Showing 120001 words to 123000 words out of 438336 words
tambaya sai akan kasuwanci. Hakan na nufin akwai abinda yake ɓoyewa ko baya son a sani dangane da shi. Kai dolene nasan komai, to amma ta yaya? Wannan shine tsallen baɗaken a gareni. Gashi ba wani jituwa muke ba, to wannan ma jiji da kansa zai barsa huɗɗar arziƙi da mutane....
★★★
Tunda Samraah tabar gidan ya sake zama sukuku. Wani lokacin ma ya gwammace ya kwana a gareji kawai. Yakan yi kwana biyu bai shiga cikin gidan ba. Duk da kuwa bai fasa musu dukkan abinda yake musu na hidimar yau da kullum ba mussaman cefane da ya dawo bisa kansa. Idan har bazai zo ba yakan bama wani almajiri dake a garejinsu ya kawo cefanen. Duk da asha ruwan tsuntsaye da yakema zuwa gidan Abba bai taɓa tambayarsa ko cigiyarsa ba. Sai hakan ya sake ƙona masa zuciya da jin komai yama fice a ransa. Yakan ɗan ji sanyi ne kawai idan ya kira Hafizzullah ko mijin Samraah yaji yaya jikinta. Yakan so a bata su gaisa, sai dai hakan baya faruwa kasancewar duk sanda zai kira tana barci. Amma dai mijin kan kirasa video call ya ganta a wasu lokutan. Harga ALLAH yana son zuwa ya ganta, sai dai ta bakin su Kawu Musa baya son mijin nata ya ga kamar an nuna ya gaza ne shiyyasa ya haƙura yake kawaici. A kwanakin nan kuma sai ya koma baya samunsa duk sai hankalinsa ya tashi, yana shirin zuwa Abujan sai ga shi ya kiransa yana mai bashi haƙuri akan jinsa shiru wai yayi wata ƴar tafiya ne, amma yana gab da komawa gida idan ya koma zai haɗashi da Samraah. To tun daga ranar kuma basu sake waya ba dai har yanzu...
Yana cikin damuwar rashin ji daga mijin Samraah ɗin sai ga ogansa yazo masa da wani batu. Wai Companyn Maash na ƙera motoci da aka buɗe kwanaki sunzo garesa suna buƙatar matasan kanikawa masu kwalin secondary. Shi kuma ya bada sunansa dan yasan yana da su. A yanzu haka kuma sunce zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu suna buƙatar ganinsa interview. Rasama abin faɗa yay, sai hawaye da suka cika masa ido yana kallon ogan nasa kawai. Bai san mizai sakankama bawan nan da shi ba a rayuwa saboda ɗunbin ƙaunar da yake nuna masa da alkairan da yay masa...
“Wai namiji da kuka Musaddiq?”.
Ogan nasa ya katse masa tunani cikin nuna damuwa. Hannu yasa ya share hawayen da shi kansa bai ma san sun zubo ba. Sai kuma yay murmushi tare da buɗe baki zaiyi magana. Da sauri ogan nasa ya dakatar da shi da faɗin, “Basai kace komai ba Musaddiq. Ka cancanci fiye da haka a wajen nan domin kai ɗin ɗan hakal ne wlhy. Da ace inada abinda yafi hakan zan maka a rayuwa. Fatana dai ALLAH yasa wannan canjin da zaka samu ya zama sanadin alkairin ka a rayuwa kai da zuri'ata. Kuma ina mai farin cikin sanar maka nima basu barni haka ba. Akwai aikin dazan dinga musu, dan haka zasuzo su gyara wannan wajen ya koma na zamani kamar yanda suka faɗa”.
A take farin ciki ya sake mamaye Musaddiq. Sujidar shikur ya farayi kafin yaje ya rungume ogan nasa. Dariya ya shiga yimasa, dan har ga ALLAH yana matuƙar ƙaunar Musaddiq saboda gaskiyarsa da riƙon amana. Ga biyayya da kwazon aiki, da wahala kaga fushi a fuskarsa koda kuwa faɗa yay masa. Mutum ne mai juriya da shanye komai koda bai masa daɗi ba....
