Showing 114001 words to 117000 words out of 438336 words
matar na shigata. Kaina a ƙasa na amsa mata da, “Eh mama nayi wanka, kayane dai ban canja ba”.
“Karki damu da wannan. Nasan Hajiya Mama na sane da ke zata kawo kayanki in sha ALLAHU. Yanzu dai ki karya sai ki dawo nan ki zauna kisha iska ni zan koma bakin aiki kada yaran suyi shirme”.
“Na gode mama ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara girma”.
“Amin ya rabbi ɗiyata ALLAH yayi miki albarka kinji”.
Yanda ta faɗa ɗin ya bani tabbacin taji daɗin girmamawar da nake bata. Zama nayi naci abincina, duk da dai bawani na kirki bane naji yamun daɗi. Bayan na kammala falon na dawo kamar yanda Mama ta umarceni. Ina zama sai ga Mama ta dawo. Cike da kulawa ta ce, “Yauwa to taso ɗiyata, dama nace miki Aunty Mama zata iya buƙatar ganinki”. Da girmamawa na amsa mata da to ina miƙewa nabi bayanta. Sosai nake ƙara tsarkake sunan UBANGIJI daya bama waɗanda suka tsara ginin wannan gida fiƙrah da fasahar yinsa tamkar an ɗakko an dasa ne ba hannu yayisa ba. Ashe jiya kallon tsoro nayi masa. Lallai na yarda masu arziƙi na inda suke. Ashe su Mom iyayen alfahari da kuɗin Abba basu wuce ƴan aiki ba a wani wajen. Ashe duk kuɗin da take kallon iyayen Mansoor suna da shi ba komai bane ba. Zuciyata tai wata irin jijjiga dalilin tuna masoyina Mansoor. A take naji hawaye sun cika min ido. Amma ban bari sun zubo ba na haɗiyesu.
Mayataccen ƙamshi da sanyin ac ke fara maka sallama tamkar ba safiya ba. Ga wani irin shiru da gidan ya bada tamkar babu wani rai mai motsi a cikinsa. Wata irin ajiyar zuciya ce ta kufce min batare da nasan dalilin hakan ba. A cikin takun nan nawa na nutsuwa da rashin hayaniya na cigaba da bin bayan Mama. (Ya Al-malik) na furta a zuciyata lokacin da muke gama haurowa upstairs ɗin tsakkiya. Ashe saman ma wasu shegun faluka ne da sukafi na ƙasan ƙawatuwa da barazana tamkar ba duniya za'a mutu a barsu ba. Rasama ina zan nutsu na kalla nayi nikam. Tako ina na gama diriricewa. Sai dai a zahiri baka isa tabbatar da yanayin nawa ba dan na shanye komai a raina ni da zuciyata mukeya bidirinmu kawai a baɗini.......✍️
_😂Ku cigaba da haƙuri dai, ni kaɗai nasan yanayin da nake ciki😞._
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_
_____________
_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
_____________
......Daga ni har Mama Balki ƙasa muka zube gaban Alaja dake zaune cikin kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya tana daƙilar tab. Gaisheta na shiga yi, batare data ɗago ba ta amsa min. Kusan mintuna biyu muna zaune kamar masu neman gafara sannan ta ɗago tana cire eyeglasses ɗin idonta da bana raba ɗayan biyu na ƙara gani ne. A kaina ta zube idanun nata, sai kuma ta ɗan saki murmushi. “Ƴammata sorry fa. Tunda mukazo ban sake waiwayarki ba ko? Nayi busy ne da yawa.”
“Ba komai Mama”.
Na faɗa kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hanuna ta cikin hijjab.
“Ohkay, yanzun ma bani da isashen lokaci. Maman Nana kije da ita wajen Sunusy ya gwadata a ɗinka mata uniform itama. Sauran kayan da zata iya buƙata kuma sai ki shirya zuwa anjima kuje shopping. Zata cigaba da zama a hannunki kafin tasan aikin da zatayi”.
“To Hajiya in sha ALLAHU yanda kikace haka za'ayi. ALLAH ya ƙara nisan kwana da rayuwa mai albarka”.
