Showing 1 words to 3000 words out of 429394 words

Chapter 1 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

924

??ࡱ?>?? R?(????????????? ?
?
? ?
?
?????????????????? ? !?!"?"#?#$?$%?%&?&'?'(?(????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????~()&

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F?(WordDocument????1(P0Table?????????,Data
???????????????????? P???FKSKS?1(P?i#?????????/'/'/'/'?&'?l+?/'??,?,?,?,?,?, ?,?,?,$)??+*?/'/'?,?,/'/'/'/'?,?+?'?+?,'?,?+'?,?,/'' ?^`????^Normal d??,CJmH sH nHtH_HOJPJQJ^JaJhA`????hDefault Paragraph Font$mH sH nHtH_HOJPJQJ^J?i`????? Normal Table0:V 4?4?l4?4?la?6 $mH sH nHtH_HOJPJQJ^J(k`????(No List ?i#?
?#?M0p??????R?P?"?,L3?C[p*DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK*

*(UMMU-MAHEER)*

*MARUBUCIYAR*

*WATA KISHIYAR>?p?=?y? (ALKHAIRI CE KO SHARRI)*

*RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW*

*HALIN KISHI*

*HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500*

*GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*

*SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*

*BAN YARDA A JUYA MUN LABARI TA KOWACCE SIGA BA TAREDA YARDATA BA*

*WANNAN LITTAFI ZARIA TV KADAI KEDA LASISIN WALLAFASHI A YOUTUBE, DUK WANDA YA AIKATA HAKAN BA TAREDA SANINA BA TABBAS HUKUMA CE ZATA RABA MU*

*IDAN HAR KIN SAN ZAKI SIYA NE SABODA KI YADA KI TURA A GROUPS NA HADA KI DA ALLAH KARKI SIYA, BAZAN YIWA KOWA ALLAH YA ISA BA DAN SOYAYYA CE HAR TAKE SAKA WA A FITAR DA LITTAFINKA A KARANTA AMMA MU SANI DUK WANDA YA DARAJA KASUWANCIN WANI SHIMA ALLAH BAZE BARI A KASSARA NASA BA*

*RUBUTUN LITTAFI SHINE KASUWANCIN MU DAN HAKA DAN ALLAH MASOYA KU TAYA MU GINA SHI BA RUSAWA TA HANYAR FITAR MANA DA LITTATTAFAI BA*

*GA MASU SO A TALLATA MUSU HAJAR SU QOFA A BUDE TAKE*

*KUNA IYA TUNTUBATA TA KAN LAYIN*
*07061838488*

*A QARSHE INA MIQA TARIN GODIYA GA MASOYA NA INA KUMA YI MANA FATAN ALKHAIRI GABA DAYA, ALLAH YA BAMU IKON AMFANA DA SAQON DA YAKE CIKIN LABARIN NAN YA KUMA YAFE MANA KURAKUREN DA ZAMUYI A CIKI* >?2??2??2?
*SHIMFIDA*
Ita Uwa tana da wani matsayi na daban da Allah SWT da kansa ya bata, kaifin harshen uwa ya zarce duk yanda muke tsammani. Cikin sani ko akasin haka furucin uwa nada tasiri akan Da wanda ba kowane ya gane hakan ba.

Idan rai ya baci musan abinda baki yake furtawa akan yaran mu, domin yanke hukunci cikin fushi yana haddasa Nadama da dana sani mara amfani a rayuwa.


Free Page 1


"Mama qarfe uku zamu tafi gidan Kamun fa, kinga unguwar su da nisa kuma Abba yace mu dena yin dare a waje" Umaimah dake tsaye daga bakin qofar daki ta fada tana kallon Babbar Macen dake tsinke danyan zogale tana jefawa a cikin babar robar dake gaban ta.
Banza tayi mata taci gaba da aikinta, se kuwa ta takwarkwashe fuska kana ganinta kasan tana fama da tsiwa da shagwaba tace

"Mama kina jina fa kikayi shiru, se kuma an jima na gama shiryawa kice ban gaya miki ba"
"Idan baki matsamun daga nan ba UMAIMAH sena bata miki rai a gidan nan, na gaya miki babu inda zaki je wallahi idan bakiyi wankin nan ba, ke ko kunya bakyaji a shiga dakinku wai sunan dakin Yanmata kin hargitsa muku ko ina da shirgin dattinki qazamar banza qazamar wofi" Maman ta dago a fusace tana fada tana kallonta.

