Showing 306001 words to 309000 words out of 438336 words
ɗin ya dinga jin kaifinsu, dan haka shi ya ɗan rissinar da nashi. Da wani irin taurin zuciya ya furta, “Isma'il ni ba jami'in tsaro bane. Amma brain ɗina da zuciyata na aiki fiye da ta wasu jami'an tsaron dake a cikinku. Ba kuma dan na kasance na daban ba. Sai dai na rayu ne a matsayar ƙin yarda da kowa hatta kaina.”
Kai Isma'il ya jinjina yana mai sake rissinar da kansa. Cike da girmamawa ya ce, “Suna gidana. Ƙanwarka kuma ta haihu namiji. Ina mai farin cikin kasancewa wanda zai fara maka albishir guda biyu. Na haihuwa dana alamomin samuwar lafiyar Ummie. Dan da taimakonta suka fito a gidan kamar yanda Mama ta sanar min.”
Wani shegen murmushi daya saka Isma'il tsayawa kallonsa ya saki, batare da yace komai ba. Sai da ya ɗan bubbuga table ɗin gabansu da yatsa sannan Isma'il ɗin ya kawo numfashi, sai kuma yaji kunya. Ɗauke kai Maash ɗin yayi da faɗin, “Bayan nan fa?”.
Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi. “Abunuwa da yawa sun faru a cikin gidan, nasan kuma ƙarin bayani kawai kake son ji, dan in har baka sani ba a yanzu kana da hanyar saninsu ko anan gaba. Sun ɗauke Alhaji, amma abinda na fahimta ba Prof.. bane ba.....”
“Nasan inda yake”.
Ya faɗa a daƙile. Sai Isma'il kawai ya saki baki yana kallonsa. Sannan cikin in ina ya ƙarasa faɗin, “Anyi uwar watsi tsakanin Hajiya Lawisa da Prof...”
Sake sakin murmushi Maash ɗin yayi a karo na biyu, kafin a wani kalar soft voice ya ce, “Miya haɗasu?”.
Tsaff Isma'il ya kwashe komai ya sanar masa. Kafin ya ɗora da faɗin, “Amma ranka ya daɗe naji yana sanarma yaronsa Commondo cewar kana Dubai ya maka tarko, yasa an yanke wutar gidan da kake ciki, da network, da ruwa. Sai kuma gaka a Nigeria. Wlhy ni gaba ɗaya ma sai na raina kaina. Anya yallaɓai baka cancanci zama jami'in sirri ba”.
Maimakon ya amsa masa sai ya miƙe yana mai maida mask ɗinsa. “Zaka iya tafiya, da ga yanzu zuwa asuba zan tura a ɗauka su Ummie”...
Da kallo kawai Isma'il ya bisa, sai da ya ga ya ɓacema ganinsa ya sauke wani nannauyan numfashi yana miƙewa. Kamar ɗazun yanzu ma rakashi akai har mota, yana barin wajen office ya wuce. Dan bazai iya haɗiyewa ba sai ya gana da ogansa....
A ɓangaren Maash ma Isma'il yana gama ficewa ya ɗaga waya yay kira. Cikin bada umarnin ya furta, “Ina son scorpions dake rayuwa a cikin yashi mai zafi kamar guda ashirin nau'i daban-daban daga nan zuwa gobe in ALLAH ya kaimu”. Da ga haka ya maida wayar cikin aljihu batare da ya kashe ba ya shige ƴar bukkar dake a wajen da aka yi ta domin hutawa kawai. Abu ya ɗakko ya fito suka bar Garden ɗin........✍️
Munga idi. Yayanmu kunamai kuma😳? Mi zakayi da shi🤦? To gaskiya kowa yay ta kansa ni dai ba ruwa na🏃🏃🏃🏃🏃🏃🏃🏃🏃.
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒏𝒊𝒏𝒆_
......Duk wanda yace yayi barci mai daɗi a daren jiya tako wane ɓangare yayi ƙarya. Dan kowa da abinda ya damesa. Daga masu shiryawar har waɗan da aka shirya mawa ɗin. A Maash Mansion dai an samu cigaban isowar Aunty Mama (Aunta Mashi'a) da duk labari ya sameta ta kuma ga komai. Abinda ya tada mata hankali shine rashin sanin inda Ummie take da Paah. Sannan ance Hajiya ƙarama da Baba prof sun bi bayansu suma har yanzu basu dawo ba. Da yake hankalin su Hajiya Mammah ɗin a tashe yake ita da Maman Malika basuyi tunanin bincika gidan Baba prof ɗin ba sai Aunty Mama ɗin ce tai tunanin hakan. Sun ji daɗin jin ya koma gida, itama Hajiya Ƙaramar sai sukai tunanin ko tana asibiti damuwa ta hanata dawowa gidan. Abu na biyu da aunty Mama ɗin tayi shine haɗuwa ita da Uncle Abdullahi da abin duniya yama yawa dan shima dai sai dare ya shigo gidan yanayinsa yasa Maman Malika bashi maganin barci aka samu ya runtsa. Police station sukaje suka fito da duk ma'aikatan gidan da aka rufe. Anan ne suke jin Samraah babu lafiya tana ma asibiti ita. Kasa magana ma Aunty Mama tayi dan ɓacin rai, sai Uncle Abdullahi ne ya balbalesu da masifa. Itama dai sunje asibitin sun ganta. A lokacin tana barci suka gana da likitar dake kula da ita.
