Showing 396001 words to 399000 words out of 438336 words

Chapter 133 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2187

cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._


........Har muka iso Nigeria ban shiga sabgarsa ba bai shiga tawa ba, koda yake ma ni barcina nasha sosai har muka iso. Su Fahad ne sukazo tarbar mu da Guards ɗinsa. Ɗan barcin da nayi yasa jikina duk babu wani ƙwari, dole na bari ya riƙo min hannu muka fito. Muna shiga motar ma idanu na rufe kawai har muka iso gida. Kafin kowa ya fito ni na fita, na shige jikin Ummie da Mama da suka fito tarbar mun. Faɗan yanda jikina ya ɗauki zafi amma suka taho da ni haka Ummie da Mama keyi. Falaq tace ai ban faɗama kowa banda lafiya ba fa, har Yaya Awwab bata tunanin ya sani. Kallonsa Ummie tayi cike da tuhuma. Sai maimakon yace wani abu akan hakan sai cewa yay, “Ummie good night”. Ya wuce warsa. Duk binsa sukai da kallo, na balla masa harara da murguɗa baki.
Babu wanda yace komai Ummie tace muma muje mu huta kowa tasa an kai masa abinci bedroom. Ni dai badan naso ba na tafi sashen namu, ɗakina kuma na shige, komai fes an gyara min, wanka kawai nayi abuna nai shirin barci. Yunwa nake ji amma bazanje ɗakinsa ɗibo abinci ba dan na fahimci can Ummie tasa aka kai. Sai nayi kwanciyata. Ko minti huɗu banyi da kwanciyar ba ya shigo ɗakin, ƙin motsawa nayi balle yama san idona biyu. Babu zato kawai naji an ɗaukan camak an fice. Watsal-watsal nake da ƙafafu ina kaima ƙirjinsa ƙananun duka da faɗin, “Ni ka sauke ni, ALLAH zan maka ihu”. Ƙin kula ni yay yaƙi kuma cewa ko ci kanki har sai da ya kaini bedroom ɗinsa ya dire a gado. Kuka na fara masa yaƙi kulani sai abinci ma da ya ɗibo ya dire a gabana.
“Ni banzan ci ba. Kuma ka buɗen ƙofa na koma ɗakina dan bazan kwana anan ba.”
Ƙafarsa ɗaya dogare da gadon ɗaya a ƙasa ya kamo haɓata yana mai ranƙwafowa kaina. Cikin wani ɗan iskan salo idanunsa sarƙe da nawa a saman lips ya furta, “Garama kici, dan rashin cin bazai hana na nema hakkina ba. Ɗaki kuma na ɗaureki ne?”. Ya ƙare maganar cikin ɗage gira. Baƙin ciki yasa ni kaima hannunsa wawura zan ciza. Ai babu shiri ya janye jikinsa da waro idanunsa waje. Na balla masa harara da murguɗa baki na ce, “Da ka tsaya mana”.
“ALLAH ya shiryeki”.
Ya faɗa yana tura hannayensa duka cikin aljihun wandon pyjamas ɗin sa. Baki na tura da jawo abincin na hau ci ban sake kulashi ba. Ina jina nayi dam na sauka nayo brush. Gadon na haye nai kwanciyata ban kulashi ba. Shima baice min komai ba yana zaune yana kallona kawai. Cikin barci na jisa a gefena ya sakani a jikinsa. Sai kawai na sake shigewa nima. Da safe kuma ba kunya na ɗora da fushina nama bar masa ɗakinsa sai a sashen Ummie muka haɗu wajen breakfast...

