Showing 300001 words to 303000 words out of 438336 words

Chapter 101 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2259

Basu sani ba Maash na cikin gidan har yanzu, ko kuwa? Amma dai sun tabbatar lafiyarsa ƙalau su dai akwai dai abinda ya faru? Ko batun babban malami da kowa ke mutuntawa da gani girma daya tabbatar da shi da kansa ya amsawa Maash auren Samraah harma ga shaidu?.
Kasancewar Samraah sananniya ce a baya, da irin yanda zancen kidnapping ɗinta da batun fasa aurenta da aurenta na biyu ya zagaya media sai aka dinga dawo da labarin yanzu. Sai dai abinda ya so raba kawunan mutane ko'a baya ba'a san takamaiman mijin Samraah ba. Wanda akaita haɗata da su editing hotunan akayi. Amma sanin waye malam yasa da yawa aka amince da wannan zance.....

💞💫💞💫💞

Gaba ɗaya Mama Balki ta rikice. Ta rasa miya kamata tayima Falaq, ga shi bata son tafiya asibiti da ita tabar Ummie ita kaɗai a gidan nan akwai haɗari. Dan tabbas komai zai iya faruwa. Hawayenta ta ƙara sharewa, tare da bubbuga fuskar Falaq da ke neman shiɗewa. A dai-dai nan aka fara taɓa ƙofa alamar za'a shigo. Hankalinta ne ya sake tashi, dan tayi alwashin data bar Ummie gara ta haƙura ta rasa Falaq ɗin. Ta gama sallamawa a bazata taji ana kulle ƙofar, da wani irin sauri ta ɗago dan tasan dai da ga ita dai Falaq sai Ummie da tun ɗazun ma take barci bayan likitocin ta sun zo sun dubata sun mata allura. Sai dai a mamakinta sai taga Ummie ce ke rufe ƙofar, bata gama dawowa a sumar wucin gadin da tayi ba Ummien ta baro ƙofar ta iso garesu. “Bilkisu Kamata” ta ce kawai tana ƙoƙarin kama Falaq. Duk da maganar bata fita sosai harshen ma a karye yake kamar mai koyon magana Mama Balki taji abinda ta faɗa. Tuni wani ƙarfi yazo mata ga hawaye na kwarara tana kuma kallon Ummie ɗin suka ɗaga Falaq. Jin yanda ake buga ƙofar da wani masifar ƙarfi ana ƙwala kiran sunan Mama Balki yasa Ummie sake faɗin, “Mubar gidan nan Bilkisu”.
Ta wajen swimming pool ɗin nan suka fita, ita dai Mama Balki sai kallon Ummie take hawaye sun gagara tsaya mata.
Da wani irin ɓacin rai Hajiya ƙarama ta koma, Baba prof na tsaye a babban falon sashensu yana kai-kawo su Azizat cirko-cirko Hajiya Mammah na zaune na sharar hawaye, hakama Maman Malika kuka take. Uncle Abdullahi dai ya fita tun ɗazun a gidan akan batun Paah. Iya su kaɗai ne a gidan sai police a ƙofar gate biyu da aka bari, amma da securitys ɗin ƙofar, da na gidan, da duk wasu ma'aikata maza da mata an tattaresu zuwa police station. Babu ma wanda yabi takan batun Fahad da Hafizzullah da basa gidan duk wannan dambarwar da ake yi. A yanda Hajiya ƙarama ta faɗo falon ne yasa duk suka ɗaga kai suka kalleta. Cikin shashsheka da sauke numfarfashin gudun da ta ɗan yi ta ce, “Ta kulle ƙofa fa matar can. Ina tsoron ba wani abu take shiryawa akan Hajiya Babba ba”.
Su dukansu babu wanda bai zabura ba. Cikin matuƙar ihu Baba prof ya ce, “Ubanwa yace ita su barta ita da ƴar tata. Idan wani abu ya samar min Ummu-Hidaya sai na kashe matar nan. Ni dama sam ban yarda da ita ba itama...”
Babu wanda ya iya cewa komai akan maganar tasa. Sai rige-rigen ficewa da sukai a sashen zuwa sashen Maash ɗin. Wani irin mahaukacin jijjiga ƙofar suka dinga yi su duka suna zagin Mama Balki. Ruɗewa Mama Balki da duk suke iya jiyosu kasancewar sun zagayo ta can baya ta sake yi. Ga Falaq ta sume musu ta ƙara nauyi. Jikin Ummie ba wani ƙarfi yake da shi ba. Amma ta daure matuƙa duk da itama jikin nata rawa yake yi. Jin motsin ana nufo inda suke dan su Baba prof na ƙoƙarin zagayowa ne su biyo ta baya tunda duk sun san da ƙofar cikin garden har biyu yasa cikin kuka Mama Balki da jikinta ke ƙara ƙarfin rawa ta ce, “Ummie ki gudu ke kawai, bari na kira Isma'il amintaccen Alhaji ƙarami ne in sha ALLAHU zai taimakemu ya kaiki wajen da wani bazai taɓa sani ba har Alhaji ƙarami ya dawo. Amma zamanki anan akwai haɗari”.
Kai ta girgiza mata, tare da mata nunin su ɗauki falaq ɗin. Babu yanda Mama Balkin ta iya haka suka sake ɗaukar Falaq, cikin flowers suka shige hannayensu dafe da bakunansu. Daga ta inda suke suna iya hango Baba prof da Hajiya Mammah dake ƙoƙarin shiga ta ƙofar swimming pool da suka bari a buɗe. Dai-dai nan Falaq ta kawo wani irin bahagon mummunan numfashi da ya saka Baba prof dake ƙoƙarin shigewa tsayawa cak. Jikin Mama Balki na wani masifar ɓari ta cire ɗan kwalin kanta ta toshe bakin Falaq dake zabura. Garrr wata ƙatuwar baƙar kunama ƙirin ta fito daga ƙarƙashin Falaq ɗin ta shige tsakanin Mama Balki da Ummie. Hakan na nufin kunamar ce ta sari Falak. Su duka kasa motsi sukayi, musamman Ummie da dama tun can fil azal tana masifar tsoron kunama a rayuwarta da maciji da ƙadangare. Kuma Mama Balki ta san da hakan. Ga shi in har suka sake wani motsi Baba prof da har yanzu ke'a tsaye sai ya gane. Haka suka zauna zukatansu na bugawa ga wata irin zufar tashin hankali data gama jiƙe Falaq babu tantama haihuwa ce ga azabar kunama......