Rasa inda Musaddiq zai kai wannan farin ciki yayi, har ya danna Number Abba sai kuma ya fasa sakamakon tsoratar da shi da zuciyarsa tayi kodan halin Mom. Haƙura yayi, sai da yamma ana tashi daga aiki ya wuce Dawanau wajen Gwaggo Gudidi. Ita ya kaima wannan labarin farin cikin, ai ko baiwar ALLAH harda kukanta tana ƙara godema ALLAH. Daga ƙarshe ta gargaɗesa akan kada ya sanarma Abba yanzu kodan mugun halin matarsa zata iya shiga ta fita ta jefesa da wani sharrin. Yana dai ganin halin da aka shiga game da auren Samraah abu kamar a film ko a labaran hikayiyin marubuta. Ya yarda da shawarar Gwaggo ɗari bisa ɗari. Daga haka suka koma hirar Samraah. Itama Gwaggo ta shiga damuwa sosai hankalinta kuma ya fara tashi, anya kuwa basuyi gangancin aurama Samraah mutumin nan ba? Duk da dai a fuska yazo musu da suffar mutanen kirki. Amma dai zatai magana da Kawu Musa domin a tuntuɓi magabatansa da sukai masa waliccin auren.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒊𝒙𝒕𝒆𝒆𝒏_
_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
______________
......Sosai hirarmu da Bahijja ya tsaya min ƙyam a rai da zuciya. Duk yanda nake yaƙin son turesa hakan ya gagara. Gashi tun ranar ban sake ganin makirin ba. Hakama cikin gidan ban sake shiga ba. Bahijja dai ta sanar min Babansa da matar babansa sun dawo daga tafiya, hakama ƙanin baban nasa da iyalinsa sun dawo suma dai. Sannan yau gaba ɗaya sunyi busy wai ana aiki ne acan sashin saboda bikin birthday da za'ayi wai na mahaifiyar tasa. Ni al'amarin ma sai na ɗaukesa hauka. Yo inba hauka ba, koma nace sunfi ita mai ciwon haukan zama mahaukata mara lafiya dake buƙatar addu'a ce wai za'ama wani shegen birthday party. Kai yawudanci ma baiyi ba. Ko kuwa dukiyar tasu ce ke neman zauta musu ƙwaƙwale ma oho musu. Sosai takaici ya kumeni, ji nake kamar na buɗe ido na gansa a gabana. Wlhy da ko zai tsireni sai na faɗa masa gaskiya sai dai ya mutu shiya sani. Ina nan kwance ina ƙullawa da kwancewa wajen ƙarfe biyu su Mama balki suka fara dawowa. Hayaniyarsu tasa na fito falo nima. Sannu na shiga musu, wasu su amsa wasu su shareni batare dana san mina musu ba. Mama Balki ce ta dubeni da murmushi, cikin kulawa ta ce, “Ai kema daga gobe za'a fara miki sannun. Dan Aunty Mama tace zaki fara aikinki. Kinga sai ki shirya idan mun gama zamu wuce dake tare wajenta kamar yanda ta bada umarni”.
Sosai naji wani irin abu mai nauyi ya soki zuciyata. Na dai danne da ƙyar ina murmushin yaƙe. Da girmamawa na amsa mata da “To mama nagode”. Daga haka ban sake cewa komai ba saboda baƙin ciki. Ni kuma haka rayuwata zata ƙare. Wahalar gidan Abba. Rabani da masoyina, auramin azzalumin mutum irin wannan mutumin da bai san komai ba a rayuwa sai kansa. Daga ƙarshe ma maimakon na shigo gidansu matsayin matar aure a ƴar aiki nazo. Nasan shine ya tsara hakan, kuma zan tabbatar masa ya tsara ramin muguntar da shine zai afka ciki daga ƙarshe. Dani yake magana Samraah Abdul-wahab gwarzo.....
_Hummm Sam-G tamu. Koda yake aunty kike tunda matar Yayanmu ta🥱🥱🚴_
❤️ Kamar yanda Mama Balki ta umarceni wanka nayi nima. A'i da yanzu ta ɗan fara kulani itama ta kawo min doguwar riga ta farin Material da suma naga sun saka a jikinsu inji Mama Balki. Nayi mamakin kayan, dan sababbine ƙal kuma daga gani ba ƙanana bane ba. Haka dai na shirya ina zancen zuci. Ganin yanda Bahijja ta tsaya tana kallona ya sani mata alamar lafiya? Da idanu. Murmushi tayi da sauke ajiyar zuciya. “Wlhy Kandala baki ganki ba. Sam bakiyi kala da masu aiki ba. Kayan nan sun sake fiddo da ainahinki na ƙyaƙyƙyawar mace wayayya. Dan ALLAH idan bazaki damu ba ki sanar min labarinki. ALLAH sai nake ji a raina ko sunanki ba gaskiya kika sanar mana ba”.
Idanu na ɗan waro mata kamar zanyi magana sai kuma na fasa nayi murmushi kawai. Dan babu abinda na ɗauki zancen nata sai shirme. A girme zan iya girmar Bahijja, amma yanayin inda take rayuwa da kuma halitta ta na mutum mai jiki yasa a ido zaka iya cewa sa'anni ne mu. Riƙoni tayi zata sake yin magana Afrah ta shigo. A wulaƙance tace, “Malamai ku Mama ke jira kuka wani zo nan kuka haɗe kawuna dan munafunc....”
