Showing 321001 words to 324000 words out of 438336 words
Shima kuma Ya Aawab koba komai nayi kewarsa. Sai da na leƙa na duba Ummie dake barcinta hankali kwance sannan na haura saman. Banyi mamakin ganin ko'ina babu datti ba. Har na nufi ɗakina sai kuma na fasa na maida akalata ga nashi ɗakin. Nayi mamakin samunsa tsaye a bakin window tsaye yana kallon waje. Ko kayan jikinsa bai cire ba. Sai da na masa kallon tsaff na gane waya yake yi dan akwai bluetooth a kunnensa. Kamar zanyi magana sai na fasa. Jikina a sanyaye dan wani masifar son kwanciya nake a waje mai sanyi na kai zaune kan carpet. Cikin dabara na kwanta tare da jan jikina na koma saman tiles na kwanta. Aiko sai na shiga sauke ajiyar zuciya a jajjare dan jin daɗin samun abinda nake so. Na lumshe ido kenan naji kawai an ɗagani a wajen. Buɗe idanun na nayi da sauri ina ɓata fuska sai ya harareni. Baice dani komai ba ya wuce dani bathroom. A bazata kawai na jini a cikin ruwan ɗumi. Kafin nai wani yunƙuri shima ya shigo cikin bathtub ɗin. Jikinsa kawai na shige na rungumeshi. Shima hannu biyu ya amshe ni sai kuma ya fara laluben lips ɗina ya haɗe da nashi. Tuni ya shagaltar da ni har ya cire kayan jikina ma ban farga ba. Sai da ya sakar min lips ɗin kuma naji kunya. Shiko ko'a jikinsa sai ma wanka da ya shiga mun.....
Da zamu fito kam ban yarda ya ɗakkoni ba. Dan nama rigashi fitowa shi ya tsaya alwala. Gaba ɗaya na fice a ɗakin zuwa nawa. Dan nasan babu wanda zan samu a saman namu. Tsaf nai shirin barci na ina mai tsayawa kallon kaina a mirror. Gani nai kamar na canja ma ni a kwanki ukun nan kar kuce na cika ƙarya. Maimakon ni da nasha jiyya a asibiti aga na fige na fita a hayyacina sai na ganni ma na murje fata ta ta wani yi kalar ɗan golden brown kaɗan mai haske bamai duhu ba. Haka dai na shirya na haye gadon na kwanta dan bana jin zan sake komawa ɗakinsa. Sai dai a mamakina ina kwanciya yana shigowa. Daga saman gadon na ɗago ina kallonsa har ya ƙaraso inda nake. Laptop bag ɗinsa ya ajiye tare da wani ɗan bowl mai ƙyau idanunsa shima a kaina. A kusa da ni ya zauna tare da kamo hannuna cikin nashi cikin low murya ya furta, “Baƙya jin yunwa kika zo nan kika kwanta?”.
Kaina na jinjina masa. Sai kuma na yamutse fuska tare da faɗin, “Tea kawai zan sha sai anjima kuma.”
“Why?”.
“Yanzu bana jin yunwa barci ma nake ji.”
Kansa ya jinjina min tare da ɗan shafar kumatuna ya sakko da hannunsa saman cikina nan ma ya shafa. Sai kuma ya yunƙura zai tashi. Hannun nasa na riƙe, hakan ya sashi komawa ya zauna yana kallona. Duk da tsigar jikina ta tashi dan bana jure kallonsa cikin ido haka na daure. Cike da ƙarfin hali naja kumatunsa. “Please My Lion Smalling kodan murnar samun lafiyar Ummie. Ya kamata a yau fuskar nan ya zama tamkar buɗaɗɗen sabon fire mai ƙamshi”.
