Showing 165001 words to 168000 words out of 429394 words

Chapter 56 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1022

santa abinda yaja hankalinsa kenan har ya nemi jin ba'asin meya faru suka nuna masa.

Hankalinsa yayi masifar tashi babu shiri ya baro kasuwar ya taho gida yana zuwa Matarsa take sake jadda masa ita ma ta gani a wayar ta an tura a group Khausar bata kwana gida ba tana gidan Yayarta shiyasa bata ji gargar din maganar ba dan a cikin tashin hankali ya sameta na tsoron ko itama Khausar din irin rayuwar da takeyi kenan tunda a koda yaushe suna tare shine babu shiri ya tafi gidan su Hadizan yaje ya tarar da Isma'il ya rigada ya kwazawa Maman labarin tana ta tashin hankali abin dai babu dadi.

Anty Bilkisu ce ta kama Hadiza da sam ta gagara kuka se zare ido takeyi kwakwalwarta tamkar an wanke ta babu tunanin komai a ciki. Ta rasa gane me yake faruwa, gaba daya duk wani motsi ko magana sake jefata cikin rudani yakeyi. A bakin qofa suka ci karo da Isma'il daya bi sahun Hadiza gurin aiki aka tabbatar masa tazo ta tafi daga can ya wuce gidansa yana zuwa yaran sukace Mamansu ta fita da Anty Hadiza dalilin kiran da yayi mata kenan akan ta dawo daga can kuma ya wuce gurin wani abokinsa ya kai masa hotunan dan ya duba masa sahihancinsu saboda zuciyarsa ta kasa yarda cewar yar uwarsa Hadiza zata aikata hakan sedai ya tabbatar masa da hotunan gaskiya ne ba hadasu akayi ba wani irin rugugin tashin hankali yake ji a cikin kansa dakyar ya iya tuqo mota ya dawo gida.

Yana sako kai Soron suna saka nasu zasu fita, daga Hadiza har Bilkisu babu wadda zatace taga sanda ya iso gabansu illah mahangurbar daya kaiwa Hadizan a fuska jini yayi tsartuwa daga hancinta da bakinta da suka fashe lokaci guda, kafin tagama sanin abinda yake faruwa ya rufeta da wani irin mugun duka kamar yanda kasan ya kama Barawo, da gudu jama'ar cikin gidan suka fito amma an gagara samun wanda ze iya kwatarta a hannunsa dan duka yake kai mata ta ko ina babu ji babu gani qafa da hannu tuni qofar gidan ta cika maqil da jama'a yan kallo harda masu daukar video dan daman hotunan sun gama karada unguwa anata yamadidi masu gaskgatawa nayi harda kafa hujja ta bata kula samari wasu kuma suna ganin ba gaskiya bane ba.

Duk irin roqo da magiya dasu Alhaji Sunusi suka ringa yi masa Isma'il be dene dukan Hadiza ba seda yaga bata motsi idanunta sun qaqqafe sannan ya tsallaketa ya shiga cikin gidan Hajiya Zuwaira da Malama Lawisa suka dagota a tare suka fasa kuka suna cewa
"Ya kasheta, Isma'il kayi kisan kai"
Daga cikin gidan Mama dako gezau batayi ba kan dukan da yakeyi mata tace
"Ai gara daya kasheta dan daman hukuncinta kenan kuma ko shi be kasheta ba ni da hannuna zan miqa ta ga Kotun musulunci a yanke mata hukunci, mun huta an rage mugun iri a doron qasa" ta qarasa tana fashewa da wani irin kuka da duk wanda yaji se ta bashi tausayi. Gabanta ya durqusa shima yana kukan tamkar mace yace
"Naje Mama suntabbatar mun hotunan gaskiya ne ba hadasu akayi ba, da gaske ne Mama Hadiza Mata take nema yan uwanta shi yasa taqi tsayar da Miji tayi aure.

Kuka suke babu me rarrashin wani, acan soro kuwa haka suka kamata aka sakata a motar Alhaji Sunusi wanda dakyar aka kori mutane da suka taru suna kallo. Asibiti suka kaita, seda likitoci sukayi dagaske kafin numfashinta ya daidaita kafin sukayi mata allurar bacci saboda jininta daya hau ya samu daidaito. Sanadiyyar dukan ta samu tsagewar qashi a hannun dama da qa targade babu adadi banda fuskarta data kumbura suntum saboda duka taimakon da Allah yayi mata be sameta a ido ba. Malama Lawisa ce ta zauna da ita Hajiya zuwaira da Anty Bilkisu suka koma gida tana taraddadin hukuncin da zata fuskanta daga mijin nata itama shiyasa bata koma gidan Maman ba kaitsaye ta wuce gidanta a ranta tana tausayawa Hadiza har kuma sannan bataji daidai da kwayar zarra ta yarda da abinda ake zarginta dashi ba. Ita shaida ce akan Hadiza a ko ina kuma zata bugi qirji ta qarya ta cewar Hadizan bata aikata abinda ake tuhumarta ba.


