Showing 3001 words to 6000 words out of 429394 words

Chapter 2 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

923

please" dan duk cikin clique din nasu ita kadai ta yarda da ita take kuma iya sakata a sabgar samarinta hakan kuma ba shi yake hana idan abin ya motsa mata itama tayi mata horon da ta saba yi ba.

Bugu biyu Qasim ya daga kiran da tayi masa da wayar Rumasa'u, sallama yayi tsabar mamakin abinda yasa ita wayar ta ake ta ce mata not reachable amma gashi kira daya nan ta same shi ya hanata magana. Seda ya maimaita sallama sau uku kafin ta bude baki cikin fushin da yake taso mata tace

"Blocking layina kayi kenan Qasim tunda gashi na same ka da wata wayar"
Qasim kuwa yana jin muryarta daga daya bangaren 'Qit' ya kashe kiran, ta zare wayar daga kunnenta tana dubawa, kashewa yayi da gaske kai lallai yau akwai babban tashin hankali ashe.

Kusan sati kenan tun waccen ranar ya dena kiranta, idan ta kira shi farko farko ze amsa amma yanayin da ya koma yi mata magana a dake ba kamar yanda suka saba bane daga baya ma seta kira ta qaraci ringing di ta baze daga ba toh abin ya qaru jiya zuwa yau ma kwatakwata bata shiga shine yanzu ze qara mata da wannan wulaqancin ai kuwa ze san da ita yake zance.

Wayar ta mayarwa da Rumah ta qara harde qafa akan Kujera tana kadasu, a ranta ayyana irin tijarar da zata masa duk randa ya huce ya kawo kansa take. Ita badan ma tana son yazo ya mayar da ita gida ba ai ba zata kirashi ba amma shi kenan.

Basu bar gurin kwalliya ba dai qarshe seda akayi sallar Magriba ko kafin su Isa Gurin Kamun ma takwas saura dan da tafiya daga gurin kwalliyar zuwa can. Ruma kamar zatayi kuka, ita ba kanta ma takeji ba dan a gida ta fada daman zasu iya kaiwa Zuwa Takwas haka kuma an barta amma Umaimah take jiwa dan yanda Mama ta ringa jaddada mata kar tayi Magriba awaje idan ba haka ba zata hadu da Abban su tasan akwai abinda ta aikata da ya saka ake horata.

Sun tarar da Anties din Amarya da daman tun suna gurin kwalliya ake doka mata waya, wata daga ciki ta tare su da wani mulmulallan Ashar tana cewa

"Banda tsabar iskanci Kamu ba dinner ba ki tafi ki share guri kiyi zamanki har takwas uban waye ze zauna yana jiranki? Kwalliyar da kika bata kudi kikayi ta tashi a banza dan rabin mutane sun kama gabansu su kansu dangin mijin naki gasu can har sun fito zasu tafi dakyar aka lallabasu suka zauna shegiya kuma baki kyau bama"

Amarya Halima ta tura baki dan daman tasan se Anty Mara tayi masifa dan tafi kowa fada a cikin Anties din nata, haka suka rankaya suka shiga Yammata na take mata baya. Amarya na zama a kujerarta Rumah ta zagaya aka musu hoto kafin ta rada mata a kunne ta tafi se gobe zata zo gidansu daurin aure da yini. Da sauri ta qarasa inda Su Umaimah suka zauna tana ce mata

"Kije kuyi sallama da Halima mu tafi Umaimah takwas fa keda aka ce kar kiyi magriba a waje".

"Kuje ina haba malama kema ba inda zakije nemi guri ki zauna yanzu fa zaa fara biki ki wani ce ku tafi baza ku tafin ba" Fannah ta fada tana qoqarin zaunar da ita seta turje tana cewa

"Barni Fannah tafiya zamuyi Umaimah muje dan Allah dare na dada yi".

