Showing 378001 words to 381000 words out of 438336 words

Chapter 127 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2971

Muryarsa a ɗashe ya furta, “Yaya little Ummu-Hidaya?”.
“Tana lafiya, tare da yima Abbunta addu'ar samun lafiya mai ɗorewa. Ta yi kewarsa kuma matuƙa”.
Wani ɗan langaɓar da kai yayi gefe yana sake ƙanƙance idanu. Jinai sam bazan iya jurar kallon ba na faɗa jikinsa kawai na ƙanƙamesa tare da haɗe lips ɗinmu waje ɗaya....

Rayuwa a Spain wata irin rayuwace da kowa a cikinmu bazai manta da ita ba. Dan mun haɗu ne mun gina wani farin ciki a zukatan junanmu da har abada bazamu manta ba. Idan ka gammu bazaka taɓa ɗauka mu ba jini ɗaya bane. Mama da Ummie sun zama iyaye. Baba ya zama Uba. Maash da Hayat sun zama manyan yayye. Fahad da Hafizzullah sun zama garkuwa. Mukam ƙanne masu matuƙar biyayya gana gaba dasu. A cikin ɗakin mijina kam ni da shi sai sambarka da alhmdllh. Dan dukkan wata soyayya da kulawa ina samu daga garesa harma wadda banyi zato da tsmani ba. Hafizzullah da Bahijja sun koma makaranta. Yayinda Fahad aka fara shiga harkokin Bussines shima. Yaya Musaddiq yazo mana hutun sati ɗaya. Na shiga matuƙar farin ciki da wannan ziyara ni da ƴan uwana da su Ummie duka. A wannan zama ne Ummie ta bamu takardun Company da Abie ya bada a bamu. Munyi kuka munyi godiya sosai. Mun kuma tattauna abubuwa masu yawa da suka jima suna damun kowannenmu. Bayan wucewar Yaya Musaddiq Falaq ta koma ɗakin mijinta dan tayi arba'in. Little Awwab nata wayo Masha ALLAH. Ya Awwab ma jikinsa yayi sauƙi sosai. Kamar yanda Ummie ke sake samun lafiya yanda ya kamata. Dan yanzu haka itama zata fara cigaba da kula da wasu harkokin Bussines ɗin ne anan. Saboda Maash da Hayatu sun koma gantalinsu na ƙasashe. Har Nigeria ashe suna kaɗawa idan ta kama. Sai dai basu taɓa sanar mana ba. Cikina ya fara fitowa ɗan kif da shi, sai dai kunya tasa kullum bana rabo da hijjab in har zan sakko ƙasa wajen su Ummie, ko na saka riga mai burun-burun da ba'a ganewa.
A hankali soyayya da shaƙuwa ta fara shiga tsakanin Fahad da Bahijja. Wannan abu yama kowa daɗi, sai dai ita Bahijja na dojewa saboda kunya. Ni da Aunty Falaq muna sake fanfata kuwa. A haka Jaga shima yazo yay mana hutu na sati biyu ya koma Saudiyya. Bayan wucewarsa bai fi da sati uku ba Abba ya kira yake sanar mana Amaryarsa ta haihu ƴan biyu duk maza. Murna sosai muka dinga yi dan mun san lokacin zuwa Nigeria yayi kamar yanda Yaya Awwab yay mana alƙawari. Gashi a ɗan tsakanin shima Yaya Musaddiq zai je ya musu hutun sati biyu. Sai abin ya sake mana dai-dai. Ganin har ana saura kwana uku suna babu Maash babu alamarsa a Spain jikinmu ya fara sanyi. Idan muna waya ko video call nai masa batun tafiyar kuma baya cewa komai sai ya basar ma. Dana fahimci hakan sai na daina masa batun gaba ɗaya. Mun daiyi ɗan gyare-gyaren muna jiran ikon ALLAH. Sai ana gobe suna da safe suka iso Spain shi da Hayat da Fahad. Munyi farin cikin dawowar tasu, amma harga ALLAH na fidda ran zuwanmu Nigeria a lokacin kam. Amma mi sai kawai yace mu shirya jirginmu zai tashi washe gari zuwa Nigeria. Tsabar farin ciki bamma san na rungumeshi agaban Ummie da Mama Balki ba harda manna masa sumba a lips. Sai da naji Hafizzullah da Fahad na dariyar shaƙiyanci sannan na farga. Ai da gudu na sakesa na bar wajen. Ummie na kirana cikin dariya ban waigo ba.
