Showing 258001 words to 261000 words out of 438336 words

Chapter 87 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2222

ƙoƙarin Mu'azz da Abdullahi su dawo gida gudun tashin hankali, idan kuma Awwab baya a gidan ki sanarma Mu'azz ya hanashi komawa gani nan zuwa yanzu nima”. Maganar yake yana tafiya, dan haka kafin ma ta bashi amsa har ya shige hanyar da zata sadashi da falon baƙi. Galala tai kawai tana kallonsa, can ƙasan ranta mamakin miya rikitashi haka take yi. Tare da mamakin girman wannan baƙo a wajensa. Amma dai koba komai ita hakan yayi mata. Dan ta kuɓuta daga abinda take gudu dai ke nan. Cikin taɓe baki ta miƙe, tare da saɓar handbag ɗinta ta fice hankalinta kwance. Ai garama taje taga show ɗin can gidan, dan babu wasu su Paah da zata kira sai abubuwa sun kankama..........✍️

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 thirty-three


.....Abincin na fara bama Ummie bayan na wanke mata baki da taimakon Mama Balki. Ci kuwa take sosai kamar ko yaushe a kwanakin nan. Lauma biyu uku sai na bata ruwan addu'a ta sha. Ba ruwan addu'ar da nake mata bane kawai, Baba ma na mata, haka akwai wani da Hayatu ya kawo yace daga Sheikh Muhammad bin Khalipha Al-Hussain yake amsowa, tuni kuma ana kawowa masu kula da ita wai ke bata. Dan haka dana tashi sai nake haɗesu waje guda ina bata, kullum kuma Mama Balki kan shafa mata sau uku a jiki, safe, rana da dare idan zata kwanta. Shi kansa Yaya Awwab daga jiya zuwa yau sune ruwan shansa batare daya sani ba. Dan kaf ruwan dake a cikin freight na kwashe na sanya masa na addu'oin a ciki, duk da ina ɗar-ɗar ɗin karya gane wajen buɗe murfin, dan haka nake ta kaf-kaf ɗin bashi ruwa yanzu da kaina. Dawowar Fahad ɗakin ya katse mana shirun da mukayi. Dan yana yin sallama yay tozali da Ummie dake zaune ina bama abinci ya ƙaraso cikin sassarfa ya wani rungumeta har sai da ta saki ƙaramar ƙara tana turesa. Ɗagowa yay cikin tsananin damuwa idanunsa share-share da hawaye yana kallonta. Itama kallon nashi take yi, sai kuma ta kauda kanta tare da zamewa ta kwanta ta juya mana baya. Ƙoƙarin komawa side ɗin data juya yayi, amma sai Mama Balki ta dakatar da shi ta hanyar riƙesa. Yayinda ni kuma ƙwallar tausayin ɗa da mahaifiyar suka cika min idanu.

Dai-dai nan aka turo ƙofar aka shigo. Tuni ƙamshin turarensa ya wani irin mamaye hancinanmu. Hakan ya samu ɗaga kai mu duka muka kallesa. Shima tsaye yay cak kamar wanda akama umarnin tsayawar. Yayinda Fahad yay wani kalar ɗauke kansa. Mama Balki ce tai ƙarfin halin masa sannu da zuwa. Da ƙyar ya amsa mata yanayinsa na ƙara komawa na ainahin stubborn ɗinsa. A cikin wani irin yanayi mai wahalar fassara batare da ya karaso ba ya juya ya fita abinsa yana jan sirrin tsaki dake bayyana fushinsa. Harara Fahad ya raka bayansa da shi shima yana jan tsakin mai kauri. Sai kuma a hankali ya furta, “Mugu kawai azzalumi”.

Har cikin tsakkiyar kaina naji shigar zagin nan. Na ɗan kalla Fahad ɗin naga yanda yake wani cika yana batsewa. Maimakon naji haushinsa sai ya bani tausayi, dan hatta da jijiyoyin kansa duk sun fito raɗa-raɗa haka ma idanunsa sun wani bala'in kaɗawa jazur a ƙanƙanin lokacin nan. Kamar wanda aka tsikara shima ya miƙe zaram. Dai-dai nan Hayatu ya shigo ɗakin da sallama. Cak Fahad ɗin ya tsaya daga yunƙurin fitar da yake yi. Sai kuma murmushi ya ɗan kufce masa, da sauri ya nufi Hayatun yana faɗin, “Oyoyo sweet Yayana”.

