Showing 84001 words to 87000 words out of 429394 words

Chapter 29 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1018

jagwalgwalon yara ba sedai su dafa abinsu suci, Habiba kuje Jellop din shinkafa za'ayi se a soya Kazar da akwai ruwan zobo a cikin Fridge se ku hada" ta qarasa tana zama akan Threesitter irin zaman gadarar nan na me abu da abunsa idonta na kan Lubna aika mata da wani mugun kallo daya sakata shan jinin jikinta kuma Umaiman tayi mata kwarjini seta miqe tana zumbura baki tabi bayan Habiba data fice daga palour.

"Kiyi haquri sam Lubna bata da kunya wallahi" Shafa'atu ta fada tana zama itama se Umaimah ta tareta da cewa

"Haba wani haquri kuma quruciyace take damunta muma duk muyi a lokacinmu ai wata rana ai bazatayi ba, naga alamar kishi takeyi dani nayi mata kwacen saurayi ko" ta qarasa tana yar dariyar da duk me fahimta ze gane bata dadi bace, yaqe ne kawai

Gyara zama Shafa'atu tayi tana dariya itama tace
"Tab jifa wata magana kema Anty Umaimah yanzu idan aka ce miki Yaya Khalil ze kula wannan yarinyar seki yarda ai ni inaga magana ma me tsaho bata taba shiga tsakaninsu ba saboda rawar kanta shi kuma kinsan baya shiri da marasa ji, itace dai take haukanta wai sonsa takeyi amma ai bata taba gigin fada a gabansa ba se mu data raina ta ringa wa hauka da Drama lokacin bikinku, ai abun ma ba gaske bane ba kuma me yuwuwa bane shirmenta ne kawai takeyi"

"Uhm Allah sarki" Umaimah ta fada tana shafa yatsunta da har sannan suna mata zafi, hira suka shigayi kadan kadan dan rabin hankalinta naga tausar zuciyarta karta botsare ta sakata yin abin kunya dan dagaske ji tajeyi kamar take kitchen din ta watsawa yar banza man da ta jiyo suna soya kaza idan yaso taga da bakinda zata sake yi mata rashin kunya har tace da Mijinta ne ze aureta.

Acan kitchen kuwa Habiba data gama kwashe Kaza daga Mai ta kashe Gas din ta bude Tukunyar shinkafar ta juya ta qara tabbatar da komai yayi kafun ta rufe ta juya kalli Lubna da tunda suka shiga kitchen din ta samu kujera ta zauna tana danna waya bata tayata da ko tsinke ba, cikin bacin rai tace
"Wai Yaya Lubna me yasa kike haka yanzu saboda Allah kizo har gidan mata ki mata rashin kunya dan kinga tana da haquri wallahi idan wata ce nasan seta kwakwkwada miki mari sedai duk abinda za'ayi ayi kuma yanzun ma idan muka koma sena gayawa Hajiya wallahi"

"Karki kuskura kiyi mun rashin kunya idan bata mare ni ba ni sena mareki a nan banza da tafi son bare akan yar uwarta ta jini. Ni wallahi ma sena raina ta na raina ajin yaya Khalil, ace akan wannan dusar ne duk ya tsallake yammata irin mu ai kuwa ya fado qasa"

"Tab wayaga daskindaridi, wai ke nan kina wa kanki kallon wata hadaddiya ne ko kyakykyawa?" Habiba ta fada tana qunshe dariya kafin taci gaba da cewa

"Ai wallahi idan da Anty Umaimah a guri ko a me goge goge bazakiyi daraja ba, fari ne fa kike taqama dashi shima Allah ne ya taimake ki na rantse da a baqa kika zo se an hada da roqon Allah zaki samu shiga koda yake da farin da komai ma gashi nan har yanzu se a slow, ni wallahi banma ci dariya ba Yaya Lubna se jiya da kika cire wadannan sosunan da kike sakawa Ruler sunan wata aba nace na godewa Allah da Hajiya kullum take jajanta sirantata ashe akwai wanda nafi qiba" Habiba da takai baqin qofa ta qarasa fada

Kukan kura Lubna tayi ta kai mata cafka ta goce suka fita tsakar gidan kafin kace me sun kaure da dambe fuskarta tayi jaa saboda bacin ran wannan cin mutunchi da Habiba tayi mata.

