Showing 219001 words to 222000 words out of 438336 words

Chapter 74 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2238

jimasa ciwo. Sai ga saman yatsunsa duk jini ya ɓata. Da sauri Paah ya kamo hannun nasa jikinsa har rawa yake. Amma Maash ɗin sai ƙoƙarin ƙwacewa yake yi. Dan so yake kawai ya ƙara kaima mirror ɗin duka ko zai samu sauƙin zugin da zuciyarsa ke masa...
“Please sweetheart relax. Dan ALLAH try to calm down. Jifa yanda kake jima kanka ciwo Muhammad”.
“Is not your business Paah. I beg you leave me alone”.
“Naƙi ɗin, nace maƙi na barkan! Miyasa kake da zuciya ne Muhammad. Fushinka yayi yawa. Taya zan Barka ka cigaba da jima kanka ciwo. Nace kayi haƙuri! Haba Muhammad”. Ya ƙare maganar cikin sanyin murya tare da jawoshi jikinsa ya rungume. Abinka da su duka dogaye, sai gasu kai ɗaya. Ƙarfi da cikar zati kawai Maash zai nuna masa saboda shi yana akan ƙuruciyarsa, shiko koba komai girma ya kamashi.
Luff Maash yayi a jikin mahaifin nasa, sai faman sauke zafafan ajiyar zuciya yake a jajjere. Yayinda Paah ke jin yanda zuciyar tasa ke gudu da ƙarfi. Sunfi mintuna uku a haka sannan ya ɗagosa. Kama hannun nasa yay suka nufi wajen gadon, zaunar dashi yay sannan yaje ya ɗakko first aid box ya dawo kusa da shi ya zauna. Hannun nasa dake ta tsatstsafo da jini ya kamo, cike da kulawa ya fara masa treating. Ko sau ɗaya Maash bai motsa ba, bai kuma kalla mahaifin nashi ba har ya kammala ya naɗe masa da bandage. Zama yay zai fara magana Maash ɗin kawai ya miƙe, da sauri Paah ya riƙosa ya maida shi ya zaunar. Bai musa ba ya zauna, sai dai yaƙi kallonsa yanzu ma. Shiru Paah yay yana kallonsa, sai kuma ya sauke numfashi a hankali yana sake tattaro abinda yake son faɗar. “Muhammad kayi haƙuri, tabbas nasan bana ƙyauta muku, sannan ban yima kaina adalci ba. Bazan kira abinda nake aikatawa da ƙaddara kawai ba, harda sa kai. Shiyyasa tabbas a rayuwa ka guji aikata mummunan aiki a ƙuruciya, idan kuma ya zama jarabawarka ce ka fara kayi gaggawar tuba. Idan ba haka ba wannan abin zai ta bibiyarka ne a lokacin girma, a lokacin da kuma kake son ka daina ɗin amma abin yabi jininka. Wannan maganar mahaifiyarka tasha faɗa min ita da maimaita min a duk sanda ta sameni a halin rashin gaskiya. Amma mi a lokacin bana gane karatunta, gani nake ai duk sanda na shirya zan iya dainawa”. Yay murmushin takaici, mai nuna ainahin ciwon da yake ji a zuciyar yasa. Cikin ɗan yarfar da hannu ya cigaba da faɗin, “Abubuwa da yawa sun faru, wasu ma suna kan faruwa da ni kaina ban san adadi ba. Ni ne ya kamata ace na tsaya muku, amma sam ban taɓa yunƙurin hakan ba koda sau ɗaya. Hatta da rashin Fahad a kusa da mu yana damuna. Sai dai ban san taya zance komai ba. Muhammad! Banso ace halin da nake ciki yayi nason da zai shafeku ba kamar yanda mahaifiyarku tasha yin fata. Sai dai a wannan gaɓar na fahimci zancen nan na masu iya magana da kance TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE. Wlhy bazan ɓoye maka ba, case ɗinka akan yarinyar nan ya tsaya min ta yanda na kasa haɗiyeshi, sannan yanda kake bama yarinyar kulawa tamkar ba abinda ake gudu bane ya shiga tsakaninku na sake ɗaga min hankali. Bana son ace sunanka ya ɓaci a duniya Muhammad, wlhy bana son abinda wani zai aibantaka da shi, koda bazan ce komai ba ina jin zafi, matuƙar zafi a cikin zuciyata. Dan ALLAH ina roƙonka idan an sallami yarinyar nan daga asibiti gobe idan ALLAH ya kaimu zan haɗa mata sha-tara ta arziƙi tare da siya mata ticket ɗin jirgi idan ba ƴar cikin garin nan bace ta koma garinsu. Idan kuma a cikin garin nan take da iyayenta nasan zata iya yiwuwa a gidan haya suke ko wani muhalli ƙaskantacce. Zan saya musu gida a ɗaya daga cikin jihohin arewa su koma can, kar su sake waiwayar Lagos har abad....”
