Showing 420001 words to 423000 words out of 438336 words

Chapter 141 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2205

dake tsaye ta dogare jikin sandarta da tana riƙeta ne badan ciwo ba fuskarta da murmushi ta ce kwantar da hankalinki Marka Hussaina ce dai ba wata ba. Tare da dukkan zuri'ata.” ta juyo tana nuna mata mu. Binmu da kallo Markan take jikinta na ƙara ƙarfin rawa. Zeenat babbar ɗiyar Uncle Sulaiman da autansu Ahmad suka shimfiɗa tabarma. Batare da an bamu izini ba muko duk muka zauna. Sai Yaya Awwab ne kawai a tsaye da Hayatu da Attahir. Dama nasan shikam bazai zauna ba, dan wani ɗan iskan kallo ma yakema Marka. Dama Ya faɗa min sai fa yaci ƙaniyar matar a daren jiya. Amma naita bashi haƙuri tunda ance ma ta tsufa miya rage mata kuma. Bai dai ce min ya haƙura ba, bai kuma cemin zai aikata ɗin ba. Tiryan-tiryan Mammi ta dingama Marka bayanin mu. Dan hatta shi Uncle Sulaiman ɗin ta jima bata gansa ba. Tunda ta samu Baba mahaifin su Mammi yasa ƴan doka suka saketa bata sake gigin zuwa ko hanyar Kano ba. Ana sanar mata Ummie ɗiyar Rabi'ah ce ta fashe da kuka da kiran ta shiga uku. Ballema da aka nuna mata su Maash kuma sai fitsari kawai mukaga yana binta. Bature matsayin jikan Rabi'ah da Maimoonatu ai kasheta ma kawai zaiyi yau. Da ƙyar aka samu ta nutsu. Yayinda Maash yaja tsaki cikin gurɓatacciyar hausarsa ya ce, “K mima za'a kashe anan ƙazama kawai. Ki jira mai miki hukunci yana nan a madakata ke da ire-iren ki yana jiranku. Ganinmu anan ma kawai ya isa miki aya tunda wayonki ko dabaranki da baƙin halinki bai hanamu zuwa duniya ba. Harma ga ƴaƴayenmu nan tafe in sha ALLAHU”. Daga haka yay ficewarsa a gidan. Attahiru da Hayat suka bisa. Yayinda Fahad ya ƙare mata tanadi shi da Jabeer ɗan Uncle Sulaiman. Dan shima kusan halin nasu ɗaya da Fahad ɗin. Gashi basu wuce sa'anni ba. Haka dai muma muka fito muka barta tana kuka da faɗin ta cuci kanta, ga shi nan kowa ya gujeta, sai ta kwana ta yini bata ci abinci ba, ba'a bari yara su shiga inda take ance ita mayyace ta cinye yaran kishiyarta. Babu wanda yafi yakanta sai Ummie ce dai harda ajiye mata kuɗi....

Koda muka koma cikin kano tattare komai akai aka ajiye gefe aka kuma shiga hidimar bikin su Mansoor da har yanzu ni da shi bamuyima juna magana ba. Sai dai nakan kamashi yana kallona lokaci-lokaci. Ɗauke kaina kawai nake tamkar ban gansa ba. Kasancewar Ummie gaba-gaba a bikin ya tilasta mana kasancewa muma. Dan ita tana can ma ta tare cikinsu ko sau ɗaya batazo nan ta kwana ba. Ina son zuwa gidan Abba na gaishesu amma sarakin nawa ya hana. Wai duka yaushe aka rabu, ya kuma hanani na kira kowa na sanar musu muna gari. Sai Hafizzullah da yazo nan ya samemu, sai da ya sanarma Hafizzullah ɗin ma kada ya faɗama kowa. To bama can ɗin kawai ba, ranar kamun amaren su Attahiru ɗin ma hanani zuwa yayi, sai washe garin ɗaurin aure shima da ƙyar har sai da na masa kuka. Abin ya konan rai amma na sharesa.......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏_


Follow this link to join my WhatsApp group:

https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq


*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.

