman layin Paah amma yaƙi shiga. Yan sanda da sukaga abin na gaske ne fa suka ce to zasu je office ai tracking layin Paah ɗin, gawar kuma za'a aikata asibiti domin ayi bincike, zuwa da safe sai a samesu a can office. Idan kuma Paah ya shigo kafin safiya a kira su su sani....

ALLAH sarki da ƙyar aka iya ɓanɓare Falilah a jikin gawar. Haka suka wuce aka barmu jugum-jugum. Nayi ƙoƙarin kiran layin Maash back amma yaƙi shiga. Dole na haƙura. A wannan dare duk wanda yace yayi wani barci to lallai yayi ƙarya. Sai dai in ɓarawo dan babu Paah babu labarinsa. Hatta Baba prof ya zo gidan tun a daren shima hankalinsa a tashe........✍️


Wai ni mima zance anan ne🤔?? Mu tattauna a comment kawai😩😩


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_


.....Zan iya cewa rashin barci da kwanan tashin hankali ya haifar min da zazzaɓi mai zafi. Haka na lallaɓa nayi wanka da asuba ganin baƙona ya wuce. Na ɗan yi mamakin hakan amma sai banbi ta kansa ba nayi salla. So nake na kwanta amma bazan iya hakan ba. Koba komai ina buƙatar son samun Maash a waya duk da nasan manyan gidan bazasu ƙi kira su sanar masa ba. Miƙewa nayi kawai jiri ya wani kwasheni, babu shiri na faɗa saman gado na kwanta. Sai kawai naji hawaye na zubo min. Sannu a hankali barci ya dinga rinjayar idanuna har mai nauyi yay awan gaba dani batare da na shiryama hakan ba.
Nayi nisa sosai a barcin wani irin mahaukacin bugun ƙofa ya farkar da ni. A firgice na tashi har ina ɗimaucewa na rasa hanyar ƙofa sai da lalube na samota. Ina buɗewa kawai aka ɗauke min fuska da mari, ban gama dawowa a hayyacina ba aka sake ɗauke ni da wani marin, tare da fisgar hannuna ƙeyyy akai waje dani har falo. Sai a lokacin ne na fahimci Hajiya Mammah ce. Dan wani irin ihu tamun a saman kai da ya neman toshe min jina gaba ɗaya tana mai min nuni da television. Juyayyun idanuna na kai ga tvn, dai-dai ana nuno hotona dana Maash a cikin jirgin nan. Ba hoton bane ya bani mamaki, ganina riƙe da bindiga, na nuna Maash ɗin da ita daka ganni kaga ƴar daba. Dan wando ne ma da riga a jikina na rashin tarbiyya. Bayana wasu mugayen zaratan maza ne abin tsoro suma sun nuna Maash ɗin da bindugun hannunsu. Sai kuma na gaba guntun video ne na harba masa wani ɗan abu kamar kibiya da ɗayan hannuna dake a ɓoye sai kawai a kan maƙoshinsa, kafin ya yunƙura cikin ƙattan nan dake bayana ɗaya a bayansa ya kai masa yanka da wuƙa a saman hannun da yake ƙoƙarin kaima maƙoshinsa zai cire kibiyar. Kaina na shiga girgizawa da wani irin sauri jikina na rawa.
“Wlhy wannan duk ƙarya ne ba gaskiya bane ba. Ba abinda ya faru kenan a cikin jirgin nan ba. Wlhy bani bace, waɗan nan mazan ma ban sansu ba, ba kuma suje inda muke ba ni da Yaya Awwab. Taya zan cutar da Mijina da hannuna to”.
“MIJIIII?!!! A gidan uban naki ya zama mijinki munafukar yarinya. Yallaɓai oya ku kamata idan taje can tayi bayani. Munafuka ce dama tunda tazo gidan nan muke zargin akwai abinda ya kawota, dole ma itace tai kidnapping Mu'azz. Dan tun bayan da Awwab yay hira da ita shike nan ta saɗaɗo ta biyosa”. Hajiya Mammah ce mai maganar a zafafe. Kuka na sake fashewa da shi dan gaba ɗaya na ruɗe. Gashi bani da wani ƙarfi jiri nake ji sosai fiye da ɗazun. Sai waige nake ko zanga Fahad da Hafizzullah amma babu su a wajen. Sai Mama da ke kuka tana son yin magana amma sun hanata. Ga aunty Falaq a gefe ta zube tana murƙususu da alama naƙuda ce. Banma san sanda nace “Mama aunty Falaq! Aunty Falaq!!”. A gigice Mama ta juya ga aunty Falaq, dai-dai nan matan ƴan sandan suka kamani suka fice da ni a falon.
A tsakar gida na samu an tattare ƴan aikin duka waje guda har su Shu'aibu duk an saka a mota da su TJ, su Bahijja har Falilah dake fama da raɗaɗin mutuwar mijinta ba'a bari ba. Haka nima aka tausani dan inda suke wajen ya mana kaɗan. Gashi an gwamutsa mazan da matan duka. Halin da nake a ciki yasa numfashina ya fara fisga, tun ina ƙoƙarin janyo shi har hakan ya gagara. Ban tashi tsintar kaina a ko'ina ba sai a cikin cell yashe a ƙasa an saka min drip....

