Showing 318001 words to 321000 words out of 438336 words

Chapter 107 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2207

ya tashi ma Maman tata. Bata ɗauki hakan komai ba sai tunanin wajen yankan ne bai gama warkewa ba. Sannu-sannu suna zuwa asibiti ganin likita kwatsam randa jiki ya rikice sai aka tabbatar mata Mamanta fa nada ƙanjamau. Ga tsutsa na fita mata ta baya Sakamakon abin da take aikatawa dan bata amfani da maganin da masu wannan ɓarna ke sha. Hankalinta ya tashi, taje domin sanarma Commondo ya sake taimaka musu ta samu baya nan yayi tafiya wai. Hankalinta ya tashi, dan asibitin basu riƙesu ba dole suka dawo gida. Wata sabuwar ƙyama da tsangwamace aka fara musu, bataga laifin mutane ba dan ko ita dauriya take saboda warin da mahaifiyarta ke fitarwa ta bayanta daya zazzago. Takai ko zama bata iyayi ma sannan toilet baya iya riƙuwa gareta. Babu kalar kukan da batai ba da magiya amma ina abinci da zasu ci ma ya gagaresu balle omon da zata tsaftacema Mamanta jiki. A haka suka kwashi watanni uku. Kwatsam wata rana zuciyarta ta ayyana mata zuwa wani company neman taimako anan bayansu. Dan haka ta shirya taje. Securitys basu barta ta shiga ba duk da magiya da kukan data dinga musu. Dole ta tsugunna a bakin gate ɗin ta cigaba da kukanta. Tafi minti talatin a haka sai ga wata dalleliyar mota mai azabar ƙyau. Harta gotata aka dawo baya. Magana driven ya mata, hakan yasata miƙewa zaram jikinta na rawa ta nufoshi. Cikin tsawa-tsawa ya tambayeta mi take yi a wajen?.
Jikinta har rawa yake dan tsoro ta sanar masa taimako take nema. Sai da ya gama saurarenta yay mata tsawa tabar wajen. Har ta juya zata tafi tana kuka sai kuma ya dakatar da ita. Hotonta ya ɗauka yay danne-danne a waya. Babu jimawa taga ya ɗago ya kalleta da murmushi. “Yarinya kakarki ta yanke saƙa shiga mota oga yace zai taimakeki a kaiki”. Cike da farin ciki ta shiga motar, shi kuma yay reverse ya koma batare da ya shiga companyn ba. Wannan shine mafarin haɗuwarta da Paah. Dan an kaita garesa wani gida, Maimakon ya taimaka mata bayan ta gama zayyane masa damuwarta kamar yanda ya buƙata sai ya nuna mata sai idan ta biya masa buƙatarsa. Da farko taƙi har tai fushi ta tashi zata fita. Sai dai tuna halin da mahaifiyarta ke'a ciki ya sakata komawa garesa. Babu ko tausayi kuwa ya keta mata haddi, a kuma ranar ta fara sanin namiji. Bayan ya gama abinda yaso ya bata kuɗi har naira dubu ɗari biyu. Haka ta tafi tana kukan baƙin ciki da na farin cikin samun kuɗin da zata kai mahaifiyarta asibiti. Sai dai me tana zuwa ta samu mahaifiyarta ta mutu an jehota ma bakin bola mutane yayyaɓe da ita suna kallo da zagin gawarta. Wannan al'amari ya ɗimautata. Ɗimautawar data yanke jiki ta faɗi bata tashi farkawa ba sai a gadon asibiti. Bayan ta farfaɗo ta fahimci commondo ne ya kawota asibitin... Wannan shine sanadin komawarta hannunsa. Ta bashi labarin komai daya faru, ya nuna ɓacin ransa tare da tabbatar mata ita da kanta sai ta ɗauki fansa dan yasan wanda yay mata wannan aikin saboda sunan companyn data faɗa. Commondo ne ya kawota Maash Mansion a sanadin Jannifer da ya jima da sani ta sanadin Hajiya ƙarama. Da farko Paah ta firgita da ganinta, dan ta tabbatar masa