Wata Fara doguwar mace ta fito daga Kitchen tana cewa
"Maman yara kenan, ki barta mana bana ji dazu tana cewa Nazifi gobe yazo ya mata wanki ba naga fa kayan da yawa idan kika ce seta wanke ai seta makara zuwa gidan bikin ko"

"Ai Antyn su Ko shekara zatayi wallahi seta wanke su kuwa na gaji da iskancin ta, shekara goma sha tara ai ba wata sha tara bace da kullum ita tana girma tana cin qasa, in ba haka ba ko dakin su Saddiqa ka shiga ai baka tarar da bolar da UMAIMAH take tarawa, ni wallahi ma baiken Nuratu nake gani da har ta iya hada daki da qazamar banza bayan ita komai nata tsaf tsaf yake" Maman ta sake fada tana Harara Umaimah dake ta faman tura baki.

"Haba, ai bazaki hada ba, da zama da mutum yana saka ka koyi halinsa ai da Umaimah batayi qazanta ba dan duk gidan nan babu wanda yakai Nuratu tsafta, su Umaimah kuwa ba'a magana" Antyn ta Fada tana zama a kusada Mama dan tayata qarasa gyaran zogalen.

"Munafuka kawai, kece qazama bani ba dai" Umaimah ta fada qasa qasa tana juyawa cikin dakinsu, Mama dake kallon Bakinta tsaf ta fahimci abinda ta fada dan daman tasan za'a rina, Umaimah se gyara da shiriyar Allah kawai. Daga cikin dakin ta ringa watso kayan wankin tsakar gida babu wanda ya tanka mata daga maman har Anty har ta gama iskancinta ta fito ta tattara su zuwa gaban fanfo ta tara ruwa a bokitai ta hau wanki.

Cikin qanqanin lokaci kuwa se gashi ta gama yanda kasan wacce ake tayawa, ta zagaya bayan gidan inda igiya take ta shanya kayanta tas ta dawo ta dauraye gurin da tayi wankin lokacin har Anty ta sauke dambun da suka girka a matsayin abincin rana. Tana dacin rai dan tunda ta fara wankin tafi ku mutu bata ce musu ba har ta gama ta shige dakinsu, can ma bata zauna ba, gadonta dake nan a hargitse ta gyara bayan data saka sabon zanin gado dan ta wanke na kai yanzu nan da nan ta share dakin ta hado ruwa ta goge ko ina kafin ta fada wanka ganin har qarfe biyu ta gota dan tun kusan goma take aikin.

Tana bandakin ta jiyo sallamar Anty Laure, qanwar Mamansu ce da suke uwa daya uba daya ta tabe baki dan tasan yanzu zasu qara haduwa su sakata a gaba da magana dan ma Allah yaso bata tarar da ita tana wankin ba amma tasan se munafukar Antyn can ta gaya mata ma, haka tayo wankan ta tareda alwala ta fito tana ta sauri, dukda qarfe biyar aka saka a katin kamun amma so take ta tafi da wuri dan seta biya ta inda Amarya taje kwalliya dan itace babbar qawarta. Daren da sukayi jiya a gurin Bridal shower ya saka Abba hanata tafiya tun sassafe dan da gaba daya ma hanata yayi seda Anty ta saka baki kafin ya kafa mata sharadin kar ta wuce qarfe shida yau amma dukda haka bata mata gwani ta ba.

Tana cikin yin sallah qawarta Rumasa'u Murtala tayi sallama, kamar ta sallame ta dakatar da ita karta shiga falon inda take jiyo muryoyin su Maman dan tabbas seta rusa mata shirin da tayi amma ba hali haka ta shiga karatun sallar sauri sauri tana jiyo ta suna gaisawa tana kuwa sallame wa ta fice falon da sauri har Hijab na neman tadeta ta kwalawa Ruman kira.

"Ke kuma fa kamar wadda aka biyo?" Anty Laure ta fada tana kallonta, seta saki murmushin da yake qara mata kyau tace
"Babu komai Momy ina wuni? Yasu Bintu? Ruma shigo mana kin ganni na kusa qarasawa ma" ta fada tana kama hannun Rumasa'un.

"Uhm kyaji dashi, ai wallahi da ace Ruma bata zo gidan nan ba da yau babu inda zakije daman se kuma Allah ya ceceki" Mama ta fada tana binta da harara.