*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._



.......Ana kammala ɗaurin aure kuma sun shigo gidan nace wai na zo mu wuce gida. Aiko bai ƙwalƙwal da idanu zan masa kuka Ummie tace ya barni mana. Ransa a ɓace ya ce, “Ummie tazo kawai mu tafi, itada bata da isashen lafiya ma. Bana son nayi wani abinda za'ace banyi dai-dai ba a dangin nan naki”.
“Ban gane ba, Muhammad mi dangina suka maka?”.
“Ni basu min komai ba, wannan yaron ne duk inda matata tai idonsa a kanta. Bana son na tsiyayar masa da ido ace nayi ba daidai ba. Idan kuma aka cigaba da tafiya a haka ALLAH zan aikata”.
Cikin mamaki Ummie ta rasa wama yake nufi, Ni kuma sai yanzu na harbo jirgin nasa. Oh ALLAH kishi da Mansoor kuma. Mutumin da ko magana ma bamuyi ba. Hayatu ne dai yama Ummie bayani a taƙaice, sai kawai ta girgiza kanta tana faɗin to ALLAH ya shiryeka Muhammad, kadai tuna yanzu shi Uncle ɗin ka ne, dan ƙanina ne. Ni dai wannan kishi naka ban san ina zai kaika ba. Sai kuyita tafiya”.
Babu kunya kuwa ya jani muka tafin, ganin haka sai aunty Falaq ma kawai tace ma Yaya Hayatu itama zata koma. Da dare akai dinner, sai dai ni bamma je ba, shima kuma hakan babu inda yaje. Washe gari ma yake sanarma Ummie abu ya taso masa zai wuce. Yana ganin kuma har dani. Ɗan jimm Ummie tai kafin tace, “Amma dai Muhammad yarinyar nan dake fama da tsohon ciki ina zakaje da ita hakane?. Sannan jibi Hafizzullah da Fahad da Matarsa zasu wuce. Haka zaku barmu gida shiru dan ALLAH”.
“Ummie Please mana. Ba kince da Mammi zaki tafi ba da kuma yaran Uncle har su biyu, ga kuma yaran nan suma ƙannin Attahir. Na miki alkawarin zan kula miki da ita. Da watan haihuwar ya kama zan dawo miki da ita. Bafa nisa ma zan miki da ita ba nan Dubai ne kawai Please”.
Badan Ummie nazso ba ta barmu. Harga ALLAH nima naji daɗin hakan, dan ina son Ummie da Paah su more abinsu. Hakan kuma bazata kasance ba sai idan mun gusa daga gidan. To ashe Hayatu ma ɗauke Aunty Falaq zaiyi su wuce. Zasu je can China akwai aikin da zasuyi shi da Yaya Musaddiq..
A randa muka dawo Lagos a ranar Paah ya kawo result ma Ummie. Alhamdullah komai lafiya lau, babu wata matsala da zata hanasu kasancewa tare. Ummie harda kukan daɗi, uban gayyar dai bai tanka ba. Garama Fahad ya ce ALLAH ya kiyaye gaba, daga haka ya tashi ya fita abinsa. Mun san duk sai a hankali zasu manta da komai, dan bazai yiwu a lokaci ɗaya ba dama. Shi dai Paah ɗin ma murmushi kawai yayi.

★Rayuwa ta sake canjawa daga wani aji zuwa wani. Dan kuwa kasancewata daga ni sai Yaya Awwab a Dubai wani ajine na karatu mai faɗin gaske. Wataran daɗi wataran saɓaninsa, dan mun sake fahimtar halayen juna kamar kowa waɗanne ma'aurata. Kulawa dai Alhamdullah ina samunta daga garesa. Hakama yaron cikina. Dan akwai aikin companyn da yake yi anan Dubai ɗin shine ALLAH ya taimakan ya kasance waje ɗaya. Sai da mukai sati biyu nama damesa da ko zai kawo min Bibaa saboda idan ya fita gidan kuma babu daɗi. Da yaga na damu sai aka samo min wata mai aiki balarabiya. Alhamdullah sai nake jin daɗin zama da ita. Dan mutuniyar kirkice ga amana da addini. Sannan tana bani shawarwari sosai akan rainon cikin nan. Muna waya da mutanen Nigeria, musamman ma su Ummie kullum ne babu fashi sai nayi waya dasu fin sau uku ita da Mama balki. Hakama su Aunty Falaq da Yaya Musaddiq da Aunty Ruky kuma ƙawa. Sai aunty Halime, Abba da Gwaggo Gudidi suma dai duk ana gaisawa. Ta ɓangaren Fahad da Bahijja da Hafizzullah ma dai hakanne. Dan har an gumtsa min gulma Bahijja na laulayin ciki. Itama dai Ruƙayya Aunty Falaq tace kamar taga an gamu fa. To muna dai zuba ido...