A hankali ta amsa da amin. Jin godiyar da Mama tayi nima sai nayi godiyar. Duk da kuwa wani irin abune mai masifar nauyi ke neman riƙe min ƙirji. Ban san a wace kalar rayuwa kuma na jeho kaina ba. Lallai na tafka kuskure. Inama Kano na nufa abina. Kai anya kuwa kuskuren nawa ba daga baro asibiti bane da nayi. (Tun daga baro gidan mijinki dai a Kano) wani gefe na zuciyata ya ayyana min. Jinai tsigar jikina yay wani irin tashi sama. A saman lips na maimaita kalmar “Miji”. (Kai ina ai bazan taɓa zama matar kowa ba sai Mansoor in ALLAH ya yarda)..
“K! waye wannan kika hayo mana har sama da shi?!”. Muryar dana tabbata naji irinta a jiya ta faɗa cikin daka mana tsawa dai-dai muna sauka steps na biyun ƙarshe. Ganin yanda Mama Balki ta dakata da sauri cikin nuna shakka ya sani mamaki. Cike da girmamawa da sauke kai ta furta “ALLAH ya huci zuciyarki Aunty Azizat. Dama mun cika umarnin Aunty Mama ne. Dan itace ta buƙaci ganinmu”.
Fuska ta wani yamutse tana balla mana harara. Da alama dai bata da abincewa. “K kuma uwar miye kike wani kallona? Shegiya mai kama da mayu!!”. Ta sake faɗa a fusace tana wani ware idanu a kaina sosai cike da nuna tsagwaran tsanar da ban san laifin dana mata ba. Duk yanda naso jin na bata girma a matsayin wadda na shigo gidansu da kuma girmata da tayi a shekaru dan zata iya kaiwa sa'ar Yaya Musaddiq amma sai naji hakan ya gagareni. Sai ma tsareta nai da idanu ina ƙare mata kallo daga sama zuwa ƙasa....
Tauuuu!!! Naji saukar wani shegen azabebben mari asaman fuskata babu zato babu tsammani. A take ta rashin jin ya yunƙuro, bamma san lokacin dana ɗaga nawa hannun ba na sauke mata nawa yatsun biyar nima a saman fuskarta dake fara sosai a dama da haggu kuma. Daga gani kasan akwai ƙarin farin kanti dan har wani yellow-yellow takeyi. Tamkar mutuwa ta ratsa gidan haka yay wani irin tsittt na wuccin gadi. Kafin tai wani irin zuba min ido like wadda tai suman tsaye. Bama ita ba hatta da Mama Balki wani irin waro idanu tayi da ɗaura hannuwa duka a saman kai bakinta buɗe. Cike da dakiyar nan tawa da taurin kai na watsar da su tamkar banga komai ba na raɓa zan wuce. Dai-dai nan ta wani saki kururuwa da girgiza tamkar tsohuwar dodanniya ta damƙo min hijjab ta baya. Sai kawai ji nai an shaƙureni tare da jawoni baya. Tabbas da banyi azamar damƙe hijjab ɗin ta gaba ba da zamesa da sauri babu abinda zai hanata kaini ƙasa a wajen. Idan kuwa na faɗi zan iya buguwa, idan ma da tsautsayi zan iya rasa rayuwata. Gaba nayi gaba ɗaya, dan yanda ta fisga ni kuma na fisge sai yay kamar an hankaɗoni ne. Na gama sallamawa babu makawa a wannan gaɓar sai na kai ƙasan mayen marbles ɗin nan mai tsananin sheƙi da ɗaukar idanu tamkar zakaga fuskarka a cikinsa. Dan haka na runtse idanuna gaba ɗaya ina mai ambaton sunan ALLAH da sallamawa baki ɗayana......
★★★★
Cikin mintuna ƙalilan Halime ta dawo ɗauke da tray. Haka kawai take ji bazata iya tsallake umarnin Abba ba. Duk da tana jin shakkar uwar ɗakinta tasan ta ƙetare umarninta. A hankali ta dire tray ɗin a gaban Abba dake zaune a dining. Tun fitowarta kuma yake famar binta da kallo ta gefen ido tamkar zai cinyeta. Ƙoƙari barin wajen take yi tamkar mai raɗa ya furta, “Baza'a zuba min ba?”.
Duk shirmen Halime sai da taji zuciyarta ta tsarga. Hannunta na rawa ta shiga zubama Abba abincin. Ta kammala tana ƙoƙarin barin wajen ya katseta da faɗin, “Uhhm Kinga zo mana”. Nan ma ƙiri tai tana kallonsa, kafin cikin sanyin jiki tai ƙoƙarin durƙusawa a ƙasa. Amma sai yay saurin girgiza mata kansa da mata nuni da kujera. Gabantane ya sake faɗuwa. Tai masifar waro idanu waje tana jijjiga masa kanta alamar dai bazata iya ba. Ƙyaleta yay, cikin gyara yanayinsa ya ce, “Minene sunanki?”. Ganin yanda yaci serious ya sata nutsuwa itama. Kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta amsa masa da, “Halime”.