✨✨✨✨

A can Kano kuwa ɓangaren Abbah kam neman yanke jiki yayi zai faɗi a lokacin da yaci karo da tashin hankalin da ke faruwa. Dan illahirin jikinsa karkarwa ya shiga yi. Baima san sanda ya fara ƙwala kiran Mom da duk abinda ake tana a kusa da shi tana gani ba daɗi kamar zai kasheta. Ƙin amsawa Abba kiran da yake matan tayi sai ma murmushi da ta saki duk da wani ɓangare na zuciyarta na mata raɗaɗin jin Maash wai Samraah ta aura. Amma babu komai tunda ga a yanda aka ƙare hakan ma nasara ce. Halime da sam ita bama tasan wainar da ake toyawa ba jiyo muryar Abba dake kamar rawa ya sata tashi a ɗan firgice daga kwanciyar da tayi a kujera. Dan yau bazata fita makaranta ba bata jin daɗin jikinta. Da ƙyar ta iya lalubar ɗan kwali ta ɗaura, a karo na farko da tun zuwanta gidan matsayin matar Abba ta shiga sashen Mom. Dai-dai nan Abba yayo baya zai faɗi da sauri ta saka hannayenta biyu ta tarosa ya faɗa a ciki. Duk da nauyin da yay mata, ga ƙaton cikinta daya ƙara fitowa haka ta daure jikinta na rawa ta kai durƙushe da shi. Kuka take tamkar ranta zai fita, UBANGIJI gafurin rahimun sai ga Alhaji Jafaru da Gwaggo Gudidi tamkar an jehosu gidan. Kukan Halime da neman temako da take yaja hankalinsu sashen Mom ɗin suma suka nufi can da sassarfa.
Mom ɗin najin motsi itama ta fara kuka tana kaiwa durƙushe gaban Abba ta kamoshi daga jikin Halime ta maida nata jikin. Salati Gwaggo Gudidi da Alhaji Jafaru suka shiga yi suma suna nufar kan Abban da gaba ɗaya numfashinsa ya gama ɗaukewa.....✍️


