Showing 132001 words to 135000 words out of 438336 words

Chapter 45 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2189

Wani irin waro idanu na masifa Mama Balki tayi, cike da tashin hankali da suɓutar baki ta furta, “Sashen Hajiya Babba kuma Hajiya?”.
“Ko bazaki kaitan ba ne?!!”.
Cikin rawar jiki mama Balki ta shiga girgiza kanta da faɗin, “To to to Hajiya ALLAH ya huci zuciyarki, za..zan kaita mana.” mama Balki ta faɗa tana kama hannuna jikinta na rawa sosai. Da ƙyar na iya danne dariyar dake cina har muka baro wajen, dan tana ambaton Hajiya babban naji tamkar na dirga tsalle dan daɗi. Muna kammala hawa upstairs ɗin a stairs ɗin ƙarshe na ɗan kallo ƙasan, sai da na haɗiye dariyar dake cina sannan na kwaɓe fuska kamar zan fasa kuka. “Mammah dan ALLAH ni dai ina neman alfarma. In dai akwai matsala da zarar kunji na banka ihu a kawo min ɗauki koda sassaƙa-sassaƙan garadan nan na bakin ƙofar gida ne a turamin idan ma ku bazaku iya ba”.
A matuƙar fusace ta watso min muguwar harara da gwala-gwalan idanunta “Sai dai a turo miki Ubanki. Ƴar iskar yarinya sheɗaniya. Da alama kema dai mahaukaciyar ce get out of my side kafin na canja miki kamanni”.
Baki na tura mata cikin sake narke fuska da yamutseta na ce, “Ai dai ubana yana aljanna in sha ALLAHU badai shi b....”
Kafin ma na kai ƙarshe Mama Balki ta fisga hannuna jikinta na rawa. Duk yanda naso ta sakan taƙi yin hakan har sai da muka ɓacema ganinsu. Kamar zata saki kuka ta ce, “Kandala baki da hankali ko? Yanzu wannan hukuncin da suka zartar a kanki bai isheki ishara ba ki koya kimtsa bakinki? Dan ALLAH ƴar nan kada ki sakamu a masifa mutanen gidan nan sun wuce fiye da yanda kike tsammani a fitina wlhy. Kiyi fatan Alhaji ƙarami bai bar gidan nan ba yazo ya fiddaki a wajen nan da wuri, zanje na samesa yanzun nan”.
Da sauri na ce, “A'a mama dan ALLAH kada ki kirashi. Miye dan tace nazo nayi aikin anan?”.
“Yarinyar nan baki da hankali, wautarki tayi yawa wlhy. Kandala wannan sashen da kike gani baida maraba da rami mai kwazazzabo da in ka faɗa a cikinsa sai abinda ALLAH yayi. Gara kiyi aiki a sashen Hajiya Mammah ɗin dan ita masifa ce kawai da takura, amma nan ranki ma zaki iya rasawa. Ni dai ki jirani anan zan je na duba Alhaji ƙaramin ALLAH yasa bai fita ba”.
Ƙasa kawai nayi da kaina batare da nace mata komai ba.. Ita ma sai bata sake magana ba tai gaba.......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_

___________


Toh Nazo maku
Da kayan arziki
Kudai kunsan mata sai da gyara
Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta
A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE
Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne
Muna da
Shedaniyar gumba
Gumba mai saying
Garin mai kabbara
Mai dalalan miyau
Wayyo dadi
Mai bunsuru
Dan jarida
Soyayya dole
Bakin kyalle
Tadire ta girke
Gumba mai likkafani
Maza taye
Zumar kwakwa
Zumar ridi
Zumar dabino
Zuma mai ma'ul ijaba
Farin jini
Mallakoki
Gumba kalla kalla da dai sauran su
A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba
Ga kuma maganin slimming
Gyaran nono
Maganin hips
Maganin Kara kiba
Da dai sauran su
Kayan mu tested and trusted ne
Muna maraba da masu siyan Daya ko sari
Muna Nan cikin garin kaduna
Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah

Ni ce taku har kullum
AMINA GACHI
07034404975
CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE
KADUNA
Phone no 07034404975