"Kaikai meye haka, baku da hankali ne?" Shafa'atu ta fada tana qoqarin raba su dan daga ciki suka jiyo hargagin Lubnan tana zagin Habiba, qin rabuwa sukayi suka ci gaba da casuwa dan dukda Lubna ta bawa Habiba kusan shekara uku a qirar jiki kusan daya suke koma Habiban ta fita kwari dan haka qarfi yazo daya kowa ta kasa kada yar uwarta.

Umaimah na tsaye akan barander ta harde hannu tana kallonsu kawai, Addu'a take Allah yasa Habiba ta damfarata da qasa dan da alama tana dab da samun nasara akanta dan ta fi Lubna dabarun damben tana kallon shafa'atu nata qoqarin rabasu suka maujeta taja gefe tana sosa inda aka daketa tana zaginsu, Allah ne ya bawa Lubna Sa'a ta tade Habiba ta fadi a qasa ta haye ruwan cikinta tana sakar mata blows a fuska bata ankara ba se ji taji an kwasheta da marin daya gigita mata kwakwalwa kafin taji an watsar da ita gefe ta qume qum da Abin flower.

Daga Habiba Umaimah data zazzabgawa Lubna mari da biyu tayi tana kallon Lubnan tace
"Saboda kin zama babbar banza zaki haye kanta kina duka se kin mata lahani?"

"Wallahi bazan yarda ba tunda kika mareni" Lubna ta fada cikin kuka tana miqewa Shafa'atu ta tareta tana kai mata wani marin ta goce tana cewa
"Wallahi bazan yarda ba haka kawai me nayi mata da zata mareni sena rama duk abinda za'ayi ayi" ta nufo Umaimah data tsaya tana jiran isowarta, dama ta samu seta nadawa yarinyar nan dukan mutuwa yau da dalili Lubna na zuwa kuwa ta cakumi wuyan Umaimah duk yanda Shafa'atu take janta tana zaginta akan ta bari ina se zare ido take tana kallon Umaimah da itama take kallonta.

"Sake ni" Umaiman ta fada cikin sigar umarni se kuwa Lubna tayi caraf tace
"Bazan sake ki ba se mun kece raini yau ko ni koke a gidan nan, kin kwacemun saurayi sannan ki Mareni duk kici banza wallahi bazan yarda ba" Lubna ta fada yana kiciniyar ture Umaiman dako gezau batayi ba, kalmar saurayinta data kira Khalil da ita ta sake zabura ta cikin shammata ta kwashi Lubnan ta watsar.

Dukan ya da Uwa tayi mata daga Shafa'atu har Habiba babu wanda yakai mata ceto dan ita Habiba kan girkinta da har ya fara kamawa ta koma ta shiga hada Salad ranta fes yau an samu maganin rashin mutunchin Lubna daman ta addabi kowa.

Ihu da kururuwa ta ringayi tun tana zagin Umaimah harta dawo bata haquru da roqon ta kyaleta bazata kuma ba dan ba dukan wasa Umaimah take mata ba, duka ne irin na wanda yake amayar da fushi seda tayi mata lilis suna jin maqota da suka jiyo ihun Lubnan suna buga qofa da roqon azo a bud dan su a zaton su ma matar gidan ce wani abun yake samunta amma basu bude ba, seda ta gaji dan kanta sannan ta qyaleta ta wuce ciki abinta ranta fes tunda yau ta samu damar lallasa daya daga cikin masu kula mata miji.