🤦🤦🤦🤦🤦


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒔𝒊𝒙_


.......Baba Prof ya ɗan jima yana waige-waige kafin ya ƙarasa shigewa ganin baiga komai ba. Yana shigewa Ummie ta miƙe jikinta na rawa saboda azababben harbin kunamar daya ratsata har tsakkiyar kanta itama. Cikin ƙanƙanin lokaci zufa ta gama wanke mata jiki. Ƙoƙarin nufota Mama Balki tayi, amma sai ta mata nuni da su kama falaq kawai, hawaye ne suka ciwo idanun Mama, dan ta tabbatar cizon kunamar nan ya shigi Ummien amma ta nuna dauriya. Haka suka kamata da ƙyar sai nishi take saboda babu damar yin kuka kasancewar ɗan kwali da Mama Balki ta saka mata a baki, yayinda ita kuma Ummie keta faman taunar lips ɗinta. Ta cikin garden ɗin Maash daga can ƙarshe da filawoyi suka lulluɓe bangon gaba ɗaya Ummie tayi da su. Mamaki ya kama Mama Balki lokacin da Ummie ta saka hannu ta shiga yaye filawar wajen duk da ƙayoyin dake famar fasa mata hannu, ƙofa ce ta bayyana da bazaka iya taɓa yarda akwaita a wajen ba saboda ta mugun sajewa da katanga matuƙa. Da ga gani kai kasan an tsara wajen ne sosai. Dan ƙafa, ce ta gasken gaske. Wani abu daga can ƙasa Ummie ta danna sai ga ƙofar na buɗewa da ƙyar, dan wani irin mugun ƙarfi ne da ita gata ta zallar ƙarfe. Dai-dai suna gama fita suka jiyo Arwa na ƙwala kiran su Baba prof. Suna ɗaga kai suka hangota ata can saman Maash ta balcony. Tabbas ta gansu, kamar yanda suka ganta. Dan haka Ummie taja ƙofar da masifar sauri ta datse. Kuka Mama Balki ta sanya tana neman number ɗin Isma'il. Amintaccen Maash da ke matsayin Kuku a gidan Baba prof, duk da dai itama Mama Balkin bata san da hakan ba, bama yasan cewar Isma'il ɗan sanda bane kawai dai yakan zo amsar bayanai a hannunsu na wani abu idan ya faru gidan lokaci-lokaci. Harta tsinke bai ɗaga ba. Hankalinta ya sake tashi, dan ta tabbatar suka zo ga ƙofar nan bata buɗe ba zasuyi yinƙurin zagayawa ne, ga Ummie dake shan azabar kunama, ga Falaq data haɗa biyu naƙuda da kunama utama. Kiran ta sake yi, sai data masa uku sannan ya ɗaga, batama zauna saurarensa ba ta shiga masa bayani. Shima can hankalinsa ne ya sake tashi, dan dama a tashin hankalin rasa inda Maash yake suke shi da duk ɓoyayyayun da ba kowa ya sani ba. Ya tabbatar musu su ɗan bar wajen kaɗan gashi nan zuwa, dan dama yana kusa da gidan yaje kasuwa ne. Ko tahowa su Baba prof sukai daga cikin gidan kafin su su zagayo shi ya iso. Hakan kuwa akayi, dan cikin ƙanƙanin lokaci ya iso kasancewar su su Baba prof na can suna kokarin neman ƙofa da Arwa ta tabbar musu ta gani da idonta an buɗe su Mama Balki sun fita harda Ummie da suka duba basu gani ba a kaf sashen. Ganin fa babu ko alamar kufan ƙofa a wajen wasu suka fara ƙin yarda da Arwa ɗin. Yayinda Baba prof yace bazasu tabbar da hakan ba sai sun zagaya ta baya dan ga sayin ƙafafun su Mama Balki nan ɓaro-ɓaro a garden ɗin. Dan haka aka bar su Hajiya Mammah da yaran, shi kuma shi da Hajiya ƙarama suka zagaya. Isowarsu dai-dai da tashin motar Isma'il daya kwashi su Ummie sai number ɗin motar da ƙurarta suka gani. Wani irin mahaukacin reverse Hajiya ƙarama tayi tare da ƙarama motar wuta suka bi bayansu. Gaba ɗaya hankalin su duk ya tashi, da ita Ummie ma duƙar da kanta kawai tayi dan juya mata yake yi sosai. Isma'il na ganin zasu ƙure musu ya wani irin yin reverse shima ya dawo baya, kasancewar ita kuma ta riga ta kwashi motar da yawa domin ƙoƙarin cimmusu sai ta kasa tsayawa. Da wannan damar ya samu shigewa wani layi da bashi da tabbacin yana ɓillewa ko a'a...