Bata basu a ɓoye ba ta sanar musu Samraah nada ƙaramin ciki ne, sai dai akwai ɗan matsala dan yaso fita sai dai ALLAH ya taimaka tana fara bleading ɗin aka kawota asibitin. Sunyi nasarar tsaida shi amma tana buƙatar bed rest gaskiya. Sannan duk wani abu da zai tayar mata da hankali ba'a sonshi. Akwai Ummie da take yawan kira ya kamata tazo asibitin ko hakan zai bata nutsuwa. Sai mijinta shima da suke buƙatar gani.
Sosai Aunty Mama ta nuna farin cikinta da har ya bama Uncle Abdullahi mamaki. Dan shi dai yasan cakwakiyar da akeyi akan batun yarinyar nan a gidan. Amma yaga autar tasu ita ko'a jikinta ma. Bai daiyi magana ba sai da suka fito daga asibitin. Gefen titi ya samu ya faka motar yana kallonta. “Auta wai halan baki san mike faruwa bane? Duk fa wannan tashin hankalin akan batun yarinyar nan ne”.
Murmushin itama tayi tana mai fuskantarsa. Ta ce, “Yaya nasan komai. Sai dai hakan bazai hanani murnar samun ƙaruwar da mukayi ba. Dan koba komai cikin dake jikin yarinyar nan jininmu ne.”
“Amma bata hanya mai ƙyau aka samar da shi ba ai kin sani”.
“Kamar ya?”.
“Fyaɗe fa Awwab ya mata”.
Karo na farko dariya ta suɓucema Hajiya Mama. Ta ce, “Humm yaya kenan, wai ku har yanzu kuna akan keken ɓeran da Awwab ya sakaku kenan? Zuwa yanzu ya kamata ace kun gama haddace halayyarsa sai dai ku bama na waje labari kuma. To wannan yarinyar matarsa ce da gaske. Duk abinda kaji Sheikh Muhammad bin Khalipha Al-Hussain ya faɗa shine gaskiyar magana. Abinda keta kai-kawo kuwa shirine kawai na magauta bana raba ɗayan biyu kuma abokan kaduwancisa ne”.
“To ke ya akai kika sani?”.
“Yaya labari ne mai tsaho, amma bari na gajarce maka shi. Tiryan-tiryan ta bashi labarin komai tun bayan ɗaura aure, ciwon Samraah da kawota asibiti Abuja har zuwa guduwar da tayi ta faɗa hannun Madam Jannifer da sakata amsota da Maash yayi, da kawota gidan matsayin ƴar aiki kamar yanda ya buƙata. Rasama abin cewa Uncle Abdullahi yayi, dan harga ALLAH zancen ya girgizashi. Sai tausayin yaron ya sake kamashi. Tabbas matarsa ta faɗi gaskiya da tace basu damuwa da damuwarsa sai ayyukansu kawai. Haka ya tada motar jiki a sanyaye suka koma gida.
Sun samu Hajiya Mammah nata masifa akan dawo da masu aiki da akayi, sai da Hajiya Mama ɗin ta mata bayanin sune suka je suka saka aka sakosu. Cikin masifa Hajiya Mammah ta ce, “Amma banda waccen shegiyar yarinyar ko?”
“Saboda mi Adda?”.
“Saboda bata da gaskiya, ita dake matsayin ƴar jarida a Kano ubanmi ya kawota nan? Dan ko kunsa an fiddota wlhy sai na maidata. Sai ta faɗi inda Mu'azz yake”.
“Addah kina kwantar da hankalinki idan abu ya faru dan ALLAH. Samraah bata da hannu akan kidnapping Yaya sam saboda ita ɗin matar Awwab ce da gaske, kuma shine yasa na kawota nan gidan a wancan lokacin” tsaff ta kwashe labarin komai ta basu kamar yanda ta bama Uncle Abdullahi. Gaba ɗaya falon yay wani irin tsitt tamkar ruwa ya cinye kowa. Hatta da Baba prof dake ƙoƙarin shigowa ƙamewa yay a ƙofar duk da ya jima da yarda da hakan, ya kuma ji bayanin Sheikh Muhammad ɗin, amma jin komai a bakin autar tasa da yanda Maash ya shigo da yarinyar gidan sai yafi jin labarin kamar shine ainahin na gaskiya. Daɓar Hajiya Mammah ta kai a kujera, yayinda Malika da Azizat suka fasa ihu a tare. Da ga ƙarshe ma Azizat zubewa tai a wajen wai ta suma.....