“Halimatussa'adiyya kenan?”.
“Eh ta faɗa a hankali”.
“Ina ne garinku?”.
“Ƴan tumaki”. Ta bashi amsa kai tsaye.
“Ƴan tumaki?”. Ya maimaita da ɗan waro idanu a kanta a tunaninsa shaƙiyanci ne. Amma sai a mamakinsa yaga ta jinjina masa kai na tabbatarwa. Kasa haƙuri yayi sai da ya furta “A wane state ne?”. Girgiza masa kai tayi da faɗin, “Katsina ne. Amma dai muna kusa da Musawa”. Jin sunan Musawa ya sashi fahimta Katsina state kenan ɗin dai da gaske. Humm mutanenmu da ganganci, ka turo yarinya mai cikar halitta jiki kamar wannan aikatau har wata jiha. Cigaba yay da faɗin, “Miyasa kike aikatau?”.
Idanunta ne suka ciko da ƙwalla. cikin rawar murya ta ce, “Inna ce tace Baba ya turani na samo kuɗin kayan ɗakin aurena”.
“Ita Innar mamanki ce?”.
“A'a gwaggona ta rasu tun ina ƙarama. Matar Babana ce, amma uwarsu ɗaya ubansu ɗaya da Gwaggona. Bayan ta rasu aka aurama Babana ita dan ta riƙemu ni da ƙanina. Sai dai kuma ta tsanemu, kullum cikin mana mugunta take, gadonmu ma da Gwagginmu ta barin mana duk ta cinye. Gashi Baba baya iya cemata komai, shima tsoron masifarta yake ma”.
Haka kawai yaji wani abu mai nauyi ya tsikarar masa zuciya. Tamkar walƙiya hoton Maman su Samraah yazo masa a cikin idanu. Da sauri ya ture zancen zucin gefe ya cigaba da faɗin, “ALLAH ya gafarta mata. Toke kina da saurayi ne da aka turoki samun kuɗin kayan ɗaki?”.
Ƙasa ta ƙara yi da kanta sosai alamar jin kunya. Wasa ta farayi da yatsunta sannan cikin in ina ta ce, “Duk wanda yazo wajena Inna korarsa take yi. Tace saina haihu a gida ɗan shege ko zata bari nayi aure. A hakan ma sai su Lami sun gama yin nasu auren”.
Sosai zuciyar Abba ta sake raunana da tsinkewa. Da ƙyar ya iya furta, ”Wacece ita Lami ɗin?”.
“Ƙanwata ce ita ta haifeta da su Lailah”.
Kasa sake magana Abba yayi tsahon lokaci. Sannan yace ta tashi taje ta cigaba da aikinta. Shima sai ya miƙe dan ya gagara cin abincin kuma ya koma ɗaki. Shirin fita yayi zuciyarsa na masa kaikawo. Bai wani jimaba ya kammala ya bar gidan batare da ya sake neman Halime ba....
Duk yanda Abba ke son yaƙar zuciyarsa game da abinda take ƙwaɗaita masa hakan ya gagara. Tun yana iya danne al'amarin har yana son fin ƙarfinsa. Yakan rasa sukuni a duk ranar da baiga Halime cikin idanunsa ba. Al'amarin tun yana bashi mamaki har ya koma bashi tsoro. Dan haka kawai yanzu rana tsaka zai baro kasuwa yayo gida dan kawai yaga Halime. Tun Mom na masa uziri idan yace mantuwa yayi harta fara tsarguwa da tunanin ya saka mata ido ne akan yawan yawon da take kwana biyun nan. Hakan ya sakata ɗan nutsuwa a waje guda. Yayinda shi kuma Abba zaman nata a gida ya zame masa takura. Dan idan tana nan ko giccin Halime baya gani saboda yanda take jin tsoron saɓa umarninta. A haka da ƙyar akai kwana huɗu. A daren cikar na biyar ya gagara haƙuri ya nufi gidan abokinsa Alhaji Sadisu mai-agogo. Tsaff ya kwashe komai ya sanarma Alhaji Sadisun. Shiko ya dinga dariya yana tsokanar Abba har sai da yaga ya ƙulu sannan ya bashi haƙuri tare da bashi shawarar yanda ya kamata suyi dan ganin komai ya tafi dai-dai. Sosai shawarar tayima Abba kuwa. Ya tafi gida cike da farin ciki....