A gurguje Please 🥺


💦❤️💦❤️💦

Alhamdullahi na shiga watan haihuwa. Gaba ɗaya kammani sun canja. Kullum wayyo tako ina babu daɗi. Na mugun ƙibewa ko nace na kumbure. Ga masifaffen cin abinci ko cikin dare na farka sai naci. Tun yana mun dariya akan cin abincin har ya koma tausayina. Duk uzirinsa idan biyar tayi yakanyi ƙoƙarin ya dawo gida dan mu fita na ɗan tattaka. Idan kuma yayi busy da yawa ne sai Nasreen ta fita dani. Ta gefe guda Ummie ta damesa akan ya dawo dani gida. Hakama Mama da Mammi da har yanzu tana tare da Ummie. Itama dai Gwaggo Gudidi kullum ƙorafinta kenan. Ita bata son na haihu a ko ina sai Nigeria. Dan wanka zata mun cikakke na jego. Ni dai nasan tana faɗane kawai dan Yaya Awwab ba yarda zaiyi da batun tafiya wankan nan ba. Amma kada nayi magana tace nayi rashin kunya shiyayasa dai nayi shiru kawai. Matsin lambar da yake samu a wajensu yasa ya fara dai-daita abubuwansa dan mu wuce gidan. Sai dai kuma muna namu ne ALLAH yana nashi. Nashi ne kuma gaskiya. A safiyar yau na tashi duk dai babu daɗi, ga wata irin zufa da nakeyi kamar mai wanka da ruwa. Haka dai na daure na fita kitchen duba Nasreen dan mu haɗa masa breakfast. Saboda idan ban saka hannu ba bazai ci ba. Komi zatai gwanintar dafawa baya ci. Sai yace ya ƙoshi. Sai idan ya tabbatar nice nai girkin koda da taimakonta ne sannan zai ci, duk fa ma cin abincin nashi duk shiririta ne. Amma da yake yanzu ina dagewa ina kulawa yana ci fiye da da daya maida chocolates abinci. Itama ina shiga ta zuba min ido. Sai kawai na kauda kaina gefe ina tambayarta mi take ƙoƙarin haɗawa. Idanun nata har lokacin dai a kaina tace bata haɗa komai ba dama tana jiran fitowata ne. Shine nace mata kawai muyi abu mai sauƙi.
Mun fara girkin dai ta kasa daurewa. Cike da kulawa take tambayata kodai banda lafiya ne? Taga inata zufa alhalin kuma bamma fita motsa jikin ba yau. Dan taga ogane kawai ya fita. Murmushi yaƙe na mata kawai nace babu komai. Kawai dai ina jin zafi ne, maybe kuma dan muna a kitchen ne. Badan ta yarda ba ta barni muka cigaba da aikin. Can dai naji fa abin bana wasa bane ba, dole naja kujera na zauna ina cemata ta cigaba bari na huta. Haka na kife kaina a table ɗin ina ambaton sunayen ALLAH. Dan wani irin juyamin cikin keyi. Nafi mintuna goma a hakan sai ga door bell na ƙara. Nasan shine ya dawo, ni kuma ke zuwa buɗe masa a ƙa'idarsa. Amma sai na kasa, da ƙyar ma nace mata taje ta buɗe masa. Da to ta amsa min ta fita.
Bata wani jima ba sai gasu ita da shi sun shigo, shi ya fara shigowa ita kuma tana biye da shi. Nasan ganin bani na buɗe masa ba ya tambayeta, ita kuma ta sanar masa. A ɗan rikice ya ke faɗin, “Samrh kina lafiya kuwa?”.
Kaina na jinjina masa ina murmushin yaƙe. Ya ce, “Ban yarda ba. Diba yanda koke zufa kamar mai aikin ƙarfi. Tun fa ɗazun naga kikeyi amma kince babu komai. Gashi har kin kai zaune kimma kasa aikin. Kinga tashi muje asibiti”.
Da ƙyar nace, “Maybe fa juyi ne kamar na wancan karon”.
“Ba wani juyi oya tashi”. Ya faɗa cikin bada umarni babu alamar wasa a tare da shi. Fuska na marairaice masa zanyi magana ya katseni da faɗin, “Karma kice komai ta shi”. Baima jira cewata ba ya ɗagani, a haka muka fita. Munje tsakkiyar ƙaton falon ƙafa ta riƙe. Tun ina ɗagata da ƙyar ina cije baki har da na gagara. Dole na tsaya cak ina hura hanci. Sake rikicewa yay, ai sai kawai ya ɗaukeni cak yay waje da ni yana sanar ma Nasreen ta same mu a mota. Kamar jira yana kaini mota kuwa na fara murƙususu. Cikin tsawa yace ma driver ya shiga mota mu wuce. Shima bayan ya shiga ya rungumeni a jikinsa, Nasreen da driver na gaba. Kafin ma mu gama barin anguwar na rikice musu. Yayinda shima ya rikima driver wai baya gudu. Dole fa driver ya ƙara gudun ma da ya wuce ƙa'ida. A hakan dai ALLAH ya kawomu lafiya asibitin. Tun a waje aka tarbemu, amma yaƙi bari a shiga da ni ni kaɗai, duk haƙurin da suke bashi sai da ya bimu labor room ɗin. Dan kai tsaye sukace ai haihuwa ce gata ma gab gab sosai. A ciki da kyar suka samu ya fito bayan ya canja min kayan da suka ɗakko zasu canja min....