Har ta gama haye stairs ɗin yana tsaye a inda ta barshi, ta kuma gefen ido yake kallonta. Ba yau ta saba rungumeshin ba. Sai dai koda kwatance bata taɓa yi a gaban Ummie ba. Sai ma idan shi yaso yin hakan ta doje. Jiyay gaba ɗaya ta saukar masa da kasala. Karo na farko sai yaji nauyi da kunyar Ummie da Mama Balki. Amma sai ya dake abinsa yama cema Hafizzullah ya bashi coffee. Tashi Fahad yay yabi Hafizzullah kitchen ɗin, sai da suka gama iya shegensu wai yayan nasu na borin kunya sannan suka kawo masa coffee ɗin. Yana amsa ya miƙe ya haura sama da shi a hannu. Ai ko suka gimtse bakuna suna dariya sai da Mama Balki ta korasu sashensu. Shigowarsa dai-dai da fitowata wanka. Dan ina shigowa bathroom na wuce dama. Alhamdullah yanzu kam laulayi yayi sauƙi sosai, dan tunda na shiga wata na shidan nan kam sai dai kwaɗayi da ciye-ciye nake. Amma ciwo-ciwon nan da jinin da nake gani duk wata kaɗan-kaɗan duk sun bari. Sai kuma ƙulafucin miji abin har kunya yake sakani. Yanda yake bina da kallon ƙurilla yasa na tura masa baki da kauda nawa idon a kansa.
Murmushi ya saki kaɗan da laluba aljihunsa ya fiddo min chocolate ɗaya da indai yana gari ko yay tafiya ne ma zai shigo sai ya shigo min da ita. Bamma san nima nayi murmushin ba da nufosa. Kofin hannunsa ya ajiye yana mai ware min hannayensa duk biyu. Shigewa nai jikin nasa ya ɗagani cak yana juyi dani. Dariya na shiga yi ina ƙanƙamesa da faɗin, “Wayyo My Hot juwa. Juwa my Hot ka bari”.
Saman gadon ya sauke ni tare da rungumeni da ƙyau shima yana murmushi. Nima ina ƙanƙame da shi ina faman sauke ajiyar zuciya. Daga haka lissafin ya canja. Tako wane fanni cikin nan baya hanani bashi dukkan kulawar data dace a zahirin rayuwa da shimfiɗarsa. Hakan ke ƙara saka shaƙuwa ta musamman a tsakaninmu da soyayya mai ƙarfi duk da har yanzu daga ni har shi babu wanda ya taɓa furtama ɗan uwansa kalmar (I love you) sai dai a aikace. Hakan kuma ya gamsar da mu ya kuma wadatar. Dan soyayya a baki ba'itace soyayya ba. Soyayya ta gaskiya ma ta wuce batun faɗi da bakin ai sai dai lokaci da yanayi su tabbatar....