Karan farko Maash ya zuba masa idanun kawai yana masa wani irin kallo mai wahalar fassara. Kallon ne ya dinga ratsa Paah sai ya gagara ƙarasa abinda ya faro ya ja bakinsa kawai yayi shiru. Wani irin murmushin ƙasaita da ɓacin rai Maash yayi, sai kuma ya ce, “Ya kayi shiru kuma, ina jinka Paah.”
“Saurarena kawai kake amma ba jina ba Muhammad abar maganar kawai”. Ya faɗa cikin ɗan borin kunya da kame-kame. “Ka kwanta ka huta dare yayi, zuwa safiya sai mu ƙarasa, amma ka daina kira min ƙara aure har ma na mata uku, kai ka sakar min Ummu-Hidaya ɗin ne da kake cireta a matsayin matata”. Ya sake faɗa yana nufar ƙofa cikin ƴar sassarfa ya fice. Tsahon lokaci Maash ya ɗauka yana kallon ƙofar kawai. Sai kuma ya cije lips ɗinsa da masifar ƙarfi zuciyarsa na masa wani irin suya. Yasan mahaifinsa fiye da sanin da kowa ya masa a rayuwa. Amma bazai ce komai ba ALLAH mai ji ne mai gani. Yana kuma roƙonsa ya shiryeshi...

🤥Humm, kai dai Paah ALLAH ya shiryeka dai to gaskiya😏. Yayanmu kayi haƙuri mahaifi mahaifine koda na banza ne😭.

💦✨💦✨💦

Tun wucewarsa daga asibitin abubuwa suka sake cinkushe min kai. Kalamansa sai faman maimaita kansu suke a cikin kaina. Duk da nasha magani zafin zazzaɓin nan yaƙi bari na. Zaune na tashi ina kallon Mama Balki da barci ya ɗan fara figa. Sai kuma na miƙe cikin sanɗa na nufi ƙofar fita.
“Samraah ina zaki je?”.
Muryar Mama Balki a bazata ta daki cikin kunnena. Cak na tsaya tare da runtse idanuna. Sai kuma na juyo a hankali cikin son wayancewa zanyi magana ta dakatar da ni.
“Baki iya ƙarya ba Samraah, kada ki farata yanzu”.
Sosai furucin nata ya dakeni, dan haka na sauke ajiyar zuciya tare da dawowa a hankali na koma saman gadon na zauna. Kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hanuna nace, “Kiyi haƙuri Mama. Ba wani abu zanyi ba. Reception zanje na samo pen da takarda zanyi amfani da su”.
“Amma a daren nan Samraah. Na kula tunda Alhaji ƙarami ya tafi baki da nutsuwa. Bana fatan ace kina son samo takarda da biron ne dan kiyi rubutun da zaki bar masa ki gudu”.
A karo na farko nayi murmushi tare da girgiza mata kaina. “Haba Mama, ai a yanzu wlhy koda shine da kansa yace na tafi gidanmu bazan je ba. Dan insha ALLAHU sai na sauke alkawarin dana ɗauka akan Ummie. Kawai zanyi amfani da sune dan ina son yin lissafi dalla-dalla. Ba kuma zai yiwu a cikin ƙwaƙwalwa ba dole sai da taswira a rubuce”.
