Showing 51001 words to 54000 words out of 438336 words
Auta da uwar gulma Bibaa kawai a wajen. Bamu tashi a falon ba sai sha biyu. Abba ko tun sha ɗaya matarsa tazo ta tasashi suka shige ko kunyar Gwaggo Gudidi bata ji ba balle mu ƴaƴa. Shimfiɗata na barma Gwaggo, dan Yaya Musaddiq ya kawo mata babban bargonsa. Zan kwanta a ƙasa tace na hawo kan bargon. Badan naso hakan ba na hau dole. Sabuwar hira muka buɗe da ita har sai ɗaya sannan barci ya kwasheta. Niko alwala na tashi nayi nai nafilfilina kamar yanda na saba sannan na kwanta. Hakan kuma bai hanani tashi uku da rabi ba na shiga ayyukana. Kafin kace mi na kammala, dan har abinci naima Gwaggo na saka mata a kula nakai ɗaki dan nasan ba lallai da rana a bata na kirki ba. Gashi ban dawoba lokacin. Kalacin ma isashe na ɗiba mata. Itako tanata mitar yanda nake wannan uban aiki ga fitar safe kuma. Ni dai bance komai ba face murmushi kawai. Yau kam Yaya Musaddiq ya shigo gidan domin gaisheta. Ya ajiye mata kayan shayi da ƙaton bread ɗin ta harda soyayyan ƙwai. Albarka ta dinga saka mana sannan mukai mata sallama muka wuce dan kar mu makara.
Gwaggo Gudidi itace ta raba komai na kayan sa ranar nan. Har maƙwafta sai da tasa Auta ya kai ma kowa gida-gida. Sannan dangin su ta ƙulla na kowa daki-daki. Wanda ke anan cikin Kano ta saka Yaya Musaddiq ya kaita ta kai ma kowa. Na Gwarzo ma tare sukaje takai duk na ɓangaren danginsu dai. Yaya Musaddiq ma da Hafizzullah ta ɗiba musu. Nima komai sai da ta ɗiba min. Hakama jama'ar gidan kowa da nashi. Kuma kowa zai iya rabama abokan arziƙinsa idan yaso. Amma sai Mom tai biris da nata anan falo har Gwaggo ta wuce bata ɗauke ba daga ita har ƴaƴanta. Abba dai ganin Gwaggon yasa shi zama ya ƙuƙƙula ya fita dasu wai zai rabama abokansa da ƴan wajen aikinsu. Ya raba ko bai raba ba oho masa.
A ranar da nakai ma ƴan office ɗinmu kowa ya sake sanin alaƙata da Mansoor, dan wasu basu ɗauka gaske soyayya muke ba saboda yanda muke komai cikin taku. MD kuwa ai kamar zai mutu. Dan masifa yayta zubama kowa a wannan yinin babu gaira babu sabar. Har dai ƴan uwana ma'aikata suka fahimci kishi yake yi. Ni dariyama ya bani wlhy. Mansoor kam yaji daɗin abinda nayi, dan bai ɓoye ba sai da ya sanar min. Murmushi kawai na masa nidai. Bayan an tashi aiki ya buƙaci kaini naga aikin gida da ake ƙarasawa. Amma sai nace masa ba yau ba ya bari weekend zai fi. Shima ya yarda da shawarar tawa. Dan haka ya maidani gida. A ranar ne kuma na fahimci wata farar mota na binmu a baya. Duk da naji tsoro sai banyi magana ba, nace bari dai na tabbatar. Ganin munzo titin shiga layinmu motar ta wuce yasa na sauke ajiyar zuciya har Mansoor na kallona.
“Lafiya irin wannan ajiyar zuciya haka kamar wadda nai shirin sacewa. Ko tsoro kike kada na wuce dake ne?”.