WASHE GARI kamar yanda ya faɗa jirginmu ya wulla zuwa ƙasarmu ta haihuwa bayan barinta kusan watanni huɗu kenan. Mun sauka a Lagos inda motocinsa da guards ɗin sa na amana suka zo ɗibarmu airport. Da taimakonsu muka shige motocin dan ƴan jarida da bamu san ta yanda akai suka san zamu shigo ƙasar ba tuni sun kewaye mu. Ga jama'ar gari da muka zame musu ƴan kallo. Ni da shi mota ɗaya muje, dan tunda muka fito a jirgin yana maƙale da hannuna cikin nashi kamar za'a ƙwaceni. Sanye yake cikin ƙananun kaya da suka masa ƙyau sosai. Ni ko abayace a jikina baƙa data mun ɗas, tare da ɗan ɓoye cikina ɗan watanni kusan shida. Ni kaina nasan na ƙara ƙyau da cikar kamala ga ƙibar da ciki ya sani fatata sai ɗaukar ido take mai birgewa. Mun sha matuƙar mamaki da ganin yanda akai ma Maash Mansion gyara. An canja fentinsa da komai na cikinsa. Su Mama Balki an maidosu ainahin sashen da Ummie ta fara mallaka musu sanda take ginin gidan. Haka itama an gyara mata ainahin sashen da tayi da sunan nata. Sai Fahad shima da Hafizzullah, a kwai kuma ainahin sashen da in yayi aure zai zauna da matarsa. Sai Hayat da Falaq Ummie tace nan zasu dawo suma tafi son ganinmu a tare waje guda. Sai kuma mai gayya mai aiki muna dai anan nasa sashen na fil azal. Sai dai yanzu daga ni sai shi ne. An kawo sabbin masu aiki maza da mata. Kowa ya yaba Ummie harda hawayen farin ciki, dan Maash Mansion ya koma ainahin wanda ta tsara a rayuwarta. Bamu wani hutaba sosai a washe gari da safe jirginmu ya sake ɗagawa zuwa Kano ta dabo tumbin giwa.......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒔𝒊𝒙_


......Motocin da suka ɗakkomu daga airport na shigowa gidan da suka kawomu na ganesa. Kallonsa nayi kawai, ganin ni yake kallo shima yasa na ɗan hararesa kaɗan. Sai ya saki mun ƙaramin murmushi. Murya can ƙasa ya ce, “Kin gane gidan ne?”.
“Hummm taya zan mance sa. Gidan da akayi kidnapping ɗina”.
“Harda sharri abun”.
Kwantar da kaina nayi a jikin hannunsa ina murmushi. Na ce, “Babu wani sharri sai gaskiya. Ai kaida Yaya Hayat ko humm”.
“Miza'a mana?”
Ɗan far nayi da idanu na, cike da shagwaɓa na ce, “Sai na bama yaranku labarin rashin jin da kukayi”.
Murmushi yayi kam yanzu sosai har haƙoransa na bayyana. Yayinda na shagala da kallonsa dan in yay irin murmushin nan ba ƙaramin ƙyau yake masa ba. Kaɗan na kaima kumatunsa sumbata. Kafin yace wani abu na buɗe motar na fice abuna. Ashe ma kowa ya fito mune kawai a mota. Duk sai naji kunya ta kamani. Haka dai na dake. Shima fitowa yay fuskar nan a haɗe kamar ba shi ya gama murmushi ba yanzu yana ƙoƙarin gyara rigar suit ɗinsa. Ido muka haɗa nai saurin ɗauke nawa na maida ga little Awwab dake hannun Hafizzullah.
Duk da gidan ba wani ƙatoto bane ba dan ko kashi ɗaya bisa takwas ɗin Maash Mansion bai kaiba shima dai yayi ƙyau. Kuma yana da nasa girma gwagwado da zai ɗaukemu mu dukanmu. Duk a falo muka zube kowa na maida numfashin gajiyar tafiya duk da ba wani nisa bane. Amma kasancewar ta jiya bata gama sakinmu ba sai duk gamu nan dai. Shi dai uban gayyar bai zauna ba ya shige bedroom ɗinsa. Sai TJ da Hayatu ne keta ɗawainuya da mu. Bamu wuce mintina goma ba aka kawo mana abinci daga gidan su Bahijja. Hameed ne da wannan aikin. Ya zauna an gaisa aka ɗan taɓa hira yace zai wuce. Aiko Bahijja ta maƙale masa dan tana kewar gida. Ba'a hanata binsa ba dan tayi ƙoƙari ma.