Alhamdullah duk da bazan ce na haihu salin alin ba, dan ansha gumurzu babu laifi. Sai dai gaskiya haihuwan tazo da sauƙi dan banyi doguwar naƙuda ba. Amma fa mata sunji a jikinsu. Dan ina samu abinda ke cikin nan ya fita sai kawai na shiɗe, sai da suka shafa min ruwa na kawo numfashi mai ƙarfi. Da kukan baby daya cika ɗakin na fara cin karo. A hankali na sake jan numfashi tare da ambaton “الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .
Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat.
اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.
Alhamdu lillahi ala kulli halin.......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒆𝒆𝒏_


......Tunda ya fito ya kasa zaune ya kasa tsaye. Nasreen da Driver ma dai na zaune jugum-jugum. Ya ciro waya yafi sau biyar da zummar kiran su Ummie sai kuma ya fasa. Gara dai ya bari ta sauka sanan. Yana nan dai yana kai-kawonsa da addu'a a bakinsa aka buɗe ƙofar. A tare shi da su Nasreen suka zabura. Tuni Nurse ɗin data fara fitowa mai ɗauke da Baby na laɓe a bayanta ta saki murmushi mai ƙayatarwa da faɗin, “بَارَكَ اللهُ لَكَ فِي الْمَوْهُوبِ لَكَ، وَشَكَرْتَ الْوَاهِبَ، وَبَلَغَ أَشُدَّهُ، وَرُزِقْتَ بِرَّهُ.
Barakal lahu laka fil mawhubi laka, wa shakartal wahiba, wa balagha ashuddahu, wa ruzikta birrahu. Congratulations da samun Baby girl ƙyaƙyƙyawa kamar kai da mahaifiyarta”
Sai kuma ta matsa mai ɗauke da Babyn ta bayyana. Wani irin nannauyan numfashi Maash ya sauke tare da zubewa ƙasa yay sujda. Kafin ya ɗaggo hannayensa a sama cat eyes ɗinsa na yin ƙyalli kamar mai shirin sakin kuka ya furta, “الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .
Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat.
اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.
Alhamdu lillahi ala kulli halin”. Sai kuma ya miƙe ya amshi Babyn ya rungumeta a jikinsa yana sake miƙa godiyar sa ga UBANGIJI tare da yimasa kirari a bayyane. Dan shine kawai mai bada irin wannan ƙyautar da dukiya ko mulki bata badawa. Ɗago babyn yay mai kama da shi sosai ya zuba mata ido yana sakin murmushi mai matuƙar ƙayatarwa da yakan jima bai yisa ba. “Dadaa na miki fatan alkairi da zuwa duniya mai cike da gwagwarmaya UMMU-HIDAYA. أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لاَمَّةٍ.
O'eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min kulli shaytanin wahammah, wamin kulli 'aynin lammah.” Ya kai lips ɗinsa saman goshinta ya sumbata tare da sake tungumeta a jikinsa. Yayi kusan minti biyu a haka duk suna kallonsa. Bakin driver da Nasreen yaƙi rufuwa. Sun ƙagara a basu baby a hannunsu suma su gani. Sai da Nurse tai gyaran murya sannan ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login