Showing 198001 words to 201000 words out of 438336 words
buɗe idanunsa ya zubama jami'in batare daya tashi ba. Ji Jami'in yay bazai iya jure kallon ba, sai ya kauda idanunsa cike da basarwa yana furta, “Sir bamu da isashen lokaci. Idan ba damuwa ka amsa mana wasu ƴan tambayoyi mana”.
“Jeka maganarka kai tsaye” Maash ya faɗa a daƙile.
Ran jami'in ne ya sosu, sai dai baice komai ba ya cigaba da faɗin, “Akwai containers ɗinka da suka tashi daga Lagos a shekaran jiya da dare zuwa ƙasar Ghana. An samu yara ƴammata a cikin ɗaya da muke da tabbacin safararsu aka shirya yi. Still dai a cikin container ɗin anyima yaran makwanci, a ƙasan shi mun samu kayan laifi”.
“Kamar......?”
Maash ya faɗa cike da rainin hankali. Yanzu kam a fusace jami'in ya kallesa. Sai dai kuma bai iya cewa komai ba ya cigaba da faɗin, “Drivers ɗin sun tabbatar mana da cewar sun fito daga companyn ka ne”. Ya ƙare maganar da tura masa hotuna gabansa. Batare da Maash ya ɗauki hotunan ba ya zuba musu ido kawai. Kansa ya ɗan girgiza cike da rashin damuwa ya furta, “A staff ɗina bana tunanin nasan waɗan nan fuskokin”.
“Ba zamu tabbatar da hakan ba, dan zaka iya hiding nasu. Sai dai kuma su containers ɗin ai bazai yiwu kace ba naka bane ba”.
Shiru babu alamar Maash ɗin zai tanka, sai da ya mula dan kansa sannan ya saki ɗan gajeren murmushi da kai hannu ya shafi kwantaccen gashin fuskarsa. Zamansa ya gyara da ƙyau gaba ɗaya hannayensa akan table ɗin ya zubama jami'in ido. “Mr Man kamar ya dace ka tuna kai jam'i ne ba alƙali ba. Damar samuwar amsar tambayoyinka kuwa zaka same su ne kaɗai a bakin lawyers ɗina”. Daga haka ya gyara zamansa ya sake lumshe idanunsa duka hannuwansa harɗe a ƙirjinsa.
Iya ɓacin rai Jam'in nan ya shiga. Dan haka ya miƙe a fusace ya fice abinsa. Murmushi Maash ya saki mai ɗan sauti batare da ya buɗe idanunsa ba.
Har yamma Lawyers na Maash na fafatawa a station ɗin, shi dai yana a inda aka kaisa har yanzu. Sai da lokacin Sallah yayi ya buƙaci yin alwala. Basu da damar hanashi. Abincin da Hayatu ya kawo masa kuwa ko kallonsa baiyi ba. Dan shi fa sam bawai cakwakiyar station ɗin ma bace damuwarsa. Hankalinsa ma gaba ɗaya baya a wajen.
Gab da magrib Baba prof... Ya iso, da ga airport kai tsaye shima station ɗin yayo, anan ya samu kusan duk ahalin gidan. Paah, Uncle Abdullahi, Hajiya Mammah, Maman Maleeka (Matar Uncle Abdullahi) sai Hayatu dake kai kawo tsakanin asibiti da aka kwantar da Samraah zuwa nan. Ko bayan isowar Baba prof.. ɗin shima ya kai awanni uku a station ɗin kafin su samu bell ɗin Maash ɗin bisa wasu sharuɗɗa masu tsauri.
Ƙarfe tara da wasu mintuna aka fiddo Maash da ga ɗakin nan. Kallo ɗaya yay ma ahalin nasa ya ɗan kauda idanunsa. Sai kuma ya cigaba da takowa a nutsensa har inda suke. Baba prof.. ne ya riƙosa ya rungume yana faman ambaton Alhamdullah. Shi dai Maash baice komai ba. Bayan ya sakesa kuma ya koma tattaɓashi da jera masa tambayoyi. “Kana jin yunwa? Akwai inda ke maka ciwo? Sun maka wani abu ne?.....”
“Grandpa! I'm not small boy now”.
Ya katse Baba prof.. ɗin cikin wata irin murya mai cike da rashin damuwa. Murmushi Baba prof.. yayi da kai hannu ya yamutsa masa sumar kansa kamar yanda yake masa a duk sanda suka haɗu. “Oh na manta Muhammad Awwab ɗina dutse na rimi ne baka fargaba sai ta ruwa.”
