Showing 75001 words to 78000 words out of 438336 words

Chapter 26 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2191

ƙwalla kiran sallar asubahi. Ya fara alwala aka fara yaf-yaf na yayyafi. A gagauce ya ƙarasa ya wuce massalaci. Kamar jira ruwan nan yake a idar da salla ya fara sauka da ƙarfinsa. Kusan duk wanda ke a massalacin da gudu-gudu ya fita domin shiga gida. Hakance ta kasance tsakanin Yaya Musaddiq da Abba. Kusan a tare suka ja wani bahagon birki a ƙofar gidan sakamakon cin karo da abinda basuyi tunani ba ko zaton gani haka. (Tabbas Samraah ce ba gizo bane, ba kuma mafarkin daya sabayi bane ba). Musaddiq ya ayyana a zuciyarsa dake faman gudu da uban sauri a cikin ƙirjinsa. Da sassarfa ya ƙarasa inda take. Dai-dai nan ta fara motsa jikinta sakamakon ruwan sama dake sauka da ƙarfi. Kuka Musaddiq ya saki tare da durƙushewa a gabanta. Gaba ɗayanta ya wawuso ya rungume a jikinsa. Hakkane ya saka Abba dawowa hayyacinsa shima ya nufesu. Cikin rawar murya data jiki ya furta, “Musaddiq da gaske Samraah ɗin ce?”. Bai jira amsarsa ba shima ya kai durƙushe gabansu. Duk wanda yazo gittawa ya gansu sai ya tsaya. Kafin kace mi maƙwaftansu sun ɗan taru a wajen. Duk mazane da aka dawo daga massalaci. Maƙwafcinsu da suke katanga ɗaya ne ya bada shawarar a shiga da ita cikin gida. Wannan shawara tasa ta saka Musaddiq miƙewa ɗauke da Samraah. Ta farfaɗo amma bata iya banbance komai kamar wadda ke a buge cikin maye. Wannan yanayi nata yasa da yawan wanda suka taru a wajen ransu ya ɗarsu da abinda bashine ba.
Abba ne ya shiga kwala kiran sunan Mum. Sai gata a firgice. Da alama ma ita sai yanzu take tashi sallar. Su Baby ma ihun Abban ne ya tashesu a nasu barcin suma duk suka fito. Kowa yaci karo da Samraah sai yay wani irin ja da baya yana zaro idanu. Musaddiq ne kawai keta ƙoƙarin ganin ta buɗe idanunta da take lumshewa da buɗewa da ƙyar tamkar me maye. Kusan mintuna biyar kafin ta buɗe idanun da ƙyar sosai ta kallesa. Cikin siririyar muryarta data surka da mayen barci ta ce, “Yay..a Mu...sad...diq”.
Jikinsa har rawa yake wajen amsa mata da, “Na'am Samraah! Kandalata nine. Buɗe idonki da ƙyau ki sake ganina. Alhamdullah ya rabbi Alhamdullah.” yanda yake sambatun yana hawaye ga dariya sai ka ɗauka ya zautu ne. Su dai su Mum na tsatstsaye ciko-ciko kawai suna kallonsu. Musaddiq da duk ya gama rikicewa ya zaro wayarsa da sauri. Mansoor ya fara kira, dan abokin kuka shi ake fara gayawa mutuwa, wani ihun farin ciki da Mansoor ɗin ya saki sai da ya janye wayar dan jin zai fasa masa dodon kunne. Daga nan yay kiran d.c.o shima dan ya sani. Shima yanda yake ta jera Alhmdllh zai tabbatar maka yaji farin cikin. Suma yan gwarzo yay kiransu ya sanar musu. Ai kafin kace mi anata shigowa gidan, dan Mansoor ma cikin ruwan nan ya taho duk da gari bai gama washewa ba, sai daga baya jama'ar gidansu suka biyosa. Sanda suka taho an wuce da Samraah asibiti domin duba lafiyarta kamar yanda d.c.o ya bada umarni. Dan sam Samraah bata cikin hayyacinta saboda allurar da sukai mata.......✍️



_Hummm dangin Samraah sai a barmu mu hyaƙata, ga ƴarku nan mun sakar muku. Su o'e duk an addabemu dama🚴🚴😞._



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_


.......Lokacin da goma tayi gidajen rediyo dana tv da yawa sun sanar da ganin Samraah. Gidan tvn su ne ya fara fitar da batun, dan danan sai ga ƴan jarida. Sai dai an hanasu kowace irin dama ta ganin Samraah, dan har lokacin barci ma takeyi ita. Ƴan gidansu ma da ƴan gidan su Mansoor duk suna daga waje ne. Sai wajen sha ɗaya ƴan Gwarzo suka iso suma. Nan fa asibitin ya ƙara cika. Dole doctor ya roƙa su ragu. Dan ana buƙatar sanda zata farko ta farka a cikin hayyacinta. Gamsuwa da hakan yasa aka ragu, Mansoor da Yaya Musaddiq da Abba sai Kawu Musa kawai aka bari, sauran duk suka wuce gida.