💥💥💥💥

Ganin Mansoor na mintuna goma da Salimah ta samu tayi shine ya taimaketa dawowa Nigeria neman iyayensa. Dan bata tambayesa komai ba sai inda ya fito da address ɗin gidansu. Duk da dai da ƙyar ta samu ya faɗa mata dan shi yace yama fi son dawwama a can. Sai da ta takurashi har lokacin da aka bata na neman ƙarewa sannan ya sanar mata shi ɗan Nigeria ce a Kano state. Bako tayi ƙasa a gwiwa ba ta garzayo. Sai dai kafin ta taho ɗin ta nema taimako wajen shahararren matashin ɗan kasuwar nan da yay matuƙar ƙarfi a Dubai ɗin wato Maash. Duk da dai bata samu ganinsa ba ta gana da makusancinsa. Shine ya taimaketa ya haɗasu a waya sukai magana ta minti biyar ko kuma tace ta masa bayani, dan akaf mintuna biyar ɗin nan bataji yace da ita ko ci kanki ba. Ko gaisuwa da tai masa kawai yace Uhmm ne. Bayan ta gama faɗar ne wanda ya haɗasun ya amshi wayar yace ta jirashi. Kusan awa ɗaya ya kirata back. Ya sanar mata Maash yace taje ta nemo iyayen shi guy ɗin, idamasu hali ne suzo Dubai tare, idan marasa ƙarfi ne ta kira ta sanar za'a tura mata kuɗin jirginsu da duk wani shigi da ficin shigowa wata ƙasa. Sosai taji daɗi tanata ma Maash addu'a da shi daya taimaketa. Yace mata babu damuwa ta dai yi ƙoƙari dan Maash zai shigo Dubai a nan da kwanaki uku, kuma kwana biyu zaiyi kacal, ba lallai kuma ta sake samun damar ganinsa ba.
Ita asalinta ƴar medugiri ce. Harkar kasuwanci ta kai Babanta can Dubai shine ya maida su can. Dan mahaifiyarsu ta jima da rasuwa daga ita sai ƙanwarta yanzu sai Babansu da shima girma ya fara kamawa. Tayi karatu mai zurfi a fannin Shari'a, tana kuma harkar kasuwancinta daga Dubai zuwa ƙasashenmu na nan masu makwaftaka da Nigeria.
A randa Salima ta iso aranar batai ƙasa a gwiwa ba sai da ta samu gidan su Mansoor. Inda ta fara cin karo da Attahir zai kai Mamy asibiti ganin doctor. Da farko bai saurareta ba sanin halin matan zamanin nan (🤔Su wai mazan nan sun ɗauka kowace mace ma irin su Azizat ne😏). Sai da ta ambaci sunan Mansoor sannan ya saurareta bayan ya jawota daga cikin asibitin suka yo waje da Mamy na ganawa da doctor kasancewar har asibiti Salima ta bisu. Bata wani ja masa aji ba ta warware masa komai dake faruwa da ɗan uwansa. Hankalinsa yayi mummunan tashi, babu shiri yay kiran Dad ya masa bayani. Dan baya son Mamy ta san komai kodan yanayin jikinta a yanzu. Shima hankalin Dad ya tashi sosai. Dan haka yace a kawo Salima office ɗinsa shi kuma Attahiru yaje ya maida Mamy gida ya samesu a office ɗin.
Hakan kuwa akayi, sai dai anan asibitin Attahir yace Salima ta jirashi ya je ya kai Mamy gida ya dawo sannan ya ɗauketa. Suna tafiya yana ƙara mata tambayoyi har suka iso office ɗin Dad ɗin. Tsaff ta kwashe duk yanda ta sanar ma Attahir shima Dad ɗin ta sanar masa. Har neman taimakon da tayi wajen Maash dan ta tabbarar in har ya saka baki a maganar Mansoor zai iya kubta. Musamman da ya kasance ba gaskiya bane set up ne. Daga Attahir har Dad sun girgiza da jin sunan Maash. Amma yaya zasuyi tunda ta riga ta kai zancen can, sun kuma san taimakon nasa ne kawai zai fidda Mansoor da gaggawa. Cikin gaggawa suka fara shirin wucewa Dubai batare da Mamy ta sani ba. Dan basu sanar mata komai ba sai shi Dad ɗin ne yace mata zai je Dubai wani Bussines zai kuma je da Attahir. Bata kawo komai a ranta ba dan yanzu daga ita har Dad ɗin jan Attahir ɗin sukeyi jikinsu sosai. Hatta aurensa da ke gabatowa shiri suke masa na musamman. A shekaran jiya suka isa Dubai. Basu kuma samu ganin Maash ba sai a daren jiya ɗin nan. Sam shi bai wani gane Attahir da Dad ba. Saboda ba dasu yay waccan harƙallar ba Mamy ce. Saima ɗaukar hankalinsa da kammanin Dad ɗin sukai ya zuba masa ido ƙasa-ƙasa, sai da Attahir ya katsesa da bayanin fitowa filo ya gaya masa gaskiyar zance gudun kada sai ya je fiddo Mansoor ko ganinsa yaga shine yace bazaiyi ba. Amma a mamakinsu sai sukaga ko shock ma fuskarsa bata nuna ba. Face bada umarnin kira masa lawyers ɗin sa da yayi. A take kuma PA ɗin nasa ya aikata yanda ya buƙata. Ya gana Da lawyers ɗin nashi da Attahir da Dad sai shi Hayatu na mintuna ashirin, kafin su ɗunguma zaman court ɗin da za'ayi na biyu akan case ɗin Mansoor ɗin. Sai dai shi banda shi. Suna wucewar ne ma ya shiga yay wanka, ya fito ya nema no ɗin Samraah. Bayan kuma ta yanke bata sake samunsa ba shi kuma duk da yaji mita faɗa bai nemota ba har yanzu.