“Ai kaima bazaka fara hakan ba sai an baka”. Na faɗa cikin kauda kai ina murmushi. Shima ƙaramar dariya yay da sake faɗin, “Hakane. Amma da zama a taimaka a banin yau zanfi kowa farin ciki. Maybe ma na ƙara samun ƙarfin aikin yanda ya kamata”.
“Humm” kawai nace na buɗe motar na fice ina murmushi. Godiya na masa kamar kullum. Yanata son mu haɗa ido amma naƙi yarda da hakan. Sai ma na wuce da sauri na shige gida abina. Amma na maƙale jikin gate ina leƙansa. Yaja kusan minti ɗaya idonsa a gate ɗin fuskarsa da murmushi kafin ya tada motar ya wuce...
★★★
Abubuwa kullum ƙara tsamari suke a gidanmu. Dan kullum al'amarin Mom da yaranta gaba yake yi. Ina sake samun tsangwama da hantara fiye da baya a yanzu sakamakon wannan batun auren. Yayinda Baby ta fito da maitarta akan Mansoor yanzu. Shi kansa ya fara nuna min tana matsa masa. Ashe tun da can ma da bata fiddo abubuwanta fili game da shi akwai abinda take shakka daga garesa, na kuma fahimci wani babban sirrinta ne ya sani duk da yaƙi fitowa fili ya faɗa min.
Sam ba'a wani shiri irin na aurar da ƴa a gidan, musamman ma mace da bikinta ke da yawan hidima. Ko kaɗan hakan baya damuna. Dan nasan Yaya Musaddiq tsaye yake akan al'amurina ta bayan fage. Dan yanzu kusan duk sati zakiga Gwaggo Gudidi tazo mana. Da alama akwai abinda sukeyi ita da Yayan. Duk da madai ashe shi Mansoor ya samu Yaya akan shi baya buƙatar komai na gida duk zai zuba. Ni shaidace akan abinda ya faɗa ɗin domin ya kaini naga gida. A randa mukaje ɗin kuma na sake kama motar nan na binmu. Hankalina ya tashi fiye da ranar, amma nai jarumtar dannewa saboda kada na tada hankalin kowa. Nayi kuma alƙawarin saka ido sosai dan na tabbatar shin da gasken binmu ake kokuwa zargina ne kawai. Tun daga wannan lokacin na saka ido fiye da koda yaushe. Babbar magana kenan wai ɗan sanda yaga gawar soja, nako tabbatar bibiyata akeyi ɗin. Dan harna haddace Number motar duk da dai mai ita kan canja ne kusan da kala uku, sannan ita kanta motar wani lokacin bada ita ake bina ba da napep ne. Al'amarin ƙuruciya irin nawa da wauta, maimakon na sanarma ko Yaya ne sai nai tunanin kada na tada masa da hankali, gara na fara sanin wanda ke bibiyar tawa dai. Wannan ɗammara dana ɗauka tasa na fara ƙin daina bin yaya na koma shiga napep. Hakama Mansoor wataran sai na ƙi biyosa, ina amfani da yanayin da yake ciki na busy yanzu akan shirin biki. A ranar farko dana fara yin ƙundun balar tarar motar nan sai aka gudu. Karo na biyu ma haka. Ganin haka na sake himma dan a ganina tsorona ake ji. A karo na uku na haɗa kai da ƴan ƙato da goran anguwarmu a ɓoye akan idan ma fita su bini a baya. Na basu numbers na motar da ake amfani da su har kala uku. Abin zai baku mamaki, dan kamar mai motar nan ya fahimci abinda nake ƙullawa ranar sai bai bini ba. Tsahon kwana uku haka na ƙara yarda yaji tsorone na sallami ƴan ƙato da goran. Sai me a randa na sallamesu a ranar na cigaba da ganin motar kuma. Raina yakai ƙololuwar ɓaci. Na fara zargin MD ne kemin hakan ko kuma Abba ko Mom ko Baby. Kai har Mansoor sai da na zarga, to sai dai kuma shi danmi zai sa a bibiyan bayan kullum muna tare. (Bincike) zuciyata ta ayyana min. Ban gamsuba, dan in bincikene ai iyayensa ne zasusa ai musu. Sannan bata wannan hanyar ba, anguwarmu zasu je. Amma duk da haka sai nace bari na gwada kowannensu.
