Showing 426001 words to 429000 words out of 438336 words

Chapter 143 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2150

na faɗa a zuciyata wata irin ƙaunar bawan ALLAHn nan na ratsa ɓargo da jikina..
Gida kam ya amshi baƙi fiye da yanda nayi zato, tsabar farin ciki harda hawaye bayan na rungumesu ko nace nama rasa wazan rungume a cikinsu. Gwaggo Gudidi nata mun tsiya wai ko dai na suma ne. Ashe Ummie ma tasan da isowar tasu mune dai aka ɓoyema ko nace ni. Kowansu ya ɗauki Baby anata sanya mata albarka da addu'oi da kwarzanta kamanninta da babanta. Yayinda Mom ta zama wata abar tausayi, dan bata ma ɗauki Baby ba sai da Abba ya daka mata tsawa da faɗin, “Oh hassadar taki ce ta motsa nan ma kenan Jalilah”.
Yanda yay matan sai ma ta bani tausayi, amma sai naga su su Gwaggo Gudidi ko'a jikinsu. Auta dai na nane dani anata bani labarin Nigeria. Bayan sun huta sunci abinci suma aka kaisu ɗayan gidan domin suyi wanka su huta. Abba kuma aka wuce da shi nashi masaukin shima inda su Fahad zasu kwana yau tunda an ƙara yawa. Koda ya shigo dubamu da dare kasa haƙuri nayi na rungumesa ina hawaye da jera masa addu'oin gamawa lafiya. Murmushi kawai yay da nuna min lips ɗinsa wai na masa kiss. Na maƙe kafaɗa da faɗin, “No Mammi ta hana sai nayi arba'in biyu”.
“Ashe zan gudu dake basu sani ba”. Ya faɗa yana kaiwa zaune. Idanu na waro na ce, “Guduwa fa?”.
“Sosai ma kuwa, su gwada su gani. One week kawai gashi na jigata ace har 80days haba kanwa na kawo duniya ma kenan. ALLAH sai dai su nemeki su rasa sace ki zanyi.”
Ni dariya ma abin ya bani a raina nace lallai ashe da sabon tsalle. Ko na samu tsarki dole na kama kaina kada mutumin nan ya sani inba hakaba ya buɗe min aiki tsaff da laɓuɓuwar jaririya shi ba damuwarsa bace.
A daren akai min ƙunshi da kitso, dan cikin yaran Uncle Sulaiman akwai wadda tai masifar iyawa harda su gyaran jiki. Duk wanda ya kalleni yaga maijego ɗanya jagab. Dan sosai gaskiya jego ya amsheni sai godiyar ALLAH.......✍️

A gurguje Please 🥺


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚_


Follow this link to join my WhatsApp group:

https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq


*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.