Tuni shima Hayatu ya ajiye kayan hannunsa ya buɗe masa hannayensa suka rungume juna. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, sai kuma na miƙe batare da nacema kowa komai ba na fita....

🩸🩸🩸🩸

Cikin yanayin gajiya ta shigo gidan. Ga damuwar dake a ƙarƙashin zuciyarta a kwanaki biyun nan game da rashin ganin Samraah. Tun a jiya bincikenta ya tabbatar mata da Samraah ce a sashen Awwab dai Hajiya Mammah da bata san an sallamota ba ta gani ba wata ba. Taso sanar ma Yallaɓai amma ta kasa hakan dan tana son ta fara sanin mi bincikensa ya samo masa akan yarinyar. In har wanda zata iya canja ra'ayinsa ne daga kasheta daya ambata sai ta fara shirinta. Idan kuma na wanda bazai iya canja ra'ayin nasa bane nan ma sai ta ɗauki mataki. Dan a wannan gaɓar bazata taɓa bashi goyon baya ba. Tanama Samraah wani irin mahaikacin so mai taɓa zuciya. Ita kaɗai tasan a halin matsanancin kishin da take ciki na Awwab a ƴan kwanakin nan musamman daga jiya zuwa yau.

Babu kowa a falon sai ƙamshi da sanyin ac. Tasan su Arwa sun fita yawonsu, dan Muhseen ne kawai ke zuwa makaranta yanzu a gidan sai Aneesa autar Hajiya Mammah ƙanwar Azizat kenan. Cikin rashin kuzari ta kama ƙarfen upstairs zata fara haura steps ɗin ta tsaya cak. Rawa jikinta ya nema fara yi sakamakon abinda idanunta ke kallo. Cikin wani irin bugawar zuciya da rawar baki ta furta, “Fahad!”.

“Yes Ummy. Surprise”.

Ya faɗa cikin fara'a yana ƙarasowa gareta. Cikin rashin kula da yanayinta ya bata side hug abinsa. Da ƙyar Hajiya ƙarama ta iya jan numfashi da kokarin controlling kanta. Amma ina jikinta karkarwa yake. Dan koda Fahad ya ɗago yana gaisheta sam bama fahimtarsa take ba. Sai da ya ɗan tanƙwaɓeta da zai gittata yana dariya sannan taji abinda yake faɗi na ƙarshe. “Oh Ummy mamakin ganina da alama ya sumar dake. Bari naje dai yanzu zan dawo karki faɗama su Azizat na dawo”. Daga haka yay wucewarsa ya barta a yanayin ƙaulani.

Sosai taji fitsarin dake a mararta na ƙoƙarin zubowa. Tuni ta saki handbag ɗinta a wajen ta juya ta fice a falon ƙafafunta na matuƙar rawa. Tana shiga motarta motar Hajiya Mammah na shigowa gidan. Ko bi takanta batayi ba ta wani irin yin reverse da mahaikacin gudu kamar ba'a cikin gida take ba ta fice har tana kusan takama ɗaya a cikin securitys ɗin ƙofar ƙafa ALLAH dai ya taƙaita yaja baya da sauri. Babu wanda ya kawo komai a ransa sai tunanin kiran gaggawa maybe ta samu daga asibiti. Dan sometimes takan yi irin wannan fitar idan hakan ta faru. Sai in ta dawo ta basu haƙuri da sanar musu abinda ya rikita tan. Shiyyasa kowa a gidan ke mata uziri da mata kallon innocent woman dako hannu ka saka mata a baki bazata ciza ba.