Da Baby da Mom na fara. Sai banga wata alamar hakan ba daga garesu. Shima Abba haka. Sai kawai na koma kan Mansoor. A randa na taresa da zancen ina magana cikin tsiwa kan basai fa yasa ana bibiyata ba zai san halina. Idan bincike yake son yi a kaina yazo ga ƴan anguwar dana tashi cikinsu tun ƙuruciya har girma mana. Amma sakawa ana bibiyata kamar son firgitar da ni ne. Tare da nuna rashin aminci a tsakanina da shi. Sagale yay yana kallona da mamaki, sai dai bai iya cewa komai ba harna fita a fusace. To ashe daga nan bai zame ko ina ba sai wajen Yaya Musaddiq suka tattauna akan hakan. Lokacin da Yaya Musaddiq ya dawo aiki yay kirana ɗakinsa.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚_
.......Da faɗa ya faramin tare da turkeni kan saina faɗa masa dalilina na jifan Mansoor ɗin da waɗan nan kalaman. Da farko naso dojewa. Amma ganin yanda ya birkicemin a yanayin da bai taɓa ba bamma san na saki layi ba na zayyane masa komai. Tashin hankali na gani sosai a tattare da shi. Ya sake balbaleni da faɗa cikin ruɗani.
“Amma Samraah baki da hankali. Yanzu wannan abin na faruwa da ke tsahon sati biyu amma kika ja bakinki kikai shiru sai yanzune kike faɗa. Shima badan kunyi haka da Mansoor ɗin ba da bamu kamo bakin zaren ba. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un Samraah baki da wayo, wlhy sam baki da wayo. Dan tabbas bana raba ɗayan biyu mutumin nan ne yasa ake bibiyarki. Dolene ma ya gano kin ɗauki videon nan. Wannan abin shi nake gudu tun farko daman, shiyyasa kullum nake cikin tunanin mafita ashe nima nayi sakaci...”
“Yaya ban gane ba. Wai kana nufin wancan mutumin mai ɗaure gashi Maashi yake komi ma oho masa”.
“Idan bashi ba wanene Samraah. Tabbas dole shine zaisa a iya miki irin wannan bibiyar. Samraah kodai kinyi wani yunƙurine a kansa batare dana sani ba, dan na sanki da shegiyar wautar tsiya”.
“Wlhy Yaya ni babu abinda nayi, kaima kasan kuma bazanyi komai ba sai da saninka. Ka tambayi Mansoor ALLAH ne shaidata shima shaidatane. Daga office bana zuwa ko'ina sai gidan nan. Weekend kuwa islamiyya ce kawai ko Malam Umaru zai tabbatar maka da hakan shima. Toni wanema yunƙuri zanyi tunda kunce nabar komai a hannunku. Wlhy ko video ɗin tunda na adanashi ban sake waiwayarsa ba balle ma na kalla har wani yaji ko ya gani. Hatta da Mansoor ranar yake cemin ALLAH ya kiyaye yana rage abubuwa ya goge video ɗin nan, da ace banda shi a wayata da an samu matsala. Amma dan ALLAH na sake adanashi kada nayi sakaci tunda na sanshi shi da goge-goge a waya na tsiya.”
“Nasan baza'a samu matsala daga gareki ba Samraah. Amma dole mutumin nan yanada cctv camara ai, idan kuma mai yawan bibiyar abubuwane to tabbas anan ya gano shine yasa ake bibiyarki. Ko kuma wani ya ganki. Ina dai zuwa bari na kira Mansoor yazo ya same mu”.