Dariya su Paah suka ɗan yi, kafin shima ya matso ya rungume Maash ɗin, hakama Uncle Abdullahi. Maman Malika ma tai masa barka. Ganin haka itama Hajiya Mammah ta bashi side hug. Shi dai komai bai cema kowa ba. Sai hankalinsa da ya ɗan maida ga lawyers ɗinsa da Hayatu dake fitowa. Cike da girmamawa suka shiga gaisheshi. Tare da jajanta abinda ya faru suma. Idanunsa ya lumshe kaɗan da sake buɗewa, suma ɗin dai batare da yace ma kowa komai ba ya motsa a hankali ya fara tafiya.
Suma duk ƙoƙarin ficewar sukayi, kowa da abinda ke a zuciyarsa. A motar da yazo da ita da safe ya shiga. Sai dai yanzu Hayatu ne a mazaunin driver. Har sun ɗauki hanyar gida a kasalance Maash da idanunsa ke rufe har a lokacin a hankali ya furta, “Hospital”.
Cikin girmamawa Hayatu ya amsa masa, tare da fita a cikin sauran motocin ya ɗauki hanyar asibiti. Sauran abokan tafiyar basu farga ba sai da akaje sauke Baba prof a gidansa. Da farko sun ɗauka ko gida su suka wuce saboda Maash ɗin ya huta, sai da drivern Baba prof ɗin ya sanar da inda yaga sunyi sannan ne a fusace Hajiya Mammah ta ce, “Eh lallai, al'amarin Awwab kullum sake gawurta yake wlhy. To amma kuma anya ba wani abun yaje aikatama yarinyar nan ko hana likitocin faɗa ba saboda ya rufe sirrinsa.”
Har cikin rai zancenta ya soki zuciyar Paah, sai dai baice komai ba. Baba Prof ne ya tambayi abinda ke faruwa? Har zagwaɗi Hajiya Mammah keyi wajen zayyane komai daya faru da safe har neman yarinyar da suka dinga yi da daddare. Wani yawu mai kauri Baba prof ya haɗiya idanunsa akan Paah da Uncle Abdullahi. Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Wayarsa ya amsa a hannun drivern sa daya kwaso kaya zai kai ciki, dan duk abinda Hajiya Mammah ta faɗa ya laɓe yana jinta. Kai tsaye Baba prof ɗin wayar Hayatu yay kira, bugu ɗaya kuwa ya ɗaga.
“Kuna ina?”.
Da ƴar in ina Hayatu ya ɗan kalla Maash dake ƙoƙarin fita a mota daya buɗe masa dan isowarsu ke nan. “Bab ba baba muna CLINIC”.
“Clinic! Yin me?”.
“Zamu duba mara lafiya ne”.
Ƙittt Baba prof ya yanke kiran batare daya sake cewa komai ba. Cikin damuwa Hayatu ya dubi Maash ɗinya ce, “Baba Prof”.
Komai baice masa ba, sai ma ƙoƙarin raɓasa da yake yi zai wuce abinsa. Dole shima ya haɗiye abinda ke bakin nasa ya bisa.
★★
Mama Balki na zaune a saman abin salla idar da shafa'i da wutirinta kenan akai knocking ɗin ƙofar. Miƙewa tai tana kallon agogo, azatonta ma Nurse ɗin data sakama Samraah ruwa ce ta dawo. Ruwan ta kalla taga ko rabi bai kai ba ma, kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Ƙofar ta nufa, sai dai kafin ta buɗe sai da ta tambaya waye?. Hayatu ne ya amsa mata da cewa, “Mama mune”.
Da sauri ta buɗe tana murmushi, tana ƙoƙarin bashi hanya ya shigo idonta ya sauka akan Maash. Wani irin washe baki tayi tana ambaton Alhamdullah. Da jerama UBANGIJI kirari. Ɗan lumshe idanunsa yayi tare da sakin gajeren murmushi ya shiga gaidata. Amsa masa tai tana ƙara godema ALLAH daya sa komai ya zama mai sauƙi.