saita tona masa asiri a wajen ɗansa da abinda yay mata. Aiko fa ya rikice yace ta faɗi duk abinda take so. Sai da ta gama ja masa rai sannan tace zata cigaba da zama a gidan, duk wata kuma zai yanka mata albashin naira miliyan ɗaya. Hankalinsa ya tashi ya nema ta sassauta masa dan miliyan ɗaya duk wata tayi yawa ai. Badan baida kuɗin bane ko hanyar samunsu. Sai dai gudun kar Awwab ya gano shi ne. Dan dole de kuɗin zai dinga fiddasu ne daga asusun company. Da ƙyar ta yarda da 200k duk wata. Dole kuma hakan yake biyanta. A hankali kuma ya fara jan ra'ayinta suka cigaba da mu'amala. Koda ta sanarma Commondo sai yace ta cigaba da biye masa ta hakane ai zata cimma burinta itama.. ta cigaba da biye masa, tare da cigaba da ɗibama Commondo bayanan duk da yake so a gidan musamman akan Hajiya Ƙarama da zuwa yanzu ita kanta ta gama gane alaƙarsu, ta kuma san Arwa ƴarsa ce. Sai dai bata taɓa tunanin bama wani bayanan nan ba dan da iya gaskiyar zuciyarta take ƙaunar Commondo matsayin Yaya daya taimaketa a lokacin da kowa ya gujeta.........✍️

_(Hummm ALLAH ya rabamu da mummunar ƙaddara. Da yawan yaranmu idan mummunar ƙaddara ta gitta ma rayuwarsu nakasassun zukatanmu suka gagara taimakonsu a matsayinmu na al'ummarsu, sheɗancin mutane irin su Paah yay tasiri a kansu ko muka dinga musu hisabi da laifin iyayensu ko wasu ahalinsu sai irin su Commondo da akema kallon gurɓatattu su rungumesu, su tallafesu, komi tsarkin zukatansu sai su koma irinsu suma. Kamar dai Siyama. A yanzu zuciyarta ta gama bushewa. Ko kisa Commondo yace tayi wlhy zata aikata saboda shi kaɗai takema kallon girmamawa. Dan ALLAH mutane mu gyara, mu kiyayi hukunta wasu da laifin wasunsu. Hakan na maidamu bayane da sake raunana al'ummar mu da fiddo gazawarmu a fili. ALLAH ka yafe mana kurakuranmu baki ɗaya. Ka shiryemu ka shirya mana zuri'a. ALLAH ka rabamu da mummunar ƙaddara. Ka kiyaye mana mutuncin mazajenmu karsu jawo ma ƴaƴanmu da mu abin kunya ta hanyar aikata mummunan aiki😭🙏. Yanzu idan Awwab yasan gaskiyar irin waɗan nan abubuwan da Paah ya aikata dan akwai ire-iren hakan da yawa da wace kalma zai iya kare kansa. Ummie Ummie Hummm ya rabba🙏😭)_


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_


......Kuka sosai Fahad yaci a jikin Ummie itama tana taya shi da sake jin tausayinsa, dan kiyayewar UBANGIJI ce kawai tasa yaronta bai lalace ba. Sai Mama ke lallashinsu. Dan Maash ya fita zuwa asibiti ɗakko Samraah kamar yanda yay ma Ummie alƙawari.

Ina zaune a saman abin salla dana idar da shafa'i da wutri hannayena biyu tallafe da fuskata na afka duniyar tunani. (Ko ina Yaya Awwab ya shiga ne? Ina Fahad da Hafizzullah? Da har yanzu ko mai kama da su ban gani a asibitin ba. Shin Ummie fa? Aunty Falaq kota haihu?) Waɗan nan tambayoyin sune fal zuciyata. Sai kuma zancen ɓatan Paah ɗin nan yana cimun rai da saka tunanina rarrabuwa akan Matarsa da Kakansu. Saukar soft hand mai sanyi akan nawa ya sani ɗago idanuna. Sosai naji shock ɗin ganin wanda banyi zato ba. Dan sam ba ƙamshinsa bane dana sani kamar dai ranar nan. Sai kawai raina ya bani yau ma na sake yin mafarkinsa kenan. Numfashi na ɗan sauke da cigaba da kallonsa dan na gama yarda mafarkin nakeyi ɗin.