Ƙarfe ɗaya da wasu mintuna Samraah ta farka. A lokacin babu kowa a ɗakin dan wanda aka bari asibitin duk sun wuce massalaci salla. Sai Nurse da aka bari ta kula da ita dan zata iya farkawa a koda yaushe. Hakance kuwa ta faru. Sai dai tana buɗe idanunta bakinta da addu'a Nurse ɗin nan ta miƙe. Sannu ta mata da farko, sai kuma ta ɗan fita kamar zatayi kiran Doctor ne. Babu jimawa sai gata ta dawo. A lokacin Samraah ta ɗan daddafa ta tashi dan wani irin fitsari take ji. Matsowa Nurse ɗin tayi gaban gadon tana mai cire wayar dake a kunnenta tai ɗan danne-danne da bai wuce sakan biyar ba ta nuna wayar akan fuskar Samraah dake kallonta. Dan ta rufe fuskarta ruff da face mask idanunta kawai ake iya gani. Baki Samraah ta buɗe zatayi magana da ƙyar dan ganin Nurse ɗin ta saka mata waya a gaban fuska. Amma saita mata nuni da wayar alamar nan zata kalla. Babu musu ta juya kanta a hankali tare da buɗe manyan idanunta da suka kumburo sosai sukayi ɗan ja a jikin fatar amma cikinsu tar-tar ta sauke su akan fuskar wayar. Numfashi ta nema janyo wa da sauri, amma hakan ya gagara sakamakon cin karo da fuskar wanda batai zato ko tsammanin gani ba shima ya zuba mata idanun nan nasa tamkar zai cinyeta ɗanya da su. Zaune yake ƙafa ɗaya kan ɗaya da salon zaman ƙasaitar nan tasa. A yanayin location ɗin da yake zai tabbatar maka da ba'a Nigeria yake ba ma. Duk da ta cikin wayane jinai kallonsa na neman yamutsa min kaina. Amma na dake a zahirance, sai ma wani irin mummunan kallo da nima nake jifansa da shi batare da nasan ina yi ba. Ƙara tsatstsareni yay da idanun cikin yanayin irin ke baki da kunya ko. Niko na yamutse fuska irin eh banda kunyar sai yaya.
Hannunsa ya kai ya shafo gashin dake a haɓarsa, cikin salon ƙara tamke fuskarsa cike da gizago shi a dole bai san raini murya a kausashe ya fara magana da ƙyar dan yanda lips ɗin ma ke motsawa kaɗan-kaɗan sai ka ɗauka bazaka iya jin abinda yake faɗa ba. Amma kuma sai na dinga jin muryar tasa raɗam a kunnena kamar ba'a waya yake ba.