"Ke kuma dana ce miki idan na fito zan kiraki me yasa kika zo?" Umaimah ta fada tana kallon Ruma bayan data zauna akan gado.
"Toh naji ki shiru, na kira Nadiya Isah wai tana gidan kwalliya ma ita shiyasa kawai nayo gaba, ni kuma Kinsan bana son kaiwa dare wallahi shi yasa nake so muje da wuri ko ba'a fara ba indai mun gaisa da Amarya Shikenan dawowata zanyi"

"Lallai ma to me kikayi kenan bari ma kiji se bayan magriba za'a fara biki qarfe biyar din da kika ga an saka dinma kawai rubutawa akayi dan ko ita Haliman yanzu ta tafi kwalliya" Umaimah ta fada tana qoqarin zura doguwar rigar fitted gown din da akayi mata a ankon bikin, se kuma me ta tuna ta cire ta ta janyo wata baqar doguwar rigar Abaya ta saka ta zauna ta hau daurin dankwali dan daman ita bata kwalliya, powder kawai ta saka se kwalli da man lebe ta gyara gashin girarta me cika da baqi hakan kuwa ba qaramin fito da sanyayyan kyanta da kalar fatar me wani irin kyau da sheqi ya sake qawata ta.

Ita dai Ruma na daga bakin gado tana kallon ikon Allah, koda yake ta saba gani baze wuce tayi irin dinkin da Mama ta hanata bane shiyasa ba zata saka ba qarshe tayi qarya tace wani guri ya yage zata shiga gidan Maman Nana me dinki ta take mata daga can su wuce, haka kuwa akayi suna fitowa Falon aka hau tuhumarta meya faru bata saka kayan ba ta nuna musu gefen Hammata inda Ruma bata san sanda ta farke shi ba wai be dinku ba. Sukayi musu sallama suka fice har sun kai qofa ta jiyo muryar Anty Habi tana cewa

"Yata Allah dai ya nuna mana ranar naki auran tunda ita waccen Allazi bokon ta auri littafi bazamu jirata ba, kina kammalawa zamu sha biki abin mu" Anty Habi ta fada tana bin ta da kallo ganin yanda tayi kyau dukda ba wata kwalliya me yawa tayi a fuskar tata ba.

"Lallai kuwa, ita Allazi bokon ai tafi wannan alqibla tunda ita naga alamar har yau bata san Annabi ya faku ba, duk wani saurayin kirki da zatayi seta kore shi da mugun halinta. yanzu da rana irin ta yau kika zo gidan nan da kinga irin diban Albarkar da tayiwa Qasim akan kawai ya gaisa da wata yarinya sanda yaje dakkota daga makaranta. Yarinyar nan saboda ta isa ta zama yar kanta a qofar gidannan ta tsaya mutane na kallonta tana zuba masa tijara ai ni nayi mamaki ma da har yau basu aiko a basu kudib su ba, Umaimah kibi a sannu dai tunda kin kori samarin qarshe idan kinci sa'a ki qare da me mata biyu ko uku ai" Mama ta fada, se ta juya bakin qofa i da Umaimah ta coge tunda Maman ta fara magana tace

"Kika tsaya ko da magana ne", cikin muryar kuka kuka tace

"Saboda kawai an miki kishiya Mama se ki ringa yimun fata nima na auri me Mata, in sha Allahu mijina ni kadai ze aura daga ni babu qari har abada" taja fuuu tayi waje.

"Hmmm" kawai Mama tace dan lamarin Umaimah kam se Addu'a.

"Oh ni Anya Yaya Malika lamarin Umaimah babu iskokai a ciki kuwa? Kiga dai farin jini irin na yaran gidan nan, tun fa kafin su gama sakandire suke tsaida mazaje amma ace Umaimah har tana shirin gama HND babu wani tsayayye abu kullum watangaririya ake, se an shirya magan rigidi rigidi se wani tsautsayin ya gifta. ita ba mummunar sufa ba bare ace finta sauran sukayi, waccen miskilar ma ta samu tsayayye balle ita me wayayyen kai ace abu ya gagara? Nifa wannan fadan nata ma gani nake bana lafiya bane gaskiya ya kamata mu tashi tsaye" Anty Laure ta fada tana kallon yayar tata.