Shirye-shiryen biki sun kankama sosai. Muna shirin wucewa Kano saboda Ummie tace gara kawai muje can ɗin ayi komai tunda muɗin duk anguna ne. Hakan yamun daɗi sosai. Dan har gyaran jiki nake son muyi aunty Zakiyya ta gama shirya mana komai. Har yanzu ni da mutumina dai ana ƴar share juna. Sai dai shifa hakan baya hanashi zuwa yasha bidirinsa a jikina. Duk kukan dazan masa kuma bazai kulani ba. Randa su Ummie zasu wuce Kano sai ya nuna wai suyi gaba ni daga baya zamu taho tare da shi. Aiko na sanya kuka sosai. Harararsa Ummie tayi, amma ya fiske abinsa yaƙi cewa komai. Daga ƙarshe ma ya tashi ya fita a falon dama muna a babban falo ne mu duka. Zan ɗaga hankalina Ummie tace karma na damu kaina na barta da shi. Ban san yanda suka ƙare ba washe gari muka wuce da su Ummien. Mun isa Kano cikin aminci, bamu wani zauna ba muka hau gyaran jikinmu dan nan ƙanwar mijin Aunty Zakiyya tazo ta same mu. Ta kuma zuba mana wani shegen lalle daya amsa suna lallale tamkar ka cinyesa saboda ƙyau. Da dare sai ga su Fahad da ɗinkunanmu. Nayi mamaki sosai dan ni bamma san an kai ba. Ashe wannan aikin Ummie ne. A ranar da yamma dole naje can gidan Abba ni da Aunty Falaq. Can ma dai shirye-shirye sun kankama. Dan su Gwaggo Gudidi na gidan ita da aunty Halima ke komai. Wai Mom taƙi shiga tace tun farko ai ba'aso a ganta a ciki ba tunda ba'a sakata ba. Kobi takanta banyi ba ma ni kam yau dan al'amarin nata ya fara bani takaici. Muka zube musu kuɗaɗe masu yawa ni da Falaq domin amfani. Hakama Abba mun bashi isasun kuɗi da zai yi hidima, sai ya kama hawaye yana sanya mana albarka. Bamu baro gidan ba sai da muka tabbatar duk wata ɓaraka mun toshe kayarmu duk da Yaya Awwab yace zai ɗauki nauyin komai muma yana da ƙyau dai aga zabuwa da zanenta kawai. Yaya Musaddiq ma dai komai normal, dan shine ma ya dawo damu gidan tare da TJ ya gaida su Ummie da musu barka da zuwa. Gefe Ummie ta jashi da Mama Balki da Baba suka tattauna abinda bamu sani ba, ko faɗan aure aka masa kuma oho mudai an ware mu. Ummie ta kawo akwati guda ƙatoto na ɗinkunan biki data musu komai iri ɗaya sai color kowa da wadda yake so shi da Fahad nacin amarci. Jinai gaba ɗaya mutanen nan nama rasa mizan ce dasu a rayuwa...

Washe gari gida ya fara amsar baƙi. Wasu a ɓangaren dangin K/mashi suka iso. Sai dangin su Mama Balki da suka nuna kara. ALLAH sarki Ummie duk da itama nasan tana son taga a irin wannan ranar a nuna wasu tawaga matsayin nata dangin na uwa da uba amma bazaka taɓa ganin damuwar hakan a fuskarta ba. Ta rungume duk wanda yazo a matsayin nata na jini. Can ma su Hafiz sun sanar min ƴan Gwarzo nacan cike da gidan Abba. A daren ranar su Yaya Awwab ma suka iso. Kasancewar isowar dare sukai ni har namayi barci, sai da asuba na ganshi. Idanu na zuba masa ya wani ɗage gira irin na kallon fa. Baki na taɓe da faɗin, “Miye ma abin kallo anan mutum duk tsufa ya taso masa”.
Hannu ya kai zai cafkoni na fice da ɗan gudu ina masa gwalo. Ya jinjina kai alamar zan kamaki ɗin nan. Ban sake zuwa inda yake ba dan mun zama busy. A ranar muka kai lefen Bahijja, daga can muka wuce gidan Abba kuma zamu kai na Yaya Musaddiq tare da iyayenmu dake jira dan tun jiya da dare akwatinsa na gidan Abban. Mun samu cakwakiya a gidan, ashe kawo wannan kaya ya birkice Mom nata tsiya harda su gori. Abu kamar wasa har Abba ya mareta, kaɗan ya rage ai ɗanyen aiki ya saketa Gwaggo dai ta dakatar da shi ALLAH ya