*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._

.........Washe gari da safe kowa yasan sunan Baby Ummu-Hidaya, dama hakan dai duk mukai tsammani. Su Yaya Musaddiq da Yaya Hayat da su Fahad sun kasa zaune sun kasa tsaye. Ashe gagarumar walima ake shiryawa batare da mun sani ba. Sai da Hayatu yake sanar mana ya kamata ace duk mu kasance cikin shiri basai anzo ɗaukar mu ba aita wane bai shirya ba wane bai kammala ba. Makeup artist aka kawo min data san aikinta. Wannan kam duk aikin Ummie ne dan da farko Yaya Awwab yaso yin bore tai masa jan ido da faɗa masa kwalliyar ma ba rufin asiri bace tunda tana ɓoye kammanin mutum. A irin wannan taron kowa ke sanin iyalinka idan ma da wani nufi a ransa yay tunanin aiwatarwa, amma idan ya gagara ma riƙe kammani ba shike nan ba. Yin wannan magana sai tasa yay kamar ya ɗan fahimta. Amma dai baice komai ba ya shige ɗaki. Dariya su Fahad sukaita ƙumshewa. Sai da Ummie tace, “ALLAH dai ya baku Sa'a ya jiku kunga ai sai ya huce kanku tunda nidai babu yanda za'ai dani.”
Dariya su Mama Balki sukayi, yayinda Fahad da Hafizzullah ɗin suka fice da gudu. Haka dai badan fa yaso ba akai min wannan kwalliya. Ammafa magana ta gaskiya na haɗu ni kaina nasan nayi ƙyau. Kada fa kice na cika kuranta kaina Bily. Gaskiya nake faɗa miki. Bani kaɗai ba hatta Baby ta fito abinta kamar ka saceta ka gudu. Yayinda uban gayyar ya fito kuma sai kowa ya dinga faɗin, “Masha ALLAH Masha ALLAH. Ina ganin ƴammatan nan nata binsa da da ido harda Bibaa. A raina nace kwayi kwa gama in sha ALLAHU mijina yayi kenan. Koma akwai ƙaddarar ƙara auren a garesa bana fatan ace cikin ku ƴan uwansa gara ya auro bare da kowa zai goga sa'arsa. Haka dai Ummie ta tsayar da shi badan yaso ba ta mana hotuna, sai suka samu damar ɗauka suma. Sune suka fara yin gaba, ni da shi zamu taho ƙarshe. Aiko bawan ALLAH na ganin sun fice ya damƙoni ya shanye jambakin da aka samun tas. Fuska na ɗan ɓata da faɗin, “Kai Yaya”.
“Kina sake cewa tak ALLAH sai ma na kwashe sauran kwalliyan.” ya faɗa a fusace. Bam na rufe bakina kuwa ban sake magana ba. Shima sai ya ɗau yarinyarsa yana mata wasa ya shareni. Oho, ai bani na kar zomon ba rataya aka bani nima. Haka har akazo ɗaukar mu ni da shi kowa na zumɓurar baki. Haka muka fita yana riƙe da Baby, amma koda mukaje wajen motar sai da ya buɗe min da kansa na shiga ya maida ya rufe da gyara min rigata sannan ya zagaya nasa mazauni inda shima aka buɗe masa ya shiga. A motar ma shareni yay yanata ɗaukar ƴarsa hoto, ashe hoton na wayone duk harda ni a ciki. Bandai tanka masa ba nima na maida hankali akan tawa wayar.
Rikicewa nai sanda muka iso naga an cika hall fal da bayin ALLAH. Kai kace a ƙasarmu ta haihuwa muke. Kai Masha ALLAH. Dan waje yayi matuƙar ƙyau da ɗaukar idanu. Mun shigo kowa idonsa a kammu, ALLAH ma ya taimakeni shiga ce a jikina ta muntunci dan shigar cikakkiyar bahaushiya nayi ƴar Nigeria yankin arewa. Haka shima manyan kayane a jikinsa harda babbar riga ga hula kamar ba Maash ɗina ba. An mun gargaɗi yafi ashirin kafin mu shiga akan kada naje ina washe musu baki. Ni sai abun nasa ma ya bani dariya. Mun isa masaukin da aka tanada domin mu, aka fara da buɗe taro da addu'a. Da ga haka aka fara abinda ya zaunar da mutane. Ganin ya ƙi ajiye Babyn a gadon da aka tanadar mata nai masa magana, sai cewa yay shi bazai ajiye yarinyarsa ba a takura mata da ɗauka, yasan kuma kowa da niyyar da yazo wajen aje a masa kidnapping ƴarsa. Ikon ALLAH sai kallo na faɗa a raina. To in ba rigimar Yaya Awwab ba, duk uban securitys da aka zuba a wajen. Ga camaras tako ina, sannan gadon ma a kusa damu yake gab sosai taya wani zaiyi wannan ɗanyen aikin ni Samraah. To amma tunda ya sakama zuciyarsa haka sai na kama kaina kawai. Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain mahaifin Bahijja da wasu manyan malamai ne suka gudanar da wa'azi mai shiga jiki akan tarbiyyar ƴaƴan tun daga rainon cikinsu da rainonsu har kawowar girmansu. Sai lokacin nasan Malam ɗin yazo ashe harda Uncle Sulaiman da Uncle Abdullahi da Baban su Mansoor. Harma da su Mansoor ɗin da Kawu Jafaru. Bayan shi wasu malaman ma sunyi ƴan wasu ƙasashe daban-daban, daga nan aka fara cin abinci. Sosai Baby Ummu-Hidaya tasha addu'oi tare da ƙyaututtuka wajen abokan Babanta da har yau bai taɓa gabatar min da su ba matsayin abokai koni ya gabatar dani garesu matsayin mata. Sai na fahimci shifa komansa da tsari, akwai abinda yake alaƙantawa da aboki akwai wanda baya sakashi a wannan sabgar. Basu kawai ba ma'aikatansa ta fannonin kasuwancinsa daban-daban sun halarci wajen, sun kuma bama Babby gifts sosai kodan faranta ran mahaifinta kamar yanda suma yake faranta musu. Harda mutuniyata Juliet. Yau dai na ɗan sake mata fuska kaɗan kinsan ance mai ɗa wawa.
Ansha hotuna sai dai kowa sai dai yazo inda muke ya samemu, kamar yanda ya faɗa kuma bai bar kowa ya ɗauka yarinyar nan ba sai dai a ganta a hannunsa ai mata addu'a. Ai yau dai naga fitina ta Yaya Awwab. Babu kuma damar ayi magana. Koda yake tsoffin nan namu naga sun goya masa baya da abinda yay ɗin. Walima kam sai san barka dan taro ya tashi lafiya. Sai a lokacin ya bama malaman da sukai wa'azi a wajen Babyn suka ɗauka suma. Sun sanya mata albarka tare addu'oi. Sannan suka ɗora da ƙara mana nasiha ni da shi akan tarbiyyarta da rainonta.
A gajiye kowa ya koma gida. Sauran baƙi na'a masaukinsu. Wasu kuwa har sun wuce inda suka fito. Tsabar barcin da nake ji wanka ma da ƙyar nayi na kwanta. Koda ya shigo yimana sai da safe ma ni kam na jima a duniyar barci. Sai da Mama balki dake shirya baby Hidaya sukai ya fice. Washe gari muka tashi da ƙananun maganganun mutane da suka cika media, marasa aikin yi a Nigeria da wasu Malam suka dinga sharhi da caccakar al'amarin bikin sunan nan da malaman da sukai lectures wai kwaɗayi ya kawosu. Yayinda wasu suke ganin su basuga abin laifi ba. Maash dai ba aiki yakema gwamnati ba, ba wani muƙami garesa a gwamnatance ba, ba ɗan siyasa ba. Ɗan kasuwa ne da guminsa yake nema kowa ya sani. Ko mi zaiyi da kuɗinsa dan mi za'ai zaman masa sharhi tunda bana wani ya sata ba. Masu satar ma suke abinda suke so balle shi da guminsa ne. Dan kawai yaje wata ƙasa yay bikin sunan ƴarsa da ALLAH yay masa ƙyauta da samunta sai ya zama abin surutu. Kai mutanenmu sai a barsu. Harda masu faɗin almabazzaranci ne. Ga mabuƙata cike da ƙasarsa. Ai duk wanda yasan Maash yasan mutum ne dake taimako wa mutane kan jiki kan ƙarfi. Kuma sanda akai aurensa yayi ne. Sai kuma dan yayi na haihuwa. Kuma a wajen walimar nan ba wani shashanci akai ba, hasalima anyi lectures ne masu amfani ga iyaye, sai abinci da akaci. Abincinne ya tsolema wasu ido dai kenan da kuma mutanen da suka halarci taron. Kai koma dai miye su suka sani.