Nan ma murmushin kawai ya saki baice komai ba, sai Hayatu ne ke tayata murnarta. Ƙarasa takawa yay a hankali zuwa gaban gadon idanunsa a kanta. Tana kwance samɓal idanunta a rufe alamar barci take. Fuskarta ta wani irin yin fayau da ita, sannan har yanzu idanunta a kumbure suke alamar taci kuka mai yawa. Lips ɗinta sun bushe tare da tsukewa waje guda sun ƙara pink sosai. Take wasu abubuwa suka shiga dawo masa game da ita. Cikin sauri ya kauda su tare da janye idanun nasa daga lips dinta, akan hannunta da aka saka ruwa ya sauke. Madaidaitan farcinanta dake da ɗan sauran jan lalle na biki kaɗan da bai gama fitaba yaja kusan mintuna biyu yana kallo, kafin ya maida ga ruwan da ake ƙara matan. Sai kuma ya janye gaba ɗaya ya matsa gaban side drawer dake a gefen gadon ya ɗauki file ɗin da aka ajiye ya fara dubawa. Juyowa yay da nufin yin magana sai ya ga ɗakin wayam, ashe Mama Balki da Hayatu sun fice. Kansa kawai ya girgiza yana ajiye file ɗin, sannan ya zagaya ta ɗayan side ɗin gadon inda hannunta ke free ya zauna kusa da ita jikinsa na gogar nata. Hannun nata ya kamo cikin nasa, ya zubama dan sauran lallen dake jikin faratan nata ido, abubuwa da yawa zuciyarsa ke tunano masa da suka shafi Ummie, mace ce mai tsananin son jan lalle, tunda ya santa kafin lalurarta lalle baya gama fita a hannunta take yin wani. Hakan ya sashi tashi da son lalle shima, lokacin yana ƙarami yakan saka mata rigima shima sai an masa. Takan ce masa maza basa lalli, amma ya tubure ya dinga bori ko yaje ya tsare Mama Balki ko mahaifiyar Hayatu akan dole su sai sun masan, dan a farkon ciwonta kafin komai ya damule har da kansa yake mata lallin a yatsun hannu saboda yasan tana so. Murmushi ne ya suɓuce masa da shi a karan kansa ya mance tsahon shekarun daya ɗauka baiyi irinsa ba. Sai kuma ya kai babban yatsarsa ya ɗauke guntun ƙwallar da suka taru masa a gefen ido kaɗan........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒐_
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
_______
.......Ɗan motsi Samraah tayi fuskarta a yamutse baki a taɓe kamar mai shirin sakin kuka. Idanu kawai ya zuba mata yana kallon yanda take laɓe bakin, ƙoƙarin motsa hannunta da tai ya sashi sakin wanda ya riƙe ya riƙe mata wancan gudun karta goce ruwan, sake yamutse fuskar tayi da ƙara tura baki.
“Cry. Cry”.
Ya faɗa a hankali saman lips ɗinsa yana kai ɗayan hannunsa a karo na farko kan fuskarta ya ɗan shafa gefen kumatun kaɗan. Idanunta ta shiga motsawa a hankali, sai kuma ta buɗesu gaba ɗaya. Cikin yanayin wadda barci bai saka ba ta ɗan zuba masa su, shima kallon nata yake...
Tar tar fuskarsa ta fara bayyana cikin idanun nawa sosai. Wani irin harbawa zuciyata tayi babu shiri na zabura. Sai dai jin an riƙeni yasa na kallesa a marairaice, batare dana san hawaye sun ɓalle min ba na fara roƙonsa cikin magiya. “Na roƙeka dan ALLAH kayi haƙuri ya Awwab, wlhy zan iya mutuwa bazan iya ba”.
Ganin bashi da niyyar tanka min sai rikitattun idanunsa daya zuba min yasa na sake fashe masa kuka mai ɗan sauti. Kansa ya ɗan girgiza tare da sakin hannun nawa ya kuma janye wanda ke a fuskata sannan ya miƙe, kaɗan ya ranƙwafo ya kama bargon. Sake marairaice masa fuska nayi ganin yanda ya duƙo kaina sai yanayin ya sake min kama da na wancan lokacin, idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe cikin soft voice ya furata, “I will go now. calm your mind”. Ya ƙarasa lulluɓa min bargon har saman ƙirjina. Idanuna na lumshe sauran hawayen dake cikinsu na ƙarasa gangarowa. A bazata naji saukar lips ɗinsa saman goshina. Kafin na buɗe idanuna a firgice harya juya yabar wajen.
Ƙofar daya maida ya rufe na zubama idanu, a hankali bugun zuciyata na sauka. Shigowar Mama Balki ɗakin ya sani kauda kaina daga kallon ƙofar. Kaina tayo kanta tsaye tana faɗin, “Kin tashi Samraah?”.
Kaina na jinjina mata da ƙoƙarin kai hannu na share hawayena, zama tayi a gefena tana mai kamo hannuna cikin nata. Cike da lallashi da kulawa ta ce, “Kukan nan ya isa mana haka Samraah. Abinda ya faru dai ya riga ya faru ai. Sai fatan ALLAH ya baki lafiya. Ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, bana son ko a fuska ki nunama Alhaji ƙarami wani abu. Koba komai shi ɗin mijinki ne, kowace mace kuma da haka ta girma. Komai zai wuce kamar bai faruba. Naga ya fita kamar cikin damuwa, gaki ke kuma kina kuka. Dan ALLAH ki daure ya samu sassauci ko'a wajenki ne. Kinga yanzu daga police station ya fito tun safe amma ko gida baije ba sai da yazo nan domin dubaki. Alhaji ƙarami abin tausayine wlhy”.
Idanuna na buɗe a hankali ina kallonta, sai kuma na kai hannuna na sake share hawayen da suka gagara tsaya min. Cikin dasashjiyar muryata na ce, “Mama ni babu abinda nai masa fa. Kawai dai shi yasan mike damunsa. Mi yaje yi police station kuma?”.