(🤔Anya kuna ganin lafiya kuwa? Kumu dai je zuwa muji ina Maash ya shige ne haka to? Duk da yaji batun Samraah na cewar gida babu lafiya🤷).

🪴🪴🪴🪴

Tun bayan wucewar motocin police da duk ma'aikatan gidan harda Baba mijin Mama Balki baban kuma Hayatu gidan yay tsitt, sai magowar Falaq mai naƙuda. Da farko duk fita sukayi batare da kowa yazo takanta ba har Baba prof. Sai kuma ga Hajiya ƙarama ta dawo wai Mama Balki ta tashi ta shirya falaq ɗin a wuce da ita hospital. ALLAH sarki Mama Balki a ruɗe take, dan haka ta amsa mata da to. Jiki na rawa ta tashi ta nufi ɗakin da akama falaq ɗin masauki. Ita kuma Hajiya ƙarama ta juya ta fita akan suyi sauri tana jiransu. Tana fita tai kiciɓus da Baba prof shima yay sau da baya. Kallon kallo suka tsaya yima juna tamkar wasu zakaru ko ragunan da suka gama tara ƙahunna da basu da aikin yi sai son yin dabbe. Kallonsa take kamar yanda yake kallonta. Kafin shi ya basar cike da ɓoye abinda ke barazanar bayyana akan fuskarsa. Ciki ya shigo, itama sai ta biyoshi. Mama Balki na'a kan Falaq dan harta wuce ɗaki da dawo da baya, ganin irin kallon da suke mata su biyun batare da sunyi magana ba ya masifar tayar mata da hankali, kafin Baba prof ɗin ya furta, “Su waɗan nan mi sukeyi a gidan nan da ba'a wuce da su ba?”.
Cikin marairaice fuska kamar ta ALLAH Hajiya ƙarama ta ce, “Baba yarinyarta naƙuda take yi, asibiti zamu wuce yanzu da ita kayi haƙuri dan ALLAH”. A mamakin Mama Balki baiyi magana ba, sai wani irin kallo da Baba prof ɗin yama Hajiya ƙaramar ya ɗauke kansa, sai kuma ya juya ya fita yana mata wani irin inkiya da hannu. Bin bayansa tai da sauri itama tana sake tabbatar ma da Mama Balki ta tashi ta shirya falaq ɗin su wuce asibiti........✍️