"In zaki tafi ga hanya nan ban riqe ki ba amma ni kam se naga kwal uwar daka, daga zuwan mu kice mu tafi ba wannan maganar"? tana rufe baki kiran Mama ya shigo wayarta data ajiye akan Table

"Kin gani ko gashi nan Mama tana kiranki kar ki jawa kanki wani Fadan ki tashi kawai mu tafi" Rumah ta fada a rikice kamar ita ce tayi laifin

"Ai se kiyi, kona koma yanzu ko ban koma ba duk daya fada ne sena sha shi toh in zaki zauna ki zauna idan kuma tafiya ce a sauka lafiya"? ta bata amsa tana kashe wayarta gaba daya dan tasan Mama yanzu idanta dosa mata kira ba haqura zatayi ba, kuma dai laifi ne dai ta rigada tayi tunda kafin Magriba akace ta dawo gashi har isha ta wuce bata komaba.

??2?? 0?? 2?? 3??
*DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR*=?y?>?p?
*And now*
*HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE*

*KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*
*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*

*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA*
*07061838488*

*A BIYA A KARANTA*

Free page 2

Biki yayi biki, an raqashe anci an sha yammata sunyi rawa, Umaimah bata an kare da lokaci ba seda aka tashi ta kunna waya lokacin qarfe goma harda rabi tayi, daga gurin zuwa gidansu kuwa taci kusan Minti talatin a qiyasi dai sha daya ce zata kaita gida lallai kam yau ta taro Match me zafi dan tasan ma kafin taje tuni an kulle gida.

A motar Mijin Fannah suka tafi da yake hanyar su daya, ita bayin daren ne yafi daga mata hankali ba, Aa Abayar data saka da zata fito ta barota a gidan Maman Nana saboda bazata shiga jakarta ba kuma batayi zaton zasuyi dare har haka ba.

Cikin taraddadin abinda zata tarar suka sauketa a qofar gidan su, jiki a sabule ta sauka tana gyara yafen dan babban mayafin data samu sukayi musanye da Fannah ko ta dan qara rufe jikinta. A darare ta qarasa jikin qaramar qofar Get din da niyyar bugawa dan tasan dai an kulle se taji takun takalma a bayan ta.

A mugun zabure ta matsa, Abbane, da torchlight a hannunsa saboda an dauke wuta yayi mata kallo daya kafin ya saka muqulli ya bude gidan ya shiga ba tareda ya ce mata komai ba haka ta bishi zugui zugui a baya, ganin yayi kamar ma besan da wanzuwarta ba yasa ta kwasa da saurin gaske tayi ciki tana qara godewa Allah da ya saka babu hasken Nepa kuma be haska jikinta da fitilar hannunsa ba balle yaga irin shigar da tayi.

Dan dama daman da ta sake ji dayaga dawowarta ba ita kadai ba dan seda Fannah ta fito ta bude mata murfin motar da ya samu matsala, yanzu da ace saurayi ne ya ajiyeta a daren nan tana ga kawai tsirenta za suyi su huta.

Dakinsu ta fada tana sauke numfashi, bata tsaya ba seda ta tube kayan ta jefa can cikin wardrobe kafin tayi maza ta fada bandaki ta watsa ruwa tareda Alwala. Tayi mamakin ganin harta idar da sallah babu wanda ya biyo sahunta, amma tasan tarko ne. Tana jin yunwa haka nan ta haye gado ta kwanta, tunda dai ta shigo gidan zance ya qare duk wacce zaayi ayi da safe ai.

Washe gari ta kama Asabar, yanda taga babu wanda ko a fuska ya nuna mata tayi laifi jiyan ya fara daga mata hankali, tana so ta tafi gidan su Halima Daurin aure tana tsoron abinda tambayar hakan ze janyo mata.

Wuraren 11 tana zaune a dakinsu, tsoro take ta fita tsakar gidan su hadu da wani daga cikin Mama ko Abban ga Yunwar data kwana da ita ta hadu da ta safiya tana ta sakudarta. Nuratu Yayarta da take bima ta shiga dakin da farantin qosai da kofin da ta zubo kunun gyada ta nemi gefen gadonta ta zauna tana aikawa da Umaiman harara dan daman tun Asuba data farka ta ganta bata ce mata komai ba sedai idan sun hada ido ta maka mata harara kawai.