taƙaita. Shine ta shige ɗaki ta rufe kanta. Bata buɗeba sai da Ummanta tazo. Sai kuma sukaga an kawo likita alamar dai akwai damuwa. Amma ba'ace musu komai ba. Oho muma dai bamu matsawa kammu sai mun sani ba muka tafi kai lefe. Tarba muka samu acan ma ta girmamawa, yayinda gidan su Ruƙayya ya rikice da ganin lefen nan kamar yanda dangin Bahijja sukai murna. To da yake su sun fisu ƙarfi, itama kuma Ruƙayya irin rayuwarmu tayi a hannun kishiyar uwa sai abin nata yafi ɗaukakuwa. Dan can ɗin ma wata drama ɗin muka gani da tafi ta Mom. Matar baban Ruƙayya harda su suma sai da aka yayyafa mata ruwa. Kai jama'a kowane gida dai akwai irin waɗan nan ashe. ALLAH ya ƙyauta ya tsarkake mana zukatanmu. Haka dai muka barosu akan sai yamma kuma an haɗu, wajen kamu dan ranar za'ayi a hall ɗin da Ummie ta kama kasancewar dai komai za'ayisa a tare ne domin sauƙaƙama juna kai-kawon.
Muna dawowa gida babu zama. Shirin kamu aka fara, ni da Aunty Falaq muka koma can gidan. Mun dai zama busy body abin tausayi. Acan ɗin ma ba zaman mukayi ba. Shirin tafiya kamun da ɗan abinda baza'a rasa ba mukayi kafin cikar lokaci. Bamu sami su Yaya Awwab a gidan ba. Ni sai hakan ma yamun daɗi, dan in yana nan wani abun zai iya cewa bazanyi na wahalar masa da yarinya ba. Sai da muka kammala shiri ne ina zaune a ɗaki ina shan complex ya shigo. Daga ni har bowl ɗin dana haɗa complex ɗin yake kallo. Ni dai na masa sannu kawai na cigaba da shan kayana dan har yanzu ba'a wani shirya bane gaba ɗaya. Kamar zai shareni shima sai kuma dai ya magantu.
A daƙilen nan nasa yace, “Babu abinci a gidan ne?”.
“Akwai mana”.
“Shine kike shan wannan shiriritan bayan kin san bake kaɗai bace. Zama da yunwa ko. Aiko zaki nutsu waje ɗaya dan dama wannan kai-kawon ya fara isata. Gaba ɗaya kun maida kanku daga nan zuwa nan kamar kun manta ma akwai aure a saman kanku. Jiba fita zakiyi amma kin zauna har ana miki wani banzan makeup a fuska. Irin ma kin maidani shashashan nan da ban san ciwon kaina ba kowane banza idonsa akan matata......”
Gaba ɗaya na zuba masa ido kawai dan ya rikice sai masifa yake. Fahimtar neman dalilin da zai sa ya hanani fitar nan yake yasa yau ni na sauke tawa zuciyar. Dan kishi tsababa a kan fuskar bawan ALLAH zai hau min bori. Haka dai yaci ya tsire ni dai na daure dan in ALLAH ya yarda bazai samu sanadin hanani rawar gaban hantsi ba. Ina ganin ya shiga bathroom sum-sum na kwashi abubuwana na gudu wajen su Ummie. Banko sake yarda mun haɗu ba har muka tafi. Sai a hanya naga ran aunty Falaq a ɓace itama nake tambayarta lafiya.
Kamar zatai kuka tace, “Yaya Hayat mana. Su duk yawon da suke kana jurewa amma yau kishi ya rufe masa ido sai jaraba yake mun wai dan mi zan yi kwalliya haka alhalin fita zamuyi. Na masa bayanin wajen nan babu maza sam duk matane fa, hatta da masu video mata ne. Amma sam yaƙi fahimtata. Daga ƙarshe ma wai wlhy na damesa da tsari nabar ganin bikin Yayyena ne sai ya hana yaga abinda za'ayi. Shine kawai na masa shiru nidai ALLAH ya taimaka kikazo kika kirani na samu na fito”.
Rasama mizan ce nayi, dan al'amarin nasu sai naga kamar wani haɗin baki. Shi wancan da bamma gudu ba ban san a wace matsaya nake ba yanzu. A hakan ma nasan yana can fam ALLAH yasa kada ya fanshe a gobe wajen walima da kuma dinner da sai anje Lagos za'ayita ita. Hakuri kawai na bata naja bakina nai shiru.......✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒇𝒊𝒗𝒆_