____________

......Riƙota nayi ina girgiza kaina. Ta tsaya tana kallona. Idanuna cike da ƙwalla na ce, “Kiyi haƙuri Mama ki buɗe min zan gwada na gani. Koba komai itama mutum ce kamar mu. Muma kuma bamu san ya rayuwa zatai damu ba anan gaba. Dan ALLAH ki buɗe min kawai ALLAH yana tare da ni”.
Sosai alamar sanyayar jiki ya bayyana a gareta na jin kalamai na. Dan haka ta nufi ƙofar dake a falon batare da ta sake cemin komai ba. Bayanta nabi ina mai jin tausayinta. Babbar mace kamila yanayin rayuwa yasa tana gurfana a gaban wadda bata wuce sa'arta ba. Lips ɗina na ciza. Kafin na furzar da iska nabi bayanta nima. Sosai tsaruwar falon farko na sashen yay matuƙar ɗaukar hankalina. Fes yake yana ɗaukar ido saboda kayan alatun da yasha. Da alama ana gyarashi kullum. Kamar zanyi magana sai kuma nayi shiru dan ganin yanda Mama Balki ke ɗari-ɗarin buɗe ƙofa ta biyu. Sai da ta runtse ido da karanto addu'a sannan ta murɗa handle ɗin. Da sauri tayo baya tamkar mai shirin zurawa a guje. Kallonta na tsaya yi kawai cike da nazari, sai kuma na sauke numfashi. “Uhhh mama, inaga kije kawai daga nan babu damuwa zan ƙarasa ni kaɗai.”
Waro idanu Mama tayi, sai kuma ta marairaice fuska idanunta na cika da ƙwalla. Ƴar nan dan ALLAH kiyi addu'a kinji, ko ki zauna a wannan falon sai zuwa anjima ta tashi ki gudo, Kinga shike nan an rabu lafiya”.
Murmushi mai kama da yaƙe kawai na mata ina jinjina kaina alamar to zanyi. Numfashi ta sauke mai nauyi, sai kuma ta haɗiyi yawu jiki a sanyaye ta juya ta fita tana waigena. Ni dai kallonta kawai nake har sai da ta maida ƙofar falon ta rufe a hankali. Sai kuma ta sake buɗewa. “Karki sake ko kulle kowacce ƙofa dan ALLAH Kandala. Ki barsu a buɗe yanda zaki samu damar gudowa koda an sami akasi”.
Kaina na jinjina mata nan ma ina murmushi. Ta sake ɗan jan ƙofar batare data rufe duka ba ta barta. Shiru nayi kawai a wajen tsaye har zuwa wani lokaci. Ni kaina a tsoracen nake. Amma inata ƙoƙarin dakewa kun dai san ɗan jarida da jarumtar wahala. Shiru sashen yake babu alamar motsin mai rai, sai ɗan yanayin kamar bashi-bashi dake bugowa daga ƙofar da Mama ta buɗe. Ƙofar na tsurama idanu na wani lokaci, kafin nayi ƙundun balar nufarta cikin sanɗa da ambaton sunan UBANGIJI......

📯📯📯📯

Farin cikin da Musaddiq yake a wannan rana bazai taɓa musaltuwa ba a zahiri. Sai dai ya barma UBANGIJI komai. Tsaff ya fito cikin shirinsa na shadda ruwan ƙasa mai haske harda hula. Sai ƙamshin turarensa yake mai sanyin daɗi. Hannunsa riƙe da takardunsa yake ƙoƙarin kulle ƙofar. Juyowa yay da sauri jin kamar mutum ata bayansa yana kallonsa. Ilai kuwa ido huɗu sukai da Umma mahaifiyar Mom da alama isowarta gidan kenan. Kauda tsarguwar kallon ƙurillar da take binsa da shi yayi, tare da sakin nutsatstsen murmushinsa ya ƙaraso inda take. Cike da girmamawa ya ce, “Sannu da zuwa Umma. Ina kwana? Anzo lafiya?”.
Cikin ɗan daburcewa da dawowa a hayyaci ta shiga amsawa bakinta a washe. Dan harga ALLAH yaron ya gama firgita mata zuciya da guntun lissafin ta. Wani kalar mahaukacin sirrintaccen ƙyawu fa taga yayi mata da ƙiba harda haske. Ga arziƙi muraran ya nuna a jikinsa kai kace ma shine ɗan masu gidan ba ɗan riƙo ba. Dan ko mahaukaci ya kallesa ya kalla Abbas yasan akwai banbanci da tazara mai yawa ta cigaban rayuwa....
“Ki shiga Umma ai su Mom ɗin suna nan ciki”. Ya faɗa cikin katse mata tunanin data lula. Firgigit kuwa ta dawo a hayyacinta. Sai kuma ta washe baki cikin in ina ta ce, “T... t.. to ɗan nan nagode kaji, ALLAH ya muku albarka ya ƙara arziƙi. Bari na shiga ɗin dai to”. Ta ƙare maganar tana tafiya da waiwayensa a lokaci guda har taci tuntuɓe tana neman faɗuwa. Ta dai samu ta dafe gini idonta a kansa har lokacin ga baki a washe kamar sakara.
Shi dai Musaddiq cike da al'ajabinta yay ficewarsa. Kaɗan-kaɗan sai ya kalla kansa ko zaiga abinda takema kallon ƙurulla a jikin nashi. Amma sai baiga komai ba. Haka dai ya tare napep ya shiga komai na masa kai-kawo a rai da zuciya. Koda ya iso gate ɗin companyn sai da ya nuna ɗan katin da ogansa ya bashi sannan aka barshi ya shiga. Sosai yake jinjina ƙudira da rahama ta UBANGIJI. Dan gaskiya wannan Company ya matuƙar tafiya da imaninsa. Gini ne iya gini da baka iya ƙuresa da idanu. Ga ma'aikata nata faman kai-kawo da securitys. Ga kayan aikin tako ina da zai tabbatar maka da komai fa da gaske ake babu wasa. Da taimakon wani security akai masa rakiya office ɗin Manager.....