Ban iya cewa da shi komai ba. Sai faɗawa duniyar tunani kawai da nayi. Harya kammala wayar bamma sani ba. Cigaba yay da kai kawonsa alamar haɗa lissafin abubuwa. Cikin abinda baifi mintuna talatin ba sai ga Mansoor yazo. Kasancewar lokacin sallar isha'i yayi suka tafi massalaci. Sai da aka idar suka dawo ina ɗakin Yaya ɗin dai har sannan. Mansoor na gaida daga haka suka shiga tattaunawa danni gaba ɗaya zuciyata bata tare da gangar jikina. Sai da Mansoor yaymin tambayar ni da waye muka je restroom ɗin a ranar? Dan tambayace da ya kamata ma ace sun min tun a waccan ranar amma basu yi ba. Saida na sauke ajiyar zuciyar dawowa hayyaci sannan na sanar musu ɗaya daga cikin securitys ɗin da suka bada tsaro a ranar ce. Na sake maimaita musu yanda mukayi. Sun sake tambayata bayan ita ban haɗu da kowa ba? Sannan itama ɗin sanda ta tafi yin wayar bata dawo bane nemana?.
“Eh gaskiya ni dai banga ta dawo ba, kasancewar ma hankalina ya tafi akan abinda ya faru ban sake bi takanta ba. Dan haka ban san miya hanata sake komawa ba. Kuma ni gaskiya bana jin nama sake ganinta har aka tashi”.
Kallon juna Yaya da Mansoor sukai. Cikin ƙarfin hali da nuna tashin hankali Yaya Musaddiq ya ce, “Anya kuwa security ɗin nan bata koma ba a lokacin. Idan lissafina yayi dai-dai, ta koma domin su fito tare kamar yanda ta mata alƙawari, maybe bata sameta ba ta shiga nemanta, ko kuma ta sameta a lokacin da take bude-buɗen ƙofar ko ma ɗaukar video ɗin. Dan inba haka ba babu yanda za'ai tai ɓatan dabo gareta. Hasashe na biyu lokacin da take faɗa maka ko wani ya jiku. Cikin biyun nan dole ɗaya ya tabbata, kuma duk inda zancen ya fito to tabbas an samu Maash an fargar da shi komai shiyyasa yasa ake bibiyarta.”
Cikin jinjina kai Mansoor ya ce, “Tabbas hasashen ka zai iya zama gaskiya Yaya. Amma ni a wannan gaɓar ma sai hankalina yaso rabuwa biyu akan wasu dalilai. Maash bawai ƙaramin mutum bane. Kana ganin ya aikata wannan kisan ya kuma san ya aikata har wata ace ta ɗaukesa a hoto mai motsi ya sani kuma ya zauna sakaci. Duk da yanda muke tunani abinda masu hannu da shuni ɗin nan suka tsana a rayuwarsu shine su binne wani laifinsu amma ya zama yana a hannun waninsu ko waninsu ya sani. Zakaga suna gaggawa wajen ganin sun daƙile komai. Idan lissafina yayi dai-dai wata fa kusan ɗaya kenan da faruwar komai. Kana ganin zai zaman ɓata lokacine akan wani bibiyar Samraah bayan yana da hanyoyi masu yawa dama zai karɓi video ɗin a hannunta batare da wata gargada ba. Karfa ka manta har hira yazo anyi da shi kuma itace tai da shi, randa aka saki hirar kuma ƙura ta tashi sosai da kace nace ɗin mutane harda masu cewa akwai alaƙa tsakaninta da shi, nasan dai kasan komai ba sai na sake maka bayani ba. Na kawo wannan hujjojin ne saboda bana son mu shagala da yawa a kan shine wanda kuma ke son ƙulla tsiyar na gefe. Kuyi haƙuri MD kansa na cikin zargina. Dan na jima da fahimtar yana son Samraah na hauka, randa kuma ta kai musu kayan saka bikin mu ya tabbatar ma da kowa hakan. Sai ƴar uwarku Baby. Tana sona matuƙa, wasu dalilai ne suke dakufeta, naji a majiya kai ƙarfi cewar tai alƙawarin sai tabi tako wace hanya domin ganin auren nan namu bai yiwu ba, dan tana da babban plan akan haka akwai kuma mai bata ƙwarin gwiwa ta bayan fage. Saboda yima kanta alwashin indai itama bazata sameni ba sai dai su rasa su duka. Da farko na ɗauki zancen shirme kawai irin nata na ƴan shaye-shaye, sai dai wannan abin na yanzu ya fara haskomin da gaske zata iya komai fa. Dan haka musa hankalinmu jikinmu domin tabbatar da ko wanene”
“Shaye-shaye kuma? Wai babyn ce ke shaye-shaye ko wa?” na faɗa ina kafe Mansoor da idanu. Murmushi kawai ya mun da faɗin, “Hum Samraah kenan, ke dai ALLAH ya shirya mana zuri'a kawai”.