Rai ɓace Fahad da Hafizzullah sukace zasuyi video suma su maida raddi, yayinda Hayatu ya tabbatar da sai ya saka an kama malam nan da masu fashin baƙin. Shi dai uban gayyar banda murmushi ma baice komai ba. Sai mune muka dinga basu haƙuri. Duk da dai nima raina ya sosu gaskiya. Al'amari kamar wasa akaita jan magana har fin kwana uku, wasu har suna ƙirƙirar comedy wai. Tab ɗin ai babu wanda yasan Yaya Awwab ya wuce Nigeria shi da Hayatu. Sai sakamakon abinda ya faru muka samu labari. Sai ga mutanen sun fito suna regretting abinda sukayin. Suka kuma faɗi gaskiyar sakasu akayi. Ashe wani abokin Maash ɗin ne ɗan tsohon shugaban kasa, kuma har taron ma fa yazo harda yima Hidaya ƙyauta ya biyasu suyi. Lallai yanzu ne na fahimci zancen Yaya Awwab ɗin na ranar walimar akan ƙin ajiye Baby. Idan ka kallesa a fuska bazakace zai aikata ba wlhy. Wannan bayyanar gaskiya yasa sabon zance sake tashi, ashe dai su maƙiya basa ƙarewa. An gama da batun su Prof da su Hajiya ƙarama dake can asibiti har yanzu tana fama da kanta jiki duk ya ruɓe ko inda take wani baya son zuwa. Ga Commondo da shima dai al'amarin nasa sai a hankali sai kuma ga wani shegen ya fito. Kuma tabbas akwai ire-iren sa da yawa damu bamu sani ba kuma suna a manne da mu ɗin. Wasu ma suna cine daga taskar sa. Haka rayuwa take, dama dole ne ka saka a ranka idan fa kama mutum alkairi a wannan rayuwar yanzu. Ɗayan biyu ne. Kodai ya amsa daga gareka d ƙyaƙyƙyawar zuciya ya gode maka da maka addu'a ya kasance na ƙwarai a gareka. Ko kuma ya kasance mai maka hassada da ya dinga raina alkhairinka garesa da ganin ya cutar da kai ta hanyar da zai mallaki fiye da abinda kake bashi, zaima iya haɗe kai da wasu a cutar da kai, ko ya dinga kusheka da aibantaka da munanaka a wajen wasu mutane. Ko ya gagara kareka a wajen masu aibantaka, da ance ga alkairinka yace ba haka bane ba. Shiyayasa muyi fatan ALLAH ya haɗamu da abokan huɗɗa masu sonmu domin ALLAH da zuciya ɗaya. ALLAH ka hana duk wani mai manufa a kammu raɓarmu ko jingina jikin shingen alfarmar dakai mana. ALLAH ka bamu ikon zama da kowa da zuciya ɗaya, ka hanamu cutar da su ko jingina jikin alfarmar da kai musu da mummunar manufa, ka hanasu damar cutar damu suma.
Kwanansu biyu suka dawo, ƴan suna suka fara shirin komawa. Babu mai bani dariya da mamaki a wannan tawagar irin Mom. Haka zakiga tanata zagaye gidan nan tana kallo wani lokacin harda hawaye. Idan ko Yaya Awwab ya shigo ko taga yanda kowa ke bani kulawa sai ta tashi ta koma tsakar gida ta zauna. Daga baya na fahimci har yanzu tana wannan aman jinin musamman idan tayi tari. Haka naima Yaya Musaddiq magana ya ɗauketa suka kai asibiti aka dubata. An tabbatar musu zuciyarta ce ta yaɓu, idan kuma bata sassautama kanta ba to lallai tana gab da rasa ranta. Dan a yanzu haka ma sai an mata aiki a zuciyar dan ta samu matsala sosai. Sai dai kafin hakan sun bata magunguna na wata uku taje ta sha kafin ayi aikin. Da wannan suka wuce akan idan lokaci yayi za'a dawo da ita........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_



Follow this link to join my WhatsApp group:

https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq


*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.

*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login