Ganin qosan da kunu ya qara wutar rura yunwar da take ji amma yanayin fuskar Yaya Nuratun yasa ta kasa ce mata zata ci, gashi babu motsin kowa a tsakar gidan qannensu duk sun tafi Tahfiz bare ta yafito wani ta saka ya debo mata. Ganinfa tana neman illata kanta dan damanita bame jumurin yubwa bace yasa ta yunqura da niyyar ta roqi yayar tata sega sallamar Qaninta.

Daga bakin qofar yace
" Yaya Umaimah kije inji Abba yana kiranki" ya juya abinsa. Seda cikinta ya bada wani qulululu, ashe ba kyaketa akayi ba jira suke gari ya gama wayewa tas ayi mata taron dangi dan taji shigowar Baba Abdullahi da Yaya Aminu babban Yayansu gidan.

"Yaya Nuratu dan Allah ki bani ko kunun ne nasha wallahi banajin zan iya tafiya ma yunwa nake ji" ta fada a marairaice dan gara ta karya bille ta roqeta, bata sani ba ko baa girka da ita ba kar taje garin diba ta qarayin wani laifin.

Banza Nuratun ta mata seda ta sake roqonta kafin ta turo mata kwanon qosan da kunun da ko rabi bata ci ba dan tana yi tana duba wani texbook nasu na yan medicine tace mata
"Gashinan Mayya se kici ai"

"Idan ni mayyace ke ma ai mayyar ce" Umaimah ta fada cikin qunquni ta ja kayan ta fara ci hannu baka hannu kwarya cikin dan lokaci ta cinye tas ta zura dogon Hijab har qasa ta fita tana nanata La'ilaha illah anta subhanaka innikuntu minazzalimin a zuciyarta harta isa qofar Sitting room din Abbansu.

Ta shiga da sallama kai a qasa kamar ta Allah ta rabe a bakin qofa tana gaishe su ba tare data bari sun hada ido da kowa a cikin su ba.? Yaya Aminu ne ya daka mata tsawa yace
"Zaki matso ciki ne kose na zo nan na tattaka ki mara jin magana kawai"

"Barta Aminullahi fada da hargagi baya gyara, nasihar dai ita zaa ci gaba har sanda Allah ze sa ta dena abinda takeyi" Taji Muryar Baba Liman Aminin Abbansu ta katse hargagin da Yaya Aminu ya fara yi mata. Wata nutsuwa taji ta dan saukar mata dan ko ba komai akwai me kareta dan baze bari su mata komai ba amma da ta gama saddaqarwa yau kashinta ya bushe dan daga Yaya Aminun har Baba Abdullahi babu me sauqi, Abba kuwa zuba ido zeyi su caskalata babu abinda ya masa zafi.

"Ina wayarki take?" Baba Abdullahi ya fada cikin zafin nan nasa, seta daga kai ta kalleshi aranta tana cewa
"Toh takunkumi zaa sakamun kenan a hanani fita a karbe mun waya tab aikuwa da sake"

"Ba magana ake miki ba?" Aminu ya sake zaburowa, qasa qasa ta harare shi kafin tace

"Tana cikin gida"
"Kije ki dakkota da duk wani abu da kika san Qasim ya mallaka miki ki kawo nan" Baba Liman ya fada.

"Duk abinda tasan nasa ne ko tsinke ne ta hado" wani mutum da sam bata lura da shi a palour bama ya fada se faman girgiza qafa yake kamar ana yaqi, Se ta dago tana kallon shi dason jin qarin bayani, amma yanayin da tagani akan fuskar Abbanta da irin hararar daya watsa mata tasa ta miqe babu shiri.

Sabuwar Iphone din da Qasim ya siya mata bayan kawo kudin auran su da kwana biyu ta dakko tana jujjuyawa, to me ya faru me zasuyi da wayar? Kuma ai ce mata aka yi ta dakko duk abinda ya mallaka mata kenan ba wai kwace wayar zaayi ba wani abun ne daban.