“Ganinki cikin zur'arki bashi ke nufin wasan ya ƙare ba. Sai dai kina da zaɓi biyu. Bakin ki ya kasance shiru ki cigaba da rayuwa da waɗan nan mutane biyun”. Hoton Hafizzullah da Yaya Musaddiq ya bayyana. Bamma san sanda na waro idanuna waje sosai ba ina ɗan zabura. Shiko hankali kwance ya ciga da faɗin, “Ko ki buɗe sa da zance a kaina ni kuma na rufe miki shi ta yanda ko mai irin harafin farkon sunana kika ji sai kin firgita. Na barki lafiya”.
Da sauri nima cikin jin wani ƙarfi na ce, “Yaƙin sunƙuru ai na mai tsoro ne. Idan ka cika namiji kabar laɓe-laɓe a bayan ƙarfin dukiya kazo muyi gaba da gaba sai a banbance waye jarumin tsakanin ni da kai. Ita Sam-G a ko ina Samraah ɗinta take, bana ado da wasu domin kare suna ko ƙarfin iko na. Sannan garkuwa da wasu domin cimma buri ai tsohon salo ne. Video ne dai bazan bayarba, kuma har abada bazaka taɓa sanin inda yake ba, kai ni kaina bazaka sake gani na ba”.
Wani jahilin murmushi ya saki da sai da ƙirjina ya harba dan wani kalar mugun ƙyawunsa ne ya sake bayyana. Idanunsa ya ɗan lumshe da sake buɗewa a kaina cikin yanayin kallon ƙasa-ƙasa, bamma san na murguɗa masa baki da janye nawa ba. Ya ɗan taɓe baki cike da basarwa. Tare da motsa lips ɗinsa a daƙile ya ce, “Ina matuƙar son wasa da mutum irinki mai taurin kai da kaifin baki. Dan haka kar kiyi gaggawa, in dai yaƙin gaba da gaba ne yana tunkaro ki, dan haka jekiyi shiri na musamman, dan yaƙi da Awwab Maash dai-dai yake da tunkarar mayaƙan duniya. Bye sai mun haɗu a filin daga”. Ya ƙare magana da salon kashe ido ɗaya ya ɗaga min yatsu biyu. Ai bamma san na zabura baya ba ina waro idanuna gaba ɗaya waje dan al'ajabi, ka jimin kwarto zai iskantani, dan wannan abun da yay ai na ƴan iska ne. Baki na buɗe zanyi magana. Ɓat ya ɓace tamkar bai taɓa bayyana a fuskar wayar ba. A hargitse na kalla Nurse ɗin da ke ƙoƙarin amshe wayarta. Itama ni take kallo. Cikin tsumar jiki na ce, “Malama sake kiransa!”.
Baki taɗan taɓe, a gadarance ta ce, “Ai shi Boss GIWA ne baya WAIWAYE.”
Cikin ɓacin rai na ce, “Wacece ke?”.
“Sanin wacece ni bazai amfaneki da komai ba. Kare rayuwar ƴan uwanki biyu shine mafi muhimmanci gareki da yin shirin yaƙin dake tunkaroki kamar yanda ya faɗa a yanzu, dan shi baya magana biyu, kada ki sakankance da yawa, in har yace zaiyi, to lallai ya gama shirya yin ne. Idan yace bazai yi ba, babu mai sakasa yin. Zan sake baki shawara akan abinda boss ya faɗa miki. Idan kin kiyaye tabbas kin tsira, domin shi tamkar ifiritin ALJANI yake. A duk inda kika saka ƙafarki yanzu ki ɗauka yana biye dake ne taku bayan taku. Rayuwar ƴan uwanki tana da matukar muhimmanci a gareki, kece kuma zaki tabbatar ma da duniya hakan ta hanyar sakawa a ranki kamar baki taɓa ji ko ganin komai ba akan Boss. Zaɓi ya rage naki, nima na barki lafiya”.