"Babu wasu iska sedai iskanci Laure kamar baki san wacece Umaimah ba. kuma da like batun tsayayye ai ba samarin me bata dasu ba, kullum zuwa suke amma mugun halinta da baqin kishi na ba gaira babu data dorawa kanta shi yake korar su. Ni damab na deba lissafa kawo mata kudin aure a wani abu, idan ba ji nayi an daurawa Umaimah aure ba shine kadai zan tabbatar da Miji ya tsaya dan a cikin sakanni tana iya tafka wautar da zata sa ace anfasa auranta.

Toh wane gantalalle ne tun be aureta ba zata fara dora masa ciwon kai ya tsaya?
nake gaya miki fa nan tayiwa Qasim cin mutunci ko kare baze ci ba wai kawai dan ya gaisa da abokiyar karatun ta shi kuma junior sace yarinyar tare sukayi secondary wallahi bakiji ba ina sallah a tsakar gidannan ina jiyota Allah Allah nake na idar na fita naci ubanta akayi sa'a yayansu yazo ya faffalla mata mari tayo ciki, ni nayi mamaki ma da har yau basu aiko sun karbi kudin auransu ba" Mama ta fada cikin matuqar takaici.

"Ashsha abu beyi kyau ba amma me yasa take haka ne, ya ilahi ke ace saurayinki baze kula wata mace ba toh inaga anyi aure kuma" Anty Laure ta fada cikin jimami tana juya hannu.

"Kema kya fada dai, shi yasa na dena raba takaici ta da kowa duk abinda tayi wanda ya gani ya gani shikenan fatana dai kullum shine ubangiji ya shiryeta dan dai wannan halin nata ba hali me kyau bane"

"Addu'ar dai kam ita ce amma dai Yaya karki qi ta tawa Allaha binciketa dai qila da sharrin iskar kin san fa daman baa ganewa se abu yayi tsamari baa fata sannan suke bayyana"

"Allah ya rufa asiri" kawai Mama tace mata ta janyo wata hirar dan ita duk wata sabga da zaace ta hada da malamai ba sonta take ba. Balle kuma Umaimah da sarai ta san babu abinda yake damunta, suma mantaqa sukayi amma ai tun tana qanqanuwarta haka take da bala'in kishi wani baze fita ba, idan kuwa abu ne idan bata dashi tofa sedai kowa ya rasa.

Tayi iya qoqarinta gurin canza mata wannan muguwar Dabi'a abin kuma yayi sauqi se a yanzu da shekarun hankali suka zo mata kuma abu ya ke sake ta'azzara, kuma a duk sanda Shedan ya buga mata gangar ta hau bata ji bata gani sedai fatan Allah ya shirya kawai.

UMAIMAH

Suna fita fuskar nan tata a cukule saboda maganar da Maman tayi suka shiga gidan Maman Nana, basu bata lokaci ba ta take mata rigar ta saka. Dinkine akayi mata na dibar Albarka ya fito mata da duk wata sura da take da ita domin kuwa Allah ya mata qira me kyau, tana da wani irin shape da ko mace ta kalleta seta qara kallo ta.

"Yanzu Umaimah da wannan Kayan zaki fita? Wai me yasa kike haka ne, baki san wannan abin da kike cin amanar iyayenki kike ba?
Ya za'ayi ki fito daga gidanku da shigar Mutunchi amma a waje a ganki da wata shiga ta daban? Wallahi ina jiye miki ranar da wani a gidan ku ze san abinda kikeyi nasan se kin gane kurenki wallahi kiyi ta biyewa su Nabila Sani su dai kin san a gida suka samu lasisin yin duk abinda sukeyi sedai su jira Kamun Allah" Rumah ta fada tana qarewa Umaimah dake daukar selfie Kallo. Kayan sun kamata matuqa ga kalar Atamfar data karbi fatarta dole ma ta fuzgi hankalinka ka kalleta.

"Sedai idan ke zakije ki fada, ni wuce muje ga me Napep din nan an samo" Umaimah ta fada ko a jikin ta tana zura wayarta a jaka daidai sanda Nana data aika ta taro musu dan sahu ta dawo, haka Rumah ta bita a baya cike da Takaicin halin qawar tata, badan gudun abinda kaje ka dawo ba wallahi seta fadawa Mama wannan muguwar dabi'ar data koya a gurin su Nabila.