"Allah nagode maka daman ai idan junin mutum rashin mutunchi da tijara wata rana ze hadu da daidai shi yayi maganinsa kingani yau duk tijarar taki da rashin kunyar da kike taqama dasu kin samu me saita miki zama kai amma Anty Umaimah nagode miki daga yanzu ma duk idan ta Sam yi mana iskanci wallahi nan zamu kawota ki saita mata zama" Shafa'atu ta fada tana kallon qanwar tata dake juye juyen ciwon jikin da Umaimah ta tara mata.

Shiru Umaimah tayi tana sauraren maganar Shafa'atun, se taji tamkar tilawar abinda kullum yan gidansu suke fada akanta na Allah ya hadata da daidai ita ne amma ita kam bata hasaso wannan ranar da za'ace ta gamu da wadda ta fita jidali, idan har aka ganta a qasa to ita taso yin badda bani amma badan an kada ita ba.

Daga wannan duka dai Lubna ta sulale ta bar gidan ba tareda ta yiwa kowa sallama ba. Alwashi kam tasha shi kala kala se dai muce Allah bada sa'a.

Shafa'atu da Habiba kuwa a gidan suka wuni har qurin qarfe hudu da kusan rabi sannan Khalil ya dawo. Shafa'atu da Habiba suka gaishe shi ya amsa babu yabo babu fallasa yana kallon Umaimah dake masa murmushi, dakinsa ya wuce tabi bayansa harya fara balle boturan rigarsa ta shiga taya shi tana cewa

"Yau ka dawo da wuri ko duk missing dina ne ya saka"
"Uhm, Uhm ina wayarki?"
"Tana palour, meya faru?" Umaimah ta tambayeshi tana karantar yanayinsa, be amsa taba seda ya daura towel a qugubsa ya sake kallon ta yana cewa
"Ya nagansu su biyu ina Lubna ko ba tare suka zo ba?"

Yatsina fuska tayi a zuciyarta tace
"Sedai uwar Lubna ba Lubna ba a fili kuma tace masa
"Ta tafi gida wai"
"Kamar ya ta tafi meyasa ba ta jira sun tafi da sauran ba?" Ya sake jefa mata wata tambayar, seta hade rai tana kallonsa tace

"Se ka kirata ka tambayeta ai kaji dalili, wato shiyasa ka dawo gida da wuri kafin lokacin dawowarka saboda kana sauri kazo kaga budurwarka ko toh na koreta".

"Ta tabbat kenan" ya raya a ransa amma be tanka mata ba ya janye gefe ya wuce bandaki ya barta tana qananun maganganu. Seda yayi wanka ya fito, ransa gaba daya a dagule, besan ya Hajiya zataji ba idan taji da gaske ne Umaimah taci mutunchin Lubnan ta kuma korota daga gidan dan abinda Lubna taje gida tana kuka kamar ranta ze fita ta gayawa Hajiyar kenan wai suna zuwa bata san waya gayawa Umaimah akwai alaqar soyayya a tsakaninsu da Khalil ba ta rufeta da masifa da zagi har tana ce mata Karuwa kwartuwa ta biyo mata miji gida ita kuma Shafa'atu tana qara zuga Umaiman tana gaya mata maganganun qarya dagaskiya daga ta rama suka hadu suka rufeta da duka dakyar ta kwato ta gudo daga gidan.

Hajiyar tayi kiran layin Umaimah a lokacin dan taji gaskiyar meya faru dukda hankalinta ya tashi sosai da ganin Lubnan tayi budu budu ga fuskarta tayi jajir gefen bakinta ya fashe leben ya kumbura dukda bata yarda da cewar Umaiman ta aikata abinda ta fada ba amma idan ma tayin dole da dalili kuma shi take so taji.