Yaya na kalla a firgice, sai naga shi babu alamar mamakin zancen akan fuskarsa. Kasa haƙuri nayi sai da na ce, “Yaya kenan kaima kasan tana Shaye-shayen?”.
Sai da ya sauke numfashi mai nauyi sannan ya furta, “Na sani Samraah. Na kumayi iya yina na ganin ta daina amma hakan ya gagara. Na lurar da Abba amma ya nuna sharri nake mata. Tun daga nan na tattarasu na watsar”.
Zancen ya matuƙar girgizani gaskiya. Kamar yanda sosai maganar Mansoor tayi tasiri garemu ita game da MD da Baby da zasu iya sakawa a bibiyeni. Dan duk abinda ya faɗa gaskiya ne. Ni komai ma sai naji ya sake susuce min. Amma duk da haka Yaya yace bazamuyi sakaci da duka ɓangarorin uku ba. Zamu saka ido za kuma ku ɗauki matakin daya dace da kowanne. Dan haka zamu kai report wa yan sanda akan ana bibiyata, amma bazamuyi batun video ba fa, zamu bar ƴan sanda suyi aikinsu, idan ma Maash ɗinne da ga baya idan fito da videon ta kama sai muyi hakan. Nanma mun gamsu, kun kuma bashi goyen baya, duk da ni dai naso ace tun yanzu muka fidda video ma wa yan sanda. Amma ban san dalilinsu na son a ɓoye video ɗin nan kamar wani suna tsoronsa.
Kwana biyu dayin haka aka kawo lefena da ga gidan su Mansoor. Akwatina har goma sha biyu shaƙe da kayan alfarma na gani na faɗa. Babu wanda zaice lefen nan bai birgesa ba. Sai dai anga tsagwaron hassada daga Mom dan ta kasa haɗiye komai. Harda zage-zagenta wai ai saurayin Baby ne na kwace da asiri. Kuma ba kowa ke kawo min asirin ba sai Gwaggo Gudidi. Abu kamar wasa dai sai da aka kwashi rigima. Dan ƴaƴan Gwaggo Gudidi duk sun zo suna gidan. Rikici akai sosai na gaske. Lokacin Yaya Musaddiq shi baya gida. Yana wajen aiki, kamar dai wancan karon ya damƙa komai hannun matar ogansa aima baƙi abincin tarba da kayan maƙulashe. A wajen aikin ma ba zama yay ba shi da Mansoor suka fita police station wajen batun ƴan sanda. Sun shigar da report tare da bada lambobin mota har uku dana basu.. Suna can har aka gama rikin nan kowa ya kama gabansa dan su Gwaggo ma sun ɗauke lefen nawa daga gidan sun wuce da shi can gidanta. Acewarsu barinsa gidan Abba bazai yiwu ba su Mom zasu iya salwantarwa saboda basu da isashen mutunci. Ashe ko hasashen su Gwaggo yay dai-dai. Dan su Mom sun shirya mummunan ƙudiri kuwa akan lefen nan aka ɓata musu shiri. Wannan yasa suka huce kaina sanda na dawo. Dan bana