Wani kalar taka birki da dukan steering Hajiya ƙarama tayi. Shima Baba prof ya kaima glass ɗin window ɗin gefensa naushi. Gaba ɗaya idanunsa sun gama kaɗewa jajur, wayarsa ya fisga a take ya shiga kiran number DCO ɗin da case ɗin Paah ke hannunsa. Yana ɗagawa ya masa bayani akan kidnapping Ummie da aka sake yi tare da bashi number ɗin motar. Yana ajiye wayar Hajiya ƙarama dake masa kallon tashin hankali ta ce, “Yallaɓai amma fa wannan ganganci ne. Tunda kaima kasan ba kidnapping ɗin nata akai ba. Nifa na kasa ganema gaba ɗaya wannan shirin naka dake neman harmutse komai.”
Ko kallon inda take baiyi ba bare ya amsa mata ya buɗe motar yay ficewarsa. Jitai kamar ta shaƙo shege ta farka mar wuƙa kowa ma ya huta. Motarta itama ta fisga a fusace ta bar wajen batare data sake kallonsa tsaye a gefen titi yana waya ba. Tasan Commando yake kira, ita ma kuma tana buƙatar ganin commondo ɗin yanzun nan. Dan su ya kamata su ɗauki Ummie kafin shi.....


❤️‍🔥💫❤️‍🔥❤️‍🔥💫❤️‍🔥

An miƙa Abba asibiti da gaggawa. Halime sai kuka take yi Gwaggo Gudidi na lallashinta. Har yamma basu ji wani ƙwaƙwƙwaran bayani akan al'amarin nasa ba. Sai kusan bayan isha'i doctor ya ɗan kwantar musu da hankali tare da son ganin Alhaji Jafaru. Dagewa Halime tayi akan saita bisa, da ƙyar Gwaggo ta dinga lallashinta Alhaji Jafaru ya fita ya tafi shi kaɗai. Babu jimawa sosai sai gashi da takardar magunguna. Wayarsa daya bari ya ɗauka ya fita. Gwaggo na tambayarsa yaya ake ciki yace mata kawai da sauƙi ayi masa addu'a. Gaba ɗaya jikin Gwaggo ya ƙara yin sanyi, yayinda Halime ke kwasar kuka. Ita kanta Mom duk tayi wani sukuku dan zuwa yanzu ta fara jin hankalinta na tashi. Gashi su Gwaggo duk sun ƙi kulata sam....