💦✨💦✨💦

Ji Abba yay tamkar ya tashi ya buga ihu da tsalle dan farin cikin hukuncin Baba. Domin ya tabbatar musu in dai Halime na son Abban zai bashi ita. Hakan yasa aka aika aka kira Halime. Koda tazo taci karo da su Abba sai da ta nuna ƙololuwar mamakinta har ta gagara yin magana sai da Babanta yay mata magana ma ta iya gaishesu muryarta na rawa. Zata ɗora da zance Abba daya san mi zata iya faɗa yay saurin katseta. Dan baya fatan ta tona asirin komai musamman akan abinda ya faru a randa ta gudo ɗin, saboda ya fahimci bata sanarma su Baban komai ba. Shirun kuwa tayi kamar ta fahimci abinda yake buƙata, daga haka mai anguwa ya sanar mata abinda ya kawo su Abba. Sake diriricewa kuwa tayi tana faman zare idanu. Da ƙyar Abba ya iya danne dariyarsa. Alhaji Jafaru da Alhaji Sadisu kuwa sai da suka dara kaɗan. Mai anguwa ma dai yayi kaɗan kafin ya ɗora da tambayarta ko tana son Abba ɗin.... Ai baima rufe baki ba suka tsinceta can ta zura a guje cikin gidan mai anguwar.
Basu Abba ba hatta da Babanta yanzu kam sai da ya dara. Fuskarsa da sauran dariyar ya dubi Abba. “Imamu kaga fa shirmen mutuniyar taka. Anya zaka iya da ita? Dan Sa'adiyya akwai wauta a tattare da ita ta ƴaƴan fari. Ni kaina wani abun idan tayi a wasu lokutan ƙuleni sukeyi. Sai dai kuma akwai himma ga biyayya. Duk abinda kaso daga Sa'adiyya zaka samesa. Gwargwado na bata ilimin addini, na zamanin ma ta fara wasu dalilai yasa dole aka yankesa....”
Fuskar Abba da murmushi kansa a ƙasa ya ce, “Karka damu Baba, ni ɗin ita nake so ba shirmen ba. Sannan nagartattun halayen nata da tarbiyyar ta suka jani gareta. Dan wauta wataran zata daina in sha ALLAHU yanzu ma akwai ƙuruciya ne”.
“To Alhamdullah Imamu, naji daɗin jin wannan batu daga gareka. Dan haka ina sake maka albishir da baka auren Sa'adiyya. Kuma bana son kubar garin nan sai an ɗaura, in har da sadaki a tare da kai da anyi sallar zuhur yanzu kawai sai ayi”.
Wannan furuci shi ya sake rikita Abba. Dan baba bai kammala rufe baki ba ko ya zaro kuɗi masu yawa a aljihunsa ya dire gaban Baban. Dariya su Alhaji Sadisu suka sanya masa. Cike da tsokana Jafaru ya ce, “Ai ka bari dai ni na biya maka Alhaji zumuɗinka”.
Dariya su mai anguwa suka saka da Baba. Yayinda kunya ta kama Abba ya kaima Alhaji Jafaru harara yana ɗauke kansa gefe. Da ga haka suka miƙe domin haramar masallaci....