Ajiyar zuciya Mama ta sauke. Batare da tambayata abinda zanyin ba ta miƙe. “Shike nan ki zauna ni bari na fita na samo miki. Kin san dai ba'a son ki yawaita motse-motse mai ƙarfi saboda ɗinkin jikinki”.
Bance mata komai ba sai duƙar da kaina dana sake yi. Itama sai ta fice abinta bayan ta zumbula Hijjab ɗin ta..........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_


......Mintuna basu fi biyar ba kuwa sai gata ta dawo. Cike da farin ciki ta miƙa min takarda da biron tana faɗin “Kinga Alhamdullah na samu ƴar arziƙi a reception ɗin ma. Ina tambaya babu musu ta ciro ta bani har shida, gasu kuma manya nasan dai zasu isheki ai ko?”.
Nima fuskata a washe da murmushi na amsa ina faɗin, “Yauma Mama Nagode sosai. In sha ALLAHU zasuyi harma ƙila suyi yawa.”
File ɗina na ɗauka na ɗaura a samansu tare da gyara pen ɗin. Gaba ɗaya ahalin Maash Mansion na shiga lissafowa a jere. Wanda na manta ina tambayarta. Hatta da adadin masu aiki maza da mata da aikin kowa sai da na rubuta su. Kafin nabi duk manyan gidan na zana halin kowa dana fahimta agaban sunansa. Hatta shi kansa Maash ɗin harda shi. Daga haka nai shiru ina nazari tsahon lokaci, kafin na ɗaga katifar na saka takardar. Toilet na nufa na ɗauro alwala. Duk da yanda nake jin jikina haka na nutsu na kabbara salla domin miƙama UBANGIJINA kukana tare da kai ƙarar wasu mutane garesa dan ya shigemin gaba wajen gano ainahinsu kozan san inda zan kama a wannan tafiyar dana shirya yi....

🌿💞🌿💞🌿

Sosai biki ya kankama a gidan Abba Imamu. Sai dai gaba ɗaya bai zoma Mom a yanda ta shirya shi ba. Dan har yanzu Abba yaƙi maidata ɗakinta. Babu irin haƙurin da bata bashi ba, hakama Ummanta tazo ta saka wanda yake jin kunya amma yaƙi sauraren kowa. Kasancewar tana a cikin gidan har yanzu yasa mutane da yawa basu san abinda ke faruwa ba. Abun zai baku mamaki idan nace muku tunda Halime ta fuskanci abinda ya faru tsakanin Mom da Abban itama ya kasa gane kanta. Kuka ta dinga masa da magiya da roƙon ya maida matarsa, idan ba hakaba itama gaskiya sai dai ya saketa. Ita haka kawai yaja mutane su tsaneta a dinga cewa dan ya aurota ne ya saki uwar ƴaƴansa. Duk yanda ya nuna mata babu ruwanta a ciki taƙi haƙura ta barsa. Kullum cikin masa nagiya take da kuka gashi bata da lafiya sosai. Dan ta kai ma a yau sai da suka je asibiti saboda yanda take amai gaba ɗaya ta galabaita. An tabbatar musu tana da shigar ciki. Zo kuga murna wajen Abba. Yayinda Halime ido yay gwalo-gwalo. Tabbas tana son yara sosai, kodan yanayin rayuwar data gashi ta tsangwama da rashin sakewa. Bata da wani wanda zatace yau ya zame mata amini tunda ƙaninta ya rasu. Ba kunya Abba na dawowa gida ya barbaɗama Auta. Murna da tsalle Auta ya dinga yi da ga ƙarshe ya kwasa da gudu yaje ya barbaɗama Mom dake tare da ƙanwarta da Ummanta da suketa tsare-tsaren biki da za'a fara nan da kwanaki biyu. Neman ɗaukewa numfashin Mom ya yi, har sai da takai hannu ta dafe goshinta dan wani irin sara mata kanta yayi na masifa. Ganin tana neman ɗagama kanta hankali Ummanta da ƙanwarta suka shiga lallashinta da mata nasiha akan tafa kwantar da hankalinta. Wata fitina ko nuna wani abu a yanzu ba nata bane. Ita da ake lallaɓawa ya maidata ɗakinta ya kamata ace ta nutsu, kai kodan bikin nan da za'a tara mutane ta rufama kanta asiri karta bari ƴan uwansa su samu lagonta. Dan yanda bata riƙesu hannu biyu ba sumafa a yanzu dole su ringa nuna mata cewar amarya ta fita a wajensu. Sannan duk hanyar da zasu ƙuntata mata a shirye suke da nemota komai ƙanƙantarta. Shi kansa Abban yanda yake jin kansa on top akan yarinyar nan yanzu idan fa ta cigaba da matsawa sauran igiya biyun ya tsinketa ba abinda zai damesa bane.