💥💥💥💥
Wani irin kallo take ma jikinta da Commondo dake a gefenta kwance. Bama tasan lokacin data fasa ihun masifa ba a kanshi. Firgigit ya tashi fuska a yatsine. Kafin cikin jin haushi ya ce, “Haba Lawy baby, miyyasa kike abu kamar wata ƙaramar yarinya. Ina barci na mai daɗi da nishaɗi kin wani tadani”.
“Nayi ɗin, amma baka da hankali ko? Mika mun?”.
Dariya ya kwashe da ita harda ƙyaƙyƙyewa. “Ka jimun ƴar iska. Mi kika kawo kanki na miki dai. Naga keda kanki kika dinga jawoni kina roƙon nayi. Shegiya kinji mazan ƙwarai ko. To miye ma in nayin, naga dai har yanzu matata kike. Kona sake ki ne? Karki manta da aurena kika je kikai aure. Dan haka inada hakki a kanki. Yanzu ba gashi kin tashi fresh ba, basar kawai hajjaju kije kiyi wanka muzo mu tattauna abinda ya dace kafin shegen tsohon nan yasan ina mahaukaciyar matar can take. Dan mune yafi cancanta mu samota mu haɗa da Mu'azz dan uban Maash tsoffinsa duka na hannunmu ai dole ya bamu abinda muke so.”
Takaicinsa ne ya hanata yin magana. Batare data tanka masa ba ta miƙe ƙawai ta hau saka kaya. Shiko dariya kawai yake kwasa ta wulaƙanci. Fuuu ta fito a ɗakin sai jin tashin motarta yaji. Baki ya taɓe dan ko'a jikinsa, shi dai ya samu abinda ya ke so. Kuma ya jisa fiye da yanda yay fata. Ya kuma san da kanta zata dawo dan yanzu a tafin hannunsa take neman mafita kawai ce hanyar binta....
✨✨✨✨
“Isma'il lafiya na ganka haka kamar wanda aka koro?”.
“Humm oga am sorry, ai badan ma na riƙe kaina ba zaka iya ganina a fiye da hakan. Tabbas Maash yana gari, dan daga wajensa nake yanzu. Anya mutumin nan bashi da aljanu? Shifa aka nuna bashi da lafiya a asibiti sannan da kunne na naji prof.. na zancen yasa a yanke wutar gidan da yake da network da ruwa, aka kuma zagaye gidansa da jami'ai. Kuma yana da tabbacin yana a cikin gidan fa. Kuma mu kammu mun tabbatar ya shiga Dubai a shekaran jiya. Amma gashi yau alamu sun nuna a Nigeria ya kwana. Wlhy ni a karan kaina da nake amsa sunan jami'in tsaron sirri al'amarin sa ya fara bani tsoro. Irin waɗan nan ne idan suka zama cikin jami'an tsaro suke aiki mai ban mamaki, idan kuma suka kasance criminals suke mummunar ɓarna dan suna da matuƙar wayo da fiƙra. A yanzu haka bana raba ɗayan biyu dama yasan da shirin duk za'a masa haka a Dubai ɗin shine ya basu ƙafa, dan ya tabbatar min yasan inda mahaifinsa yake ma”.
“What?!”.
“Wlhy oga haka yace ya sani, kaga tabbacin duk motsinsu kenan yana sane. Sai dai abinda ya ɗan ruɗar da ni anan prof ba shine yay kidnapping Alhaji Mu'azz ba, kuma bana jin Maash ɗin zai yi hakan saboda kisan da akama drivern. Anya kuwa matar nan ko Commondo ɗin nan basa cin dundumiyar prof ta ƙarƙashin ƙasa?, dan bana raba ɗayan biyu Alhaji Mu'azz na hannunsu”.