Wani irin mahaikacin gudu tayi ko'a titin. ALLAH dai ya taƙaita titin anguwa ne. Gashi kuma anguwan masu kuɗi ba wani yawan kai-kawon mutane ake samu ba, motocin ma sai jefi-jefi. Yanzu kam dama rana da wahala ka gani kasancewar duk ana wajen aiki. A cikin ƙanƙanin lokaci ta iso gate ɗin gidan yallaɓai. Horn ta dinga dannawa daya rikita maigadi, jikinsa har rawa yake wajen buɗewa. Ruɗanin da take ciki ya sata mantawa gaba ɗaya yau bata saka niƙaff ba. Sannan kuma da motarta ta amfanin ko yaushe ta shigo gidan bata ɓadda kama ba kamar yanda ta saba. Kasancewar a duka kamanni biyun na baɗini dana zahiri tana da power ɗin shigowa gidan yasa babu wanda yay mamakin ganinta sai dai mamakin yanda ta shigo. To amma idan suka auna da kafin zuwanta wadda tazo zasu iya kallon abin a wani abu daban kuma. A dai-dai ƙofar falon gidan tai parking, ko rufe motarta batayi ba ta afka ciki. Babu kowa a falon, sai tv dake magana ƙasa-ƙasa. Hannunta ta kalla da nufin neman waya, wayam babu handbag. Tunanin ta barta a mota ya sata jan tsaki. Juyawa tai da nufin ɗakko wayar dai-dai nan wanda zata fita ɗakowar dominsa ya fito. Baiyi mamakin ganinta ba, dan yasan zata iya zuwa ɗin dama..

Zaune ta kai dan wata irin hajijiya take ji na neman ɗibarta. Da ƙyar ta iya haɗa kalmar, “Fahad ya dawo, yanzu haka yana gida”.

Zaune ya kai shima a hankali batare daya ce mata komai ba. Sai ma file ɗin hannunsa daya ajiye yana mai dafe kansa da duka hannayensa biyu. Jin shiru baice komai ba ta ɗago ta kallesa. Muryarta har rawa take wajen sake faɗin, “Yallaɓai baka ji abinda na faɗa bane?”.

Wani irin murmushi ya saki, mai bayyanar da tsantsar ɓacin rai da tsufarsa. Ya ce, “Na jiki sarai, shima wanda ke bincike akan yarinyar nan ya kawo sakamakon yanzu”.

Bai gama rufe baki ba ta ɗauki file ɗin ta fara dubawa cikin rawar jiki. Abubuwa masu muhimmanci kawai take dubawa. Abu na farko daya fara jan hankalinta shine cikakken sunan yarinyar. Samraah Abdul-wahab Gwarzo. Na biyu aikin mahaifinta da sanadin rasuwarsa har ma da inda ya rasu. Na ƙarshe MATAR AURE. Rawa bakinta ya fara da ƙyar ta iya haɗa kalmar, “Ba...ban fahimci komai ba yallaɓai”.

Murmushi ya sake saki, sai kuma ya kalleta da idanunsa dake jazur kamar tsohon maciji. Musamman yanda tsufarsa ta sake fitowa fili sai taga har baƙinsa ma ya sake bayyana fiye dana baya mai tsananin shining ɗin hutu. Shima ɗin kallonta yake cikin ido, batare daya janye ba ya furta, “Ita ɗin ɗiya ce ga Abdul-wahab Gwarzo (jirgin mota)”.

Kaɗan ya rage zuciyar Hajiya ƙarama ta ɓaro. Ta wani irin miƙe zambar jikinta na karkarwa tace, “What! Jirgin mota? Drivern mahaifin Ummu-Hidaya da kenan?”.

Kansa kawai ya ɗauke daga kallonta alamar tabbatarwa. Cikin kaushin murya ya cigaba da faɗin, “Tabbas nayi kuskuren ƙin bibiyar bayan Abdul-wahab kamar yanda nake biye dana Ibrahim Alonso. Idan baki manta ba nayi hira da yarinya shekara ɗaya data gabata a Kano sakamakon turamin program ɗin bikin buɗe Company da Awwab yayi. Zargin akwai dalilin da yasa ya amsa mata zaiyi hira da ita alhalin bai taɓa yi da ko manyan channels ba yasa na baro India nazo danna tabbatar da ko akwai alaƙa a tsakaninsu. Tako ina bincikena babu ta inda wata alaƙa ta alaƙanta su, dan haka ban maida hankalina ga cikakken sunan yarinyar ba....”

“Wai kana nufin itace yallaɓai?”.

Hajiya ƙarama da gaba ɗaya take a gigice ta jeho masa tambaya cikin katsesa. Iska ya furzar mai kauri tare da miƙewa tsaye. Taku ya fara hannayensa duka biyu a goye ya ce, “Of course itace yarinyar”.