Muma dai abincin kawai mukaci na marairaicewa Ummie kan zamu fara gaba ni da Falaq da Hafizzullah kafin su taho anjima. Dan har yanzu tara ma batayi ba. Hanyar bedroom ɗin da Maash ya shiga Ummie ta nuna min. Ta ce, “Maza jeki mijinki ne da wannan ikon. Idan ya amince ni nawa addu'a ne daughter. Kema tashi ki gayama naki”. Tai nuni da Falaq. A kunyace duk muka tashi, yayinda Fahad da Hafizzullah ke faman mana dariyar shaƙiyanci. Samarin nan sun ishi kowa. Bare mu da suka sama ido ALLAH ya aurar da su mu huta dai. Idan kuma da mai so a fans ɗinki bily yazo na sayar masa😂.
Banyi mamakin samunsa yana barci ba hankali kwance. Dama nayi zargin hakan tunda naga ya shiga bai fito ba kusan awa ɗaya da rabi. Ashe shi barcinsa yake sha hankali kwance. Kayan daya cire ya zube a kujera yana cikin duvet abinsa ya ƙure ac ya rage fitilar ɗakin kamar dare. Kusa da shi na ɗan zauna dan harga ALLAH na matsu naje naga ƴan uwana bazan iya haƙura har sai ya tashi dan kansa ba. Sai da na ɗan zubama fuskar tashi ido na kusan mintuna biyu kafin na kai yatsana saman girarsa mai cike da baƙin gashi na shafa. A hakankali na gangaro har saman hancinsa na sauka kan mitsitsin bakinsa. Sosai barcin ya masa nauyi dan bashi da alamar motsawa. Sai kawai na rankwafa na sumbaci lips ɗin nasa. Ina ƙoƙarin janyewa caraf aka riƙe nawan. Idanu na waro sosai dan mamaki. Ashe idonsa biyu yay likimo. Mintsini na dinga kai masa amma kota kaina baibi ba, sai ma jawoni da yay saman gadon ya sakani cikin bargon. Duk shagwaɓa da roƙon da nake masa yay kunnen uwar shegu dani ya shiga yin yanda yaso dani. Bamma san na bada kai bori ya hau ba. Dan mutumin nan ku barni da abuna kawai ni nasan sirrin kayana.

Cike da shagwaɓa nake kallon agogo tamkar zanyi kuka. Shiko ko'a kwalar rigarsa gashinsa yake tsanewa tamkar bai san inayi ba. Haka na ɗauka mai na shafa na gyara fuskata inata faman kumbure-kumbure. Rasa yaya ma zanyi nayi, dole na ɗauka waya na kira Aunty Falaq nace ta taimakeni da akwatin kayana. Dariya ta dingamin da tsokana, sai da taji zan mata kuka tace gashi nan a kofar ɗaki ta ajiye. Haka na leƙo na ɗauka. Shiri nayi cikin siket da rigar lass da duka min ƙyau sosai na fito a matar Maash ɗina. Shi dai yana zaune yana kallona. Sai da na gama nazo inda yake, cikin sanyin murya na ce, “Yaya to waye zai kaimu?”.
“Ina?”.
Ya tambaya cikin halin ko'in kula. Idanu na waro ina kaiwa zaune kusa da shi. Cikin sake marairaice wa nace, “Dan ALLAH my Hot kada kasa na maka kuka. Kafa san gidan Abba zamuje yaufa ne sunan. Ɗazu ma tambayarka Ummie tace nazo nayi shine.. shine kai kuma...”
Na kasa ƙarasawa.
“Uhhm Ni kuma! Ni kuma mi?”.
Ya faɗa cike da salon ɗage gira sama. Hannayena duka biyu na saka kan fuskata na ce, “Ai ba saina faɗa ba. Dan ALLAH kace muje ALLAH so nake naje naci shinkafar sunan irin saukewar farko ɗin nan kaga fa har sha biyu saura”.
“Ohhh kice kwaɗayi ma zaki je ashe?”.
“ALLAH Yaya Awwab bazaka gane ba. Tunfa muna Spain nake sha'awar cin shinkafar suna, kaga tunda yanzu ga dama ai sai naje naci ko”.