Tayi kiran layinta kusan sau uku bata daga ba ta mayar da akalar kiran kan Shafa'atu itan ma samma kal.
"Ai Hajiya bazasu daga ba, dan fa bakiji irin mugun abun da Shafa taje tana fada mata bane a kanmu ta na kwance mu gara kawai ki kira Yaya Khalil din shi yaje ya same su a gidan" Lubna ta fada tana matsar kwalla, Hajiya ta kalleta kawai ta dauke kanta gefe tace

"Ai mu bamu da wani mugun abu ko abin kwance kai da Shafa'atu zata gayawa Umaimah, kuma idan Shafa ta muzantamu ai kanta ta muzanta ko tunda ubanda ya haife ki shiya haifeta karki manta, ba dangin uwa kadai kika hada dani ba, dani da Najib Uwa daya Uba daya suka kawo mu duniya dan haka keda Shafa abu daya ne a gurina" tana gama fadar haka ta mayar da kiran zuwa layin Khalil.

A taqaice tayi masa bayanin zuwa da dawowar da Lubna tayi gidan da abinda ta fada mata ta qarasa maganar da cewa
"Na kira wayarta bata amsa ba idan ka koma kayi bincike ka gane gaskiyar abinda ya faru dan bana son abinda ze kawo wata baraka tsakanin matarka da yan uwana saboda yanzu idan wannan yarinyar ta tafi tana yada abinda ta gaya mun ko gaskiya ne ko qaryane Allah kadai yasan abinda hakan ze haifar a cikin dangi dan haka kaji ta bakin Umaiman idan Habiba da Shafan sun dawo nima zan tambaye su yanda akayi" da haka sukayi sallama abinda ya saka shi ya tattaro ya dawo gidan kenan kafin lokacin tashin sa.

Sanda ya fito daga wanka bata dakin, yana shafa mai ta shigo da Try ta dora kayan abinci akai ta ajiye akan Table din dake gaban gadon fuskarta a hade kamar wadda ya zaga shi se ta bashi ma dariya yace

"Toh kuma me akayi miki kike faman bata rai bayan kin korar mun budurwa ina ta sauri nazo muyi hira"
Dagowa tayi daga zuba masa abincin da takeyi ta aika masa da wata mugur harara seta dire farantin ta miqe tana cewa

"Wallahi duk yar iskar yarinyar data sake tako qafarta gidan nan da sunan budurwarka tayi mun iskanci se dai ta koma gida a gurgunce, saboda tsabar raini da ba'a ganin mutunchina duk abinda zakayi kayi a waje mana amma shine za'a biyoni har cikin gidana yarinya ta zauna akan kujerun da ubana yayi mun tana zagina tana gaya mun da yanzu itace a gidannan bani ba, toh wallahi ka gaya mata dukan dana mata yau kadan ne nan gaba idan muka hadu ko kallon banza tamun sena saba mata kamanni Mtsw" taja tsaki tana wullar da serving spoon din da yake hannunta.

Kallon ta kawai Khalil ya tsayayi har ta gama, ya fuskanci Tijara a jininta take idan kuma tanayi manta dawa take ko a gaban waye takeyi idan ya tsaya kulata zata zubar masa da mutunchine a gaban masu ganin girmansa tunda dai yaji abinda yake so cewar ta daki Lubnan toh bin ba'asi ma be taso ba dan yasan dalilin dai Kishi ne sila Allah ya rufa asiri shi kuma ze san ta yanda ze fahimtar da Hajiya abinda ya faru kafin ta bata rawarta da tsalle a idonta.
Abincin yaja ya faraci bayan ta fice daga palour, a lomar farko ya gane ba girkinta bane girkin Habiba ne dan Allah yayi wa bakinsa baiwar shaida dandano indai ya saba jinsa.