Da sauri na yunƙura da nufin cafkota, sai dai wani irin jiri ya nema kwasata dole na koma saman gadon jagwaf ina mai dafe kaina dake juya mun. Dai-dai nan Doctor ya shigo tare da Nurse. A kaina suka rufu suna jera min sannu. Niko gaba ɗaya ma bawai ina jinsu bane ba da ƙyau. Dan hatta ɗakin jinake yana amsa amon muryarsa tamkar a yanzun ne yake jera min gargaɗin ko barazana zan jirashi ma ban sani ba. Sama-sama nake jiyo doctor na faɗin, “Barcin nan bai gama sakinta ba. Sister Fadila gyara mata kwanciya”. Daga haka ban sake jin su ba.

★★Sai yamma lis na sake farkawa. Yanzu kam Alhamdullah dan duk wanda ya kalleni yasan ina a hayyacina. Dukan ƴan uwana kuma an basu damar shigowa dubani. Ina zaune a gadon na jingina da filo Gwaggo Gudidi na bani shayi. Gaba ɗaya idona ya kasa barin kan Yaya Musaddiq, kaɗan-kaɗan kuma nakan ce masa ya kira Hafizzullah ya ji yana lafiya. Yanda nake ɗin sai kowa ke ganin kamar ban gama saki bane shiyyasa. Niko ni kaɗai nasan a halin da nake ciki. Wani furuci da Mum ta furta lokacin da ƴan gidan su Mansoor suka zo ya saka ɗakin yin tsit duk aka zuba min ido har ina jin jinina na yamutsawa.
A gatsine bayan ta kallan da ga sama har ƙasa lokacin da Gwaggo ke lallaɓani na ƙarasa shan shayi ta furta, “Ai waɗan nan kidnappers ɗin ma dai masu mutunci ne da wayewar kai. Yanda duk wanda aka kama ke dawowa wujiga-wujiga amma ita Samraah gata nan fes da ita. Sai ma uban haske data sake ga fata sai ƙyallin jin daɗi take yi kamar mai yaron ciki. Koda yake ance idan sukaga masu ƙyau musamman ƴammata sukan maida su kamar matansu ne suyita musu gata kuma. Maza ne dai ke shan baƙar wahala da duka. Da alama kema dai sa'ar kika ciwo kansu ɗiyata, mudai in ma wani bai aureki a cikinsu ko ya lalata miki rayuwa ba ai Alhamdullah, duk da kema ɗin ba abin yabo bace tunda dama ko ina yawonki kike yi tumma kan faruwar hakan”.
Gwaggo Gudidi ce ta katse shirun ɗakin idonta akan Yaya Musaddiq daya wani dunƙule hannu. Gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun gama fitowa alamar yau ɓacin ran maza ya fito fili. Ya ɗan motsa da alamar zai yunƙuro Gwaggo ta katse hakan ta hanyar duban Mum da ƙyau. Murmushi ta sakar mata itama, sannan ta furta,........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_



.......“To banda abinki Jalilah ai kidinafa ɗin dama kala-kala ne. Duk wanda ya fahimci wanda suka ɗauki Samraah kuma ai yasan ba masu neman kuɗi bane. Akwai wata manufa da ake son cimmawa. Ba kuma na raba ɗayan biyu akan rahamar da UBANGIJI yay mata ta samun miji kawai ake son aga an tarwatsa. Sai kuma ALLAH da yake shi maji roƙon bayinsa ne sai gashi ya rusa duk wani makircin masu makirci ƙarfin addu'a yayi tasiri dan gashi UBANGIJI ya dawo da ita gida a lokacin da magauta wannan aure basu so ba. Kuma in sha ALLAHU babu fashi ranar juma'a iyanzu tana nan da igiyoyi uku a kanta”.
