Showing 207001 words to 210000 words out of 438336 words

Chapter 70 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2229

bayanin maido Samraah da sukai nan dan a cigaba da kulawa da ita duk da dai shi ba sunanta ya ambata ba ya dai ce yarinyar dake jiyya. Amma kuma yanata tunanin a ina yasan fuskar yarinyar ne tun ɗazun. Cike da girmamawa Hajiya ƙarama ta amsa musu. Tare da musu jagora har cikin manyan ɗakunan jiyyarsu na vip na ƙarshe a daraja. Kowa baiyi mamakin rashin biyosu da Maash yayi ba, dan sai da Baba prof ya koma da kansa ya masa umarnin bari a shiga da ita kasancewar tare ya tafi da nurses dake ɗauke da gadon ɗaukar mara lafiya. Amma mi, ammakinsu ma ko kallon inda Nurses ɗin suke baiyi ba yanzun ma ya sake ɗaukarta camak yay cikin asibitin. Da kallo kawai Baba prof ya bisa abubuwa da yawan gaske na masa kai-kawo. Dan a wannan gaɓar ya gama sarewa da al'amarin jikan nasa. Sai ma yake wasiwasi anya kuwa shine ya aikata fyaɗen nan kamar yanda Nafisa ta faɗa. Dan al'amarin akwai matuƙar ban al'ajabi a cikinsa da ma ban tsoro.
Acan daga ciki suma kansu kallonsa kawai suke kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa musamman ma Hajiya ƙarama da bata ga abubuwan daya faru a farko ba sai wannan ɗin. Dan baki ta hangame har sai da taji iska na kai mata har maƙoshi sannan ta iya haɗiyewa da ƙyar.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙_


......Baba prof da bai koma ciki ba Nurse ɗin nan ya aika yace a sanarma su Paah su fito yana jiransu. Babu jimawa kuwa sai gasu ɗaya bayan ɗaya. Hajiya Mammah da Mama Balki da Hayatu sai shi uban gayyar kawai aka bari. Dan haka Baba prof ya sake aika Uncle Abdullahi yace yay kiran Hajiya Mammah saboda sanin halinta shi kuma baya buƙatar jan wannan maganar a waje shiyyasa ma da Maash ɗin yace a bama yarinyar sallama bai tanka ba. Ya kumace a kawota nan ɗin ne tai jiyya dan yasan asirinsu zai kasance a rufe tunda dai Hajiya Ƙarama ta gida ce. Rai a ɓace Hajiya Mammah ta fito. Dan itafa gaba ɗaya an ɓata mata shirinta. Dan har magana ta gama da waccan likitar akan ta riƙe Samraah har sai nan da wasu ƴan kwanaki da za'a iya fahimtar da ciki ko babu. Idan akwai ta fallasa a gaban kowa, idan kuma babu zata biya ko nawa ne aima Samraah dashensa sai kowa ya gama sani sannan ta tafi plan na gaba da za'a zubar da cikin wajen zubarwar a kashe Samraah. Sai kuma gashi cikin abinda bai wuce awa guda ba shegen yaron nan daya zame mata masifa da bala'i ya hanama rayuwarta rawar gaban hantsi tun yana mitsitsinsa ya rushe komai. Suma waɗan nan ƴan human right ɗin sai taci abu takazansu dan sun mata aiki ba'a yanda tace musu ba. Idan kuma basuyi himmar ƙarasawa ba ALLAH sai sun biyata maƙudan kuɗinta...