Cike da wani irin salo ya ɗan ɗage girarsa duka biyu da mun alamar kallon fa?. Samun kaina nayi kawai da ɗan ɓata fuska. Cikin ɗan ƙunƙunin da nai zaton duk a mafarkine kawai na ce, “Ni ka bar min gizo”.
Idanu ya ɗan lumshe a hankali. Tare da rungumeni a jikinsa. Gaba ɗaya naji jikina ya wani mutu. Musamman da ya ɗaura mitsitsin bakinsa akan kunnina can ƙasan maƙoshi ya furta, “Kona mutu sai na dinga zuwa miki a fatalwa ma”.
Da sauri nayi ƙoƙarin janye jikina zuciyata na harbawa da sauri-sauri. Amma sai ya hana hakan yama sake ƙanƙameni da ƙyau yana sakar min numfashin sa a cikin kunne. Dole na sake ƙanƙamesa muryata na rawa na ce, “Please Ya Awwab mafarki nake ko gaske kai ne?”.
Baiyi magana ba, sai mintsinin da ya sakar min a gefen cinyata babu shiri na ɗan gantsare tare da faɗin, “Ouch!!”. Ina ɗan kai masa duka a bayansa. Ɗagoni yay yana kallona cikin ido, kafin ya motsa lips ɗinsa a hankali ya ce, “Kin yarda ido biyu ne?”.
Murmushi na sakar masa nima tare da faɗawa jikinsa na ƙanƙamesa. Cikin rikicewa nake jera masa tambayoyi. “Yaushe ka dawo? Ina ka shige ne? Ina Ummie na? Aunty Falaq ta haihu ne? Anga Paah? Ina Fahad da Hafizzullah ban gansu ba.......”
“Shiiii!!!. Wanne zan amsa a'a ciki to? Ammien unborn”.
Ya faɗa cikin kunnena da raɗa. Ajiyar zuciya na sauke tare da ɗagowa ina kallonsa. Idanuna cike da ƙwalla na ce, “Please My Lion duka ka amsa min, waye kuma Ammien Unborn ɗin?”.
Nunani yay da yatsa.
Sai naji gabana ya ɗan faɗi, muryata har rawa take na ce, “Ban gane ba ALLAH Yaya”.
Ido sosai ya zuba min kawai yana kallona. A hankali na fara ganin ƙyalli a cikin idanunsa alamar hawaye na taruwa. Sai kuma ya ɗan duƙo ya sumbaci idanuna dake kallonsa da hancina da baki na. Kafin ya riko hannuna shima ya sumbata. Murya can ƙasan maƙoshi lips ɗinsa na motsawa a hankali ya furta, “Samrh! ALLAH ya mana ƙyauta da abinda kuɗi ko ƙarfin mulki basa badawa. Naso yin kuskuren wasa da rayuwar ƙyautar da UBANGIJI yay mana. Am sorr...”
Da sauri na kai hannu na rufe masa bakin ina girgiza masa kai. Hawaye na silalo min na ce, “Baka min laifin komai ba Yaya. Dan ALLAH karka bani wani haƙuri. Komai daka gani a rayuwar bawa ƙaddararsa ce tazo da hakan. Ina tayaka murnar samun ƙaruwa”. Na ƙare maganar da shigewa jikinsa sosai na ɓoye fuskata dan kunyarsa naji tana sake shigata mai tsananin. Ga wani irin farin ciki na matuƙar ratsani wai ni Samraah ke ɗauke da ciki irin na haihuwa. Nima zan zama Mama”.