❤️🌟❤️🌟❤️

Tun a mota faya ta fashema Falaq, da ƙyar ALLAH yasa suka isa gidan da Isma'il yake rayuwa kafin fara aikinsa a gidan Baba prof.. dole shi da Mama Balki suka kamata zuwa ciki, dan Ummie kam bazata iya ba zuwa yanzu ƙarfin ta ya gama ƙarewa. Ita kanta sai da suka komo suka kamata suka fita da ita a motar zuwa ciki. Suna shigowa kukan jariri na jaraɗe gidan. Da sauri Mama ta nufi ɗakin, har ta shiga sai kuma ta dawo jikinta na rawa ta buƙaci sabuwar reza da ko towel ne. Zuwa Isma'il yay ya ɗako, yana kawo mata ta koma ciki. A mamakinsa sai ya ga Ummie ma ta miƙe. Ƙoƙarin dakatar da ita yayi amma sai ta masa murmushi kawai cikin ƙarfin hali ta shiga ɗakin itama. Mama Balki na hanata amma a hakan cikin yanayin da take sai da ta taimaka mata suka amshi haihuwar Falaq ɗin. Dan ma Alhamdullah komai yazo da sauƙi. Dan suna gama yanke cibi sai ga uwa itama ta biyo. Mama ce ta cigaba da gyara Falaq, yayinda Ummie ke rungume da jinjiri a jikinta hawaye na sauka mata da alama akwai abinda ta tuna ko yake dawo mata da irin wannan yanayin. Haka dai Mama ta gama tsaftace komai ta gyara jariri da uwarsa ta kuma taimakawa itama Ummie ta gyara jikinta daya ɓaci. Bawan ALLAH Isma'il sai gashi da kayan da duk zasu iya buƙata na sakawa harda na jinjiri sai likitan Ummie. Yana ajiye musu tare da abinci ya nunama Mama Balki komai yay, likita ya duba Falaq duk da yace ba aikinsa bane aka kuma duba Ummie su duka akai musu allaurar dafin harbin kunama sannan suka musu sallama akan zai koma kan aiki kar a nemesa. Addu'a Mama balki ta masa Ummie dai na kwance rungume da jariri kamar mai barci....

🌿✨🌿✨🌿

Dole Isma'il yay hanzarin shiga kasuwa yay cefane sannan ya kama hanyar komawa gidan Baba prof. Yana zuwa kuwa motar data ɗakko baba prof na isowa. Gaishe shi yayi kamar yanda kowa ke gaishe shi a ransa yana mamakin ganin yanda duk Baba prof ɗin ke'a hargitse. Haka dai ya lallaɓa ya shige kitchen ganin Commondo ya iso shima. Yana shiga kitchen ɗin ya ɗauka ruwa da lemo ya kai falo, in da ya samu har commondo ya shigo. Yana ajiyewa ya juya ya koma kitchen ɗin. Inda ya saba laɓewar ya laɓe yau ma. Aiko sai ga muryar Baba prof ɗin cikin tashin hankali...
“Daga nan zuwa dare ina buƙatar ganin gawar Lawisa a Maash Mansion ”.
A wani kalar firgice Commondo ya juya ya kallesa. Batare da yasan ma mi yake ba ya ce, “Yallaɓai saboda me?”.
“Saboda daman hakan shine plan ɗina, sai dai ba a yanzu naso yin hakan ba. Amma naga tana neman shiga min hanci dolene kuma na fyatota.”
“Eh bazan ƙi baka goyon baya ba ranka ya daɗe. Sai dai inaga ya kamata mu dai sake nazari. Lawisa nada sirrikan ka a hannunta da yawa. Sannan ko babu komai kana buƙatarta a yanzu.”
“Duk wani sirri dake a hannunta bashi da wani amfanin da zai min. Kawai a kaudat......”
“Niko keda sirrin da zai maka amfani Adams”. A bazata sukaji muryar Hajiya ƙarama a kansu. A tare duk suka kalleta, a yau babu kunya babu tsoro ta nuna Baba prof da yay galala yana kallonta. Dan sam baiji ko alamar shigowarta falon ba ma kodan a gigice yake........✍️


🥱Tofa. Manyan shegu yaya dai?.


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login