A ɓangaren Maash kuwa bai bar asibitin ba sai da aka gama yima Samraah dukan abinda ya dace. Duba magungunanta da sake bincikata in and out. Sai dai kuma anan ɗin ma dai doctor ɗin data duba Samraah ɗin dan ba Hajiya ƙarama bace saboda ba faninta bane. Abinda ta fara bincike da tambaya shine reping ɗinta akayi ne?. Shiru Maash bai tanka ba, bai kuma da alamar tankawar. Dan haka Mama Balki ta girgiza mata kai alamar a'a. Rasa abin cewa tayi, dan dukkan alamu na jikin Samraah ya tabbatar da anje mata babu tausayi. Amma tunda ita Mama Balki tace ba haka bane sai ta tambayi mijinta, acewarta tana son ganinsa taji dalilinsa na nuna irin wannan rashin tausayi akan yarinya ƙarama. Kasa sake cewa komai Mama Balki tayi, sai ɗan satar kallon Maash ɗin da take ta gefen ido. Shi kuma yay masifar haɗe girar sama data ƙasa dan haka doctor ta haɗiye maganganunta a cikin rai dole.
Ruwa tasa aka sakama Samraah dan tana buƙatarsa. Kasancewar akwai cannula ɗin wancan asibitin da ba'a cire ba sai hakan ya sauƙaƙa musu. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa barcin ya fara ɗaukarta dan shi dama suke buƙata tayin. Kiran wayar da Paah ya addabesa da shi ya sashi miƙewa cikin ɗan ɓacin rai sai dai bai ce komai ba bai kuma ɗaga wayar ba. Ƙofa ya nufa abinsa batare da yayima ko Mama Balki sallama ba.

Dishi-dishi nake ɗan hangosa, cikin mayen barcin dake ɗaukata a hankali batare da tunanin zai ma jini ba na furta, “Dan ALLAH ka dinga duba min Ummie akai-akai da bata abinci da maganinta. Kace kuma ina gaishet....”

Cak ya tsaya daga yunƙurin fitar da yake yi, hannayensa duka a cikin aljihun wandon suit ɗin nasa. Tamkar mai ciwon wuya ya juyo da kansa a hankali ya zuba su a kanta. Idanunta masu cikar gashi dake a ɗan kumbure har yanzu a lumshe suke. Kallon kusan minti ɗaya yay mata ciff kafin ya motsa a hankali cikin tafiyar nan tasa tamkar baya so ya fice. Da kallo Mama Balki ta bisa, sai kuma ta saki murmushin da har haƙoranta suka bayyana. A hankali ta furta, “Humm Alhaji Ƙarami”. Sai kuma ta juya ta zubama Samraah da har ta fara sauke munshari idanun nata. Shigowar Hayatu ne ya katseta. Sallama yay mata dan yasan ba lallai yau ya samu damar sake shigowa asibitin ba tunda suna tare da boss. Gashi ma acan office jiransu ake sakamakon meeting da yasa Juliet ta tara na gaba ɗaya exco ɗin companynsa na cikin Lagos dama wajen Lagos masu alaƙa da abinda ya faru. Ya kuma tabbatar dole meeting ɗin zai jasu lokaci mai tsayi....

🌺🌺🌺🌺🌺

“Magana ta gaskiya sai kun kula Attahir. Kun fa san Hajiya nada hawan jini. Yanzu badan ALLAH ya taƙaita ba a wannan faɗuwar da tayi fa komai zai iya faruwa. Dan ɗayan biyu ne. Paralysis ko heart attack. Saboda a kwanakin nan bincikenmu ya nuna zuciyarta na samun matsi sosai da yawan damuwa. Dan haka dan ALLAH ku kula. Zamu riƙeta anan zuwa 2days, ga wannan sai kaje konan pharmacy na asibiti ka samo dan data farka za'a buƙacesu”.
Numfashi mai nauyi Attahir ya sauke tare da jinjina kansa. Kafin a hankali ya ɗaura da yima doctor ɗin godiya sannan ya miƙe. Tafiya kawai yake amma shi baima san a inda yake jefa ƙafa ba. Dan shi a karan kansa yana buƙatar gadon ne a wannan gaɓar. Da ƙyar ya iya kai kansa pharmacy ɗin cikin asibitin ya miƙa musu takardar da doctor ɗin ya bashi kawai. Koda pharmacist ɗin ya duba ya sanar masa kuɗin baima bi takansa ba ya zaro ATM ɗin sa a wallet kawai ya miƙa masa. Hakama da aka saka adadin kuɗin bai wani dubaba ya amsa ya saka pin ɗinsa. Ledar ya amsa ya koma ɗakin da aka kwantar da Mamy.

