Showing 372001 words to 375000 words out of 438336 words
Badan sun so hakan ba saboda matsuwar zama da Mama Balki suka je duk suka aiwatar. Badai a samu zama ba sai bayan sallar isha'i har su Maash sun dawo gidan. Dama suna asibiti ne wajen su Paah. Sai da suka ga komai ya daidaita sannan suka taho. Baba prof da Hajiya ƙarama na ƙarƙashin kulawar hukuma da likitoci. Sai Arwa da Paah da suke a kulawar asibiti dan su basu da alaƙa da jami'an tsaron. Har lokacin ina nane da su Abba. Sai tambayoyi nake zuba musu akan kowa da bayan tahowata. Cikin ƙarfin hali Abba ke amsa min, dan ya kasa kallona saboda kunya. Nima na fahimci hakan, amma sai ban nuna masa ba. Gwaggo Gudidi kam bakinta ya kasa rufuwa da yaba gidan ita da Kawu Lurwanu. Shi kansa kawu Musa na fahimci na manya kawai yake dan sai faman jinjina kai dai yake kasancewar yanzu duk muna a sashen Maash ne.
Kallo ɗaya da nai ma Maash da suka shigo na fahimci a matuƙar gajiye yake. Koma nace alamominsa sun nuna tamkar ma bai da lafiya. Dan sai faman kai hannu yaje saman goshi time to time. A haka yay dauriyar zama suka gaisa da su Kawu Musa. Naji daɗin yanda ya girmama iyayena. Ga Ummie nata ɗawainiya da su itama kamar babu abinda ya dameta. Nan ko itama ɗazun ina kallonta tana sharar hawaye sai dai tana jin motsina ta goge fuskarta ta dake. Sai lokacin na fahimci ɗazun ma saboda mu take dakewar ashe. An gaggaisa da yima juna godiya da addu'oi kafin su Kawu Musa su bama Mama Bilki da Falaq haƙuri, sun amshi laifinsu da kuskurensu ƙwarai da gaske. Sun kuma nuna nadamarsu tun a wancan lokacin dan har Lagos ɗin sunzo nemanta rashin ina zasu kama yasa suka haƙura suka koma. Hatta gadonmu da aka raba da sunan Falaq a ciki, sun kuma tabbatar da yana nan ajiye basu ci ba. Wannan magana ta karyarwa Abba zuciya ya hau sharar hawaye shima. Haka ya shiga bamu haƙuri har Yaya Musaddiq da Maash ya kira a waya video call tun fara zaman. Yanda yake kuka yana faɗa mana wlhy duk Mom ce take cewa su sayar tunda shike wahala da mu, ko yaso bijire mata baya iyawa, wani lokacin sai sun ɗaga abu sun sayar ta dawo yayta kuka da ga baya a ɓoye. Baya jin daɗin abinda ke faruwa da mu a gidan musamman ma ni, amma bai san miyyasa baya iya tsawatar mata ba. Shi kansa yasan an zalunceni fiye da kowa a cikinmu, dan badan tsarewar UBANGIJI ba da kuma tsayawar Yaya Musaddiq akan tarbiyyata dana lalace kamar yanda Mom taso, sai dai shi ALLAH ba'ai masa dole, a ƙarshe dai gashi nan komai yana neman juyewa a kansu. Yanzu haka ba'a san inda Baby take ba. Sun je har dangin mijin nata satin da ya wuce suka musu korar kare akan sanda akai auren ai basu sani ba. Suje can su nema ƴar su suma tuni sun fidda mijin nata a cikin jerin ƴaƴansu. Ashe sauran matansa ma dake tare da shi zaman ƴaƴansu kawai suke yi tuni an raba aurensu tun sanda yayma amaryarsa fyaɗe ta baya ta tona masa asiri. Shine ya gudu yabar ƙasar, daga baya ya dawo ya auri Baby bada saninsu ba. Ƴan uwansa tsiraru da aka gani wajen bikin nasu na binsa ne saboda kwaɗayin abin duniya. Wannan al'amari ya ɗaga mana hankali. Yanzu haka Jalilah na asibiti yau kwana biyu kenan. Ga Abbas sun daki wani yaro a makaranta babansa babban mutum ne yasa an kamasu an rufe yau kwana biyar kenan shima. Munyi yawon bashi haƙuri babu adadi yaƙi sauraren mu ni da sauran iyayen yaran...” kuka ya sarƙe Abba. Daga ni har Hafizzullah da Yaya Musaddiq kukan muke muma. Yayinda gurin kowa yay tsitt, sai ma Ummie ce ke lallashin Hafizzullah dake kusa da ita da Fahad. Niko ina jikin Gwaggo ne da itama ke kukan. Hakama Falaq kuka take sosai ganin muna kuka.