Ta gagara ƙarasawa saboda saukar idanunta a kaina. Ɗauke kaina nayi tamkar banga kallon da take min ba. naja ƙaramin mayafin Bahijja na yafa nai ficewata na barsu..
“Kan uba Bahijja kinga kuwa abinda na gani tattare da yarinyar nan?”. Afrah ta faɗa cikin jimami da shiga ruɗani. Ƴar dariyar shaƙiyanci Bahijja tayi. “Yo mi kika gani?”.
“Bahijja anya ba ƴar leƙen asiri bace ba. Sam yarinyar nan batai kama da wadda ta fito a cikin wahala ba. Musamman kwana biyun nan da tayi a gidan nan jikinta ya sake murjewa sai ainahinta ya fito. Duk da muma yawancinmu badaga ƙauye aka kawomu ba rashin gata ne da neman rufin asiri amma yarinyar nan fa ta fita daban a cikinmu wlhy.”
Cikin son basar da zancen Bahijja ta ce, “Babu wani leƙen asiri. Itama dai neman rufin asirin ne ya kawota. Acikin ƴaƴan talakawan ma ai akwai ƙyawawa da yawa irinta har ma da wanda suka fita. Kin san dama irinsu gatan ne kawai babu, amma da sun samu kulawa sai ki gansu tarr da su”.
Badan Afrah ta gamsu da bayanin Bahijja ba tai shiru. Dan Bahijjar na gama bata amsa ta nufi hanyar fita itama. Kai kawai Afrah ke jinjinawa da sake tabbatar ma kanta dole ne ta sakama yarinyar nan ido a gidan nan, dan sai ta san ko ita wacece....
Koda na fito falon ma gaba ɗayansu suka zubomin ido. Hatta da Mama Balki naga alamar shock a tattare da ita. Tuni na ƙara gyara yanayina, dan na fahimci fa nima sai na yarda na ari wata rayuwa kafin na cimma burina akan mutumin nan dama zaman gidan nan. Sam bana fatan zama a cikinsa na dogon lokaci. Amma ina da burin son sanin sirrin cikinsa da mutumin nan keta faman ɓoyema duniya. Hakan kuma bazai taɓa ya kasance ba sai na zauna a matsayin da kowa ke kallona a yanzu na ƴar aiki. Ta wani gefen kuma begen ganin mahaifiyarsa da tausayinta na tsungulin min rai da zuciya. Sai dai ban san ta ina zan kama ba har yanzu. Gaishesu nayi kawai na koma gefe kaina a ƙasa...
“Tab ɗi lallai akwai rigima a gidan nan. A banga laifin Hajiya Azizat ba. Anya kuwa babu alamar tambaya anan gurin?”. Aunty Falilah ce tai maganar cikin nuna baƙin cikinta muraran a kaina. Dama na fahimci ita da sauran ƙawayenta su Aunty Kubrah basa ƙaunata sam. Kafin wani ya sake magana Mama Balki tace muje. Dole kowa ya haɗiye abinda ke a ransa muka fice. Cikin raɗa Bahijja dake ta gefena ta ce, “Kiyi haƙuri karki damu da su. Su dama su Aunty ƴan neman fitina ne, sam basa riƙe girmansu a cikinmu saboda suna gadarar yaran Mammah ne a gidan. Itace mai juya akalar kowa a gidan kuma hatta da mai gidan kansa da matarsa”.
Murmushi kawai nayi batare da nace komai ba. Dan ta gefena su Afrah ne idan har nayi magana zasu jini. Sosai an sake ƙawata gidan. Tako ina ka kalla kasan za'ayi shagali ne. A maimakon cikin gidan yau garden muka nufa. Bamma san sanda na furta “Masha ALLAH” ba a zahiri. Dan tsayawa muku misalin haɗuwa da tsaruwar da garden ɗin nan yayi ma ɓata lokaci ne. Sai dai abin mamaki bamu tsaya anan ba. Ta wata ƙofa da ganyen flower ya baibaye muka sake ratsawa sai gamu a wani killataccen waje da yafi wancan ƙatoton da muka ratso, wani irin shiryayyen adon furanni da koriyar ciyawa akai masa tako ina masu ƙamshi. Ga ƙaton swimming pool da ruwansa ke wani kalar ƙyalli da walwali tamkar ba normal ruwa ba. Ƙasa-ƙasa Bahijja dake kusa da ni ta furta, “Wannan sashen garden ɗin babu mai shigowa cikinsa sai a irin wannan ranar. Sau ɗaya a shekara kenan kawai”.