Hadiza
Seda ta kwana biyu kafin ta farfado daga baccin dolen da likito ci suka ringa sakata, har sannan Malama Lawisa ce tareda ita tayi mata sannu sannanta taimaka mata tayi wanka da ruwa me zafi sosai ta gasa jikinta. Seda ta rama sallolin da ake binta a kowacce sujjadarta seta yiwa Allah kirari ta roqeshi daya kawo mata dauki cikin halin data tsinci kanta wanda har sannan bata tantance shi ba. Shayi ta hada mata tasha ta zuba mata abincin da Anty Bilkisu take kai musu a boye dan daga Mama har Yaya Isma'il babu wanda yabi sahunsu balle susan halin datake ciki. Bata cibatace ta qoshi, ta jingina kanta jikin pillow data saka mata ta rufe idanunta da suka qanqance saboda kumburinda fuskarta tayi tayi shiru bazatace ga abinda take tunani ba.

Gajiya Malama Lawisa tayi da shirun Hadizan ta numfasa tace
"Hadiza ki zalimci istigfari da hailala kinji, shiru ko tunani bazasu amfana miki komai ba kiyi ta neman taimakon Ubangiji Allahya bayyanar da gaskiyar wannan Al'amari".

Bude ido tayi dakyar ta kalli Malama Lawisan kafin cikin muryarta da bata fita tace
" Umma ki fitar dani daga duhun da nake ciki, bansan meya faru ba. Mun rabu da Mama lafiya yau dan kwanakin da suka wuce mun samu sabani har tayi fushi dani amma yau mun tashi lafiya dan ita tace mun na fita aiki ma.
Umma tunda na fita mutanr suke kallona suna fadar maganganu dana kasa gane kansu sannan an bani takaddar sallama daga aiki akan dalilin da bansani ba nima. Anty Bilki ta kirani tace nazo muka fita tareda ita daga nan Yaya yace muzo gida bansan komai daya faru ba se yanzu na ganni a Gadon Asibiti dan Allah Umma ki fahimtar dani ko gaya mun me na aikata da har Mama takeyin irin kalaman nan akaina tace ta barwa Duniya ni, menayi da yayi zafi harda na zama abar kallo da zunde a gurin mutane" ta qarasa fada muryarta na rawa alamar kuka.

Shiru Malama Lawisa tayi kamar ba zata ce komai ba kafin kuma ta miqe ta dakko wayarta dake jikin chaji ta dawo kusada Hadizan, hotunan ta bude mata tareda rubutun dayake tareda su ta miqa mata wayar Hadiza ta karba tana kallonsu daddaya har zuwa kan rubutun ta karanta idonta ya tsaya kyam akan rubutun tana sake maimaitawa a zuciyarta. Wayar ta miqa mata ta maida idonta ta kulle bayan data zame ta kwanta a zuciyarta tana maimaita Hasbunallahu wani'imal wakeel, Allahumma ajirnifimusibati wa'aklifni khairan minha" yinsu takeyi babu iyaka har seda taji wani hayaki daya lullube mata kwakwalwa ya washe,jirin daya fara dibarta daga kwance ya tsagaita mata kafinta bude idanunta da suka kada sukayi jajir lokaci daya ta kalli Malama Lawisa da itama ita take kallo tace

"Umma, yanzu Mama ta yarda da cewar ni yar Lesbian ce"
"Abin akwai rudarwa Hadiza, da ace fada mata akayi qila ta qaryata amma wadannan hotunan sune suka bada tabbacin abinda aka fada" Malama Lawisa ta fada Hadiza tayi saurin tareta da cewa
"Kema kin yarda kenan? Idan hakane me yasa zaki zauna dani, me yasa baku bari ya kasheni ba kowa ya huta da masifar da na jawo muku?" Ta fada tana kallo taze Malama ta girgiza kai tace
"Ni bazance naAmince ba saboda ina kyautata miki zaton bazaki aikata hakan ba amma a yanzu ba kowa ne ze iya tsayawa yayi dogon tunani ba, komai ana buqatar shaida ne kuma gata an samu kinga kuwa zeyi wahala kafin ka fahimtar da mutane gaskiya ko akasin haka akan wannan al'amari. Koma menene yanzu ba lokacin mayar da magana bane ki yi haquri ko samu lafiyarki ta daidaita idan yaso daga baya se a san abinda za'ayi. Koda ace dagske kina aikatawa idan kika tuba tuba na gaske kika nemi yafiyar ubangiji kika gyara rayuwarki se kiga komai ya wuce tamkar be taba faruwa ba".