Har dare yay nisa babu Dad babu Mansoor. Babu kuma wanda ya kirashi koda sau ɗaya yaji yaya Mamyn take. Haka ya kwana cikin asibitin shi kaɗai, sai a washe gari bayan sallar asuba yana fitowa a massalaci fita yay a asibitin dan likita ya tabbatar masa Mamy zata iya kai sha ɗaya ma bata farka ba. Kai tsaye gidan ƙaninsa na ɓangaren Ummie ya nufa. Kakarsu mace ta rasu, sai tsoho mai ran ƙarfe da ya ragema Ummie kawai. Bai tsaya kwana-kwana ba ya zayyane masa komai dake faruwa. Sosai hankalin kakan nasa ya tashi, Attahiru na gabansa ya shiga bugama sauran ƴaƴansa waya duk yace suzo yana buƙatar ganinsu. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa duk sai gasu, ALLAH ya taimaka ma abin ya haɗa da weekend. Sake saka Attahir yay ya maimaita duk abinda ya faɗa masa. Suma ransu yay matuƙar ɓaci da wannan hali na ƴar uwarsu. Tun tana budurwa sunyi matuƙar yaƙi na ganin ta ajiye waɗan nan banzan halayen amma a banza. Kullum shari'arta da miji bata wuce akan wannan halin na son kuɗi da ƙarya. Gashi nan dai sai da takai ta watsa farin cikin gidanta da kai wa matsayar da suka dinga guje mata sannan hankalinta ya kwanta. Itama autar tasu Sakeena zama da gurɓataccen miji ashe ya canja musu ita ta koma irinta. Ɗunguma sukai su duka harda tsoho zuwa asibiti suka dubata. Sunko samu ta farka, haka duk suka jajanta mata sama-sama. Gaba ɗaya kunya ta hanata iya kallon kowa a cikinsu musamman ma Attahiru. Nauyin yaron take ji, dan yanada matuƙar haƙuri da kawaici. Duk irin banbancin da take nunawa tsakaninsa da ɗan uwansa bai taɓa ɗauka ya sakama ransa balle har taga ɓacin ran hakan akan koda fuskarsa ce. Yau ga wanda take matuƙar nunama soyayyar ya tsallaketa ya wuce akan mace. Duk da dai tasan ita duk ta jawo komai, sosai take jin dana sani da nadamar ƙwaɗayayyar rayuwarta a yau.

Kwananta biyu a asibiti babu ko ƙyallin Dad. Tana son ta tambayi Attahir tana jin tsoron jin abinda bashi zuciyarta take son ji ɗin ba. Dan tana matuƙar so da ƙaunar mijinta. Hasalima kamanninsa da Mansoor ya ɗebo yasa take fifita soyayyarsa akan sauran yaranta. A ranar aka basu sallama. Tun da suka baro asibiti taga an ɗauki hanyar gidan babanta gabanta ke faman faɗuwa. Sai dai tsoro ya hanata tambaya har suka iso. Isowarsu babu jimawa suma su Amal suka iso. Dama suna Abuja gidan kawunsu ne. Sanda zasu wuce India su aka turasu can sai yau suke dawowa.
Anan ɗin ma babu wanda yace mata komai har tsawon kwan biyu, abu ya dameta amma itama tsoron jin abinda bashi take son ji ba ya hanata iya tambaya. Zuwan Sakina biyu gidan babu mai tankama wani ita da ita. Su duka sun ɗauki zafi da juna tamkar ba ƴan uwa ba jini ɗaya. Hasalima a baya sun fi shiri da juna matuƙa, dan rayuwar ƴammatanci gaba ɗaya Sakeenar a gidanta tayita ma..
Attahir dai yakan zo da safe kullum kafin ya wuce aiki ya gaisheta. Hakama idan ya tashi sai yazo nan ya gaisheta sannan yake wuce gida. Kamar wasa a haka kwanaki suka dinga tafiya tana a gidansu. Ga baba ma sama-sama yake amsa mata gaisuwa. Baya shiga sabgarta baya kuma bata damar shiga tashi har gata da watanni biyu cif a gida. Su Amal ma tuni suka tattara kayansu suka gudu gida. Dan sunce bazasu iya zama gidan Baba ba saboda gidansu komai najin daɗin rayuwa suna da shi. Nan ko duk da ƴaƴan baban maza sun tsaya akan al'amuransa shima kasancewar matarsa ba itace kakarsu ba abubuwa da yawa sai a hankali kawai. Ta kankane komai daga ita sai nata jikokin Mamy ma sai tayi da gaske wataran take samun abinci a gidan. Dan ma Attahir baya gajiya da kawo mata kayan shayi da ƴan kayan maƙulashe. Amma itama da tuni yunwa ta kai rayuwarta ƙasa kam.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_