Maash ne cikin ƙarfin hali yay gyaran murya. Duk kallonsa mukai, cikin dakewar nan tasa ya furta, “Inaga kukan ba shine mafita ba. Addu'a ne kawai. Sannan in babu damuwa ina son sanin sunan shi mutumin dake tare da yarinyar”.
Cikin kuka da zabura Abba ya faɗa masa. Kansa kawai ya jinjina yana miƙewa. Sai da yay ɗan taku biyu a hankali ya furta, “Sai da safen ku”. Daga haka ya haye sama. Da kallo duk muka bisa. Sai da ya ɓacema ganinmu Sheikh Muhammad ya ce, “Abubuwa sun masa yawa. Zuciyar ce kawai a tsaye. Inaga muma ya kamata duk muyi haƙuri mubar komai zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu. Dan ita kanta mahaifiyarsa likitocinta sunzo ganinta. Muma kuma muna buƙatar hutu. Ɗiyata tashi kije ga mijinki kinji”. Ya ƙare maganar yana nuni da ni. Ji nai kamar na nutse a wajen dan kunya. Sai da Gwaggo ta miƙar da ni. Sum-sum na wuce zan tafi Mama Balki Sarkin ƙarfin hali ta dakatar da ni. Kwandon data shirya abincin Maash ɗin ta bani, haka na amsa babu musu na haura saman nima da ƙyar. Na jima tsaye a bakin ƙofar batare da nasan miya kamata nayi ba. Komai da kowa tausayi suke ban a gidan. Hatta ni kaina tausayin kaina nake ji da kaina. Kusan mintuna biyu sannan nai ƙarfin halin buɗe ƙofar na shiga da sallama a bakina.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._
......A kwance na sameshi rai-rai saman kujera idanunsa a lumshe hannunsa dafe da kansa. Ƙafarsa ɗaya a ƙasa ɗayar a saman kujerar ya ɗan dogareta. Har na ajiye basket ɗin saman table na ƙarasa gabansa bai ko motsa ba. Babu alamar ma yasan da shigowata, dan kallo ɗaya zaka masa kasan ya mutaƙar yin nisa a cikin tunani. Gwiyawuna na kai durƙushe ƙasan carpet ɗin saitin inda fuskarsa take. Idanu na zubama ƙaramin pinkish lips ɗinsa da suka bushe na wasu sakanni. Kafin a hankali na kai hannuna saman nashi daya sa a kansa na janye. Har lokacin bai buɗe idanunsa ba, sai na ƙara jin gaba ɗaya zuciyata ta karaya. Mutum mai kaarfin hali irin Ya Awwab kaga yanayinsa ya canja haka ai ba ƙaramin abu bane ba. Bance da shi komai ba na ɗaura hannuna akan botiran shirt ɗinsa na fara ɓallesu. Har sai da na gama duka kafin na miƙe, saman jikin nasa na haye na kwanta gaba ɗayana na kwantar da kaina a ƙirjinsa. Sai kawai na saki masa kuka, dan jina a jikin nasa sai naji wani irin raunin zuciya ya sake mamayeni. Komai daya faru a ɗazun da yanzu ya zame min kamar yanzu-yanzu yake kan faruwa.
Nafi minti ɗaya a hakan batare daya tanka min ba kafin naji saukar hannayensa a saman bayana. A hankali muryarsa can ƙasan maƙoshi sosai ya furta, “Miya faru kuma?”.
Sai kawai na sake ƙanƙamesa nima, a hankali na furta, “Nayi kewarka”.
Rungumeni ya sake yi da ƙyau shima yana wani jan nannauyan numfashi da busa min iskar cikin kunnena. Yanzu kam mun ɗauki tsawon lokaci a hakan da har mu kammu bamu san adadi ba, har na daina kukan na koma jan ajiyar zuciya kamar yanda shima yake yi. Muryata acan ƙasan maƙoshi na furta, “My Hot”.
“Uhhyim”.