Wani irin kuka ne ya kwace mata da seda zuciyar Malama Lawisa ta karye hawaye suka fara zubo mata itama.
"Wallahi Allah shine shaidata Umma ban aikata ba ba halina bane, bansan mena tsarewa mutane a duniya da a kullum suke bibiyata da sharri ba. Yanzu wane ne ze yarda dani? Waye ze wankeni daga wannan mugun zargin da aka jefani a ciki" Hadiza ta fada cikin tsananin kuka tamkar ranta ze fita, babu zato se ji sukayi daga bakin qofa ance

"Ni na yarda dake Hadiza kuma Ubangiji ze wanke ya kunyata maqaryata da masu munafunci".
Da sauri ta daga kai ta kalli inda take jiyo maganar, Khalil ne a tsaye, ba zata iya fassara yanayin dake kan fuskarsa ba ya qaraso cikin dakin wata Mace me tsananin kama dashi tana biye dashi a baya.

*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ?AR'UWA, WATA-?ILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
?ar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassa?e da garin magunguna na gargajiya, waWanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taSa haihuwa ba?* Ko kuma sun taSa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa Sari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? ?ar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata Waya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haWa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*?ar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haWa miki magunguna kala biyar, waWanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daWewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haWi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiWa?* ?ar'uwa ko ki faWa ko kar ki faWa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan Waya wanda zai dinga shan ?aramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ?ara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huWu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haWin sabaya=?
?* HaWin sabayarmu duniya ne ?ar'uwa. Baza muyi miki ?aryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga she?i, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haWin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk Wauri Waya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuWin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuSeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo=?
?=?
?=?
?*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 43

KHALIL
Cikin injin markada sumunti wayarsa ta subuce ta fada dalilin da ya saka ya kwana biyu kenan be kira gida ba haka idan an kirashi ba'a samunsa. A kwana na uku ya samu wata wayar ya siyi sabon layi ya dora dan baze iya swapping layukansa ba dole se ya dawi Nigeria se kawai ya siyi wani ya saka akan wayar yayi backup na numbobinsa ta Gmail.

Hajiya ya fara kira ita take gaya masa Jalila nata neman sa bata same shi ba ya kirata yaji dan zuwanta gidan kusan nawa tana tambayar Hajiyan koya kirata kamar dai akwai wata matsala yace toh ze kirata. Bayan sun gama magana da Hajiya ya kira Umaimah. Lafiya lau sukayi magana ko a murya be tsinci wani abu daze nuna akwai wata matsala ko wani abu ba, suka sha hirarsu yace tayi saving number da ita zeyi amfani kafin ya dawo ya maida wancan layin. Yaso ya gaya mata a kowanne lokaci daga gobe zata iya ganinsa dan ya gaji da zaman yayi kewarta sosai ammakuma so yakeyi ya shammaceta sedai kaw???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ai ya kira waya yace azo adauke shi daga Aiport shi yasa yayi shiru suka rabu suna nanatawa juna yanda kowanne yayi missing dan uwansa.

Ya manta shaf da kiran Jalila da Hajiya tace yayi yaci gaba da sabgoginsa se bayan Magriba yana masallaci ta kirashi, bata bari ko gaisuwa sunyi ba tace
"Khalil meyake faruwa, menene gaskiyar abinda matarka take yayatawa a gari?"

"Kinga ki nutsu kiyimun magana a hankali yanda zan fahimta, Bangane me kike magana akai ba, meya faru a ina kuma me take yadawa?" Shima ya jefa mata tambaya dan be fahimci inda kalamanta suka saka gaba ba. Se Jalilah taja numfashi kafin tace

"Kana ji ko, shekaran jiya matarka ta aika mana da wasu hotuna dukkanmu harda Hajiya, amma na saka Khalifa ya goge na wayar Hajiyan bata gani ba. Na kuma ce kar wanda ya gaya mata ballantana hankalinta ya tashi, yanzu ni abinda kawai nake so naji dagaske ne abinda ta fada ko kuwa qarya ne?"

"Jalilah" Khalil ya kira sunanta cikin qosawa da maganar da sam be gane inda ta dosa ba kafin yace
"Dan Allah kiyi magana irin wadda zan gane, ban san wane hoto kike magana akai ba ballantana na fada miki gaskiya ko qarya akansa".
"Toh, kana WhatsApp da wannan number ne? Gara na tura maka ka gani da idonka zefi sannan muyi magana, ak na zata kaima ta aika maka ne shiyasa kaji ina maka magana kaitsaye" Jalilan ta sake fada ko kafin ya amsa mata da yana WhatsApp din ko bayayi ta kashe wayar se shima ya shiga WhatsApp din yana jiran saqonta.