Tunanin me dame ma Qasim din ya taba siya mata ta shiga yi, shi ba gwanin siyan kaya bane gara dai kayan maqulashe duk zuwa da abinda ze kawo mata. Wardrobe ta bude ta zaro lesina guda biyu daya dinkakke ne dayan baa dinka ba se Atamfa guda daya itama dinkakkiya kayan toshin wannan qaramar sallar da yayi matane, ta saka Atamfar Leshin kuma daman yau tayi niyyar saka shi.

Ragowar tarkacen Jaka da takalmi da mayafai ta debo ta hada cikin babbar Leda, ta kalli turarukan dake kan Mudubin su wanda suma a cikin kayan take ta tabe baki a fili tace

"Bazan hada dasu ba tunda bansan me zaayi ba" Nuratu dai se kallonta take ta zare cajar wayar daga soket ta hada ta sake fita.

A tsakiyar ta dire musu ledar, mutumin dazu ya jata gabansa ya hau duddubawa yana cewa "su kenan dai ko? Ko da yake idan ma da saura zan tambaye shi muji" ya miqe yana sabar ledar Yaya Aminu yayi saurin dakatar dashi da cewa

"Dan jira dan Allah" ya saka hannu ta dauki wayar dake saman ledar ya miqa mata yana cewa
"Budeta ki goge komai na ciki"

Umaimah da tayi mutuwar zaune saboda mamaki ta karbi wayar tana juyawa, tsawa Abba ya daka mata yace

"Zakiyi abinda akace ne ko kin tsaya kina kallon mutane".
Jiki na rawa ta cire password din wayar ta shiga setting nan take tayi resetting nata komai ya goge. Bayan wayar ta bude ta zaro allura ta zare Sim dinta da rigar wayar dan zuwa yanzu ta gama fahintar abinda yake faruwa tana gamawa ta miqa musu wayar.

"Ita rigar wayar fa" Mutumin ya fada da ganinsa irin mara mutunchin nan ne daman, dake gidan tsiwar ya tarar kai tsaye tace masa
"Ai ba shi ya siya mun ba"
Shidai ya kinkimi leda yayi waje suka rakashi da kallon takaici.

"Gara da Allah yasa akayi haka ashe dan qananan mutane ne bamu sani ba gara da Allah ya kiyaye mu hada zuri'a dasu" Baba Abdullahi ya fada.

"Karo na Uku kenan Umaimah karo na Uku, na rantse da girman Allah ku zama sheda,saura wata biyu ta kammala karatun ta, idan har aka kai wannan lokacin bata fitar da tsayayyen miji ba a masallaci zanyi shela duk kuma wanda ya nuna yana son ta zan bashi ita sadaka. Badai juninki rashin mutunchi da rashin jin magana ba toh kici gaba, nidai bazan bari baqin cikin ki ke kadai ya dameni ba tunda haka kika zaba wa rayuwarki shikenan" Abba ya fada cikin kaushin murya

"Aa Alhaji kausasa kalami ba naka bane, Addu'a dai da nasihar ita za'a ci gaba dayi mata amma irin wadannan kalaman su suke sake ta'azzara al'amuran a maimakon a samu sassauci se kaga abu na qara lalace wa. Ke kuma Umaimah ki nutsu, ki sani fa kullum girma kike qarawa ba wai baya kike komawa ba. Me yasa zaace kullum aka tashi kwatancen rashin kirki kece a gaba yanzu jin dadin kine ace an fasa auranki har sau uku cikin abinda be wuci shekara daya da rabi ba?

Toh kar kiga kina samun maneman duniya ta ringa miki kida kina taka rawa. Duk namijin kirkin da ze zo neman auranki aka gaya masa an taba fasawa da wasu har sau uku se ya nemi jin ba'asi kuma bakisan abinda zaa gaya masa ba, ki yiwa Allah ki kama kanki ki san me kikeyi ki qyale zukatan iyayenki su huta" Baba Liman ya saka baki.