Da mamaki nace mata, “Saboda mi?”.
“Saboda bana kowa da kowa bane. Bakiga an zagayesa da waya ba. Uncle boss kaɗai ke shigowa cikinsa, dan tanan shine jikin part ɗinsa”. Ta ƙare maganar da ɗan nuna min wata hanya da aka ƙawata da koriyar ciyawa tamkar a irin lambun mafarkin gaibu ɗin nan. Na jima ina kallon ƙofar abubuwa masu yawa namin kai-kawo. Sai dai bance komai ba face ɗan kalle-kallen garden ɗin da nake yi. Komai a tsare a tsaftace. ga Docorretion ɗin da akai masa ya bala'in sake ƙawatashi. Hannuna da mama tazo ta kama ya sani kallonta firgigit, murmushi tamun da faɗin, “Zo muje ke anan zaki zauna har sai an buƙaci ganinki”.
“Mama saboda mi?.
“Saboda Aunty Mama bata bada umarni na shigo da ke har nan ba”.
Komai ban sake iya cewa ba har taja hannuna muka fito a wajen. A ƙaton garden ɗin na farko muka dawo. Ta kaini can wani ɗan lungu ta ce, “Zauna anan. Kar kije ko ina dan ALLAH dan akoda yaushe zan iya zuwa kiranki”.
Kaina kawai na jinjina mata. Dan koda bata roƙeni ba ma bazan tashin ba. Nakai zaman mintuna talatin a wajen dukan tunanina naga Yaya Musaddiq. Yau wani irin kwaɗayin son jin muryarsa nake shi da Hafizzullah. Tamkar wadda hankalinta ke dawowa jikinta a wajen nake jin ƙarfin zuciyata da komaina dake neman ƙwacemin a kwanakin nan na fara dawowa. Sai kawai naji harshena ya ɗauki ambaton sunayen ALLAH. A jere na ringa sauke ajiyar zuciya kai kace a barci na farka. Ratsa kunnenna da sautin muryar malam tayi yana karanto addu'a ya sani lumshe idanuna a hankali. Ji nake hatta da jinin jikina yamutsawa yake yi har a cikin farautana har malam ya kammala. Ajiyar zuciya na sake saukewa a karo na babu adadi, dai-dai nan sai ga Mama Balki ta dawo kirana.
Nasha mamakin ganin wajen yanzu dan cike. Dan komai da alama an tsarashi ne hatta da mutanen dake a wajen. Ɗan bin kowa da kallo nake ƙasa-ƙasa nima har muka isa inda su Bahijja ke tsaye jere. Dai-dai nan mc ke shelanta fitowar mai gayya mai aiki tare da tabbatar da shi a madadin mai birthday ɗin. Tsitt wajen yayi kowa ya sake maida hankalinsa ga hanyar da Bahijja ta nunamin ta sashensa. Duk da yanda zuciyata ke tafasa na kasa ɗauke idanuna daga kallon wajen nima. Ƙanjamammiyar baturiyar nan mai shegen iyayi da yaje da ita wajen taron buɗe companynsa ce ta fara fitowa sanye cikin doguwar riga milk da wasu shegun dogayen takalmanta. Siririn tsaki na saki tare da ɗauke kaina a wajen gaba ɗaya.
“Woow masha ALLAHU”. Da Bahijja dake a gefena ta faɗa ya sakani ɗagowa na kalleta. Ganin yanda ta saki baki da hanci da idanu tana kallo ya bani mamaki, kaina kawai na girgiza zan ɗauke caraf ta kamo hannuna. ”Dan ALLAH ki kalla ado ya namijin ɗawusu Aunty Kandala. Wlhy Uncle Boss na kasheni da salonsa, komai ya saka a jikinsa sai kiga kamar danshi dama akayi kayan, wani lokacin sai nakeji kamar na ciza uwawuna”.
Takaicin shirmenta ya sakani dalla mata harara. Nai ƙoƙarin fisge hannuna amma ta sake damƙeshi. Haushi ya sakani kallonta, amma sai naga ma ita hankalinta sam baya a kaina. Takaici ya sani girgiza kai kawai nakai dubana ga abinda take zuzutawar batare da nasan dalili ba nima..........✍️
_Bayin ALLAH kuyi haƙuri dani Please. Wlhy biki gareni na ƙanwata asabar ɗin nan. Jiya kuma rasuwa akai mana data bugeni sosai. Amma in sha ALLAHU komai ya kusa dai-dai da amarya taje ɗakinta zaku cigaba da ganina yanda ya kamata. Kuyi hakuri