........Tun fitarsu a ɗakin jiyyar yarinyar har barinsu asibitin akan idanunta ne. Numfashi ta sauke mai nauyi tare da ture ɗan kwalin kanta baya. Dauriya kawai take da danne abinda ke matuƙar cimata zuciya. Wayarta ta ɗauka a ɗan zafafe, tai ƴan danne-danne tare da kaiwa kunnenta. Ana ɗagawa daga can ta ɗan sauke ajiyar zuciya. Sai kuma cikin ɗan farin ciki mai gauraye da sauran damuwa ta furta, “Sabon labari”.
Cike da zumuɗi daga can akace mata “Name fa Hajjaju masu Lagos da kayan cikinta.”
“Hummm Jannifer bar batun wasa Please. Yarinyar nan ce fa suka maido asibitin nan yanzu”.
“What! Kina nufin Samraah?”.
“Yess. Yanzu haka tana nan tare damu. Ban san miya faru ba suka maidota nan ɗin. Naga dai mutuniyarki a zafafe cikin matuƙar damuwa kuma. Yanzu kam na fara zargin akwai abinda take ƙullawa. Na kuma yi alkawarin sai na bincikosa a koma ina taje ta bizne shi”.
“Karki wani damu Hajjaju wannan duk mai sauƙi ne. Ko ni nan na isheta. Har mi akai akayi Alaja Nafee kuma. Matar da bata iya komai ba sai da shawaran banzan Madan Rubayya ɗin nan. Ni dai kawai yanzu shawaran da zan baki kawai kiyi ƙoƙarin ki kula da yarinyar nan da ƙyau, tunda dama tun farko kayanki ce. Kin zauna sakaci ne Alaja Nafee ta nema ƙwacewa. Banzama irinta da ta ƙare a ƙarƙashin guzumomi irin su Rubayya. Dan bana raba ɗayan biyu shakkar Rubayya ɗinne ya hanata taya yarinyar kafin ke, tunda itama ai mayyar ce. Saboda haka kiyi amfani da wannan damar akan ita yarinyar kiyita banka mata maganin da zai fidda mata sha'awar namiji gaba ɗaya a ranta, ina tabbatar miki da kanta zata kawo miki kanta tana kukan ki mora albarkacin jikinta. Haba Alaja Lawusa kamar baku bane Lagos ɗin. Ni fatana ma idan zakije honeymoon da ita aje dani koda a ƴar riƙon handbag ce”.
Dariya mai ƙayatarwa Hajiya ƙarama ta saki, tare da sake lume kanta a cikin kujera idanunta a lumshe tana siffanta cikakkiyar surar Samraah data jima tana birkita mata lissafinta. Dan tun randa Jannifer tayi kiranta ta sanar mata da zuwan yarinyar gidan matsayin gift da Mashi'a tai shirin kawoma Hajiya Babba dan ta kula da ita ta gama jin ƙaguwa da son ganin yarinyar. Saboda haka ta azalzali Paah suka dawo Nigeria washe gari badan ma sun kammala abinda ya kaisu ba. Koda suka iso tai ido biyu da Samraah sai da numfashina ya nema shiɗewa. Dan yarinyar irinsu ne ake kira da full option. Komai yaji yanda ya kamata. Sai dai kash abubuwa da dama sukai mata katanga da hakan, tayi