Da sam ba haka take ba, da wuya kaga Umaimah ta saka kayan daya bayyana surar ta dan ba tarbiyyar gidan su bace amma shigar su Poly tunda ta hadu da sababbin qawaye irinsu Halima Mailafiya, Fannah Babagana, Nabila Sani se Fauziyya Kura, Izawaqa Mansur da ita Rumasa'u da daman tun Secondary suke tare . acikin su Ruma ce me sanyin Hali ba kuma tayin irin abinda sukeyi.

Nabila da Fauziyya sun fi kowa budadden ido a cikin su bayan Ruma sune mafiya kusanci da Umaimah kumasu suke qara dorata akan duk wani bigire mara kyau kasancewarta me saurin yarda da sakewa da mutane, gashi ita a rayuwarta tana jin maganar qawa kusan sama data kowa.

Tun tana dardar idan zaayi bikin qawar su aka fitar da Anko su suke kawo Style dinda zaayi na zamani na rashi mutunchi tace baza abarta ta saka a gida ba su suka kawo mata dabarar kin sakawar ta bari seta fito waje, dan a Auran Fannah ma dinki biyu aka mata. Wanda ta saka ta fito daga gida daban haka bayan sunje gurin bikin ta cire ta canza wani.

Rumasa'u na matuqar baqin ciki da wannan dabi'a tasu kuma duk ta yanda zata fahimtar da Umaimah cewar tsakanin ta dasu akwai Banbanci na tarbiyya da mutunchi taqi ta ji, sabo da shaquwar da take tsakaninsu tun yarinta ita tasaka ta kasa fita daga cikin group din nasu amma duk da haka kullum cikin yi musu Nasiha take bata damuwa da kyara da hantara da kiranta bagidajiya da sukeyi ita dai fatanta su dawo kan Hanya.

Haka suka kama hanya, suna cikin tafiya Kiran Fauziyya ya shigo wayar Ruma.
"Bawa Umaimah wayar" ta fada bayan data amsa, seta miqa mata tana tabe baki dan yana yin da tayi mata magana ya sa ta tuna da fadan da sukayi shekaran jiya a makaranta akan zasuje sabon gari a saka musu farce da kitson qari duk na shirin bikin, tayi musu nasihar data saba Shine Fauziyyan ta zageta har tana kiranta bagidajiya batayi sanya ba itama ta rama danta fara gajiya da yanda suke maida ita kamar wata bolar su dan kawai tana da haquri shine ashe ita bata wuce ba.

"Umaimah muna Beejay fa, yanzu zaa fara yiwa Lims kwalliya" Fauziyyan ta fada bayan da Umaimah ta karbi wayar,

"Kai haba dai har yanzu shida saura fa"

"Dalla se waccen yar yawar taji kawai ku wuto nan akwai motocin da zasu dauke mu an kusa gama mata ma fa" Fauziyya tayi saurin kwabarta sukayi sallama.

Me Adaidaitan ta gayawa inda ze juya dasu, Ruma ta kalleta tace

"Ban gane ba ina kuma zamuje?"
"Kin fiya matsala wallahi toh saqo zan karba na manta ne se yanzu" ta fada tana tsuke fuska.

Agogon wayar Rumah ta kalla kamar tayi magana kuma tayi shiru, haka suka qarasa tafiyar babu me cewa wani qala har me Adaidaita ya sauke su a bakin gurin kwalliyar.

"Me kuma zamuyi anan kedai nasan ba kwalliya kike ba bare nace" Rumah ta sake fada bayan sun sauka

"Wallahi Rumah kin fiya matsala, bana gaya miki saqo zan karba ba.." Se tayi shiru ganin Nabila ta nufo su fuskar nan tasha kwalliya kamar Aljana se karairaya take dinki ta irin na jikin Umaimah amma sam be mata kyau ba saboda jikin ba iri daya ba, siririya ce ta gaske ga tsaho tana dashi se ta zama kamar wata bulala.

"Mu shiga ciki an kusa gama mata" ta fada tana kama hannun Rumah dan itace zatayi qorafi, haka suka shiga Reception din, abin takaici Amarya Halima na zaune ashe layi ma bezo kanta ba. Wai wata akeyiwa da an gama se ita.

Hira suka shigayi da daukar Hotuna, Umaimah na daga gefe kadan kadan take saka baki tana danna wayarta da tun suna hanya take ta qoqarin kiran Qasim amma ta kasa samun sa.
Tsaki taja ta kalli Rumah tace "Bani aron wayarki nayi kira

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login