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Mansoor ya sauke yana mai lumshe idanunsa. Yayinda Mamyn sa tai ɗan murmushi kawai. Hakama Dad ɗinsa da su Kawu Lurwanu duk murmushin sukayi. Attahir kuwa mintsinin Mansoor yayi yana kashe masa ido ɗaya cike da tsokana. Hakama ƙannensa Islam da Sakeena dake zaune kusa da Samraah duk murmushin sukayi. Aiko Mum kamar zata haɗiyi zuciya, amma dai ta danne tana murmushin yaƙen itama kamar kowa. Abba ma baice komai ba, da ga ƙarshe ya wayance da an kirasa a waya ya fita yana amsawa. Yaya Musaddiq ma a hankali ya dinga sakin ajiyar zuciya jijiyoyin kan nasa na saki sannu-sannu, dan koba komai amsar da Gwaggo ta bama Mum ta fanshi duk wani ɗaci da fushin daya yunƙuro masa. Ni dai kaina a ƙasa ina satar kallon Yaya Musaddiq, zancen Gwaggo ya sakani jin kunyar kowa dake ɗakin musamman ma family ɗin Mansoor. Dan dama tunda suka shigo ban sake yarda na kalli kowa ba. Ko magana da ƙannensa ke mun ƙasa-ƙasa ɗan murmushi kawai nake musu. Lokacin sallar magrib kowa ya watse. Iyayen Mansoor da ƙannensa suka wuce. Hakama Mum da su Kawu Lurwanu Yaya Musaddiq ya tafi kaisu masauki. Shi dama Abba tun wayar nan daya fita bai sake dawowa ba. Su Baby kam har yanzu ban gansu a asibitin ba. Dan ko Abbas dake matsayin babbansu bana jin yama zo dubani, koma basu san na dawo bane oho, koda yake da wuya ace hakan ta kasance gaskiya.
Daga ni sai Gwaggo Gudidi aka bari, sai bayan sallar isha'i ne Yaya Musaddiq da Mansoor suka dawo. Babu jimawa da shigowar tasu sai ga d.c.o da yaransa guda biyu. Sun nuna jin daɗinsu na ganina garau yanzun, dan doctor ma yace zai sallaman da safe tunda banda wata matsala a tare dani, sai rashin ƙarfin jiki na allurar da suka min, tun ma a daren yay niyyar sallamata Mansoor ya ce a barni sai washe gari dai na sake jin ƙarfi da kuzari. Mun gaisa da su suka jajanta min kan abinda ya faru. Kafin d.c.o ya tabbatar min dana kwantar da hankalina na kuma basu haɗin kai mutanen nan ko su waye su sai sun kamasu an hukuntasu.
Amsa masa nai kawai da kaina dan nasan abinda yake faɗar bamai yiwuwa bane ba. Wani ma idan nace ga wanda yay kidnapping ɗina cazai ƙarya nake yi. Su kuwa koda ma sun san gaskiya babu abinda zasu iya yi ɗin kamar yanda yake faɗa. To shi hatsabibin aljanin ma zai basu wata ƙafane da zasu gane shine, dan magana ta ALLAH al'amarin mutumin nan ya fara sakani a firgici, dan bana jin na taɓa cin karo da makirin mutum, hatsabibin gaske da ko tsoro bazaka taɓa karanta a yanayinsa ba irin wannan mutumin. Ga shi yayta wani shan ƙamshi cikin gadara da karfin iko kai kace shike mulkar ƙasar. Ta wani ɓangaren kuma ina buƙatar rayuwar ƴan uwana. Dan wannan mutumin babu shakka zai iya aikata abinda ya faɗa koma fiye da shi tunda na gani da idona sanda yake zare wuƙa a jikin wani. Ga kuma abinda Nurse ɗin nan tace, a duk inda muke yana biye damu ƙafa da ƙafa. Zan kare rayuwar ƴan uwana kamar yanda yay min barazana, sai dai fa idan yasan wata baisan wata ba. Nayi alƙawarin saina ƙullama rayuwarsa tarkon da bazai taɓa iya kuɓutar da kansa ba. Dan saina tabbatar masa da *_TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE_* da ƴar Abdul-wahab Gwarzo yake magana. Nashi kuma wasa ne, bai san mi ake kira kaidin mata ba sai na tabbatar masa.....
Taɓanin da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login