Wayarce ta subuce daga hannunsa tsabar kidima ya bita ya dauka ilahirin jikinsa babu inda baya rawa. Khausar ce ta fado masa arai, wato abinda ta fada kan wanda zatayi musu a gaba se yafi na baya kenan innalillahi amma Khausar ta cika la'ananniya da bata tsoron Allah, me Hadiza ta tsare mata a duniya data zabi ta cutar da ita cuta mafi muni tayi mata qazafin Lesbian, Lesbian fa? Tasan girman Zunubinsa Neman Jinsi kuwa laifi ne babba wanda akansa aka halakar da Al'ummar Annabi Lud. Dabi'ace da ko cikin dabbobi basa aikata ta se a cikin mutane gafalallu da suka rigada suka juyar da zukatansu daga neman Rahamar Ubangiji.

Number Jalilah ya shiga kira a ransa yana tunanin toh a ina har Khausar ta samu numbobin yan gidansu dukka dan idan yaji daidai har Hajiya Jalilan tace an turawa, tana dagawa yace
"Jalilah yaushe ta turo muku da wannan saqon, bama wannan ba a ina ta samu numbobinku kinsan yarinyar data aiko ne?"

"Bangane a ina ta samu numbobinmu ba kuma Umaiman zaka ce na sani kana cikin hankalinka kuwa Khalil?" Jalilah ta fada cikin mamakin kalamansa da basuyi kama da yasan me yake fada ba. Se ya tsaya cak yana maimaita Sunan Umaimah a zuciyarsa, Umaimah fa yaji tace Umaimah dai wadda ya sani ko kuma wata shaidaniyar aka samu me irin sunanta? Sabida ya tabbatar yace mata

"Wace Umaimah haka ta gaya miki sunanta?"
"Karka rainamun wayo Khalil, Umaimah nawa muke da ita banda matarka? Daman ta fada tace idan ka sani qaryatawa zakayi ashe kuwa dagaske ne gashi kana neman ka rainamun wayo ka nuna itama baka gane wa nake nufi ba. To wallahi ba'a zuri'ar mu ba, idan aure kake so kaje ka nemo yar mutunchi amma ba zaka kwaso mana kara da kiyashi ka kawo mana ba" Jalila ta fada cikin qunar ran jin ze raina mata wayau.

Cikin tsawa Khalil ya mayar mata da cewa
"Ya isheki malama, yanzu saboda kema bakida hankali har Umaimah ce zata gaya miki abu ki hau ki zauna saboda baki san halinta ba ko? Ita Umaiman a ina ta jiyo wannan maganar kuma yanzu bayan ku se waye ya sani?"

"Tabbas abinda take fada ya tabbata tunda gashi har mara hankali kake kirana saboda asirin lalatacciyar da kake neman kwaso mana ya tonu, daman ginin daka digirgiri hankali ka tada ita zaka kawo kusada mahaifiyar mu ka goga mata bala'i ana neman Mata a cikin gidan da take ko? to ka kirani da komai ma kai kajiyo amma wallahi baka isa ba. Ko asiri tayi maka se mun karyashi kuma da ni nace kar a gayawa Hajiya amma yanzu da kaina zan tafi na gaya mata yau base anjima ba tunda naga akamar baka san me kake yi ba" Jalilah ta hayayyaqo masa se yaja tsaki,hannu ya sa ya dafe kansa daya dauki ciwo lokaci daya kafin yace

"Qarya takeyi wallahi sharri sukayi mata kuma itama Umaiman bayin kanta bane na sani sakata akayi amma duk ma wanda yake da hannu a cikin wannan al'amarin wallahi bazan barshi ba, sena bi mata haqqin bata mata suna da sukayi kuma karki kuskura ki gayawa Hajiya komai kinji na gaya miki idan kuma kika fada kika tayar mata da hankali shikenan"
"Ba shakka Khalil to Allah ya taroka dan naga alamar ka zauce" Jalilah ta fada kafin yace wani abu ta kashe wayarta a ranta tana gasgata zancen Umaimah datace yasan komai akan maganar. Badan tana tsoron ta zama silar motsawar Hawan jinin Hajiya ba da a daren nan zata je ta gaya mata amma dukda haka se ta sani dan ita kadaice zata iya hanashi auran nan ya hanu.

Khalil kuwa tana kashe wayar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login