Umaimah kuwa palour ta fita tana mita Shafa'atu da Habiba suka bita da kallo ta shige dakinta se suka miqe suka fara shirin tafiya, Habiba ce ta buga mata qofa ta fito ganinsu da jaka a hannu tace

"Aa ina kuma zakuje naga kun dauki jaka?"
"Tafiya zamuyi kinga yamma tayi ga Yaya ya dawo mun hanashi sakewa gara mu tafi mu baku guri" Shafa ta fada se Umaiman ta bata fuska tace

"Haba ku bari seda Magriba mana se mu mayar daku gidan tunda dai ba wani guri zakuje ba"

"Aa Anty gara muje dan nasan yanzu Yaya Lubna nacan Allah kadai yasan qaryar data hada ta gayawa Hajiya gara tun bata qulla sharri ba mu koma gida" Habiba ta sake fada, se Umaimah ta yamutsa baki tace
"Allah ya kyauta, ku jirani toh ina zuwa" ta juya dakinta.

Cikin kayanta da suka matseta ta zabarwa Habiban kala uku masu kyau laces ciki babu wanda ya shiga ruwa sau biyu wani ba ba'a taba wanke shi ba qibar da tayi ce ta saka duk kayan suka matseta seta waresu zata bayar. Kayan kwalliya ta qara mata dasu da turaruka ta sake ware wata ledar daban cikin kayan baccin ta ta dauki guda biyu masu Azabar kyau na daukar magana ta sakawa Shafa'atun ta qara mata da wata humrar sirri da Halima Qawarta ta kawo mata taji dadinta dan haka ta dibarwa Shafan sannan ta debar mata kayayyakin gyaran da Anty bata gajiya da aika musu dasu.

Fitowa tayi ta bawa kowa ledarta suka karba suna godiya tace su jira tayiwa Khalil magana ta qarasa dakin yana zaune ya jingina da fuskar gado yana waya dan haka taja gefe ta tsaya tana harararsa, kashe wayar yayi ya kalleta ba tareda yayi magana ba tace
"Zasu tafi"
Wallet dinsa ya bude ya zaro dubu biyar ya miqa mata ta karba ta koma ta basu, seda ta raka su har qofar gida sukayi Sa'a Adaidaita ya sauke wata mata seda ta kalleta dakyau ta gane Rufaida maqociyarta ce da wata da take zaton qanwarta ce goye da baby tayi qiba tayi kyau su Habiba suka shiga ya wuce dasu ita kuma ta tsaya suna gaisawa.

"Ai baki da kirki dai Amarya" Rufaidan ta fada tana qarasowa qofar gidan Umaiman, ta saki murmushi tace
"Na yarda amma kiyi mun afuwa tunda kin dawo yanzu zan shigo ko yaushe in Allah ya yarda"

"Toh shikenan dukda dai ban dawo ba se jibi share share zamuyi yanzun" Rufaidan ta bata amsa daga haka sukayi sallama ta juya cikin gida.

Su Habiba sun rigada sun gyara mata gidan dan haka ta samu guri a palour ta zauna tana duba hannunta da yatsun suka tashi da alama dai se taje koda Chemist ne an duba dan har sannan tana jin zafi akan fatar ga kuma tashin da gurin yayi. Bude qofa Khalil yayi ya fito yana kallonta ta dauke kai, haushin sa takeji shi har yana da bakin tambayarta wata yar iska ma ko saboda kawai yaga tayi sanyi kwana biyu shine ze nemi ya taka ta to su zuba su gani.

Zama yayi a kujerar dake kallon wadda take kai yana kallonta yace
"Akan wane dalili zaki zagi Lubna kiyi mata gori kuma saboda ta rama ki rufeta da duka har kika ji mata ciwo"

"Kan babbar bala'i au abinda ta gaya masa kenan?" Umaimah ta ayyana a zuciyarta a fili kuwa gyara zama tayi irin na me shirin tarar duk abinda ze zo tace
"Saboda na isa shiyasa na daketa kuma ba Lubna ba ko uwar Lubna da ubanta ne suka zo cikin gidan nan suka gaya mun makamanciyar maganar data fada akanka tayi mun gadara sena ci ubansu ballantana ita qaramar Alhaki".
*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS*

*Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so*

*Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa*
*Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah*

*A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu*
*Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki*
*A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu*
*Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah*
*Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan*
*07031876677*
Ko

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login