Idanunsa da ya kafeni da su ya ɗan jaa luuu yana jinjina min kansa. Sai kuma ya kalla agogon ɗakin. A saman lips ya furta, “Sai yaushe zaku dawo?”.
“Lah Yaya bacan zamu kwana ba wai?”.
Kansa ya girgiza min alamar a'a. Sai kuma ya miƙe ya nufi akwatin ya ɗauka kaya. Sai da ya kammala sakawa sannan ya dawo inda nake da wani ƙaramin kit a hannunsa. Sarƙace ya ciro a ciki da kansa ya saka min harda ƴan kunnenta da zobe da abin hannu. Tayi ƙyau sosai daka ganta kaga diamond. Kallonsa nayi idanuna cike da ƙwalla. Sai ya ɗauke kansa tare da faɗin, “Let's go”. Baki na buɗe zanyi magana ya ce, “Shiiiii!!! Bana son surutu”. Daga haka yaja hannuna muka fice. Falaq da Fahad da Hafizzullah kawai muka samu a falo wai suna jirana. Sai Hayatu dake waya a gefe Little Awwab a hannunsa. Gaisheshi suka shiga yi, ya amsa musu da kai, kafin ya tambayesu su Ummie. Falaq tace sun kwanta suna hutawa wai kar a tashesu sai lokacin tafiya gidan suna. Murmushi kawai ya ɗan yi da maida kallonsa kan Hayat daya gama wayar ya nufo mu, sai da ya amshi little Awwab a hannunsa sannan yay masa nuni da mu. “Waɗan nan ya za'ai da su?”.
Murmushi Hayatu yay da amsa masa da “An gama shirya motocin tafiyar tasu. Hafiz da Fahad sunce zasu iya kaisu sai guards da zasu musu rakkiya, idan sun ajiyesu sai su dawo”.
“Okay yayi hakan ma”.
Daga haka yaja bakinsa yay shiru. Sai Hayat yace muyi himma. Sosai dukanmu farin ciki ya kama mu. Musamman ma su Fahad da aka samu ƙafar gantali, dama a matse suke tun ɗazun. Banyi zaton zai biyomu har wajen ba. Amma a mamakina sai naga ya miƙe riƙe da little Awwab ɗin ya kama hannuna muka fito. Har jikin motar da zamu shiga ya buɗe min da kansa yay min nunin na shiga. Tsayawa nai kawai ina kallonsa kamar yanda shima yake kallona. Sai da mukaga hasken camara kammu sannan muka dawo hayyacinmu. Duk juyawa mukai, Hafiz da Fahad ne ashe ke ɗaukar mu hoto. Da sauri suka shige mota suna shafar kawuna. Nima sai kawai na shiga inda ya buɗe min ɗin na zauna. Ɗan duƙowa yay ya gyara min gyalena da ya ɗan sauka sannan ya saka mun little akan cinya ya sumbaci gefen kumatuna. Cikin kunne ya raɗa min, “Banda rashin ji babyna bata gama ƙwari ba”.
Kafin ma na ɗago na kallesa ya janye jikinsa ya rufe ƙofar. Kallonsa nayi idanuna a narke. Kafin na motsa lips ɗina a hankali na furta, “Zanyi kewarka”.
Wani ɗan iskan Murmushi ya sakar min da ƙanƙance idanunsa ya ɗan ɗage min gira ɗaya. Sai kawai na duƙar da nawa kan nima ina murmushi ganin Hayatu na kallonmu. Sai da muka fita a gate ɗin Fahad dake gefen Hafiz dake driving yay gyaran murya da faɗin, “Gaskiya mudai Aunty a dinga sassautawa kar a ƙona mu”.
Daga ni har Falaq kallonsa mukayi, duk da nasan baya cema Falaq aunty. Yayinda Hafizzullah ke dariya ya ce, “Faɗa musu dai. In ba haka ba ALLAH ban komawa school sai da mata”.
Dariya Falaq ta saka, yayinda na riƙe baki ina kallon Hafizzullah ɗin ta mirror. “Lallai yaron nan zama da Fahad yasa kaima ka fetsare ko? Aiko

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login