Idanunsa ya ɗan lumshe sai kuma a bazata ya ɗan saki murmushin. Cike da farin ciki na rungumeshi ina faɗin, “Thanks you my Handsome.” yanda nayi maganar ina hura masa iska a kunne sai kawai naji ya birkitoni. Banyi zaton halin da ake ciki zaisa ya nuna wata buƙata ba. Amma mi sai labarin ya canja salo. Duk yanda naso zame kaina bai fa barni ba sai da abinda nake gudun ya kasance. Sai dai fa misalta muku yanda yau ɗin ta kasance hummmm abine da bazai yiwu ba. Dan wannan sirrina ne, amma dai ta shiga cikin jerin wasu kwanaki masu matuƙar muhimmanci da bazan taɓa mantawa ba a rayuwa ta. A shi kansa nasan hakanne, sai dai ba lallai ka gane ba kasancewar halittar sa ce kamar hakan yakan iya shanye komai a zuciyarsa shi kaɗai. Da yawan miskilai akance idan abin farin ciki ya samesu kakan iya gani koda a fuskarsu ce shi dai bawan ALLAHn nan sam ba haka bane, zai iya haɗiye miki farin ciki da damuwa ka kasa gane masa. Duk da dai kam na jigata sosai, dan da ƙyar na iya yarda ya taimaka min muka gyara jikinmu saboda barcin da ya gama cinye idanuna ga zazzaɓi. Bamma san yaya akai ya sakan wani kayan barcin ba sai can fitsari ya tadani na gansa ya baje takardu a saman carpet shima yana daga kwance ruf da ciki yana faman daƙilar laptop, gefensa akwai sallaya da Alkur'ani alamar salla ya idar ya kuma dawo wannan aikin. Nayi mamaki, dan banyi zaton zai iya sake wani abu ba musamman a yanda komai ya kasance. Shine ya taimaka min nayi fitsarin dan jiri nake gani, ya sake maidoni ya kwantar. Gabannin asubahi na farka da ciwon ciki. Kafin kiran salla sai amai nake yi ga zazzaɓi sosai a jikina. Hankalinsa yay matuƙar tashi. Babu shiri ya nemo doctor Larai ta asibitin su Hajiya Ƙarama bayan an idar da sallar asuba. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gata. Sama-sama nake jiyo muryar Ummie da Mama Balki da doctor Larai ɗin a kaina... Sai da Ummie ta riƙoni jikinta ta rungume sannan na ɗan buɗe idona, da ƙyar na iya furta “Ummie ruwa zan sha”.
Fuskarta cike da damuwa ta ce, “Ruwa kike so?”.
Kaina na ɗaga mata hawaye na zubo min. Dan sam bana jin daɗin jikina. Har Mama Balki ta ɗakko ruwan Dr Larai ta hana su bani, ta tabbatar musu amai zanyi idan nasha. A ɗan samu na ɗumi dai a bani kafin ta gama haɗa ruwan da zata saka min. Haka dole akayi, sai dai ni ruwa mai sanyi nake so. Dan haka na sanya musu kuka. Dai-dai nan Maash ya shigo da abu a hannu. Tunda yay sallama idonsa a kaina ƙyam, kai tsaye in da naken ya ƙaraso, Ummie nata ƙoƙarin lallashina nasha ruwan ɗumin. Da ƙyar dai na yarda nasha maƙwarwa biyu kawai. A hakan ma sai da nai yunƙurin aman ALLAH dai yasa banyi ba.
Bayan doctor ta gama haɗa ruwan ta buƙaci a gyara min kwanciya. Nayi zaton zai bar Ummie da Mama Balki sumin amma babu kunya ya kamani da kansa daga jikin Ummie ya kwantar da ni saman dagon duk yanda doctor ɗin ta buƙata. Yana zaune a gefena shi da Ummie sun sakani tsakkiya hannunsa riƙe da nawa aka ɗaura min ruwan. Da farko yamutse-yamutsen fuska na dingayi da ruwan ya fara shigata, sai da ya fara gauraye jikin nawa sannan na fara sauke ajiyar zuciya.
Ummie ce cikin sauke numfashi ta dubi Dr Larai, da karyayyen harshen nan nata ta ce, “Doctor kodai asibiti zamu koma ne. Yarinyata na buƙatar text gaskiya musam dalilin ciwon cikin nan da take ta complain.”