(🤔Ya kamata nayi tambaya anan ma ko na wuce???)



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_


......Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya zagaye ƙasa. Dan ta ko ina ƴan media yaɗashi suke abinka da babban mutum. Gashi daɗin daɗawa an tabbatar da zuwa yanzu Maash na gadon asibiti ne ma a wajen ƙasar. Ga batun mahaifinsa da ba'a gani ba. Ma'aikatan jirgin da aka nuna wancan guntun video sun fito sun tabbatar ma duniya duk abinda aka gani ya faru, dan a yanzu haka suma suna a asibiti ne saboda raunikan da aka ji musu, biyu da ga cikinsu ma sun rasu. Mugun kiɗimewa Sheikh Muhammad bin Khalipha Al-Hussain yayi da gani wannan labari. Dan shi bai san mike faruwa ba yau ya tashi baya jin daɗi ko television bai buɗeba balle redio, hakama waya. Sai da Hameed ya kira shi yana sanar masa sannan ya buɗe tvn yaga wannan ƙulli. Dan daga gani kasan an shirya komai ne ma'aikatan jirgin nan kuma su ci kuɗi. Number ɗin Maash ya fara nema sai dai kuma bata shiga. Hayatu, nan ma bata shiga. Haka ya dinga bin duk wani yaron Maash makusanci dake a ƙasar da wajen ƙasar dan so yake yaji ina Maash ɗin yake wannan al'amari ke faruwa haka? Ko da gaske yana a gadon asibitin ne?. Amma amsa ɗaya yake samu suma basu san inda Maash yake ba. Hayatu ma an nemesa an rasa tun barowarsa prison da suka sami damar fitar da Mansoor bayan an tashi a shari'ar da lawyers ɗin Maash ɗin suka kawo ƙarafafan hujjoji da ya tabbatar da komai shiryashi akai akan Mansoor. Abinka da komai akan tsari a ranar suka saki Mansoor ɗin aka cafke abokin nasa...


Su kansu su Attahir ɗin a kiɗime suke da jin abinda ke faruwa. A take Attahir ya fito yay magana a media. Bayan ya kira wani abokinsa ma'aikacin BBC. Zancen Attahir ya fara saka mutane a ruɗani, ba'a gama hakan ba sai ga Sheikh Muhammad shima ya fito ya ƙaryata batun abinda ya faru a jirgi. Ya kuma tabbatar da Samraah matar Maash ce shi da kansa ya amshi walliccin aurensa, ya kuma bada hotuna da bidiyo da akayi a wajen ɗaurin auren dama saboda gudun abinda zai iya zuwa ya dawo kasancewar aure ne na babban mutum da akai kamar a sirrance tunda babu wanda ya sani har family ɗinsa. Tofa, zantuka sun fara canja salo, dan an rasa ina za'a ɗauka a yarda. Batun farko na Maash na asibiti bayan Samraah da yaranta sun nema halakashi? Ko kuwa batun Attahir da mahaifinsa da suka tabbatar da a yau ɗin nan sun gana da Maash a Dubai kuma lafiyarsa ƙalau. Harma da taimakon da yay musu basu ɓoye ba. Hakama Salima da lawyers nashi, sun kuma tabbatar da shima Hayatu ko awanni biyar ba'ai da ɗaukesa ba. Dan lafiya Lau suka fito a prison da shi suka shiga mota ya shiga sun iso gidan Maash ɗin sukaga babu motar da yake ciki a tare da su. Nan kuma gidan Maash an zagayesa da securitys.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login