Wannan nasiha da ƙanwarta ta mata ne ya sakata kama kanta badan taso ba. A haka aka shiga shagalin bikin Baby. Danginta da ƴan gwarzo sun cika gida tako ina. Tun ranar alhamis aka fara event, dan wasu irin mahaukatan kuɗaɗe mijin Babyn ke kashewa tamkar baisan ciwonsu ba. Duk da kuwa bikin Abba ya dawo dashi baya ne akan yanda aka sanyashi an zaftare har sati biyu a ciki. Ranar juma'a aka kawo lefe na nunama tsara harda key ɗin motar da aka zubo kayan. Wannan bajinta ta ragema Mom raɗaɗin dake damunta a cikin zuciya game da cikin Halime. Ta dinga yanka ƙananun habaici da ɗagawa ma mutanen Gwarzo. Faɗa take yanzu ne akai biki na ƴar gata ba irin na Samraah da har yanzu basu san ina ya dosa ba. Maybe ma Abba da Musaddiq sun saidata ne ko turata karuwanci. Yo inba haka ba wane irin aurene wata kusan takwas basu taɓa sanin miji ba itama bata taɓa zuwa gida ba. Ai dole ne akwai abin ashshar da ake ɓoye wa. Duk da kalamanta sun tada hankulan su Gwaggo Gudidi duk da zuwa yanzu suna waya da Samraah dan hatta su Kawu Musa tana ɗan kira sai suma suka ji kamar basu ƙyautama Samraah ɗin ba. Amma dai sun shanye a fuskokinsu babu wanda ya tanka Mom da haukarta. Washe gari asabar aka ɗaura aure. Abu na farko daya fara bama mutane mamaki shine ango daga shi sai abokansa guda uku yazo wajen ɗaurin auren. Sune suka amsa masa auren a matsayin waliyyay. Kowa yayi zato da tsammanin yanda yake faman ɓarin kuɗi kamar babu gobe sai ƙofar gidan Abba an rasa wajen faka motocin gayyarsa data ango. Amma sai gasu su huɗu a mota ɗaya rak kamar dangin mayu. Jikin Abba shi kansa ya fara sanyi, sai dai bai iya yace komai ba har aka kammala. Zuwa dare maimakon an shirya amarya a miƙata ɗakinta sai akacema Abba wai ai wajen dinner za'aje sai zuwa gobe ango zai ɗauki amaryarsa daga gidansu sai airport zasuje honeymoon ne. Sai bayan sun dawo zai wuce da ita gidanta. Tofa anan ne fa ƙananun magana suka ɗan fara tashi, haka aka shirya tafiya dinner kowa bakinsa da abin faɗa. A wajen dinner an ɗan ga wasu mata a matsayin danginsa. Sai abokansa da suka ɗan zazzo da matansu. Dan ko wajen bada tarihinsa ƙanwarsa ce ta bada. Dinner kam tayi dinner, dan anci kaji ansha lemon roba gwargwadon iko. Ga bag da aka raba cike da kayan rabo a ciki. Amarya baby da ƙawayenta sai feleƙe ake abin nema ya samu. Haka Mom dan tare da ita akaje dinner sai nuna isa ake. Hatta da Umma sai da taje abinta ko kunya. Ƙarfe ɗaya da wani abu na dare aka tashi, su dai ƴan Gwarzo ma tun kusan goma da wani abu suka saka Musaddiq ya dinga fito da su yana sakawa a napep ana maidosu gida dan sun gaji. Lokacin da su Mom suka dawo su tuni sunyi nisa a barci. Ita kam Halime dama bata da wani sakewa a bikin saboda laulayinta mai addaba ne. Koda yaushe tana ɗaki kwance. Da ƙyar take ɗan yin dauriyar fitowa ta gaida ƴan gwarzo. Dan hakama dinner ɗin bataje ba sukai zamansu ita da Abba a gida yana tattalin kayarsa da lallashi itako tana zuba masa taɓara..