Murmushi Doctor Larai tayi, cike da girmamawa ta ce, “Ranki ya daɗe in sha ALLAHU nai miki alƙawarin samar da duk wata kulawa gareta anan gida. Text kuma ina ganin basai mun sake mata ba. Dan result ɗin da wancan asibitin suka bada game da ciwon nata babu wani kuskure. Sai dai kamar yanda suka faɗa tana buƙatar bed rest sosai gaskiya. Dan cikin nan har yanzu bai zauna da ƙyau ba.”
Idanu sosai Ummie ta waro da ga ita har Mama Balki. Duk da ita Mama Balki taso zargin hakan. Itama Ummien taso zargin hakan amma dai tafi son ji a bakin likitar dai. Murmushi Dr Larai tayi da faɗin, “Oh baku sani ba ashe. Da alama Alhaji ya shirya muku bazata ne dai kenan”. Ta ƙare maganar tana ɗan kallon sashen da Maash yake kamar yanda Ummie ma ke kallonsa. A mamakinsu sai suka ga ya ɗan kauda kai yana murmushi.
Kasa haƙuri Mama Balki tayi sai da ta sanya dariya. Sannan ta ce, “Kai Masha ALLAH. Alhaji ƙarami kuma sai a ɓoye mana mijin? Ko dai kishiya ce shiyyasa ba'a son mu sani?”.
Ɗagowa yay ya kalla Ummie, sai kuma ya maida idonsa akan Mama har lokacin da guntun murmushin a fuskarsa. A nutsen nan nasa ya ce, “Ni Mama ba ruwana. Ita ce tace nayi shiru da bakina tana jin kunyarku, tana son kuma mu rama yanda Ummie ta ɓoye mana samun lafiyarta muma”.
Bamma san na buɗe idanuna da sauri ba duk da nauyin da suka min. Fuskata a marairaice kamar zanyi kuka. Da wani shegen salonsa ya kashe min ido ɗaya tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya ce, “Koba haka kika ce ba?”.
Tsabar kunyar da naji bamma san na saki kuka shagwaɓa da faɗin, “Ummie kin gansa ko. ALLAH ni sharri yake mun”.
Ranƙwashi Ummie ta kai masa bisa kai, kafin hamnun nata ya sauka a kan nasa ya miƙe yana murmushi yay hanyar ƙofa. Dariya Dr Larai da Mama Balki suka sanya. Itama Ummien sai ta girgiza kai tana murmushi da kamo hannuna cikin nata ta ce, “Ƙyalesa kinji. Nasan shine bake ba. ALLAH ya baki lafiya, ya saukeki cikin aminci kinji”.
Kasa amsawa nayi da Amin, dan sai naji gaba ɗaya kunya ta lulluɓeni fiye da farko. Wlhy Maash na neman sakani taɓarewa. Ban sake yarda na buɗe idanun nawa ba, ina dai saurarensu sunata cigaba da murnarsu Ummie harda sujidar shukur tayi, lallashin da Mama Balki naji tana mata yasa na fahimci hawaye take yi. Ban san yaya suka ƙare ba dan barci ya fara cin ƙarfi na. Ko shigowar Fahad da Hafizzullah sama-sama na jiyo barci yay gaba da ni........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_
.......A ɓangaren Baba prof sai da likitansa yaje gida ya dubashi. Dan Uncle Abdullahi na tare da shi. Doctor ya tabbatar masa da jininsa ya hau sosai. Ya kamata kuma ya kwantar da hankalinsa koma mike faruwa dan bugun zuciyarsa har ya canja. Nan dai ya bashi shawarwari tare da masa allurar barci dan ya ce yana buƙatar hutu na awa kamar goma. Baba prof ɗin bai musa ba. Dan shima a karan kansa yana buƙatar hakan kam gaskiya...