Sake ƙanƙameni yay sosai a jikinsa shima kamar zai maidamu abu ɗaya cikin kunnena ya furta, “Nima ina tayaki murnar samun ƙaruwa Aljannata”.
Dariyar na sake ƙyaƙylƙyalewa da shi ina sake ɓoye kaina a cikin jikinsa. Sosai naji motsin fitar sautin nashi murmushin shima a cikin ƙirjinsa. Mun jima a haka kafin ya ɗagoni ya sumbaci lips ɗina. Tare da nuna min nashi alamar nima nayi masa. Kafaɗa na maƙe masa alamar naƙi ɗin.
Fuska ya ɗan yamutse yana wani ɓata ta. Hakan ya sani kai yatsana manunuya na ɗalli small pinkish lips ɗinsa ina murguɗa baki da faɗin, “Ɗan kurma kawai”.
Ƙaramin murmushi ya ɗan saki da alamunsa kawai na gani ya ɗauke kansa. Batare da yayi maganar ba dai ya miƙe dani a haka ya nufi ƙofar fita. Mamakine ya kamani, da sauri na ce, “Yaya bafa a sallaman ba. Ina zaka je da ni”.
“Saidawa”.
Ya faɗa a taƙaice yana ficewar dani. Dole sai nice na lumshe idanuna tare da ɓoye fuska a ƙirjinsa saboda kunyar mutane. Dan muna fitowa a ƙofar ɗakin mukaci karo da ƴar sandar nan. Mugun sandamewa tai tana kallonmu, sai da muna gab da gitttata ta ɗan dawo hayyacinta tana gaishesa. Amma bai ko kalleta ba balle naji ya amsa yay gaba. Sai jina nai ya saka a mota shima ya shiga. Kwantar dani yay kaina a saman cinyarsa. Bamma san wanda ke janmu a motar ba sai da Hayatu ya ce, “Auntyn mu yaya jikin?”.
Da sauri na buɗe ido muryata har rawa take na ce, “Yaya Hayat da ma harda kai?”.
Ƙaramar dariya yayi da faɗin, “Eh mana”.
Ajiyar zuciya na sauke mai ɗan nauyi. Ban sake magana ba sai yunƙurin tashi zaune. Sai dai gogan ya maidani ya kwantar yana tsuke fuska. Dole na haƙura na koma na kwanta. Daga ƙarshe ma na lumshe idanuna tare da juyar da fuskata ina facing cikinsa. Daga haka nayi luff sai sauraren wayar da aka kirashi yake amsawa nakeyi. Sai dai furucinsa yay matuƙar ɗaukar hankalina. Dan cikin kaushin harshe yake faɗin, “Ko waye ya taɓa koda bangon gidan ne a cikinsu ku kamashi yallaɓai”.
Ban san mi'akace masa daga can ba. Na dai ji ya yanke wayar kamar a ɗan fusace ya wurgata sit ɗin gaba na gefen Hayatu dake driving. Daga haka ya kwantar da kansa shima jikin kujerar ya lumshe idanu. Babu wanda ya sake magana har sai da naji alamar gida muka dawo. Bamma san na ware idanu ina kallon ikon ALLAH ba. Har ƙofar sashensa Hayatu ya faka motar. Duk yanda nake masa kallon mamaki shi yaƙi yarda mu haɗa ido, sai ma taimaka min da yay na fita a motar, kafin nai wani yunƙuri ya ɗaukeni cak babu ko kunyar Hayatu dake a wajen ya nufi sashensa da ni. Ni dai na riga na faɗa a hannun ƴan sari sai a hankali. Dan kunya dai kam wala a idanun Maash. Banyi zaton akwai kowa a sashen ba sai da muka shigo falon, jin ya tsaya cak yaƙi saukeni yaƙi magana kuma yasa na buɗe idanun nawa. Haɗa ido mukayi, dan haka na ɗan ɗaga gira da kaɗa idanun nawa alamar yaya dai.