Ya amsa min shima a ƙasan maƙoshin. Kaina na ɗago ina kallonsa. Idanunsa dake lumshe na shafa kaɗan. Sai ya shiga buɗesu a hankalin. Har cikin raina sai da naji tsoron ganin yanda suka canja, sai nai ƙoƙarin rissinar da nawan ina sauke ajiyar zuciya. Haɓata ya kamo ya maido da fuskar tawa, dole na sake kallonsa cikin idon. Alama yay min cikin yanayin ɗan ɗage kai da gira. Sai kawai na sake marairaice masa fuska zan saki kukan. Kansa ya girgiza min yana lumshe ido alamar kar nayi. Baki na taɓe hawayen na sakkowa da gudu. Sake rungumesa nayi na sakar masa shi.
Motsawar ƙirjinsa naji kaɗan, sai kuma hannunsa daya tura a cikin gashina. A cikin kunnena ya furta, “Ni dai kar a haifa min yarinya mai saurin kuka”. A yanda yay maganar ne ya sani fara kai masa ƴan ƙananun duka, sai yay ƙoƙarin riƙe hannun nawa yana murmushi. Daga haka ya tashi zaune da ni a jikin nasa. Bathroom ya kaini, da taimakonsa mukai wanka muka fito. Mu duka mukai shafa'i da wutri. Ganin ya ɗauki Alkur'ani ya hau karatu nima sai kawai nayi amfani dana wayarsa. Sosai yin karatun Alqur'anin ya kawo mana sauƙi a zukatanmu. Harna ɗan samu ya sha tea da abincin Mama balki lauma kusan biyar. Nima na ɗan ci, da ga haka ya ɗan zauna dube-dubensa a laptop wanda nasan kawai yana yine badan hankalinsa na a wajen ba. Ni dai dake kwance a jikinsa tun ina kallonsa har barci ya ɗaukeni ban san sanda ya gama ta kwanta ba...
Washe gari na tashi da zazzaɓina kamar yanda na saba. Nai ƴan amaye-amayena ya dai taimaka min nayi wanka na kwanta sai barci. Lokacin da nake farkawa rana ta ɗaga. Haka na kimtsa na fito neman abinci dan yunwa nake ji. Shi ko da'alama ma ya jima da barin gidan. Ina sakkowa su Ummie na shigowa da Mama Balki da Fahad sai Hafizzullah. Ashe daga asibiti suke duba jikin Paah da su Baba prof. Jikin Arwa dai kam babu daɗi, dan yarinyar nata aman jini. Wai da safen nan Commondo yake ta roƙon a kaisa ya dubata ta ganshi ya ganta koda sau ɗaya ne matsayin mahaifinta. Abin ƙaddara anama shirin sallamarta dan tun dare ta dawo hayyacinta ita sai kuka data kwana yi kawai. Tana yin ido huɗu da Commondo ɗin babu wanda ya lura ta finciki almakashin hannun nurse ɗin dake canja mata bandage ɗin goshinta sakamakon faɗuwar da tayi a jiya taji ciwo a wajen kawai ta cakamasa a gefen wuya. Ƙoƙarin riƙeta akeyi amma ina sake zarewa take tana caka masa tana kuka da yimusu ALLAH ya isa shi da uwarta. Da kƴar aka iya riƙeta aka ƙwace almakashin, shine kawai ta hau tari sai aman jini, yayinda aka kwashi Commondo zuwa taimakon gaggawa rai a hannun ALLAH. Shine fa akai kiran Maash ya tafi asibitin shi da su Ummie hankali tashe. Yanzu dai haka Commondo sakamakon abinda Arwan ta caka masa wata jijiyarsa ta tsinke. Ita kuma da ƙyar aka shawo kan aman jinin da take yi suka sakata barci. Baba prof kuwa tun a daren jiya allurar da Hajiya ƙarama ta masa ta fara nuna kanta. A yanzu haka daga ƙafarsa zuwa ƙugu duk sun sandare sun daina aiki. Dama Allurar bata mutuwa bace. Zata sabdarar da mutum ne ya zama babu inda ke motsi a tare da shi sai kansa kawai. Da yake gaɓa-gaɓa take bi yanzu haka ta sandarar da ƙafafun zuwa ƙugunsa. Itama Hajiya ƙarama data farka a barcin da suka sakata tana jin abinda Arwa taiwa mahaifinta ta sake rikitowa a gado batun da ake paralysis dai ta tabbata gareta bayan abinda Baba prof ya shayar da ita da bai fara nuna kansa ba dai ita. Al'amarin dai babu daɗin ji sam.