Nasiha yaci gaba dayiwa Umaimah dake faman rusa kuka. Bata taba jin baqin cikin fasa auranta da akeyi ba irin na Alqasim dan da gaske take son sa kuma yayi daidai da irin mijin da take mafarkin samu a rayuwarta amma daga faruwar dan wancan abin shine zece ya fasa auranta har ya turo a karbar masa komai nasa da yake gidan su bayan koma menene shine sila ai, akan me ze kula wata mace suna tare bayan yasan Irin HALIN KISHIN ta, sam ba jin Baba Liman din ma take ba harya gama nasihar sa yace ta tashi taje wanda ba haka Yaya Aminu yaso ba, yaso ya mammaketa dan tun jiya Mama ta gaya masa fitar da tayi da sanda ta dawo yaso amma ze bita cikin gidan seya ci ubanta wallahi.

Kuka wiwi ta fita tanayi, sam ta manta da tasu da Mama kai tsaye dakin ta ta wuce ta zube tana ci gana da rusa kuka kai kace mutuwa aka mata. Mama dake sallar walaha ta sallame tace

"Idanna idar na tarar dake a dakinnan Umaimah sena lahira ya fiki jin dadi ki tashi ki fita karki qara mun baqin ciki akan wanda nake ciki"

"Ai wallahi ko kashe ni zakiyi babu inda zanje, gurin wa zanje nayi kuka idan ba dakin uwata ba" Umaimah da har sannan bakinta be mutu ba ta fada tana ci gaba da rusa kukan ,kwafa Maman tayi ta tayar da sallarta, harta idar kuwa tana zaune bata tashin ba tayi kuka kana ganinta kasan daga qasan ranta take kukan nan.

"Mama ya zanyi, kullum ina roqon Allah daya ragemun zafin kishi, wallahi Mama ji nakeyi kamar zuciyata ta kama da wuta idan na ganshi da wata macen, me yasa shi ya kasa kiyaye wa ko ze kula mata me yasa zeyi akan ido na?" Ta fada cikin tsananin kuka.

"Dan ubanki keba musulma bace? Duk girman abinda kike ji idan kika nemi taimakon Allah zakiji sauqin sa, amma seki biyewa zuciya ki zama kamar mahaukaciya kiyi abinda ranko ya raya miki se saga baya kizo kina Nadama toh kici gaba Nadama kuwa yanzu kika daura dambar yinta. Ina jiye miki tsoron gaba Umaimah idan baki canza Hali ba wata rana sekin tsinewa wannan mummunan HALIN KISHIN naki" Mama ta fada tana ficewa daga dakin, ga tausayin Umaimah ga takaicinta.

Ranar haka ta wuni zur tana aikin kuka, idan ta tuna wai fa Qasim ya fasa auranta se tayji duniyar ta mata zafi ita yanzu ina zata kuma samun kamar sa Dan gayu daya iya daukar wanka ga kalamai masu sanyaya zuciya, duk idanta hau zafin ta yasan yanda yake bi ya lallabata, gashi ya mata alqawarin idan ya aureta har mutuwa ita kadai ce matarsa har rabtsuwa ya mata da Alqur'ani amma shine daga dan wannan abin zece ya fasa auranta.

Tunawa tayi da Ibrahim saurayinta na f??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????arko da aka yi musu baiko tun tana Aji biyar na secondary, shima fa akan kawai ta mari wata yar iskar Cousin dinsa da take sonsa, suka tareta a islamiyya ita da qawayenta kowa ta mata mari biyu tana dawowa gida da daddare se ji tayi wai Babansa yace baze aureta ba.

Bayan shi se Lagin, koda yake shi daman tafiyar su bazata zo daya ba dan namamajone, daya rabu da tarin tarkacen yan matansa ya gwammace ya fasa auranta bayan har an saka musu rana wata shida yace ya fasa yanzu ga Qasim, a qarshen watannan fa suke zancen saka rana tunda watanni biyu suka rage mata ta kammala HND dinta.

Sun gama tsara komai daidai da gidan da zata zauna ya kaita ta gani wanda aka tsara shi iya tsaruwa kadan ya rage a kammala, kullum cikin tura masa irin kayan da take so ya saka mata a lefe take shi kuwa yana lafta kudi yana siya yanzu shikenan wata banza zeje ya kaiwa?

Abinda ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login