Nasa kan shima ya jinjina da cat eyes ɗinsa ya mun nuni da cikin falon. Ai babu shiri na kalla falon da sauri wlhy duk zatona wani abu yake nuna min. Amma mi sai caraf idanuna akan Fahad, Hafizzullah, Aunty Falaq. Ummie, Mama Balki. A wani irin ruɗewa na dirgo jikin nasa. Na koma bayansa da sauri na ɓuya ina jin tamkar ƙasa ta tsage na shige ciki. Dariya Falaq da Hafizzullah da Fahad suka kwashe da shi. Hakan ta sani sake maƙalewa a bayansa ina jin kamar na saki ihu.
“Haba ƴar Ummie yaya da ɓuya kuma?”.
Wani karyayyen harshe mai nuna rauni da sanyi ya ratsa cikin kunnena. Fuskar Ummie da tai min kamar gizo a kallon dana musu ɗazun ce ta shiga dawo min. Da sauri na ɗan leƙo kaina daga ta bayan nasa zuciyata na harbawa. Sai kawai Maash ya damƙoni ya kawo gabansa. Rawa jikina ya fara ganin tabbas fuskar Ummie ce zaune Hafizzullah da Fahad sun sakata tsakkiya ga baby a cinyarta. Da ƙyar na haɗiye busashen yawu na na furta, “Ummie!”.
“Yes dear”.
Ta faɗa fuskarta na sake ƙawatuwa da fara'a. Sake daburcewa nayi, na juya na kalla Maash dake bayana a tsaye har yanzu. Sosai idanuna suka firfito. Sai dai na gagara magana. Hannuna ya kama tare da fara tafiya da ni a hankali har gabanta. Bamma san na ƙwace hannun ba na zube a gaban nata gwiyawu biyu a ƙasa jikina na rawa. Hannunta ta miƙomin, ai da sauri na ɗaura nawa akai ina ƙarasawa jikinta da jan gwiwa. Sai kawai na samu kaina da fashewa da kuka na faɗa jikinta na rungume ita da jinjirin saman cinyarta. Itama ƙanƙamenin tayi da ƙyau a tare muka saki kuka. Munfi mintuna biyu a haka har sai da yay ƴar gyaran murya Mama Balki tazo ta ɗagomu Hafiz ya zare jinjiri da muka matse sannan muka tsagaita. Fuskata Ummie ta riƙe a cikin tafukan hannayenta cike da nuna ƙauna ta ce, “Yaya jikin naki?”.
Kuka na sake fashe mata da shi da rungumeta sosai na ce, “Ummie na warke. Ummie dama kin gama ibadar ALLAH shine babu wanda ya sanar min. ALLAH kaine gagara misali. Ikonka da hukuncinka zartaccene akan komai. Ya rabbi muna godiya da dukkan ni'imokinka garemu. Ya ALLAH ka hanamu saɓa maka akan son zuciya”. Sai kuma na zame a hankali nayi sujidar shukur. Naja tsahon mintuna kafin na ɗago ina mai jera godiya ga UBANGIJI. Kafin na sake ɗagowa na rungumeta.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒔𝒊𝒙_


.......Zuwan likitan Ummie ya taƙaita zaman namu. Duk da dai an ɗan taba hira da zaka iya rantsuwa da ALLAH mun jima da sanin juna musamman ma Ummie da ke jan kowa jikinta. Barcin da allurar ke saka Ummie yasa dole taje ta kwanta. Mu kuma muka dasa sabuwar hira duk da dai akan abinda ya faru ne ga kowannenmu a kwanakin nan uku. Mama Balki ce da taga dare na ƙara zurfi dan Maash tunda ya raka Ummie ɗaki ya haye sama abinsa bai sakko ba tace nima na tashi na wuce tunda ba lafiya gareni ba. Badan naso ba dole nabi umarninta dan dama ƙarfin haline kawai sam bana jin daɗi.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login