“Nasan babu abinda kikayi masa Samraah. Amma nasan kukan nan da yaga kinayi ma ya isa ya sake ɗaga masa hankali. Ki daure ki daina kinji. Idan shima yaga kin kwantar da hankalinki zai fi samun nutsuwa wajen baki kulawar da duk kike buƙata. Sannan ya fuskanci abubuwan dake gabansa. Dan nasan akan batun nan naku wata sabuwar cakwakiyace kuma. Su suna kallo al'amarin da wata suffa daban, idan kuma baya gadama ba duk abinda zasu yi bazai sanar musu alaƙarku ba dan da kike ganinsa nan akwai taurin kai da kafiya. Bamu san abinda ya faru ba da safe folisawa suka cika mana gida wai sunzo kamashi” daga haka ta cigaba da lallashina har na sake komawa barci raina fal mamakin zancen kamashi da tace anyi, a yanda yake da kuɗi da power ɗin nan har jami'an tsaro zasu iya kamashi ashe?...
💦💢💦💢💦
“Ni nai sa'a da masoyi mai fara'a, shi ya fara sa shadda duk garinmu an shaida bai ɗaya. Ni na shirya, zana baka soyayya, koda ƴan baƙin ciki zasu haɗiyi zuciya. Ni na dace, na faɗa ko na dace, da sahibi imamullah mijin ƙwarai”.
Halime kenan, ke raira waƙarta cike da nishaɗi tana wanke-wanke a babban kitchen dake mallakin kowa da kowa. Wanke-wanke take na kwanikan da akaci abincin rana da tayi, yau kuma ne zata fita a aiki Mom ta amsa. Da farko aikinta take hankalin kwance sai dai shigowar Mom kitchen ɗin da abinda tai mata ya ƙona mata rai. Maimakon ta biyema Mom ɗin sai kawai ta shiga raira waƙa. Idan tayi wannan sai ta saki ta kama waccan harta kammala wanke-wanken. Kasa haƙuri Mom dake tare da mai-aikinta tana bata umarnin abincin dare da zata ɗora musu tayi. Cikin fusata ta shaƙo wuyan rigar Halime ta baya ta fusgota.
“K ƙaramar ƴar iska waƙe-waƙe ai bazai kai miki ba. Rama abinda nai miki ya kamata kiyi sai na san kin cika matsiyaciya”.
Idanu kawai Halime ta zuba mata, sai kuma tayi murmushi da kai hannu ta janye hannun Mom ɗin a jikinta. Ƙoƙarin juyawa take ta ƙarasa aikinta Mom ta sake ƙoƙarin damƙota cikin masifa da haushin shirun da tai matan, dan so take ta tanka mata akwai abinda zata saka mata a gashi. Wani shegen tsalle Halimen tayi gefe kai kace tayi gamo da wani bala'i ne. Hakan yasa mai aikin Mom da ita kanta Mom ɗin sai da suka zabura. Sai kawai tsabar wulaƙanci Halime ta fashe da dariya. Galala Mom da mai aikinta sukai suna mata kallon mamaki. Itako sai ta kallesu sai ta fashe da dariya, da tayi kamar zata tsagaita sai ta kallesu ta sake fashewa da dariyar. Wani irin tuƙuƙi zuciyar Mom ta shiga yi, tana yunƙurowa a fusace zata sake shaƙo Halimen sai kawai ta kauce mata tare da ɗaukar kayanta data tara a kwandon kife kaya tai ficewarta. Sai dai taje bakin ƙofa sannan ta ɗan dakata. Juyowa tai ta kalla Mom har lokacin fuskarta da sauran dariyar ta ce, “Ƴar baƙin ciki, so kike na biye miki muyi dambe dalin Imamu ya talauce saboda ke kin gama shan daɗin romin zabbi. To wallahi bashi yiwuwa nima sai na dandali arziƙin nan. Ɗan romon kifin nan dana kaji da ban samu naci a gidanmu ba sai na sha farina ya sake fitowa nayi ɓul yanda zanje ƴan tumaki ana ku matsa ga matar Alhaji Imamu nan ta iso haaaah”. Ta ƙare maganar da gatsine mata baki tana yin gaba abinta.
Kasa ko motsi Mom tayi, sai zuciyarta dake wani bala'in yunƙurowa. Wai itako yaya zatayi da mahaukaciyar yarinyar nan a gidan nan. Tayi bala'in, tayi fitinar, tayi boren, tana kan asirin amma duk a banza. Babu irin maganin da batai amfani da shi ba a kofar shiga ɗakinta da cikin abincin da Abba da Halime zasu ci amma ko gezau. Jiya har layun da teacher ya bata