Uncle Abdullahi bai baro gidan ba sai da yay barci ko nace aka kira wayarsa. Yanda ya baro gidan a gaggauce yana bama ɗaya daga cikin ma'aikatan umarnin kwanciya a falo dan ya dinga ankare motsin Baba prof ɗin zaka tabbatar da kiran da akai masa mai muhimmanci ne. Wanda aka saka kwanciya a falon yana ganin Uncle Abdullahi ya fita ya wani faɗa saman kujera ya kwanta, koba komai banza ta faɗi yau. Dan har wani barbaje ƙafafu yake ransa fes. Bai wani bi takan Baba prof ya hau barcinsa harda minshari. Da wannan damar baƙon da basu san da shi ba a gidan tun ɗazun ya sami damar shigowa ya wuce har bedroom ɗin Baba prof ɗin. Tsaye yay a kansa yana kallonsa, sai kuma yay dariya da faɗin, “Mugu kenan uban mugaye”. Ƙaramin kwandon kaba dake a hannunsa ya buɗe yana kallon kunamin ciki manya-manya har guda uku. Baƙa, sai fara tass tamkar mara jini. Ga kuma mai kamar gold. Yanda suke ta faman ɗaga bindina sama zai baka tabbacin dama kawai suke jira. Murmushin mungunta kawai ya saki tare da ɗaukar su ɗaya bayan ɗaya da hannunsa dan shi yasha maganinsu babu abinda suke masa, Safar ƙafar prof ya buɗe ya saka ɗaya. Ya buɗe wandonsa😳 ya saka ɗaya. Sannan ya ɗakko hula a gefensa tsabar iya mungunta ya saka ɗaya a ciki ya kifama Baba prof hular a ka. Hancin sa ya kama ya ɗan ja cike da shaƙiyanci ya ce, “Barci lafiya tsoho, ni JAGA ina gaisuwa”. Ya juya yay ficewarsa yana dariya....
Jaga🤔😳??????.
💦💦💦💦💦
Kai kawo kawai take tana faman lissafa mintuna. Kaɗan-kaɗan kuma ta kalla wayarta dan babu abinda take fatan gani a yanzu sai kiran Jannifer. Rawar da ƙafafunta keyi da jin zuciyarta kamar zata wantsalo saboda ƙaguwa ya sata faɗawa saman gadonta. Ƙirjinta ta dafe tare da shaƙar numfashi ta fesar. Ita likita ce ta san irin wannan saka abu a rai yayta azalzalarka zai iya kawo heart attack ma. Dan bugun zuciyarta yay masifar ƙara ƙarfi. Kamar da wasa taji abu ya soketa. Jimm ta ɗan yi sai kuma ta share. Ƙara sukar ta akayi a wani wajen da ban. Azabar data ratsata ta waje biyu a lokaci guda yanzu kam ya tilastata tashi zaune tana kai hannu wajen da ɗan wawwaigawa amma babu komai a inda taken. Tashi tai ta fara ɗage-ɗagen filos da duvet, ɗayan hannun kuma tana taɓa inda zugin ke ƙaruwa mata har waje biyu. Kamar wasa sai da azaba ta sata sake kaiwa kwance, nan ma aka sake ɗalla mata. Ina bazata iya jurewa ba, da sauri ta mirgina ɗayan gefen tana sakin ihu. Aka ƙara bata wani harbin. Kafin dai ta fasa ihun da aka kawo mata ɗauki an mata ɗalli yafi bakwai. Zufa kuwa ta gama jiƙeta ta sharkaff harda sakin fitsari. Da sauri Bahijja dake laɓe ta fice tana dariya.