Washe gari lahadi da aka tashi da shirin wucewar baby da mijinta shi kuma Musaddiq ya shirya wutowa Lagos. Sunyi waya da mijin Samraah zai je wajenta ya kwana washe gari litinin zai haɗu da wanda zai masa jagorar wucewa ƙasar Chaina kamar yanda MD ɗin sa ya bashi a rubuce. Dan haka ya shiga sallama da ƴan uwa anata koke-koke. Abinka da tsoffi gani suke tafiya Chaina ɗin nan kamar tafiya lahira ne. Dan wasu ma da farko da ca sukai basu yarda Musaddiq ɗin yaje ba. Sai da Abba ya dinga basu haƙuri da nuna musu muhimmanci da cigaban da Musaddiq ɗin ya samu har suna wataran zai shafesu sannan suka haƙura badan sun so ba. Sai dai sunyi farin ciki da jin shi da Hafizzullah zasu je wajen Samraah ne a yau kafin shi ya wuce gobe. Dan rigima da Hafizzullah ya saka masa akan son zuwa shima yaga Samraah ɗin ne yasa shi fidda yan kudaɗensa ya saya masa ticket ɗin jirgi saboda shi ta sama zaibi zuwa Lagos ɗin sai ya saima Hafizzullah ɗin shima zasu wuce tare. Kafin ma mijin Baby ya iso su sun fito, dan motar company ce zata kai Musaddiq ɗin airport. Haka suka wuce ƴan uwa da abokan arziƙi na musu fatan alheri. Tare da saƙon gaisuwa ga Samraah buhu-buhu aunty Zakiyya harda saƙo a cikin kwali datai nannaɗe da su Musaddiq basu sani ba. Hakama Gwaggo Gudidi ta haɗa kayan maƙulashe irinsu tuwon madara, carbin malam, gullisuwa, aya, gyaɗa, riɗi, cike da leda viva tace a kaima ɗiyarta. Wai maybe tanada ciki kunya ta hanata faɗa, ba kuma a raba masu ciki da son kaya kwaɗayi irin waɗan nan. ALLAH sarki Halime itama sai da ta bada zuma mai yawa a gora da uban aya da take saidawa a kaima Samraahn duk da a hoto kawai ta santa. Ta kuma saka Abba dole ya bada naira dubu hamsin a kaima Samraah ɗin. Sosai Musaddiq yayi mamaki bada waɗan nan kuɗi, amma haka kawai sai yaji a ransa aikin aunty amarya ne. Sosai yaji kima da darajar yarinyar na ƙaruwar masa a rai, har sai da ya share ƙwalla. Dan tunda tazo gidan nan abubuwa da yawa suka sauya. Abincinsa, tsaftar ɗakinsa bata ƙyashin shiga ta gyara, komai kuma tana yimasa a mutunce da girmamawa. Yana kiranta aunty tana kiransa Yaya. Da yay magana sai tace ai ita ɗan uwa take kallonsa kuma babban yaya bawai ɗan mijinta ba. A bata da lafiyar nan duk rintsi bata bari ya fita da safe bai karya ba koda ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login