ƙoƙarin riƙe kanta har zuwa sanda ta gama shiryawa sai kuma ga wannan abin ya faru da yay matuƙar ƙona mata rai, dan a yanzu haka ita kaɗai tasan irin kalar zafin yaron nan Awwab da take ji a rayuwarta. Wani irin kishi take ji tamkar ta kashe banza a wuce wajen dan son Samraah take na gaske. Har ma ta gama yankema kanta shawarar auran yarinyar zatayi ta ɗauketa daga Nigeria zuwa duk ƙasar da take so sai ta dinga kai mata ziyara....
“Alaja!”.
Jannifer ta katse mata tunani. Firgigit ta dawo hayyacinta tana mai sauke nannauyan numfashi. Cike da basarwa taja ɗan sirrin tsaki da faɗin, “Sorry Jannifer na tafi wata sabgar ne kuma.”
Dariya Jannifer ta ƙyalƙyale da shi daga can, cike da shaƙiyanci ta ce ko dai kin tafi tunanin kayan alatu ba”.
Murmushi Hajiya Ƙarama tayi tana mai cije lips ɗinta. Kafin a hankali ta ce, “Ke dai Jannifer sheɗaniya ce wlhy. Lallai da ace bakiyi ridda daga musulimci zuwa kiristanci ba da ba ƙaramar sheɗaniyar matar hausawa musulma akayi ba. Amma yanzu mun bar musu, dan inba ma wanda ya sani ba taya zai taɓa yarda kin haɗa iri da fulani. Humm ALLAH dai ya jiƙan General. Ya tafi yabar baya da ƙura. Maybe da za'a shawarcesa a dawo da shi duniya yaga Munirra ɗinsa yanda ta koma kamar bata taɓa haɗa jini da yan arewa da musulunci ba da dakansa zai kashe kansa ma wlhy”.
“Hummm Hajjaju kenan masu Lagos da jama'ar cikinsa. Ai duk nawa wasan yara ne. Idan kuna guri mu kuma wake ta tamu ƙananun ƙwari. Mufa a riddar kawai muka tsaya sai ɗan cinikin goron nan da muke kafawa a faifai da ɗan hutawar nan muna more ƙuruciya. Ku kuwa fa, idan akace ai tone-tone ai kema musulman sai sun gwammace riddar kikayi wlhy”.
“Uhhm to ya isa. Dan ke baki gajiya da zakuɗe-zakuɗe. Yanzu dai sai anjima idan na tashi zan zo gida na sameki mu ƙarasa. Dan zan ɗan shiga theater”.
“Hummm” kawai Jannifer tace daga can tare da yanke wayar tana dariya. Itama sai Hajiya ƙaramar tai dariyar kawai tana ƙoƙarin ajiye wayar, a dai-dai nan wani kiran ya sake shigo mata. Ido ta zubama number na tsawon lokaci, YALLAƁAI ɓaro-ɓaro ya fito. Mamaki ya sake kamata dan rabon da mai number yay kiranta ta jima sosai, dukan tara-tara ƙirjinta ya shiga hi har sai da wayar ta kusa yankewa ta dawo a hayyacinta. Da sauri ta ɗauka tana miƙewa ta nufi ƙofar office ɗin ta murza key cike da rashin gaskiya....

_🤔Hummm wai ina matan nan suka dosa ne? Sannan waye yay kiran

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login