Ƴan suna kam dama yau duk suka kama ganansu da safe. Ƴan Kano ne kawai dake shirin wucewa gobe idan ALLAH ya kaimu suma. Naso nace zan bisu, na dai daure saboda halin da gidan ke'a ciki. Ummie ta musu alƙawarin in sha ALLAHU da zarar Falaq tayi arba'in ita da kanta zata ɗaukemu da su Maash duka muje garesu dangi suga Falaq su kuma ga mazajenmu suma mazajen namu suga dangin namu. Gwaggo Gudidi taji daɗin hakan, tace maybe ma sannan Halime amaryar Abba ta haihu dan cikinta ya fara tsufa. Jin hakan Ummie tace to shikenan hakan ma yayi kawai. Suma dai washe gari suka wuce gida ya koma da ga mu sai mu.
Hajiya Mammah dai wasan ɓuya take da kowa. Garama Hajiya Mama ta shigo sun gaisa da ƴan Kano har sau biyu. Yau kuma dana tashi jikina babu daɗi sosai dan har ruwa sai da aka sanya min shima ta shigo ta dubani. Sai dai daka ganta kasan bata cikin walwalarta. Duk ta zube a kwana uku kacal idanunta a kukkubure alamar taci kuka sosai. Bama su kaɗai ba mu kammu kowa ya kallemu yasan dauriya ce kawai, shiyyasa ko tattauna zancen abinda ya ke faruwar kowa ya kasa zama yayi da ɗan uwansa. Ga ƴan jarida na damunmu sai dai kowa yaƙi cewa komai a gidan dan uban gayyar bai kula ba. Ya Awwab ɗin ma kwata-kwata ya daina yini a gidan. Sai a yau ɗin da bani da lafiya daya kasance dani na fahimci shima bashi da lafiyar. Dan zuwa yamma duk dauriyarsa sai da ya kai kwance dai. Dole hayatu yazo masa da likitansa. ALLAH sarki Ummie duk ta damu. Shawara da likitansa ya bada akan ya kamata ya samu hutu gaskiya, idan dama hali yay nesa da ƙasar kona ɗan wata ɗaya ne dan jininsa ya hau sama sosai, har yanama zuciyarsa barazana. Hankalinmu ya tashi matuƙa. Duk da yace shi babu inda zai je bamu bi takansa ba Hayatu ya fara shirye-shirye bayan sun tattauna da Uncle Abdullahi. Ɗari bisa ɗari Uncle Abdullahi ya bada shawarar gaba ɗayanmu ya kamata mu wuce ɗin, batun Paah kuma a barshi a hannunsa dan yanzu kunya da tashin hankalin abinda Baba prof ya aikata ma Ummie da iyayenmu da wanda shima ya aikata yasa hatta da shi kansa ƙarfin hali kawai yake na fuskantar gidan. Amma idan akai ɗan nesa da juna zukata suka huta koba komai a tattauna wasu abubuwan. Da wannan shawarar Hayat da Ummie suka amince, cikin ƙanƙanin lokaci akai duk abinda ya dace musamman ga ni da Hafizzullah da Bahijja da Ummie ta amshe da bamu taɓa ƙetare ƙasar ba. Mama da Falaq da su sauran hakan ba komai bane. Haka kuwa akayi sati biyu ciff da faruwar komai muka ɗage zuwa ƙasar Spain kamar yanda Ummie ta buƙata, dan tana son kaima kufan mahaifinta ziyara, inda itama idan za'ace inane tushenta dole tace can ƙasar dan ba'a ado da ƙasar mahaifiya. Naso ace munje asibiti kafin mu wuce. Amma Uncle Abdullahi ya hana hakan. Hajiya Mammah ma bata yarda mun ganta ba. Ita ko Hajiya Mama dama ta koma a satin daya gabata.........✍️
_Ku ƙara hakuri dani dai kunji bayin ALLAH, ni kaina bana gane kaina saboda rikicin gidan Yayanmu maash😂😂😂🤪._
Barka da juma'a. Ina fatan kowa na lafiya. Fataken dare ga shi nan na baki ƙyauta🏃🏃
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_
........A randa suka wuce a ranar mahaifin su Azizat tsohon mijin Hajiya Mammah ya iso Nigeria shima. Ya zo da buƙatar amsar yaransa. Hankalin Hajiya Mammah yay matuƙar tashi, taita roƙonsa amma sai buɗar