Kusan cin karo sukai da Rubayya dake ƙoƙarin zuwa ta sanar mata plan ɗin su fa na neman rugujewa dan Hajiya Mammah na tare da ƴar uwarta Mashi'a a ɗakin Mashi'ar bata san mu suke tattaunawa ba, ko kallonta Bahijja batai ba tai wucewarta. Da kallo ta bita ita kuma zuciyarta na ayyana mata itama nemanta Hajiya ƙarama keyi, shiga tai ranta a ɓace, sai ta sameta cikin wannan hali. Kamata tai ta riƙe dan yanda jikin Hajiya ƙarama ke rawa ga zufa ta mata sharaf ya isa baka amsar babu lafiya. Neman shiɗe mata take, dan haka ta rungumota jikinta sai ko ta samu nata rabo itama aka bata har harbi biyu. Tuni ta saki Hajiya ƙarama a ƙasa ta ƙwalla ƙarar data jawo hankalin mutanen gidan. Har rige-rigen shigowa Hajiya Mammah da su Arwa akeyi. Mamaki ya kama kowa yanda Hajiya Rubayya ke birgima a ƙasa tana ihu da rike inda aka harbeta. Ga kuma Hajiya ƙarama kwance a ƙasa tai sharkaf da zufa tama kasa kukan ita dan abinda ke harbin nata fa na jikinta kuma basu daina ba. Arwa ce ta fara nufarta, hannu tasa ta kamo mahaifiyar tata zuwa jikinta, kafinma ta gama mannata an bata rabonta. Ƙara ta ƙwalla da sakinta timm a ƙasa tai baya tana ɓalla ihu da riƙe hannunta.
Da sauri Hajiya Mama ta ce, “Ya Salam mike faruwa ne haka? Ke Arwa lafiya?”. Tai maganar tana kaiwa zata taɓa Hajiya ƙarama Hajiya Mammah ta riƙeta da jawota baya. “Auta! Baki da hankali ne. Kina ganin daga taɓa da ƴarta tayi itama tana ihu ga Rubayya kwance ke sai ki kai kanki?”.
“Amma Adda ya kamata musan mike faruwa ai”. Hajiya Mama ta faɗa cike da damuwa. Masifa Hajiya Mammah ta fara mata dan ita wani irin kishi ne ya taso mata. Ganin Rubayya a ɗakin Hajiya ƙarama sai zuciyarta ta ayyana mata amanarta suke ci ALLAH ya saka mata. Duk yanda Hajiya Mama taso taimaka musu Hajiya Mammah ta hana. Ashe shi tsautsayi baya wuce ranar sa. Dan Azizat na maƙale a baya sai ji sukai ta ƙwalla ƙara. Juyowar nan da zasuyi kanta sakamakon tsallen data buga gefe kawai Hajiya Mammah ta maye gurbin ƙafarta akan baƙar narƙeƙiyar kunamar data ɗalli Azizat ɗin a ƙara. Itama ƙarar ta fasa tana mai yin tsalle gefe dan har cikin tsakkiyar kai taji harbin nan. Ai ko kaɗan ya rage Hajiya Mama data firgita itama ta taka ALLAH dai ya kiyaye Ilham ta riƙeta da sauri tana faɗin “Mama Scorpion”.
Garrrr kunamar dake neman ceton ranta itama ta shige ƙasan gado Hajiya Mama na kallonta da Ilham. Sai yanzu suka fahimci abinda ke faruwar...
Dole fa aka kira ma'aikatan gidan. Anci sa'ar akwai wanda suka sha maganinta. Dole sune sukai kama-kamar ɗaga su Hajiya ƙarama zuwa mota. Anan ne wasu kunamun har biyu suka faɗo ashe a jikin Hajiya ƙaramar suke. Asibiti aka wuce da su su duka biyar din. Su sunata ihu Hajiya ƙarama kuwa tuni ta suma ma ita dan azaba. Wannan al'amari ya matuƙar bama kowa mamaki. Duk da ana shan kashe kunamu a gidan harma macizai a wasu lokutan saboda garden amma ba'a cikin gida ko ɗaki irin haka ba. Abinma tambayar miya kawo kunama har cikin jiki haka? Ba kuma ɗaya ba har uku, Babu mai basu amsar tambayar nan dan basu sani ba.
Duk wannan bidirin da akeyi fa babu wanda ya sani a ɓangaren su Maash. Sai Hafizzullah ne dake salla ya ɗan fito. Ana wucewa da su asibiti kuma ya koma ciki shima abin na bashi mamaki. Shine ya samu Fahad ya tashi. Tambayarsa yayi ina