Al'amarin tamkar almara bayan idar da sallar azhar aka dakatar da mutane. Mata dake cikin gida sai shelanta ɗaura auran Halimatussa'asuyya Yousufa da angonta Imam Gwarzo suka jiyo. Bakin Abba kamar zai taɓa kunne. Sai faman gaisawa yake da mutane cike da farin ciki. Kafin kace minene har labari ya fara yawo a gari. Gidan mai anguwa aka koma da su Abba. Sai da sukaci abinci sukai nak sannan Baba yay musu jagora zuwa gidansa kamar yanda ƙannensa biyu da akai komai da su suka bada shawara....


💢💦💢💦💢

A hankali na tura ƙofar idanuna a rufe na shiga cikin sanɗa. Yayinda zuciyata ke wani irin harmutsawa saboda ƙarni da tsamin dake tashi sosai a falon. Abin mamaki da al'ajabi shima ƙaton falone da aka zubama komai na more rayuwa da ƙawa. Sai dai mafi yawan abinda ke a cikin nasa an gama faffasashi. Dan hatta da television dake a jikin bango an mata rugu-rugu. Ta saman farin Mable's ɗin kuwa mai tsananin sheƙi tako ina fitsari ne har da su katsi, abinci ruwa da wasu nau'in kayan ciye-ciye kamar su fruit duk sun ruɓe. Hatta a saman carpet ɗin ma da ya gama fita a hayyacinsa al'amarin ba'a magana. Kai labuloli kansu wasu an fincikosu wasu kuma an goge datti da su. Sai ɗigo-ɗigon jini a wajaje daban-daban shima har a jikin bango. Bamma san sanda zuciyata ta karye ba sai ɗumin saukar hawaye da naji a saman kumatu na. Sosai nayi kuka a wajen kafin na cigaba da ƙarema falon kallon. Akwai dining table ta can gefe da aka ƙawata a cikin glass da ya raba tsakaninsa da falon. Sai dai shima an gama hargitsashi wasu kujerun ma a karye suke. Table ɗin ma kansa tuni an maida sama a ƙasa. Ta ɓangaren damata akwai ƙofofi guda huɗu, sai tsakkiyarsu ƙafar bene da akai ma wani kalar style mai ɗaukar hankali da birgewa. Numfashi na sauke a hankali nan ma tare da yunƙurawa na nufi ƙofifin, har na kusa sai kuma na tsaya cak saboda shawarar da zuciyata ta bani akan fara gyara wannan falon koda ma zan shiga cikin tunda ban san mizan tarar ba ko tarbar da zan samu daga mai sashen......✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_


_________

_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_


https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG



https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
___________

.......Komawa nayi baya ta hanayar dining ɗin nan ina mai addu'ar samun kayan shara. Ƙofar kitchen ɗin akwai key a jiki, dan haka na murɗa a hankali, sai da na leƙa cikinsa sannan na shiga gaba ɗayana ina sauke numfashi. Babu komai a cikinsa shima. Sai dai shi ɗin fes yake babu wani datti sai ƙura ta rashin gyarawa. Sosai kitchen cabinet ɗin da aka ƙawatashi da shi yay matuƙar ƙyau kamar ka zauna kayita kallo. Ganin ina neman shagala a kallon cabinet na zabura neman kayan shara. Cikin Sa'a kuwa sai gasu na samo a store dake cikin kitchen ɗin duk masu aiki da wuta. Cike da ɗoki da zumuɗi na kwaso duk abinda zan buƙata. Tun daga store ɗin da shima babu tarkace sosai na fara gyarawa har zuwa kitchen, sannan na fito dining ɗin. A nan kam na jigatu kafin na dawo falon mai gayya da aiki. Tun ina yin aikin da marmari har na fara jigata. Amma haka na dinga dauriya. Sau biyu ina jima hannuna ciwo. Na maida abinda zai iya maiduwa. Wanda suka tashi a aiki na tattarasu na fitar can barandar da aka ƙawata ta waje bayan na zuge labule na ganta. Ashe wajen glass ne amma an rufesa da wani irin abu mai taushi nasan duk dan kar taji ciwo ne. Kaf labulolin data jeho na tattaresu dan duk abincine da fitsari a jikinsu. Hakama carpet ɗin na cireshi shima. Hatta wanda sukai min nauyi da yawa haka na dinga turasu,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login