.......Wajen kamu ya matuƙar ƙayatuwa. Ya kuma tara mutane fiye da zaton mai zato. Dan ta kowanne ɓangare amare da angunan ƴan dangi ne. Babu wani hayaniya masu kiɗan ƙwaryane aka ɗakko sai mawaƙiyar nan khairat da taima amare da angunansu waƙar aure. Mufa mune amararori, tako wane ɓangare akwaimu. Shigowar amare hannayensu riƙe da juna cikin shiga iri ɗaya komai ya sake kankama. Bayan an kaisu har masaukinsu aka buɗe taro da addu'a kafin a fara abinda ya tara mutane. Dan so ake kafin magrib dai in sha ALLAHU a kammala kada a tauye hakkin kowa. Ko maƙiyi yaga wannan kamu yasan yay matuƙar ƙayatarwa. Alheri tv sun nuna komai live, sai wasu gidan tv da aka gayyato daban sai kuma masu ɗauka a wayiyi dan yanzu kowa ya zama mai ɗaukar hoto da video sai dai addu'a. (ALLAH ya hanamu ɗakko abinda zai zame mana damuwa wataran🙏).
Tiɓis muka koma gida ga kaina na ciwo. Kai rainon ciki ma dai sai addu'a. ALLAH ya ƙarama iyayenmu rahama da gafara. Samun oga na gida ya sani jin shakkar shiga ɗakin, sai da ya fita Masallaci na lallaɓa na shiga. Kafin ya dawo har na kwanta. Koda ya dawo kuma saina lafe kamar mai barci, dan ni kaina nasan na taro Match. Washe gari aka tashi da shirye-shiryen ɗaurin aure. Tako ina gidajen a ɗinke suke da ƴan uwa. Duk da ina son tafiya cikin ƴan uwana haka na daure. Baƙin daketa shigowa daga sassa daban-daban dan gayyatar ɗaurin auren nan ta zaga fiye da inda ba'a zato, auren ƙannen Maash ba wasa ba, tun daga sallar asuba bai dawo gida ba sai kusan sha biyu. Ina ɗakin ina shirin ya shigo. Gaishe shi nayi dan da safe bamu gaisa ba. Ciki-ciki ya amsa kamar yanda yake yi ƴan kwanakin nan. Kamar na watsar da shi sai kuma na tambayesa na kawo masa tea? Dan nasan bai ci komai ba har yanzu. Idanu ya zuba min sosai yana kallona. Nima kallon nasa nake yi, sai kuma na janye ina ƙoƙarin wucewata. Cak na tsaya sakamakon riƙonin da akayi, kafin ma nace wani abu ya jawoni ya zaunar saman jikinsa ya rungume. Daga ni har shi ajiyar zuciya muka saki masu ƙarfi. Cikin kunnena ya furta, “Ni na gaji da wannan faɗan haka nan”.
Maimakon bashi amsa sai kawai na sakar masa kuka. hawayen da suka cika min ido suka shiga gangaro min suna sauka saman ƙirjinsa. Murmushi ya ɗan yi da har naji alamunsa. Sai kuma muka sake ƙanƙame juna sosai.
“Humm miyasa kike son bamu wahala. Gaba ɗaya kin zama mafaɗaciya.”
“To ba kaine kake sakani yin faɗan ba. Kamun laifi kuma ka fini fushi harda ringa mun mugunta.”
“Nima ai kin mun laifin, na shigo gida ina ɗokin zuwa na ganki kawai ki wani shareni kina gaida wani a gabana ni kamar baki san da ni ba. Kin san ko zafin da naji, da ƙyar na danne zuciyata ban hukuntaki ba”.
“Amma kaifa ka fara min laifin, sai kuma ka fini jin haushi. Ina fama da kaina ka tasoni babu shiri zuwa wata ƙasa. Babu tarba, babu kiran waya, ban ganka ba, da ga ƙarshe ma akace min ka wuce wata ƙasar irin ma ni bana cikin tsarinka ɗin nan. Na kiraka a waya baka ɗauka ba, baka biyo kiran ba kace min koda uzirine ya riƙeka baki sanyi a raina. Ka dawo kuma kana wani shashasha min ƙamshi. ALLAH naji ranar kamar na baro ƙasar nan ko'a ƙafa ne”.
“Ya rabba! Yanzu dai duk misunderstanding ne ya shiga kawai. Bayan Ummie na a duniyar nan kece mace ta biyu mai matsayin da babu mai irinsa a gareni Samrh. Gaba ɗaya abinda kike tunani ba haka bane ba......” tsaf ya zayyane min komai daya faru, tare da tabbatar min wayarsa lokacin a Dubai ya manta ta tsabar hankalinsa ya tafi ga wancan uzirin, shima sai daya dawo a randa ma zamu wuce yaje ya ɗauka wayar a office daya barta yake ganin miss calls ɗin. Yayi niyyar mun bayani a jirgi yaga na sake tunzura har inama Juliet masifa.
Sosai na sake rungumesa da faɗin, “Kayi haƙuri, ni kawai na ɗauka tsabar muhimmancin harkokin ka ne suka fini. Ita kuma ALLAH bana sonta, taita maka wani iyayin banza. ALLAH wataran sai na karya mata ƙafafun nan kamar na sauro”.
“Trouble maker, kawai sai ki karya mata ƙafafu?. Yanzu ni dai tashi time zai ƙure, idan na dawo ma ƙarasa faɗan”. Yay maganar yana ɗaukata camak zuwa bathroom. Da kansa yay mun wanka nima na taimaka masa yayi. Koda muka fito a gurguje na fara taimaka masa ya shirya dan su Uncle Abdullahi nata kiranshi ashe har sun iso tun ɗazun. Matuƙar ƙyau yayi a cikin manyan kayan dan yau harda babbar riga. Ga gyaran fuska mai ƙyatarwa yasha. Haka na gyara masa gashin nan na ɗauresa sannan na saka masa hula ta yanda ba'a ganinsa. Ni kaina bamma san lokacin dana furta masa, “Mijina kai ƙyaƙyƙyawane”.
Wani silent murmushi yay da jan kumatuna ya kashe min ido ɗaya da faɗin, “Duk ƙyauna na kai wannan SARAUNIYAR MATAN”.
“Uhm, saika sa mata sun zaneni ta ina na zama sarauniyarsu?”.
“A fadar Muhammad Awwab mana”. Ya faɗa cikin soft murya da sumbatar lips ɗina. Ya kuma ɗan duƙa ya sumbaci cikina da ya fito sosai ɗan kif

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login