“Tashin hankali. To amma tayaya tazo Lagos bayan ma'aikaciya ce? Ta yaya kuma Lagos ɗin ma take zaune a Maash Mansion? A ƙarshen zance shine tayi aure bayan fasa aurenta da saurayinta da suka jima a tare. Abin tambayar anan waye ya auretan? Waye kuma yay kidnapping ɗinta kafin auren har sau biyu? Tabbas akwai abinda ya kawota Maash Mansion, minene shi?. Yallaɓai wlhy zan haukace, wane irin ruɗani da tashin hankali ne haka yazo mana a rana ɗaya? Gashi mun gagara magance batun likitocin nan abu sai ƙara nisa yake, duk da dai ba wannan bane kaɗai hope ɗinmu wancan ma zasu iya mana illa tunda ko ganinta bamayi a yanzu balle sanin halin da take ciki”.

Amaimakon amsa mata dukkan tambayoyinta da maganganunta a mugun fusace yay wurgi da ɗan abin deco.. ɗin dake a saman Centre table ɗin gabansu........✍️

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 thirty-four


......Mugun tsorata Hajiya ƙarama tayi har sai da ta rumtse idanunta da toshe kunnenta jikinta na rawa. Shima nashi jikin rawar yake yi na tsantsar ɓacin rai. Kafin ya shiga maimaita kalmar, “Dole akwai abinda Awwab ya sani, dole shine ya shirya komai. Ta ya yarinyar dake a Kano zata dawo Lagos? Ta ya ɗiyar Abdul-wahab zata shigo Maash Mansion matsayin ƴar aiki? Ta ya?!!! Ta ya?!! Ta yaya?!!!!”.

Ya faɗa cikin wani irin ƙaraji da ya sake firgita Hajiya ƙarama. Dan bata taɓa ganinsa a irin wannan fushin ba duk da kuwa ita shaidace akan hatsabibancin sa tun ba yanzu ba. Da wani irin fushi ya danna gefen kujerarsa, zuuuu sai ga gurin ya buɗe. Wata ƴar loka ce ta bayyana, kwalaben manyan haɗaɗɗun giya masu tsadar gaske suka bayyana. Ɗaya a ciki ya ɗauka, batare da tuna akwai mai amsa suna surukarsa ba a wajen ya ɓalle murfin ya dasa a bakinsa ya shiga kwankwaɗar kayansa. Shike sha, amma Hajiya Ƙarama ita ke binsa da kallo kamar tsohuwar mayya. A yanda take jinta yau ɗin nan kamar fa ta amsa itama ta kora. Sai dai kuma tasan hakan zai iya ɓallo mata aiki ne a wajen Paah.

Tas ya shanye abinda ke ciki, tare da yin wurgi da kwalbar sannan ya koma cikin kujera yay wata irin lafewa yana sauke numfashi da ƙarfafan ajiyar zuciya tamkar wanda yay wani uban gudu a sahara. Sun kwashi mintuna biyar a haka shiru, kafin ya miƙe batare da ya kalleta ba ya ce, “Kije gida zan nemeki.”

Baki ta buɗe zatai magana ya ɗaga mata hannu alamar baya son jin komai. Kanta kawai ta jinjina tare da miƙewar ta fice. Da harara ya raka bayanta, yana jin a ransa amfaninta ya kusa ƙarewa a garesa. Juyayyun idanunsa ya maida kan ƙaton hotonsa dake a falon shi da mahaifin Ummie wato Ibrahim. Hoton yay matuƙar ƙyau musamman da suka kasance cikin manyan kaya, su sukansu kuma bakunansu ɗauke da murmushi. Hannayensu riƙe da jariri dake a cikin showal mai tsananin ƙyau da ɗaukar ido. An yi hoton ne a ranar sunan Muhammad Awwab. Shine kuma jinjirin dake a hannun nasu suna kallonsa fuskokinsu ɗauke da murmushi. A fusace ya rarumi ɗayan deco ɗin saman table ɗin ya wulwula sai ko akan hoton. A take gilashin jikinsa ya tsatstsage. Yatsansa ya karkaɗa alamar gargaɗi ma hoton sannan ya wuce fuuuu zuwa bedroom ɗinsa....