Nannauyan numfashi ogan nasa ya sauke dan tabbas maganar yaron nasa abar a duba ce. Idan kuwa haka ne lallai wannan wani point ne da zaisa su sami Commondo ko Hajiya Lawisa a hannu. Dan dolene su kama ɗaya a cikinsu. Lokacin da zai fara motsi shima yayi a garesa. Maganar ɓoye kai da ainahin matsayi ta ƙare. Sun cigaba da tattaunawa musamman akan takun da Maash ɗin yazo da shi. Shi kansa ogan nasa kai kawai yake jinjinawa da hatsabibancin yaron. Dan tunda suka fara aiki akan wannan case ɗin matsayin jami'an sirri da yawan bayanai shine ke basu kafin su su binciko. Dan ba ƙaramar gudunmawa yake basu ba akan aikin nan, hatta baza mutane cikin family ɗin shine ya bada shawarar da ƙirƙirarta. Kuma har yanzu bai san ainahin shine ogan ba saboda wani dalilinsa da ya barma kansa sani. Shi kansa Isma'il ɗin sai kwanan nan ya sanshi, kuma shima bai san ainahinsa ba balle alaƙar data alaƙantashi da Maash ta zahiri.......✍️
🤔To oga kai waye? Muma ya kamata mu sani ai koya kuka ce🤷?.
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚_
......Ba ƙaramin shock ta shiga ba lokacin da take shigowa gidan taci karo da duk ma'aikatan sun dawo gida. Ga batun auren Maash da Samraah zance dai ya fito. Ko kallon inda Baba prof yake batayi ba. Ita ta duba Azizat tai mata allura aka maidata ɗakinta. Tana ƙoƙarin tashi ta shige ƴan sandan dake bincike akan ɓatan Paah suka zo gidan kusan tare da Uncle Abdullahi da ya fita. An samu wayar Paah da sukai tracking, sun sameta a gaba kaɗan da inda aka sami gawar drivern sa, da alama an yardata ne daga baya. Dan a yanzu haka suna kan yin wani bincike na duk inda aka shiga da wayar a jiya kafin a yardar da ita suna fatan samun nasara. Sannan an samu sayin yatsun hannu har na mutum uku a jiki shima suna kan bincike, shiyyasa zasu bibiyi duk inda yaje ɗin...”
Tamkar jira Baba prof keyi cikin nuna jin daɗi ya ce, “Idan ko hakanne officer ya kamata a fara da duka sayin yatsun hannayenmu mu da muke gidan nan, tunda daga nan ya fita zuwa gidana. Can ma kuje ayi komai yanda ya dace kafin shegun su farga su ɓadda sawu” ya ƙare maganar yana wani sakin murmushin mungunta da kallon sashen da Hajiya ƙarama ta ke. Da sauri ta gyara yanayinta tana mai watsa masa wani mugun kallo ta ɗauke kanta. Sai ya sake sakin wani murmushin da cije lips ɗinsa. A ransa yace (ƙaramar shegiya zanyi maganinki. Sai na dafaki a tsaye ai. Zaki tabbatar da ni Uban ubanki ne a iya hatsabibanci).
Ɗari bisa ɗari ɗan sandan ya yarda da batun Baba prof ɗin, sai dai yace zasu je su dawo dan babu kayan aiki a tare da su yanzu. Duk kuma wanda ya fita daga gidan zuwa kafin su dawo yana cikin suspect nasu. Daga haka suka fice.. Fitar tasu bai fi da mintuna ba wayar Hajiya Mama ta fara tsuwwa. Ganin mijinta yasata ɗagawa cike da zumuɗi. Duk idanu suka zuba mata. Wani irin miƙewa tayi cike da tsantsar farin ciki ta furta, “Alhamdullahi ALLAH mun gode maka. Yanzu haka kuna a cikin gidan nashi kenan?”.
“To Masha ALLAH muna zaman jiran ji daga gare ku, dan fatanmu kawai asan ina Awwab yake yanzun”. Ɗan jim tai alamar saurare kafin ta yanke kiran ta dubi duk wanda ke a falon da wani irin zaƙuwa ta ce, “Ana fatan samun Awwab a cikin gidan nan. Ashe an katse masa duk network da wutar gidan ne da ruwa. A yanzu haka Daddyn Irfan ya tabbatar min sunata shiga da fitar ganin an ɓalle ƙofofin gidan, idan har yana a ciki zuwa dare zasu taho Nigeria da shi”.
Wani irin makirin murmushi Hajiya Ƙarama ta saki tana kallon Baba prof da zufa ta gama jiƙema gaban goshi. Da yatsa ta masa alamar 1-1 tana kashe ido ɗaya. Sai kuma ta miƙe zumut tana faɗin, “Alhamdullahi, mun godema ALLAH”. Yanda tayi ɗin ya saka kowa maimaita kalmar Alhmdllh ɗin Maman Malika da Hajiya Mama harda rungume juna. Ita kanta Hajiya Mammah ta nuna farin cikinta duk da har yanzu batun auren nan na Maash ya kasa haɗiyuwa a wuyanta. Zancen Baba prof ne ya katse musu murnar tasu.
“Anya kuna ganin ya kamata Awwab ya dawo ƙasar nan babu iyayensa a gidan nan, babu matarsa, babu Fahad?”.
Gaba ɗaya murnar tasu ta koma ciki, dan gaskiya Baba prof ɗin ya faɗa.