★★★
Wata irin ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi jin na faɗa kan abu mai taushi saɓanin inda na gama sadaƙarwa zan faɗi. Rawar tsorata dana riga nayi jikina keyi, dan haka na sake ƙanƙame abinda na faɗawar ina mai sake matse idanuna dake a kulle. Sai dai me, wani kalar wakitawa ƙitjina da zuciyata sukayi a lokaci guda, a take tsigar jikina ta fara mimmiƙewa. Gabana ya sake faɗuwa jin yanda wajen ya koma tsitt tamkar babu wani rai mai numfashi. Gaba ɗayan numfashina ne ya ɗauke daga illahirin gangar jikina nima, tare da wata irin girgizawar zuciya taban mamaki. Sake ƙanƙame abinda na faɗawar dai na sake yi. Wani irin jifff!! Ƙirjina ya sake bugawa a karo na biyu jin tabbacin mutum ne, mutum ɗin kuma daga ji ba jikin mace bane, sannan ƙamshin dana shaƙa na neman jirkice min tunani gaba ɗaya. Ga tsitt ɗin da wajen ya ɗauka lokaci ɗaya tamkar an tsaida numfashin kowa da komai na gidan. Sassauta riƙon da naima koma minene na fara yi, sai kuma na shiga ɗago kaina a hankali ina ƙoƙarin buɗe idanuna. Akan farin riga armless ta sport wear fara tas na fara saukewa. Sai ƙaton damtsen hannu dake a murɗe sosai fari mai ɗan duhu kaɗan dan fatar batai irin tas ɗin nan na mahaukacin fari ba. (Jikin namiji) zuciyata ta ayyana min, dai-dai da bugar hancina da ƙamshin turarensa ya sake yi. Cikin wani irin sauri da shiga tsananin tashin hankali na ɗago gaba ɗayana na sauke idanuna akan fuskarsa.........✍️
_🥺🥺Hukumar tawada da alƙalami tace a tafi yajin aiki.🥱_
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_
.......Cak numfashina ya tsaya, illahirin jikina ya saki gaba ɗaya. Da ga ni har shi muka zubama juna ido. Yamutsawa kaina ya farayi saboda wani sinadari mai ƙarfi dake fitowa daga cikin cat ayes ɗinsa yana shiga cikin nawa. Wani irin kallo yake min mai kama da gargaɗi koma tsanace ban sani ba. Dan duk yanda naso dakewa hakan ya gagara. Tuni naji wani irin kwarjininsa ya gama mamayeni da cikani tamkar mu kaɗaine a wani matsatsen lungu. Hatta da iska ma ta fara min wuyar shaƙa neman komawa fisgar numfashi nake yi. Wani matsiyacin kallo daya dalla min tare da ƙoƙari janye jikinsa daga nawa ya sani tafiya gaba ɗayana baya zan faɗi. Bamma san na fasa ƙara ba da komawa gaba ɗaya jikin nashi na ƙanƙamesa tamkar zan huda shi na shige ciki...
Kusan kowa dake a wajen sai da ya sake waro idanu. Yayinda tuƙuƙin baƙin ciki da kishi mai tsanani ya gama mamaye zuciya da ruhin Azizat. A yanda take jin bawan ALLAHn nan a ranta ko macen sauro ta tsani ta taɓa mata shi, ai tuni idanunta sun sake rufewa. Batama san lokacin data isa gabansu ba. “Wlhy sai na kasheki ƴar iska. Bayan maita ma harda bin mazan mutane”. ta faɗa cikin ihu mai ƙaraji tana damƙo hannun Samraah da ƙoƙarin janta baya daga jikin Maash. Wani mugun kallo ya watsa mata. Sai kawai ta fashe da kuka tare da sakar min hannun tana ƙoƙarin kaimin mari. Nima tamkar wadda aka farkar a barci dai-dai nan na dawowa a hayyacina, Cikin wani irin sauri da shiga tsananin tashin hankali na sakesa gaba ɗaya tare da turashi. Sai da me ko gezau, yana nan a tsayensa ƙyam saman ƙafafunsa tamkar dasashiyar bishiyar data kafu a muhallin daya dace da ita. Kallo ɗaya yay min da shegun idanun nan nasa kalar na maguna