A hankali Kukunsa dake laɓe yana kallon komai ya shiga jinjina kansa. Da baya-baya ya koma ya shiga ta cikin store. Stick ya ɗauka cikin dabara ya janye abinda ya kare cctv camaras ɗin dake a kitchen ɗin ta koma yanda take kamar komai bai faru ba. Dan duk leƙen da yay da naɗar abinda ke faruwa a rubuce camara ɗin bata ɗauka ba. Ba yau ya fara hakan ba, domin a ankare yake, ko it kanta camara ɗin babu wanda yasan ya fahimci akwai ta a kitchen ɗin fama cikin gidan baki ɗaya, sai dai bai taɓa cin karo da samun abinda yasan ogansa zaiyi farin ciki ba irin yau, dan koshi kansa a yau ɗin nan ya matuƙar girgiza da shiga mamakin ganin fuskar Hajiya ƙarama a matsayin wadda ta jima tsahon shekaru tana kawoma Baba prof ɗin ziyara amma bai taɓa ganewa ba saboda shigar ɓadda kama da take yi idan zatazo. Ba kuma su taɓa zama a wannan falon sunyi magana ba sai yau ɗin. Aikinsa ya cigaba dayi kamar yanda ya saba....

💓★💓★💓

A hankali na murɗa handle ɗin ƙofar na tura kamar mai jin tsoron gamo da wani abun firgici. An rage hasken ɗakin ya koma dif sosai. Sai sanyin ac da ƙamshin fresheners dana saka kafin na fita. Ɗan dube-dube na fara kafin idanuna su sauka akansa. Yana can tsaye daga jikin window duka hannayensa goye a bayansa ya ƙurama waje kallo. Cikin sanɗa na ƙarasa shiga ɗakin. Tray ɗin dake hannuna na ɗaura saman Centre table dake a tsakiyar sofas. Kafin na ƙarasa takawa har inda yake cikin sanɗa. Cikin rufe ido da killace duk wata kunya dake cike da zuciyata na ƙarasa ta bayansa a hankali na warware hannayensa dake goye a bayansa na rungumesa ta baya, hannayena zagaye da shafaffen cikinsa. Dan abinka da dogo bawani na iya kai koda kafaɗarsa bane. Data samansa ne ma hannayena bazasu iya kullesa ba saboda yanda ƙirjinsa ke a buɗe alamar motsa jiki. Jikinsa akwai zafi sosai alamar zazzaɓi ko kuma duk ɓacin ran ne oho.

Duk da dabaibayin dana masa sam bai motsa ba, na ɗan ciza lips ɗina ina mamakin taurin zuciyarsa. A zahiri kam muryata na maida can ƙasa da ƴar shagwaɓa na ce, “My Lion!”.

Shiru bai amsa ba. Na ɗan yi jimm kafin na motsa hamnuna na mintsinesa a saman cikinsa kaɗan na sake faɗin, “My hot! Please answer me ko naita maka kuka”.

Nan ɗin ma kamar bazaice komai ba. Dan kusan fin minti ɗaya kafin naji saukar hannunsa saman nawa. Sosai shima ɗumin hannun nasa ya ratsa min nawa har sai da na ciza lips ɗina kaɗan. A hankali ya jawoni daga bayansa ya maidoni ta gabansa ya tsayar da ni. Har cikin jini da ɓargo na nake jin kaifin idanunsa na ratsani. Dan haka koda kwatance ban iya gwada ɗagowa na kallesa ba. Saukar hannunsa mai ɗumi naji akan haɓata, ya ɗago fuskata sama ta yanda zamu iya ganin juna. Amma sai na lumshe nawa idanun dan bazan iya kallonsa ba. Yafi minti ɗaya yana ƙarema fuskar tawa kallo, ina jin hakanne ta hanyar kaifi da tasirin ƙarfin idanunsa a kaina. Da wani irin ƙyar, tamkar wanda akama dole cikin maƙoshi ya furta, “Mi kike buƙata?”.

Sai da na ƙara runtse idanuna da ƙyau kafin na ɗaga hannuna na ɗaura yatsana manuniya akan jikinsa alamar shi. Ina ji ya ɗan furzar da numfashi mai ɗan sauti kafin ya furta, “Open your eyes”.

Kafaɗa na maƙe masa da faɗin, “Uhm-uhmmm!”. Cikin shagwaɓa.

“Why?”.

“Ina jin kunyan ka”.

“What is kunya?”.

Bamma san sanda na ware duk girman idanuna ba a kansa. Cikin suɓutar baki na ce, “Bama ka sanshi ba?”.

Kansa ya jinjina min kawai idanunsa da gaba ɗaya suka canja launi a cikin nawa, ya wani ƙankancesu da shanyesu sun koma wasu luu-luu da su tamkar mai son

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login